Showing 54001 words to 57000 words out of 122205 words

Chapter 19 - BUZU BOOK2 COMPLETE 2

18 Jan 2026

582

da shi.
Ya shiga makaranta, bisa tallafin karatu, a can ya samo mana wannan ƙungiyar.
Shi kuma lokacin Fatuhu ya fara zuwa kasuwa, ni kuma na riga na yi aure.
Zailani ya gaza jan Fatuhu ƙungiya, saboda mutum ne mai tsantseni da ra'ayin riƙau. Ni kuma har a lokacin mijin da nake aure, ba shi da komai ba na samun irin rayuwar da nake so. Sannu a hankali na ci gaba da hulɗa da Zailani ya kai ni ƙungiya, ya zamana ba na rasa kuɗin kashewa dai.
Fatuhu kuma ya ja Zailani kasuwa, suke kasuwanci tare, sai dai duk da tasirn ƙungiya, Zailani ya kasa tara abin da Fatuhu yake da shi.
Kin san waye mutum na farko da na fara bayarwa?"
Jamila ta girgiza kai alamar a'a.
"Babban yayanmu, da iyayensu su ka mayar da mu saniyar ware a gida"
Jamila ta jinjina kai a ɗan tsorace ta ce "Sai kuma ki ka ba da wa?"
Hajiya Sa'a ta yi murmushi ta ce "Zan ƙarasa miki nan gaba kaɗan, yanzu bari mu ƙarasa gida, akwai abin da nake son yi"
Jamila ta jinjina kai tana satar kallon Hajiya Sa'a.

Hajiya Sa'a ta ajiye Jamila, sannan ta ja motar ta tafi. Tana tafe ta kira layin Alhaji Zailani.

Sai da ta kusa katsewa, sannan ya ɗaga tare da yin sallama.

Ta ce "Ai na zata ba ka ɗaga ba ne"

Ya ce "A'a ina tuƙi ne? Lafiya?"

"Ƙalau, tambayarka abu zan yi"

Ya ce "Ok, ina jin ki"

"Ashe kwanaki da aure zaka yi?"

Ya ce "Yaushe?"

"Kwanakin baya mana, za ka auri wata yarinya Nana"

Kamar tana gabansa ya tsuke fuska ya ce "Waye ya gaya miki"

"A'a ba sai ka ji wanda ya gaya mini ba, zancen Duniya ba ya ɓuya ai, sai dai ka sani na san da abin da ka ke nema, ni ma shi nake farauta"
"Sa'a ban fahimci abin da ki ke nufi ba fa, ki yi mini bayani gwari-gwari "

"Za ka fahimta ne, ka je ka nutsu ka yi nazari" ta kashe wayar ta ajiye ta ci gaba da tuƙinta.

*****

Yana zaune a takure a gurin, ya yi shiru tamkar mai jiran tsammannin wani abun, aka buɗe ƙofar ɗakin da yake . Wasu tiƙa-tiƙan murɗaɗɗun maza suka shigo. Ba su yi wata-wata ba, suka yi sama da shi, suka fito da shi daga gurin da yake zaune.

Wani ɗakin aka sake kai shi, sai dai yana shiga ya yi turus, ganin mutumin da yake zaune a cikin ɗakin.
Ƙartin suka juya suka fice, suka bar shi daga shi sai mutum biyu a ɗakin.

"Bismillah ka zauna mana" cike da tsoro ya ƙarasa ya zauna yana rarraba ido, ya sunkuyar da kansa.

"Mahmudu, ɗagowa za ka yi ka kalle ni ai"
Ya ɗaga kai ya saci kallon mutumin, ya mayar da kansa ya sunkuyar.

"Na san wannan zaman takurar ya ishe ka zuwa yanzu, kasancewarka mutum da ya saba da 'yanci a baya.
Ina son ka buɗe kunne ka saurare ni da kyau, tambayoyi nake son na yi maka, muddin ka gaya mini gaskiya ka bani amsa, zaka iya samun sassauci, ko ma na yi umarnin a sake ka, ka yi tafiyarka gaba ɗaya"

Ya jinjina kai ba tare da ya ɗago ba.

Mutumin ya sauke rawnain fuskarsa ya ce "Na san an yi maka wannan tambayoyin an kum a baya, yanzu ma zan sake jaddada maka su, me yasa ka sace Imam ka kai shi Nigeria, da ka kai shi kuma me ka yi masa?"

Kamar ba zai yi magana ba, sai kuma ya girgiza kai ya ce "Ban sace shi ba, kuma ban yi masa komai na cutarwa a Nigeria ba"

"To me yasa ka tafi da shi Nigeria ba ka sanar da kowa ba?"

Mahmudu ya ce "Wannan wani sirri ne da ba zan iya tona shi ba, ko da za ku salwantar da rayuwata, wani abu wanda daga ni sai shi Imam"

Abduou ya jinjina kai ya ce "Da amincewar sa ku ka tafi Nigeria kenan?"

"A'a hasalima bai san komai ba, ba wani da zaɓi ne da ya rage, sai abin da na aikata ɗin"

"Mahmudu, na fuskanci zama da maɗaukin kanwa ya sanya maka farin kai. Rayuwa da Imam ya sanya ka koyi baƙin taurin kai irin nasa. Amma ka snai, kama da wane ba ta wane, kuma  ina fatan ka san da tun da aka ɗaukko shi daga Nigeria har yau ba ya hayyacinsa, bai yi magana da kowa ba?"

Mahmudu ya girgiza kai ya ce "A'a ranka ya daɗe. Rashin gane kowansa ba shi da nasaba da zuwansa Nigeria"

"Saboda me?"

"A can ɗin ma ba gane kowan yake yi ba"

Abduou ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Zoben Azurfarsa fa guda ɗaya da baya hannunsa, ina fatan ka san inda wannan yake?"

A zabure Mahmudu ya kalli Abdou matawalle, jin abin da ya faɗa.

"Ka daina zaro mini ido, kwanaki biyu kawai ka ke da su, ka faɗi inda zoben yake, ko kuma ka rasa rayuwar ka baki ɗaya, zaɓi ya rage naka"

Abdou ya miƙe, ya ja rawaninsa ya rufe fuskarsa ya fice daga ɗakin.

Cikin matsanancin tashin hankali, ya bi bayan matawalle da kallo. A Nigeria babu wanda ya san ma'anar zobunan da suke hannun Imam. Kuma ya yi iya ƙoƙarinsa gurin ba shi dukkanin kariya, balle ya ce wani ya san muhimmancin su ne ya karɓa.
Matuƙa ya ji yana son ya ga Imam, ya gana da shi, sai dai ya san ko mai zai yi babu mai ba shi wannan damar. Ga shi ya ji Abdou ya ce tun da aka dawo da shi, bai farfaɗo ba balle ya yi magana. Gefe guda kuma yana jin tsoron kar a koma a Nigeria a bibiyi Nana, saboda za ta shiga matsala ba kaɗan ba.
Koma a wani hali take ciki yanzu? Ya tambayi kansa yana jin wata irin damuwa ta mamaye zuciyarsa, tare da ɗora wa kansa laifi amincewa da auren Imam da Nana, ya kuma ɓoye mata komai a kan Imam ɗin. Ya dafe kansa da yake jin tamkar zai tarwatse dan damuwa.

****
Nana ta nutsu da zaman gidan Nene, duk Nenen akwai faɗa kamar yadda Hajara da mijinta suka din ga faɗa, amma sam hakan bai damu Nana ba, dan ba ta yi mata abin da za ta yi faɗan.
Nana ta fuskanci Nene sana'ar Abinci take yi, wasu lokutan tun safe idan ta fita sai daf da magariba take dawowa. Ta kan dawo tar e da yaran da suke yi mata aiki, su fara rage aikin Abincin sayarwar da za a yi washegari.
Nana tana jin yadda Nene take yi musu bala'i bisa kuskure kaɗan. Nene ta din ga gwada Nana, da ajiye kuɗi ko ina ta ga dama, ko ma ta fita ta bar ɗakunanta a buɗe, amma ko allura ba ta taɓa rasawa ba.
Kullum sai ta ba wa Nana Abinci, na safe kan su fita na sayarwa ta ba ta na rana, idan sun dawo ta ba ta na dare, har da ma tsaraba ta masu ciki.
Ma'aikatan Nene sun ɗauka ma, Nana 'yar uwatta ce.
Idan sun dawo Nana kan fito ta ce za ta taya su aiki, Nene ta yi ta faɗa ta ce ba za ta yi ba. Sai dai hakan ba ya hana Nana kama musu wasu ayyukan.
Nana ta shafe kusan wata guda a gidan Nene, ta ga kullum sai Nene ta ba ta Abincin nan sau uku, ba ta taɓa nuna mata ta gaji da ciyar da ita da take yi ba, wasu lokutan har tambayarta take yi, ko tana son cin wani abin ne daban.
Da daddare ta kira Nana, Nana ta fito ta zauna a kusa da ita. Ta buɗe takarda fal kifi ta ce "Nana ga kifi ko za ki iya ci, idan ƙarnin ba zai dame ki ba".

Nana ta dube ta ta ce "Nene, dama ina son mu yi magana ne"

Nene ta ce "To ina jin ki"

"Na ga kullum sai kin bani Abinci sau uku a rana, na ce ko za ki ba ni wani aikin na din ga yi miki, a maimakon Abincin da ki ke ba ni, ko gurin sayar da Abincin sai na din ga bin ki, ko wanke-wanke na din ga yi miki"

Ta dubi Nana, sannan ta numfasa ta ce "Ni kuwa duk rashin imanina, da wannan tsohon cikin sai na saka ki aiki, dan dai abin da za ki ci sau uku ba zai gagara ba. Ban san takamaiman abin da ya kawo ki ƙasar nan ba, ban san kuma lokacin komawar ki ba, amma ba na tunanin abin da za mu ci ni da ke zai gagare ni. Ba zan ɓoye miki da fari ban so zamana da ke a gidan nan ba, saboda ba na son matsi da takura ko kaɗan, da su Auwwalu sun matsa ne, dan kora da hali na so yi miki. Amma yanayin ki ya nuna mini ki na ɗauke da damuwa mai nauyi a zuciyarki. Ba ƙaramin dalili ne zai sanya yarinyar mace, mai ƙanan shekaru kamar ki, ta baro gida ta taho uwa Duniya ba ga juna biyu. Kuma ki na yawan zama ki yi shiru, fuskar ki ɗauke da damuwa. Na kuma jarraba ki ta ɓangarori da dama, ban ga alamar rashin nutsuwa a tare da ke ba, shi yasa na ji zan iya zama da ke. Amma Nana tsakaninki da Allah wannan juna biyun na ki, na halal ne? Kuma da sanin iyayenki ki ka taho nan?"
Tambayar Nene ta yi wa Nana mugun zafi a ƙirjinta, amma sam ba ta ji haushinta ba, dan kowaye dole ya yi irin wannan tambayar. Sai da ta ji hawaye ya cika mata ido, da tuna ire-iren waɗannan tambayoyin dole ta ci gaba da amsa su, a cikinta da abin da za ta haifa, muddin ba gano inda Sayyid yake ta yi ba.
Ta haɗiye wani irin yawu mai zafi ta ce "Nene cikina na halal ne, ni matar aure ce, ban kuma gaya wa iyayena zan taho nan ba, sai da na riga na yo nisa da gida"

"To saboda me, kuma ina mijinki?"

Kawai Nana ta fashe da kuka, ta ce "Shi na fito nema, mijina da danginsa"
Nene ta ce "Shikenan, ya isa haka ki kwantar da hankalinki, mu bar maganar ma yi wani lokacin. Amma sai dai ki yi haƙuri, dan dole sai mun ƙarasa wannan maganar Nana, saboda ni uwa ce, dole na mu'amalance ki na yi miki nuni da abin dai-dai da akasin haka. Ban ga alamar ki na magana da wani a can gida ba, ko ta tarhon hannunki ce ba. Mahaifiyarki tana raye?" Nana ta jinjina kai tana share hawayenta.
Nene ta ce "Shikenan, share hawayenki mu ci kifin"

Ta girgiza kai ta ce "Ƙarnin hawa kaina yake yi na ƙoshi" daga haka Nana ta tashi, ta koma ɗakinta. Sai dai ta din ga kuka, saboda ita kanta ba ta san ta ina al'amuran za su warware ta cimma abin da ta fito nema ba.

Shukura ta rasa gane kanta da kanta, saboda rashin lafiya da take ta fama, ga Sagir ya rage ba ta kulawa, duk da yana ta ɓoye-ɓoye amma tuni ta daɗe da gano shi, sai dai ta maze ita ma ba ta nuna masa ba.
Hajiya Amina ce ta je gidan, Shukura ta ji daɗin zuwanta sosai da sosai, a nan Hajiyar take gaya mata batun Nana.

Cikin damuwa Shukura ta ce "Wallahi Mami, tun da aka yi auren nan, nake jin tausayinta, gaba ɗaya ban ga riba a abin da babanta ya yi mata ba. Babu bincike babu komai a ce an aura mata mutum, wasu lokutan na kan rasa ina tunanin mutanenmu yake tafiya"

"Ke dai a yi sha'ani kawai, amma na jinjina batun ni kaina"

"Shikenan an saka rayuwarta a gagari, ga ƙarancin shekaru" suka ci gaba da jajanta lamarin. Hajiya ta fuskanci yanayin Shukura kamar ba ta da cikakkiyar lafiya, ta kira Doctor Sharif ya zo ya duba ta.
Shukura ba ta so ba sam, dan ko ƙaunar ganin Sharif ɗin ba ta yi, amma tuna ta yi wa Hajiya Alƙawarin komai ya wuce, ta yi tawakalli ta dangana ya sanya ta haƙura.
Ya zo har gida ya yi mata gwaje-gwaje, ya kuma tabattar mata da tana da juna biyu.
Hajiya Amina ta din ga murna, a duk lokacin da aka ce ga wata mace da ciki, sai ta yi ta murna, ta ji dama ita ce.
Shukura ba ta wani yi murna ba, saboda ita gaba ɗaya haihuwar ma ta fita daga kanta.
Da yamma Hajiya Amina ta koma gida, saboda tsabar zumuɗi, tana zuwa ta tarar da Alhaji Zailani a gida, ta hau ba shi labarin Shukura wani cikin ne da ita. Wata irin mummunar faɗuwar gaba ce ta ziyarce shi, yana tsoron a wannan karon ma, kar a nemi ya bayar da wani abu da ya danganci iyalinsa.

Hajiya Amina ta din ga jin wani irin bacci, tana idar da sallar isha'i, ta ɓungire a gurin ta hau bacci.

Ita da Nana ta gani a falo, a zaune suna hira, kamar yadda suka taɓa yi kwanaki lokacin Nanan, na zuwa gidan rainon Haidar.

Ta ce "Hajiya, kin kuwa ci gaba da bibiyar Likitoci a kan matsalar rashin haihuwar ki?"
Hajiya Amina ta ce "Nana ai ni na haƙura ma na bar wa Allah, yanzu shekaruna sun wuce na haihuwa"

Nana ta ce "A gurinki ba, a gurin Allah yana bayar da falalarsa a inda ya so, da kuma lokacin da ya so ne. Ki daina biye wa wannan mijin naki, ya din ga sarrafa rayuwar ki yadda yake so. Ki nemi mafita a kan matsalolinki.
Kuma Shukura ta dage da Addu'a, kar wannan ɗan ma ya sake raba ta da shi"

Maganar Alhaji Zailani ce ta tashi Hajiya Amina daga mafarkin da take yi, tana kallonsa kawai ta ji gabanta ya faɗi"

"Lafiya ki ke kwance a ƙasa haka ki ke bacci?"

Ta ce "Bacci ne ya ɗan ɗauke ni ban sani ba"

Ya ce "To ki tashi ki koma gado mana, kar wuyanki ya yi ciwo" Ta yinƙura ta tashi ta canza kaya ta hau gado ta kwanta, sai dai ta din ga jin mafarkin da ta yi da Nana a jikinta, tamkar a zahiri ya faru.

Fadila ce zaune a kusa da Alhaji Fatuhu, gefenta kuma jaririnta ya yi wayo, yana ta bacci.
Ta miƙa masa lemon da ta haɗa masa a kofi, ta zuba masa ido, yana sha a hankali.
A ranta take faɗin "Ubangiji Allah ka bawa wannan bawa naka lafiya, albarkacin ayoyin Alkur'ani'
Ta kalle shi tsaf, ya yi rama ta ban mamaki, dan ma yanzu ya ɗan ciko, ba kamar da ba" ya shanye ya miƙa mata kofin, ta karɓa ta ajiye a gefe. Ta matsa kusa da shi tana ɗan ƙara gyara masa filulluka.
Ya ce "Na gode sosai, Allah ya yi miki albarka, ya raya miki Muhsin"

Ta ce "Amin Daddy"

"Da lafiyata ƙalau, da mun yi sauri, nan da wata wata taran, ki kuma haifo mana wani" Murmushi ta yi ta ce "Allah ya baka lafiya ya tashi kafaɗunka" ya amsa da Amin yana riƙe hannunta cikin nasa da ya yamuste kamar na tsoho.
Hajiya Suwaiba ta ce ta shigo ɗakin, Fadila ta ɗan zabura ta ja da baya.
Hajiyar ta ja tsaki ta ce "A hakan ma da kake wani abin ka ke ƙoƙarin yi, ai sai ku rufe ƙofa kar yara su faɗo, a lalata mini tarbiyyar yara"
Fadila ta ce "Haba Hajiya, abu na ba shi ya riƙe hannuna, and laifi ne dan ya riƙe hannuna wani abin ki ka ga na yi?"

"Kar ki yi mini rashin kunya dai? Idan ma yin ku ke, ku ƙarata ku da Allah"
Ran Fadila ya yi mummunan ɓaci, ta yinƙura da niyyar, ta ɗauki ɗan ta ta bar ɗakin, amma ya riƙe hannunta, ya hana ta tafiya. Hajiya Suwaiba ta gama bala'inta ta tafi ta bar su.
Idan ya ce Suwaiba ba ta ƙoƙari a kan rashin lafiyarsa ya yi ƙarya, tana iyakar ƙoƙarinta amma wasu lokutan tana da saurin ƙosawa gashi haryanzu azababben kishi na ɗawainiya da ita.

****
Gidan Maijidda kuwa, Iliyasu bai taɓa tsammanin,    Maijidda na da taurin kai haka ba. Gaba ɗaya ta tarkata shi ta yi watsi da shi. Iyakarta da shi, ta girka Abinci ta ba shi, idan buƙatarsa ta tashi, ya yi kiɗansa ya yi rawarsa. Gaba ɗaya ta sanya damuwa a ranta, ta rame sosai da sosai, dan ko Abincin kirki ba ta iya ci, kusan kullum cikin kuka take, ko ta zauna ta yi shiru. Ga shi ya lura 'yan uwanta sun fara gajiya da sinturin kai ƙararta da yake yi, ba yau ba gobe.

"Anya ka na ganin haka rayuwar Imam za ta ci gaba, duk lokacin da ya farka sai ihu da fizge-fizge, sai dai a yi ta yi masa allurar da zai yi bacci? Idan aka bar shi a haka rayuwarsa fa ta nakasa kenan har abada"

Sultan ya ce "Abdou, ni kaina ala'amarin nan yana damuna, na rasa yadda zan yi. A ɓangaren ƙwaƙwalwar ma, babu wani gamsashshen bayanin abin da ya faru da shi. Ta ɓangarenka ma babu wani nagartaccen bayani daga bakin shi yaron, balle mu ji ko wani abin ɗin aka yi masa".

"Sultan, ka ƙi bayar da dama a sanya 'yan doka, su maguza yaron nan, ya faɗi gaskiya ko ya ƙi Allah"

Sultan ya girgiza kai ya ce "A'a, duk ranar da Imam ya samu lafiya, muddin ya ji labarin an cuzguna masa, zai yi fushi, kuma zai ji babu daɗi kai ka san irin alaƙar da take a tsakaninsu."

"Amma yanzu ai yanzu a kan gaɓar bincike a ke Sultan. Amma tun da haka ka ce Shikenan, za a ci gaba da bin komai sannu a hankali"

Sultan ya amsa da "Yauwwa"

BAYAN WATA ƊAYA

Sabo turken wawa, rashin ganin Ƙaisar da Nana ta daina yi, ya sanya ta din ga tunanin ko wani abin ne ya faru da shi.
Sai dai yau kwatsam cikin barcinta, ta ganta a cikin Librarynsa. Sai dai ta gurin ƙwalam babu litatafai babu kayan rubutunsa sai mudubin da yake nuna mata abubuwa a cikinsa.
Ta waiwaya ta lelleƙa, amma babu Ƙaisar babu alamunsa.
Wani littafi guda ɗaya tal, ta hango a kan teburin rubutun Ƙaisar, ta ƙarasa ta nufi teburin ta ɗauki littafin.

Bangon littafin na fatar wata dabba ne. Dan har da gashi-gashi a jiki. Yanayin bangon littafin ya sanya ta yi tunanin, ko mene ne a rubuce a littafin ba yanzu ya faru ba, ya kwana biyu da faruwa. Littafin ba wanda ta karanta tarihin su Lanti ne a ciki ba, wani ne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login