Showing 111001 words to 114000 words out of 122205 words
je Nigeria ya taho da Nana, dan ya san tun da Hammad ya dawo, yanzu duk inda za shi su na tare.
Da ƙwarin gwiwa yanzu Nana take girki, kasancewar ta sa wanda take yi wa girkin.
Bayan da Nana ta kammala girkin rana tana shirin, kai wa sashen Imam, Asal ta same ta ta ce "Ba sai kin kai wa Imam Abinci ba, baya nan sai dare zai dawo, ki shirya masa abincin dare kawai"
Nana ta amsa mata da to.
Tun da Imam ya dawo, yake kaiwa yana komowa yana jiran ya ga ta ina za a kawo Abinci, saboda yunwar da yake ji. Ga shi dududu ƙarfe goma ya dawo, amma Asal har ta kwanta bacci. Ya yi hamma bai san adadinta ba, saboda yunwar da yake ji.
Sallamar Nana ta saka ya kalli hanyar shigowa, wannan karon a kwando ta zubo kayan Abincin.
Sai dai yau saɓanin hijjabi, doguwar riga ce a jikinta milk, da mayafin rigar. Tun da ta yi sallama ya amsa a ƙasan maƙoshinsa ya sunkuyar da kansa ƙasa bai kuma magana ba.
Ta ƙarasa ta ajiye kwamdon, ta sauke kwanukan, har za ta yi masa zancen saƙon nan da aka bayar, sai ta fasa dan kar ta wargaza shirinta. Da wani na iya ganin halin da zuciyar wani ke ciki, da Imam ya daɗe da jin kunya, saboda bugun zuciyarsa, ga wani irin azalzalarsa da take yi, ya sake kallon Nana, dan ba ya tunanin ya taɓa ganin wanda doguwar riga ta yi kyau kamar baƙar kukunsa 'yar Nigeria.
Ta zuzzuba masa abincin, ga kayan marmari ga kuma shayi na musamman.
Da ta zuzzuba masa.
Ta numfasa ta ce "Ɗazu na yi girkin rana, aka sanar mini da baka nan, na ce duk lokacin da ba zaka kasance a gida ba, ina son a yi mini izini na dafa maka ka fita da shi, ba zan so shugabana ya kasance da yunwa ba, tun da alhakina ne girka maka Abinci" Ta yi maganar cikin girmamawa tana sunkuyar da kai.
Jin ya yi shiru ya sanya ta ɗaga kanta, ta ga tuni ya ɗauki shayi ya kai bakinsa yana sha. Kawai ta ɗan juya ƙwayar idonta, tare da yin murmushi. Sai da ya kusa ƙwarewa, saboda tabbas ya san irin wannan kallon, amma a ina? Yana matuƙar son ya yi mata magana, amma ba ya iya wa. Nana ba ta ba shi damar ɗaukar wani mataki ba, ta tashi ta nufi hanyar fita. Tun da ta tashi ya bi ta da ido har ta fice.
Abin duniya duk ya dame shi, Nana kuwa ta cika da murna, ganin saƙonninta na isa yadda take so, sai dai tana buƙatar ƙara samun kusanci da shi.
Cikin marairaicewa yake kallonta, fuskarsa ɗauke da damuwa ganin yadda take kuka tamkar ranta zai fita, ga shi ta yi duhu ta rame, ba kamar yadda ya santa ba a baya.
"Ma vie, ki yi mini afuwa, ba laifina ba ne, ina jin yadda ruhinki yake motsi a cikin jikina, dan Allah kar ki yi fushi da ni ki yi mini uzuri " Ya yi maganar yana ƙoƙarin rungume ta ya rarrashe ta. Ja da baya ta yi tana girgiza masa kai tana kuka ta ce "Ba ka so na Sayyid, ka yada alƙawari ka tafi ka bar ni, ka manta da ni, ka bar ni da dakon ruhinka, da ya hanani sukuni sai da na fito nemanka, ba ka yi mini adalci ba Sayyid"
"Ma vie, ban ya da alƙawari ba, gangar jikina ce a Nijar, amma ruhina yana Nigeria dan Allah ma vie"
Asal ta yi ƙuri da ido tana kallon yadda ya haɗa gumi a cikin bacci, sai numfarfashi yake yi da kyar yana faɗin "Ma vie, ke rayuwata ce, ban yi miki butulci ba"
AYSHERCOOL
1K NE VIA 0069685771
Aisha Adam stanbic bank
08081012143
76
Asal ta zuba masa ido tana kallon ikon Allah.
Shiru ta yi jikinta ya yi sanyi tana kallonsa, sai dai ta yi shiru ta ci gaba da kallonsa. A razane ya farka, sai dai ya juya ya ci gaba da baccinsa.
Da safe ya lura da Asal ba ta walwala, ta ƙi sakin jiki da shi ma gaba ɗaya.
Har ya share ta sai kuma ya tambaye ta ko lafiya?
"Lafiya kalau" ta amsa masa a taƙaice.
Ya fita ɗan tattaki, yana jin mafarkin da ya yi a jikinsa, amma ya kasa tuna mafarkin abin da ya yi. Cikin girmamawa ma'aikatan ke ta risunawa su na gaishe shi.
Babu yabo babu fallasa ya din ga amsa musu. Zuwa ƙarfe goma Nana ta kammala girki. Sai dai yau ba su haɗu ba kwata-kwata.
Har lumshe idanunsa yake yi bayan da ya sha kunun gyaɗar da ta yi, ga lafiyayyen ƙosai mai zafi.
Ya karya tsaf ya gama, Asal ta fito daga ɗaki ta cika ta batse. Kallo ɗaya ya yi mata ya maze, ganin ya basar da ita ya sanya ta ƙura masa ido ya kalle ta, yana mamakin dalilin da ya sanya ta ke yi masa wannan kallon.
"Imam ina fatan inda ka tafi, ba cin amanata ka yi ba"
Kallon rashin fahimta ya yi mata ya ce "Me ki ke nufi?"
"Ni kaina ban kai ga tantance abin da nake nufi ba, amma na fara ganin wasu abubuwa me da ban gane musu ba, abin ya tsaro ta ni ne"
Ya ce "Yi mini bayani"
"Ka na kiran wata da rayuwarka a cikin baccinka"
Ya yi mata ƙuri da ido, sannan ya ce "Kin tabattaa?"
"Ba ka yarda ba ƙarya nake yi maka kenan?"
"A'a ban ce haka ba, amma kin ce bacci nake yi, kin ga mai bacci kuma bai san abin da yake aikatawa ba. Wataƙila shirmen mafarki ne kawai, wataƙila ma ke na gani a cikin baccin nake kira da rayuwata"
Sai kuma ta yi murmushi ta ce "Kuma haka ne, wallahi har na ji zuciyata ta yi sanyi, ka yi haƙuri da abin da na yi "
Ya yi murmushi yana kashingiɗa ya ce "Ban haƙura ba tukuna"
Ta ce "Ai ba zan sake ba, ina kishinka ne sosai. Da ina da hali ko fita sai ka daina yi. Ina sane da duk masu ƙoƙarin yi maka kyautar 'ya'aynsu su na so ka aura. Imam kai nawa ne nikaɗai Imam Hammad, babu wata mace da za ta iya samun kafar da za ta shiga zuciyarka. Inda na gode wa Allah, ka yi daban Imam, ba ka da rawar kai, da kule-kulen nan, da ko a cikin barorin nan, da suke rawar ƙafa ka yi saɗaka da su, sai ka saurare su. Shi yasa nake ƙara ƙoƙarin na kare gidana ina fatan ba ka ga laifina ba"
Ya sanya hannunsa yana shafa gashin kanta, ya ƙanƙance idanunsa yana kallonta, daga bisani ya saki murmushi ya ce "Gimbiya Asal, sarauniyar mata masu kishi ta duk faɗin Agadez"
Ta zumɓura baki ta ce "Ta duk Duniya dai, ni in dai a kan ka ne. Da ina da yadda zan yi ma sai ka daina kallon kowace mace, sai maza kawai" Ta yi maganar har cikin zuciyarta.
Kawai ya kama dariya, dan shi gaba ɗaya dariya ma ta ba shi.
"Ya ka ke dariya kuma?"
Hammad ya ce "To ya ba zan yi dariya ba, ina ji ina gani an bani kyautar mata na mayar da hannun kyauta"
Fuskarta ɗauke da damuwa ta ce "Dama ka na so kenan?"
"To waye ba ya son mace? Ina so mana. Amma tawa kawai"
"So ka ke sai ka saka ni kuka" Ta yi maganar idanunta na cika da hawaye.
Lumshe idanunsa ya yi yana buɗewa, yana kallonta. "Ga abinci ki karya" Ta noƙe kafaɗa.
Nana ce ta yi sallama, Asal ta kalli inda ta shigo, ta tsuke fuska haka kurum yau ta ji haushin Nana ya ninku a zuciyarta.
Nana ta yi saurin sunkuyar da kanta, dan Asal a zaune take a kan cinyar Sayyid.
"Zan kwashe kwanuka" ta yi maganar muryarta har harɗewa take yi, saboda abin da ya taso mata.
"To ni dai yanzu ka kira ni da rayuwarka a zahiri, tun da ka ce ni ka ke kira a mafarki" Ta yi maganar kamar ba ta san Nana ta shigo ba.
Ras gaban Nana ya faɗi, ya lumshe idanunsa yana murmushi ya ƙi magana.
Kawai Nana ta fusata ta tattare kwanukan za ta yi waje.
"Malama ki ajiye ban karya ba, ki fita kya dawo ki kwashe" Ko waiwayowa Nana ba ta yi ba, wata irin zabura ta yi cikin matsanancin fushi, amma ya riƙe ta ya ce "Cherie na sha gaya miki, irin wannan halayen naki ga na ƙasa da ke, babu abin da za su janyo miki sai tsana da raini. Ita kuma rayuwa a na son ko kana guzurin maƙiyi ka yi na masoyi"
"Amma Amour kana kallon abin da ta yi mini, ko sau ɗaya sai na sanya a ladabtar da yarinyar nan ta san matsayina a gidan nan"
Ya ce "A'a, ke ce baki kyauta ba abin da ki ka yi. Ita ba ta tashi cikin jerin hadimanki ba, kawai dai kin ɗaukko ta ta yi miki aiki ne, dan haka sai kin din ga yi mata uzuri"
"Wane uzuri ne ba na yi mata, abin da ta yi mini wulaƙanci ne tana sane, ban da yadda take kula da abincinka na aminta da ita a kan hakan, da sai na hora ta sannan na kore ta ta bar gidan nan"
"Shikenan ki yi yadda ki ke so, tun da ba zan faɗa ki ji ba"
Ya yi maganar yana ture ta daga jikinsa.
"Imam fushi ka yi da ni a kan wannan mummunar yarinyar?"
"Ba a kanta na yi fushi ba, yadda ba kya jin magana ne ya ɓata mini rai, idan ki ka ci gaba da sanya wa ma'aikatanki ƙiyayyarki, babu abin da ba za a iya haɗa kai da su a yi miki ba. Idan na isa a bar maganar nan. Ba na son yadda ki ke tafiyar da ma'aikatanki wasu lokutan, ba na son yawan shiga maganar ne, amma raina ki za su yi"
Asal ta yi shiru ta tsuke fuska, ta sauka daga kan cinyarsa baki ɗaya.
****
Alhaji Fatuhu ma duk da yadda yake fama da kansa, sai da ya je gurin jana'izar Abba, kuma da shi aka yi zaman makoki. Ya ji mutuwar nan sosai da sosai, saboda Abba mutuminsa ne. Ko da yake jinya a sati ya kan je sau biyu ko uku duba shi. Ya kan zauna su yi hira sosai mussaman idan ya tarar jikin nasa da sauƙi.
Kusan kullum Hajiya Sa'a gani take mafarki take yi, idan aka wayi gari za ta ga Abba bai mutu ba, amma ta ga babu alamun hakan. Ba ta ƙara kiɗimewa ba sai ma da aka yi kwana bakwai da mutuwar, kowa ya watse ya bar gidan.
Ɗakin Abba ta tafi da daddare, ta buɗe ɗakin tana rintse idanunta tana jin tamkar za ta gan shi ya ɗago, da wannan murmushin nasa irin na fuskar mahifinsa.
Amma ta ga ɗakin nasa wayam, babu komai.
Wasu irin zafafan hawaye suka shiga sintiri a kan kumatunta, ba ta taɓa dana sanin shiga ƙungiyar asiri da duk wasu miyagun laifuka da take aikatawa ba, sai da ta rasa tilon ɗan da Allah ya ba ta a rayuwa. Wanda babu irin ƙoƙarin da ba ta yi, domin ganin ta kare shi da sadaukarwar ƙungiya. Ashe bonono ta yi rufe da ɓarawo bayan janyo Jamila cikin harkar ƙungiya, wanda ta yi hakan ne, domin janyo Jamila kusa da ita yadda za ta samu mallakar jinin Nana.
Ta zauna a gaban ƙatuwar katifarsa, ta din ga wani irin kuka mai sauti, da sai da ƙirjinta ya fara yi mata zafi.
*****
Asal ce zaune a kan carfet, saman kujerar da take kai kuma wani babban mutum ne, cikin shigar buzaye, kansa ɗauke da rawani.
"Ki na ji na da kyau ko?"
Ta jinjina kai cikin nutsuwa, ko ƙwaƙƙwaran motsi ba ta yi.
"Ina fatan haryanzu ba ki manta dalilin da ya sanya ki ka auri Hammad ba"
Ta amsa da "Eh ban manta ba"
"To barka, yanzu ya dawo, kuma babu abin da zai canza, za ki ci gaba da gudanar da aiki, kamar yadda yake a baya. Ba na buƙatar kuskure ko kuma wani uzuri. Duk wani motsinsa da duk abin da yakamata mu sani mai muhimmanci ki sanar da ni, idan kuma ki ka bari ni na gano ba ki sanar da ni ba, ranki zai yi mummunan ɓaci"
Jiki a sanyaye ta jinjina kai. "Dole a ci gaba da aiki tuƙuru, domin nesanta shi da kujerar Sultan, da mahaifinsa ke ta ƙoƙarin kusantar da shi da ita, mu na buƙatar kujerar nan ko ta halin ƙaƙa, dan haka ina nan ina saka miki ido da kuma sauraren ki"
Asal ta sake jinjina kai, jikinta babu ƙwari ta tashi ta fice.
Da ƙyar take ɗaga ƙafafuwanta, damuwa duk ta cika mata kai, ta ma rasa wane tunanin yakamata ta yi.
Da ta koma gida, ta tarar da hadimai na gyara ɓangaren Imam, ga ƙamshin turaren sa, da alama bai daɗe da fita ba.
Cikin tsawa ta kore su gaba ɗaya, ta ce su ajiye aikin su fita daga sashen, sannan su kira mata Nana. Jiki na rawa suka ajiye suka fita.
Nana tana tsaka da karatun Alkur'ani saƙon Asal ya iske ta, sai ta hau tunanin kiran me take yi mata. Duk da ta san abin da ta yi mata da safe.
Nana ta tashi cike da ƙwarin gwiwa, dan ji take yi daidai take da Asal, tun da duk abu dai ba za ta raba ta da ranta ba.
Nana ta shiga fuskarta a haɗe ita ma, ta shiga ɗakin ta tsaya, tana ta huci tana son ta balbale Nana da faɗa, sai kuma ta kasa ganin yadda Nanan ta tsuke fuska ita ma, ta yi mata wani irin kwarjini.
Amma duk da haka ta maze cikin dakiya da ƙarfin hali ta ce "Amm tambaya nake son yi miki, ban sani ba ko nice a ƙarƙashinki, da zan din ga yi miki magana kina ji na ki yi mini banza"
Nana ta ɗaga kai tana kallonta. "Ko ba ki gane me nake nufi ba ne? Abin da ki ka aikata da safe"
Nana ta ce "Na gane, gani na yi bai kamata na tsaya ina kallon ku a yanayin da ku ke ba, ko na din ga sauraren maganganunku ba. Hakan zai zama kamar munafunci ne, shi ya sanya na tafi, amma ki yi haƙuri"
Asal ta watsa mata wani banzan kallo cike da tsana ta yi ƙwafa sannan ta ce "Daga yanzu aikinki ba iya girkin Imam ba ne ba, har da gyaran sashen sa, ba na buƙatar kowa ya din ga raɓar inda yake."
"Amma ɗaukko ni ki ka yi na din ga girki kawai, ya za ki haɗa mini da aikin shara da goge-goge. Kuma masu yin aikin su uku ne, ni kuma nikaɗai ce, aikin bai yi mini yawa ba kuwa?"
"Kin san a kan kuɗi nawa na biya na ɗaukko ki? Ko a Nigeria ba na tunanin ko za a sayar da kaf danginku, za ku iya biyan kuɗin da na biya na karɓo ki ba. Dan haka ina da hurumin sanya ki duk abin da na ga dama"
"To Gimbiya Asal, babu damuwa zan yi abin da ki ke so. Duk da dangina ba za su iya biyan kuɗin da ki ka biya ba. Amma na san wataƙila mijina zai iya biya ya fanshe ni" Nana ta yi maganar tana murmushin da Asal ba ta gama gane kansa ba.
Nana ce ta ƙarasa aikin gyaran falon nan, ta yi goge-goge. Haƙurƙurtar da kanta ta din ga yi, da ta tuna mijinta take yi wa wannan aikin. Duk da ayyukan sun yi mata yawa. Ita dai fatanta Ubangiji Allah ya sanya Sayyid ya tuna ta domin ta san matsayinta.
Tana kammalawa ta koma kitchen, ta ɗora girkin rana. Ta kammala ta kai ajiye.
Ta ƙara goge ɗakin saboda ta san halin Asal sai ta tafi za ta huta, za ta sanya a kirawo ta, ta hau yi mata kinibibi da sanabe kala-kala.
Ta gama aikin goge-gogen kenan, ta gano wani photo album. Ta ɗauka ta nutsu tana dubawa, duk rubutun French ne a jiki.
Shafin Farko hoton Sultan ne, wanda ba dan yanayin shekaru da fuskarsa ta nuna ba, sai ka ce Imam Hammad ne, wanda tsananin kamannin har Muhsin da ta baro a gurin Nene.
Ta buɗe ɗaya shafin ta ga hoton wani, shi ma fari tas mai kama da su Sayyid sai dai shi ma babba ne. Kowanne a ƙasa da sunan sarautarsa.
Sai kuma ta shiga wani shafi mai ɗauke da hoton Sayyid a ƙasa an rubuta Imam Hammad Jalal Agadez. Wani murmushi ya suɓuce mata ta ce "Ka fi kowa kyau a cikin album ɗin nan Shugabana." Ta furta cikin murmushi. Hotunan wannan matasan da suka yi wa girki a gidan Sultan su ma kowanne da sunansa a ƙasa. Amma a farkon sunan kowanne da Imam.
Nana ta din ga mamakin to kowa ma Imam ne kenan?.
Muryar Asal ta jiyo sun nufo cikin falon, ta hanyar da take kyautata zaton a nan turakar Imam take, kuma tana tunanin ɗaya hanyar sashen Asal za ta mayar da kai, kai tsaye.
"Imam, wai ina zobenka ne?"
Ta yi maganar tana ɗago hannunsa, Nana kuma tana hango su daga inda take zaune.
"Ya karye yana gurin gyara"
"Gurin gyara kuma Imam? Ya za a yi dakakkiyar azurfa kamar wannan a ce ta karye? Ka san fa muhimmancin da zoben nan yake da shi a gurinka, ya za a yi ya karye?"
Daidai lokacin suka ƙaraso tsakiyar falon, ya ce "Zobe ya ɓata ban san inda yake ba, ina fatan kin gamsu yanzu. Kar ki sake yi mini maganarsa.
Yanzu zan fita, kar ki manta da saƙona"
Sai a lokacin suka ga Nana da ke zaune a cikin falon.
"Me ki ke yi a nan?" Asal ta tambaye ta.
"Babu komai, gyra ɗakin na yi"
"Kuma sai ki nemi guri ki zauna sai ka ce ɗakinki? Imam yana da baƙi anjima, za ki sake dafa wani abin, kuma za su sha shayi, ba na son wauta ko makamancin haka" Nana ta jinjina kai ta kalle shi ta ce "Barka da yammaci Sayyid, in sha Allah zan yi"
Asal ta ɗan yi shiru tana nazari jin ta kira shi Sayyid ba Imam ba.
A ɗan corridor ɗin ta tsaya tana zancen zuci, jin ana maganar zobe. Wane zoben kenan? Ko dai zoben da ya ɗauka ya ba ta ne? A'a ba ta tunanin haka wataƙila dai wani abin ne daban.
Gyaran murya da ya yi da