Showing 72001 words to 75000 words out of 122205 words

Chapter 25 - BUZU BOOK2 COMPLETE 2

18 Jan 2026

575

matasan matan sannan suka ɗauki hanyar tafiya.

Tana jin yadda suke ta hirarrakinsu a cikin motar, amma ta kasa tofa komai, da ta rufe ido, ɗan jaririnta take hangowa, gefe guda kuma zuciyarta cike da fatan Allah ya sa tafiyar nan, ta yi mata rana.

A ƙalla sun yi tafiyar awanni biyu da rabi a mota, sannan suka isa wani gida.
Hansatu ta yi musu bayanin, a nan za su sauka su huta, washegari ta kai kowacce inda ta ɗaukko ta za ta kai ta. Nana ta din ga addu'a da fatan Allah ya sanya ba mugun hannu ta faɗo ba, duk da kafin ta taho Nene ta bata layi ta saka a wayarta, ta ce mata duk abin da ta ga ba ta yarda da shi ba, ta kira ta ta sanar mata.
A duk lokacin da Nana ta ɗaga wayar ta kalla, sai ta tuna Hajiya Amina, Haidar da kuma sauran jama'arta na Nigeria.

A gidan nan suka yi salla, aka ba su abinci suka ci, sai dai Nana ta yi mamaki ganin mata da yawa a gidan. Duk da ƙabilu ne daban-daban matan, akwai Zabarmawa, akwai Bugaje, da hausawa da sauran ƙabilun ma da ba ta sani ba a Nijar. Wai gidan kamar kamfani ne, wannan matan aiki ake nema musu, duk ciki Nana ce kawai 'Nigeria a cikinsu. Gaba ɗaya ta takure kanta ta kasa jikinta da su.
Gaba ɗaya daren ranar, Nana ta kasa bacci, ta din ga tunanin Muhsin, da tunanin ko zai yi kukan rashin ganinta.
Washegari Hansatu ta ce wa Nana ta shirya, ta ɗauki kayanta su tafi. Haka kuwa aka yi ta sake ɗaukarta su ka fita.

Nana ta sha mamaki, ganin haɗuwar da gurin cin abincin ya yi, kuma babban abin da ya ƙara bata mamaki, gurin cin abincin tamkar hotel.
Suka shiga cikin gurin, Hansatu ta kai Nana wani katafaren ofishi, da yak3 gurin mai kula da ɗaukar ma'aikatan, da yake namiji ne. Rawaninsa ne ya tabattar mata da buzu ne, ganinsa kawai sai Nana ta ji wani irin sanyi, tamkar ta ga Sayyid.

Nana ta gaishe shi, ya amsa sama-sama yana ɗan basarwa.
Hansatu ta ce masa "Wannan ita ce ma'aikaciyar, na kawo ta a yi mata gwajin, a gani idan za ku ɗauke ta" Ya ɗaga kai ya  sake kallon Nana ya ce "Sannu ko"

Nana cikin girmamawa ta ce "Yauwwa sannu da aiki"

Ya miƙo mata ƙunshin wasu takardu ya ce "Ga wannan duba, ki ga yadda tsarin aikin namu yake, ki gani idan sun yi miki, kafin mu je inda za a yi miki gwajin, idan kin ci sai ki sanya hannu a takardun, ki fara aiki da mu"
Nana ta saka hannu ta karɓi takardun, amma ta ga rubutun French, ta kalli Hansatu, ta kalle shi ta ce "Ai ban iya fransanci ba"

Ya kalli Nana ya ce "Ba ki yi makaranta ba?"

Ta ce "Na yi, amma ni ban iya French ba, turanci na iya sai Hausa"

Hansatu ta ce "A yi haƙuri Yallaɓai, 'yar Nigeria ce, daga Nigeria take"

Sai kuma ya kalli Nana ya faɗaɗa murmushinsa ya ce "Daga Nigeria ki ke? Ki ka baro babbar ƙasa kamar Nigeria ki ka zo jamhuriyar Nijar ki yi aiki da mu?" Nana ta ɗan risunar da kai tana murmushin dole, ganin yana murmushi shi ma.

Ya ce "Ahh to ai 'yan Nigeria ƙawayenmu ne, ba ma ƙawaye ba 'yan uwanmu ne. Dan haka zan ba ki aiki amma da sharaɗin za ki koya mini turanci, idan kin yarda na baki aiki" Nana ta yi murmushi, saboda yanayin yadda ya yi maganar cikin zolaya. Ya yi 'yar dariya ya ce "Ai duk wanda ya zo Nijar, mussaman daga Nigeria baƙonmu ne, akwai buƙatar mu karrama shi sosai da sosai, ko dan ƙara zumuncinmu da mutanen Nigeria. Dan haka babu wani abu, wannan wani ci gaba ne ma zan iya cewa gurin Abincinmu ya samu, kin ga girke-girken da ba a yi a nan, na can ƙasar kya din ga yi mana.
Mu na da gurin kwana na ma'aikatanmu, awa ashirin da huɗu muke yi mu na aiki. Kamar yadda ki ka gani babban gurin cin abinci ne da manyan mutane ke zuwa cin abinci.
Masu sayar da abinci daban, masu girki daban, ke za ki kasance a ɓangaren masu girki ne. Mu je mu zagaya ku ga gurin sosai da sosai.

Ya jagoranci su Nana, ya nuna musu gurin, tsarin ya yi wa Nana sosai, duk da abin da ba ta ji daɗi ba, maganar zuwa hutun sati ɗaya ne kacal, duk ƙarshen wata.
Su Hansatu za a din ga tura wa albashinta, su cire nasu kason su bawa Nana sauran.
Ita Nana duk hakan bai dame ta ba, babban fatanta buƙatarta ta biya kawai.

Suka kammala duk cike-ciken da za su yi, aka sallami Hansatu, Nana kuma aka kaita gurin kwanan ma'aikata.
Ɗakin da aka kai Nana, su uku ne a ciki, da banɗaki a ciki. Ta ajiye jakar kayanta, Hansatu ta kalle ta ta ce "To Nana, kamar dai yadda ya gaya miki, mu kamfani ne, kuma a ƙarƙashinmu ki ka zo nan, dan haka gurinmu albashinki zai din ga tafiya, mu zamu din ga sallamar ki"
Nana hakan ko a jikinta, dan ita ko ba za su ba ta komai ba, indai akwai gurin kwana da abinci, kuma kwalliya za ta biya kuɗin sabulu, hakan ba damuwarta ba ne ba.

A fili ta ce "Babu damuwa, hakan ma na gode sosai da sosai, Allah ya saka da mafificin Alkhairi".

"Amin, a hakan ma gaskiya kina da sa'a sosai da sosai, sai da muka kawo musu mata uku, da ƙyar suka ɗauki ɗaya, wai duk ba su yi musu ba, wasu kuma sai an zo yi musu gwaji sai su faɗi. Amma ke ya ce ba zai yi miki ma gwaji ba, kawai an ɗauke ki aikin.
Abin da zan gaya miki kawai shi ne ki kula, ki kula da kanki sosai da sosai, banda ƙazanta banda son jiki.
Sannan kar ki ga kin tsallake wannan matakin, ya ɗauke ki aiki a haka cikin sauƙi, ki zata miƙe ƙafa za ki yi, mace ce mai gurin nan, kuskure kaɗan za ki ta ci mutuncinki ta kore ki. Su kan su ma'aikatan kwantar da kai suke yi, su na yi mata biyayya, duk wata tijara da bala'inta kawai ki toshe kunnenki ki yi haƙuri." Nana ta yi shiru, sai da Hansatu ta gama gaba ɗaya sannan ta numfasa ta ce "To Ubangiji Allah ya iya mana"

Hansatu ta amsa da "Yauwwa Amin"

Hakanan Nana ta ji a jikinta, ba za ta ɗauki wulaƙanci da cin zarafi ba, duk da kuwa abin da take son cimma. Ko Nene da ake kambama faɗanta da masifarta, ba ta cin mutunci, kuma duk abin da za ta yi faɗa a kai, to a kan gaskiya ne. Amm yanayin yadda Hansatu take yi mata bayanin mai gurin nan, a kaikaice dai ba ta san darajar mutane ba.

Ɗakin da Nana take, ita da wasu Zabarmawa ne guda biyu. Ta yi alwala ta yi sallar Azahar.
Ta daɗe a kan abin salla, tana gaya wa Allah, cikin magiya a kan ya sanya ta samu abin da ta fito nema, ya kuma raba ta da duk wani sharri da abin ƙi.
Bayan ta idar, ɗaya daga cikin 'yan ɗakin, ta ce mata ta zo su je ta zagaya da ita.
Can ɓangaren da ake girke-girken ta kai Nana, suka zagaya daga nan ta kaita cikin gurin da ake sayar da abincin. Nana ta yi mamakin girman gurin, da yadda gurin Abincin yake da tarin kwastomomi. Sai dai da gani ka san na manya ne, dan duk waɗanda suke zuwa gurin cin abinci akwai alamun abin hannu a tattare da su.

*****

Ɓangaren su  Shukura cikin jikinta ya tsufa sosai, sai dai a wannan karon ta dage fafur ta ƙi yin awo a Asibitin su Doctor Sharif.
Gefe Sagir ya jewa mahaifiyarsa, da maganar son dawo da Yusra, amma ta ce ba ta lamunta ba, ba ta buƙatar ya sake rayuwa da Yusra, gara yaje ya auro wata can daban, amma ba Yusra ba.
Gaba ɗaya ya shiga damuwa, saboda mugun sabo da shaƙuwar da ya kuma yi da Yusra.
Ita ma Hajiya Halima tun da ta samu labarin, Sagir ne tsohon mijin Yusra yake zuwa gurinta, ta din ga bala'i ta ce ko shi ne autan maza, Yusra ba za ta koma hannunsa ba, balle a sake ci mata mutunci a sako ta. Ga shi daga shi har ita su na son junansu. Dan haka ya yanke shawarar tafiya gurin ƙanin mahaifinsa ya yi masa magana.
Shi kuma ya kira Hajiya Halima ya din ga yi mata faɗan dan me za ta hana shi mayar da matarsa alhalin sulhu alkhairi ne, wancan karon da auren ya mutu ma, gutsuri tsomarsu ce ta kashe Auren.
Mussaman ta kira Sagir gida, ds ya je ya same ta, ta dirarar masa da bala'i.
"Wato ƙarata ka je ka kai wa ƙanin ubanka saboda mace ko Sagir?"

Ya girgiza kai ya ce "A'a Hajiya ba ƙararki na kai ba"

"Rufen baki ko na make ka, ba ƙarata ka kai ba ya kira ni yana faɗa? Tun da abin da ka zaɓa kenan, ka je ka yi duk abin da ka ga dama"
Kalaman na Hajiya, tamkar ɗsure shi ne da jijiyoyin jikinsa, gaba ɗaya ya rasa abin da yake yi masa daɗi ba ya son ya yi abin da daga baya zai zo yana dana sani, saboda rashin amincewar Hajiyarsa.

****
Daren yau sam Nana ba ta samu isasshen bacci ba, da yake sai washegari aka ce za ta fara aikin, ba ta yi aikin komai ba ranar.
Raba dare ta yi tana nafilfili addu'oi, saboda a jikinta tana jin wani abu game da gurin, wanda ta kasa tantance ko mene ne.
Washegari da safe, suka shirya ita da 'yan ɗakinsu, suka tafi gurin aikin Abincin.
Kayan girki ne ga su nan a zube, kamar abin banza, yanayin yadda aka jibge kayan a gurin, Nana ta sha jinin jikinta, ta san aiki ne tuƙuru za a yi shi gurin.
Aka ba su jadawalin abinccicikan da za a girka a ranar, Nana ta san wasu, wasu kuma ba ta san su ba.
Su na nan tsaye shugabar ɓangaren na ƙara yi wa Nana bayani, da gurɓatacciyar hausarta, sai ga mutumin jiya shigo.
Gaba ɗaya suka wani ruɗe, masu gyara tsayuwa na yi, masu kama aiki suna yi, Nana dai ta ƙame a gurin da take. Ba yabo ba fallasa ya din ga amsa gaisuwar da ake yi masa, sai da ya zo kan Nana ya saki murmushi ya ce "Baƙuwarmu, ya ki ka ga gurin namu, ba dai wata matsala ko?"
Nana ta girgiza kai ta ce "Babu matsala"

Ya ce "Yauwwa, ki saki jiki ki yi aikinki da mu, kamar kina Nigeria, duk abin da ba ki gane ba, ga shugabar sashin nan, idan kuma ba haka ba ni ki zo ki same ni ki yi mini magana"
Ta jinjina kai ta ce "To in sha Allah, na gode sosai da sosai"

Ya kalli matar ya ce "Dan Allah kar a ce za a sakar mata aiki lokaci ɗaya, a koya mata abin da ta sani ba a hankali, kafin a sakar mata aiki"

Matar ta risuna ta ce "In sha Allah, amma za a yi mata gwajin ne ita ma?"

"Kin ji na ambaci hakan ne, a maganata?"

Ta girgiza kai ta ce "Tuba nake"

Ya ce "'Yar Nigeria, a yi aiki lafiya"

"Na gode sosai" Nana ta yi maganar cikin girmamawa. Ya wuce ya fita. Bayan ya fita suka juya yare, suka ɗan yi maganganu, sai dai duk da Nana ba ta jin yaren nasu, ta san gulmarta suke yi. Suna aiki amma gaba ɗaya hankalin Nana ba a kan aikin yake ba, yana kan halin da Sabir yake ciki. Tana ta tunani yaya yake? Yana rigima ko kuwa bai damu ba ya kwantar hankalinsa, haka ta yi ta wasi-wasi a zuciyarta.

*****
Hajiya Amina ce ta yi shirin tafiya Umara, ta tsaya a Egypt za ta kwana biyu, ta tsaya a ɗan binciki lafiyarta. Sai dai ta din ga ji a ranta, yakamata a ƙara bincika mata matsalarta ta rashin haihuwa, mussaman da take tuna maganganun Nana. Sai dai gefe guda tana tuna yadda Alhaji Zailani yake gargaɗinta a kan shi ya fauwwala wa Allah, bai damu lallai sai ta haihu ba, tun da an nemi magani ba a dace ba.
Sai dai a wannan karon, ta sake jin tana son jarraba da bibiyar lafiyarta, da ganin likita, ko za a dace, tun da ba ta daina al'ada ba ma.
Da harshen turanci suka tattauna da Likitan, ta yi masa bayani, ya rubuta mata gwaje-gwaje ya ce ta je ta yi, ciki har da hoto.
Kasancewar komai na su ba kamar na ƙasarmu ba, cikin ƙanƙanin lokaci aka yi duk gwaje-gwajen, aka tura wa Likitan sakamakon.
Bayan ta koma gurin Likitan ya duba na'ura mai ƙwaƙwalwarsa, ya kalli Hajiya Halima ya ce mata "Sakamakon hoton da aka yi mata, ya nuna babu mahaifa a jikinta gaba ɗaya" wata irin ƙara cikinta yayi, zuciyarta ta buga a jejjere da ƙarfin gaske, sai ta hau kame-kame tana tunanin, ko kunnuwanta ba su ji daidai ba? Ko kuma turancin nata ne ya ƙwace.

Cikin rawar murya ta ce "Ka tabattar da abin da ka gaya mini, ko kuma nice ban fahimta ba?"

Ya ce "Na tabattar, shi ne sakamakon gwajin da aka turo mini, amma idan ba ki yadda da sakamakon ba, kina iya zuwa wani Asibitin a sake duba ki!.

Yammm ta ji kanta yana yi, ta daina gane komai, hankalinta ya rarrabu kashi-kashi, tana son yi wa likitan tarin tambayoyi amma kanta ya kulle.
Shin da gaske ana iya samun mace babu mahaifa, ko kuma wani abin ne daban? Ya aka yi duk tsawon lokacin da ta ɗauka tana bulayin neman haihuwa ba a taɓa gaya mata ba ta da mahaifa ba sai yanzu?.

Gaba ɗaya Hajiya Amina, ta rasa kalmomin da za ta tattaro ta sake furta wani abu. Jikinta rawa kawai yake yi, wani irin gumi yana tsatstsafowa ta kowace kafa ta gashin jikinta.
Likitan ya ci gaba da yi mata bayani, amma ta kasa fahimta.
Ba ta san ma da ya aka yi ta bar Asibitin ba, ta koma masaukinta saboda tsabar ɗimuwa. Ta kuma rasa wa za ta kira ta sanarwa wannan maganar.
Gaba ɗaya kanta ya juye, dan ba ta ma iya tuna yadda su ka ƙarƙare da Likitan ba.
Tana so ta zubar da hawaye, ta ji sanyi a ranta, amma abu ya gagara idanunta suka bushe zuciyarta ta yi nauyi. Babbar tambayarta ita ce, dama ana iya samun macen da ba ta da mahaifa? Ko kuwa ta ta ce ta yi ɓatan dabo?. Tambayar da ta rasa wa za ta yi wa, balle a ba ta amsa.

*****

Nana kuwa gurin nan aiki ake yi tamkar babu gobe, duk da ba ta da son jiki, amma aikin yana da yawa ga babu isasshen hutu, sai aikin ɗorawa da saukewa.
Ga shi ta kasa sakin jiki da ma'aikatan gurin, saboda yadda suke tsangwamarta, da nuna mata ƙabilanci, saboda ita ba 'yar ƙasar su ba ce ba. Sam ba sa gaban Nana, duk da tana ɗan saka ido ta ga, ko akwai wata mai hankali da za ta ji ta yarda da ita, a kaikaice ta ɗan fara ƙwanƙwasa cigiyar Sayyid. Sai dai gaba ɗaya ba su yi mata ba ma'aikatan gurin, gaba ɗaya ba ta ji ta aminta da ko mutum ɗaya daga cikin su ba.
Kullum da safe Al hussain, mutumin da ya ɗauke ta aiki, sai ya zagaya su ya ga yadda suke gudanar da aikin safe da yamma.
Da ya zo ma'aikatan suke nutsuwa, kowa ce ta kame kanta, marasa kamun kai kuma su fara ɗan karairaya. Shi kuma ya tsuke fuska yana basarwa. Sai dai da ya ga Nana sai ya saki fuska, ko ba ta kula shi ba, shi sai ya yi mata magana.

"'yar Nigeria ya alƙawarinmu ne?"

Nana ta ɗan saki fuska ta ce "Wanne?"

"Au har kin manta?"

Ta yi murmushi ta ce "Duk lokacin da ka shirya, sai mu fara"

Ya ce "Kin san akwai wani abokina, sonake kafin na haɗu da shi, ko gaisuwa na iya da turanci, saboda ya iya turanci ni ban iya ba, ya juya yare ya yi ta magana ba na gane me yake cewa, to kin ga yakamata na ba shi mamaki nima"

Nana ta ce "Gaskiya ne, shi ma Buzu ne kamar ka?"

Al Hussain ya ce "Ya aka yi ki ka san ni Buzu ne?"

"Ga rawani nan ka na yi" ya yi dariya ya ce "Kash, to shikenan tun da kin gane, shi ma buzu ne, mun kwana biyu ma bamu haɗu ba, ban je Agadez ba"

"Duk Buzaye a Agadez ku ke?"

Ya girgiza kai ya ce "A'a, sai dai mun fi yawa a can, ko kina son zuwa ne? Mu na da wani gurin Abincin ma a can, babban wannan sai a mayar da ke can" Nana ta girgiza kai ta ce "A'a tamabaya dai kawai na yi"

Ya jinjina kan ya ce "To yaya aikin?"

"Alhamdillah"

"To ma sha Allah, Allah ya taimaka"

Tun da suka fara hirar nan, Nana ta lura da irin kallon da ake yi mata, saboda ya tsaya sun yi hira. Sai dai ita ba kallon ne ya dame ta ba, a jikinta take jin sam ba ta kyauta ba, tsayawa da ta yi tana magana da Al Hussain har take yi masa murmushi ba, saboda ta san da Sayyid yana gurin, ko da makamancin wasa ba za ta taɓa aikata hakan ba, saboda yadda yake tsananin kishinta.
A hankali ta ce "Ka yi haƙuri Sayyid, babu yadda na iya ne, duk a ƙoƙarina na son zuwa gare ka ne, ka yi mini afuwa" ta furta a hankali kamar mai raɗa.

"Nana wai a ina ki ka san Al Hussain ne?"

Nana ta ɗaga kai ta kalli Shugabar gurin nasu, da take yi mata tamabaya cike da tuhuma. Kamar Nana ba za ta yi magana ba, sai kuma ta ce "Waye hakan?"

Matar ta ce "Kamar yaya?"

Nana ta ce "Wanda ki ke tambayata"

Gaba ɗaya suka kalli Nana, jin yadda take bawa Adama, shugabar ɗakin girki. Ita kuwa Nana ko a jikinta da irin amsar da ta bawa Adaman.

Cike da takaici Adama ta ce"Mutumin da ya fita yanzu"

Nana ta ce "Au sunansa kenan dama? A nan Nijar na san shi, meyafaru?" Ta yi maganar tana tsare Adama da ido, tana jiran abin da za ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login