Showing 21001 words to 24000 words out of 122205 words
yadda na iya ne nake shan na Asibitin ma, ni wahalar da ni suke yi"
"To ai wannan ba na Asibiti ne ba, dan Allah ka daure ka taimaka, ba dan ni ba"
Da ƙyar ya yarda ya karɓa, ya ɗanɗana ya ji babu ɗaci, sannan ya ci gaba da sha, sai ma ya ji ɗumin maganin ya yi masa daɗi.
Bayan ya shanye, ta dafa masa shayi kuma, ya ɗora dan duk wahalar ciwon da yake ciki, ba ya iya haƙura da shan shayi.
Nana ta dage da bawa Sayyid, wannan ruwan maganin, tana addu'ar Ubangiji Allah ya taimake su, ya sanya ya karɓe shi.
Cikin ikon Allah, sai kumburin da ya yi, ya fara sacewa a hankali, har yana iya cin Abinci sosai. Nana kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha.
Nana ta din ga murna, ganin ana samun ci gaba a yanayin jikinsa. Har banɗaki yana iya zuwa, ba tare da ta kama shi ba, yana tafiya a hankali a hankali da kansa yana iya yi wa kansa Wasu abubuwan.
Yana zaune tsakar gida, yana shan shayi ta ce "Ashe maganin Sarkin baka yana yi"
Ya kalle ta, ta ce "Ka san Sarkin baka?" Ya ɗan yi shiru yana kallon ta.
"Ranar da aka kai ni, kai na an kai ka, zaku tafi lokacin, ni kuma a lokacin na ji na fita daga hayyacina. Kai mun fa daɗe muna haɗuwa da kai."
Ya yi murmushi ya ce "Ruhina ne ya addabe ki, sai da ki ka nemo ni, ki ka aure ni ki ka nutsu"
Ta ɓata fuska ta ce "Ba wani nan, kai ne ka din ga bi na dai, har ka aure ni".
Ya ɗan sake zuƙa shayin hannunsa ya ce "A'a. Har gidan da nake ki ka bi ni fa"
"Ni ba bin ka na yi ba, kuma ai kai ka ce a biya maka sadakin aurena"
Ya maze ya ce "Ai gani na yi kin liƙe mini, har cikin ɗakinmu na gadi ki ka bi ni, na ce kai yarinyar nan idan ban aureta ba, akwai matsala haka za ta yi ta bina saboda ruhinta da yake jikina. Kina ganina kuma ki ka rikice"
"Ni ba ina sane na shiga ɗakinku ba, Jummai ce ta ce na ajiye muku Abinci, kawai na ji ana kirana a cikin ɗakin, ban ma na san na shiga ba. Kuma ni da na shiga wannan tsohon na gani. Kuma ai kai ma idan ka ganni kallona ka ke yi"
"A'a faɗi gaskiya dai, ni ki ka leƙo ki gani, ranar ba ki ganni ba, sh... Kawai ya ga tana hawaye. A diririce ya ajiye kofin hannunsa ya ce "Mene ne?" Ta yi masa shiru.
"Laifi na yi miki? Wasa fa nake yi" ta yi masa shiru, tana matse ƙwalla. Ba wai wasan da yake yi mata ne ya sanya ta kuka ba. Tuna yadda aka yi auren abin da Baba ya din ga faɗa da wanda Mama ta din ga yamaɗiɗi da ita, abin ne kawai ya dawo mata.
Ji ta yi yana goge mata hawaye, fuskarsa ɗauke da damuwa, ya ce "Ba zan sake ba" Kwaɓe baki ta yi cikin shagwaɓa, wasu hawayen na ziraro mata.
"Na ce na daina fa, ki bari ƙirjina ya fara nauyi" da sauri ta saka bayan hannunta, tana goge hawayen fuskarta.
"Yauwwa dama ina so mu yi wata magana, mai muhimmanci da ke"
Ta tattara hankalinta, gabanta na dukan uku-uku cike da wasi-wasin wace maganar zai yi da ita haka?.
Ayshercool
08081012143
57
Ya yi mata alama da hannunsa, a kan ta nutsu ta kwantar da hankalinta. Ta jinjina masa kai, duk da gabanta na ci gaba da faɗuwa.
"Amm na san kina haƙuri a kan abubuwan da suke faruwa, duk da kin ce mini ba kya so na din ga irin wannan maganganun, amma sun zama dole na yi. Ina ƙara yi miki godiya da nema miki yardar Allah, na san ba ni da abin da zan biya ki da shi a wannan Duniyar. Ke ce komai nawa da ki ka rage Asmy. Sannan ɓangaren abin da ya shafi auratayyarmu, shi ma na san...
Ta katse sh6ta hanyar cewa "Amm ni dai a bar wannan zancen, bari na je na ɗora wakena"
"A'a ki tsaya mu yi magana"
"A'a ba sai mun yi ba"
"To kar na sake jin kin bi dare ki na taɓa ni" Kamar ta yi tsuntuwa ta ɓace, saboda azabar kunya, ita a zatonta ma ya manta gaba ɗaya. Cikin azama ta miƙe ta ɗauki robar wakenta, ta nufi inda take girki. Tana tashi ya kashingiɗa yana dariya.
Nana tana ta fifita wuta, yana daga zaune yana kallonta. Wani irin abu ne yake yi masa yawo a jikinsa, a game da ita.
Yana jin zai iya yin komai, dan tabattar da ci gaba da zamanta mallakinsa, shikaɗai.
Juriyarta, sadaukarwa da kuma tsananin tausayinta, ya sanya yake jin ina ma yana da wani abu da zai iya kamanta faranta mata rai, kamar yadda take ta wannan ɗawainiyar da shi. Ya san in dai a wannan Duniyar ne ba shi da abin da zai biya ta. Duk da matsananciyar damuwar da ya kan shiga, da jin cewa ya zama silar nakasta rayuwarta, ta zama tana rayuwa ba tare da tunanin wani abu da take so ta cimma ba. Kullum tunaninta a kan sa ne kawai.
Tana ɗagowa suka haɗa ido, ta murguɗa masa baki, ta ci gaba da fifitar wutar gabanta.
Ya tako zuwa gaban murhun ya tsuguna.
"Dan Allah ka tashi, saboda numfashinka fa"
"Kawo na yanka miki salak ɗin"
"A'a kar ka yanke hannu"
Ya ce "Ki kawo zan iya" Ta tsuke fuska ta kalle shi ta ce "Saboda sauƙi ya samu, kana iya fitowa da kanka yanzu, shi ne za ka din ga damuna ko?"
Ya yi murmushi, ya zauna a gefe yana kallon ta, da ta ɗaga ido, sai su yi ido huɗu da shi, sai ya yi mata murmushi.
Su na cikin cin abinci, ya ce "Ki na kiran Ummi?"
"Ba na samun ta, ita ma ta kira ni wayar ba na ji. Uwani ta ce haka garin nan yake babu network, sai a yi kira fiye da sau goma ba ka samu mutum ba.
"Idan na ƙara jin sauƙi, zamu je mu gaishe ta, mu yi mata godiya"
Ta ce "Alhamdillah, lallai sauƙi ya samu."
Ya ce "Eh, ina jin hakan a jikina nima. Mu je waje na ɗan tattaka na ga gari"
Nana ta faɗaɗa murmushinta ta ce "Allah abin godiya, wallahi Sayyid da har na fara fitar da rai da kai, na karaya sosai wallahi" Cikin murna ta saka hijjabinta, suka fita. Su na tafe a hankali ta kalle shi ta ce "Gaskiya na yi mamaki, ashe da gaske magungunan sarkin Baka yana yi"
Ya tsuke fuska ya ce "Na gaji da jin zancen Sarkin Bakar nan"
Nana ma ta yamutsa fuska ta ce "Sayyid ka yi haƙuri, amma na yi farin cikin yadda maganin da na gani a gurinsa ya yi maka aiki. Ina yi masa fatan idan a kan daidai yake, Ubangiji Allah ya ƙarfefe shi ya dafa masa, ko dan saboda yadda yake taimakon mutane. Idan kuma a kan kuskure yake Ubangiji Allah ya ganar da shi, ya ba shi ikon tuba kafin lokaci ya ƙure masa."
Sayyid ya yi mata banza, suka ci gaba da takawa a hankali su na zagayawa.
Wani irin sanyi ne ya fara ratsa Nana, ganin Sayyid ya durfafi wata hanya, ta kuma kasa ce masa uffan, balle ta hana shi. Su na tunkarar gurin, ƙirjinta na bugawa da sauri da sauri.
Wata irin narkekiyar bishiyar kuka suka tarar a gurin mai ban tsoro. Yanayin yadda take ɗauke da wasu irin murɗaɗɗun rassa, da yadda murtuka-murtukan jijiyoyinta suka huda ƙasa suka mamaye gurin. Ga wani irin ƙaton kogo a jikinta, hakan ya nuna daɗewar da bishiyar ta yi da wanzuwa a gurin.
"Asma'u" ya kira sunanta kai tsaye. Ta kalle shi cikin matsanancin mamakin yadda ya kira sunanta na yanka kai tsaye.
"Ji nake yi kamar na san gurin nan"
Jiki a sanyaye Nana ta ce "Nima haka, amma ni dai na san ban taɓa zuwa gurin nan ba, amma ina jin kamar na san gurin, amma dai... Sai kuma ta yi shiru bayan da gurin ya gauraye da duhu aka yi wata irin walƙiyya, haske ya mamaye gurin. Tsohon nan ta gani a tsaye, riƙe da sandarsa ya zubo wa Nana idanunsa marasa kyan gani. Jikinta ne ya ɗau kyarma, ta ƙara rikicewa bayan ganin a hankali wasu halittu da take kyautata zaton ire-iren su Ƙaisar ne su na bayyana a bayansa.
Tsohon ya kalle ta, ya buɗe baki ya fara magana. "Ina sake yi miki barka da zuwa, garin da kakanin kakaninki su ka durƙusa suka haifo matsalar da har abada ba za ta daina bibiyar zuriyar su ba. Zan ci gaba da azabtar da rayuwarki, za ki ci gaba da biyan bashin nan, ko bayan ranki, muddin aka ci gaba da samun haihuwar masu irin tauraronki."
Yana rufe bakinsa, ɗaya daga cikinsu da Nana take kyautata zaton jininsin mace ce, saboda yanayin wani irin tsohon mayafi da ta yafa a kanta. Ta tunkaro Nana gadan-gadan.
Tana zuwa matar, ta hankaɗa Nana ƙasa, sauran suka rufu a kan Nana, su na zira hannunsu a mararta, su na ciro gudan jini.
"Ya hayyu ya ƙayyum ya Allah. Allah ka kawo mini ɗauki, Sayyid, Sayyid, Sayyid ka tashi" Ta yi maganar tana jijjiga Sayyid da yake kwance a gefen ta yana bacci.
Ya ja jikinsa ya tashi ya ce "Ma viee lafiya kuwa?"
"Sayyid marata ciwo take yi. Sayyid marata. Sayyid babyna. Ba na son na rasa jaririna a wannan karon, Dan Allah ka taimake ni"
Cikin rashin fahimta ya ce "Meyafaru ne?"
"Marata ce take ciwo, Sayyid ba na son cikina ya zube, ina son jaririna Sayyid ciwo marata take yi sosai" Ta yi maganar tana zubar da hawaye. Ya saka hannunsa a mararta, ta saka hannayenta ya dafe hannunsa tamkar hakan ne zai hana cikin zubewa.
Ya ce "Ki yi Addu'a" Kawai ta jinjina kai, amma Addu'a kam, ko ɗaya ba ta zo kanta ba, dan ta manta komai daga cikin kanta.
Cikin rauni Nana ta ce "Sayyid fitsari nake ji, ya matse ni"
Ya ce "To mu je ki yi"
Ta girgiza kai ta ce "A'a ba na son na je na ga jini ya zubo, cikin ne zai zube"
Ya ce "A'a ba za ki gani ba" . Ta miƙe ya kama hannunta, ya haska fitila har banɗaki, su na zuwa a tsorace ta yi fitsarin, sai dai tana yi sai ga jini. Wani irin kuka ta fashewa da Sayyid. Ta miƙe jikinta yana rawa.
Ya rungume ta ya ce "Ki yi haƙuri, kin ga dare ne, ki daina kuka. Kuma idan za ki yi ɓari, jinin da ki ke zubarwa ya fi wannan kin manta?"
"A'a idan jini ya fara zuba, shikenan ciki zai zube"
Ya ce "A'a, ba haka ba ne, ai bai zuba da yawa ba" Ya lallaɓa ta da ƙyar, ta gyara jikinta, ta ɗauraye jikinta, da banɗakin su ka koma ɗaki.
Karatun Alkur'ani ya kunna a waya, ya ajiye a gefen katifar da suke kai, kamar yadda ya ga tana yi, a duk lokacin da su ka shiga yanayi na tsoro.
Suka kwanta yana ɗan shafa ta, cikin sigar rarrashi.
A hankali ta ce "Sayyid"
"Na'am"
"Da gaske mun fita ɗazu ko?"
"Eh mun fita"
"Mun je can bayan gari, har ka ce mini kamar ka san gurin?"
"Eh haka aka yi, mun je"
Ta sake cewa "To daga nan meyafaru?"
"Faɗuwa ki ka yi, na riƙe ki muka dawo gida. Tun da muka dawo kuma ki ke bacci"
Ta yi shiru ba ta sake cewa komai ba, ta ƙara lafewa a jikinsa cikin tsoro. Yau ma kwana suka yi, tana gane-gane da jin abubuwa daban-daban masu razanarwa.
Wannan bafulatanar matar ce, ta ƙara zuwa ta tsaya a saitin tagat Nana tana kiran ta, a kan lallai sai ta fito ta ga yadda suke gudanar da bikin girka. Nana ta ƙara rintse idanunta tare da ƙanƙame Sayyid.
Da safe ta tashi da wani irin nauyin jiki, ga sanyi da ta kasa daina ji. Ta duba ta ga ba ta kuma ganin jinin nan ba. Ta yi wanka ta rama sallolinta, sai dai Sayyid bai tashi ba. Da ƙyar ta samu ya yi alwala ya yi salla.
Ta gaishe shi, amma bai yi magana ba sai kallonta da yake yi. Hakan ya sanya ta fuskanci maganar ta ɗauke.
Ta tambaye shi za ta fita, amma bai ko ɗaga kai ya kalle ta ba. Ta saka hijjabi ta fita ta bi 'yan matan gidan Uwani gona roron gyaɗa a gona.
Allah ya taimake ta, ta samo da yawa ta zo tsakar gida ta baje ta domin ta sha iska.
Ta ɗora musu Abinci, ta kammala ta fara dafa masa maganinsa, kawai ta ga ya fito daga cikin ɗakin. A zaton ta, ko banɗaki zai shiga, ta tashi da nufin kai masa ruwa, kawai ta ga ya nufi fita waje.
Da sauri ta bi shi tana faɗin "Sayyid ina za ka je ne haka?" Ya yi mata shiru yana ƙoƙarin buɗe ƙofar. Ta riƙo hannunsa, amma ya waiwayo fuskarsa a ɗaura kamar bai taɓa dariya ba, saka hannu ya hankaɗe ta, ta faɗi a gurin, ya saka kai ya fice daga gidan. Da gudu ta shiga ɗaki, ta ɗaukko hijjabi, ko takalmi ba ta saka ba, ta bi bayan sa. Ga yamma ta yi liƙis, hanya babu kowa, ta ga ya nufi hanyar inda wannan bishiyar ta kuka take.
"Sayyid dan Allah, dan Allah kar ka koma gurin nan. Me za ka je ka yi?" Sai dai tamkar ba mara lafiya ba, saboda yadda yake sauri.
Sai da ta ɗan haɗa da gudu, Saboda saurin da yake yi, amma ta ji gefen mararta ya ƙulle. Ta daure ta cim masa.
Babu tsammani ta furta "Bismillah wa hifzan min kulli shaiɗanin marid." Aya ta bakwai cikin suratul saffat, kamar yadda Malam Auwal ya taɓa cewa ta yawaita nanata ayar. Gaba ɗaya ta shafe a cikin kanta, sai da ta faɗo mata yanzu. Tana karanta ayar, ta riƙe hannunsa ya ja ya tsaya ya yi shiru ya sunkuyar da kai.
"Mu koma gida" ta yi maganar tana jan hannunsa, tamkar raƙumi da akala, ya bi ta suka koma gida. Allah ya taimake ta, babu wanda ya gan su har su ka isa gida. Ta rufe ƙofar.
Su ka shiga ɗaki, ta kunna fitila ta kalli Sayyid cikin damuwa ta ce "Sayyid me yasa ka fita? Me za ka je ka yi a wajen da?" Ya yi shiru ya sunkuyar da kansa ƙasa fuskarsa babu annuri a ciki.
Ba ta sake ce masa komai ba, ta fita banɗaki ta yi alwala, ta dawo ta yi salla, amma ta ga ba shi da niyyar tashi ya yi.
"Sayyid, ba ka yi salla ba fa" Nan ma bai kula ta ba, dan haka ba ta sake magana ba, ta zubo masa Abinci ta zo gaban sa ta ajiye. Ta tashi ta ninke hijjabinta, tana waiwayowa, ta ga ya kifar da Abincin ya tarwatse a tsakar ɗakin, yana wani irin huci.
"Sayyid wai meye haka ne? Idan ba ka cin abincin sai ka zubar mini a ƙasa?" Sai dai tana rufe baki, ya wulwula kwanon ya yi jifa da shi guri ɗaya. Ya miƙe ya fara fatali da kayan ɗakin. Take Nana ta fuskanci ba lafiya ba. Jiki a sanyaye ta rakuɓe tana kallon sa.
Tana tunanin yanzu kuma abin har ya kai ga haka? Ba ta yi yinƙurin hana shi ba, ya yi kaca-kaca da ɗakin, ya fita tsakar gida ya nemi guri ya kwanta a dandaryar ƙasa.
Inda ta yi wa Allah godiya ba su da maƙwabta, da kowa sai ya san abin da ya faru. Haka ta durƙusa ta hau aikin gyaran ɗakin, ta kintsa abin da za ta iya kintsawa. Ta dawo tsakar gida inda yake kwance. Ta durƙusa a kan sa, ta dafa shi ta ce "Tashi mu je ka kwanta a ɗaki, nan akwai sauro kuma ƙwari za su cije ka"
Da ƙyar ya tashi, suka koma ɗaki, ya nemi guri ya kwanta a ƙasa. Kawai Nana ta zauna ta zura masa ido, cikin matsananciyar damuwa, duba da yadda take maganin ƙaba amma kai na daɗa kumbura.
A haka dare ya tsala, ta gaji ta kwanta a gefen sa, zuciyarta fal da damuwa. Bacci na ƙoƙarin ɗaukar ta, ta ji tasowar guguwa ta buɗe idonta, ta gan su kwance a cikin sahara, ga yashin saharar na wani irin hanƙoro iska za ta mamaye su. Ta saka hannu ta rungume shi saboda guguwar saharar. Sautin tsohon nan ta ji yana wata irin dariya. Ji ta yi an hankaɗa ta, sai da ta wuntsula ɗakin gauraye da duhu, amma ta ga alamun Sayyid ne zaune a kan katifa shi ne ya hankaɗa ta. Ya tashi ya koma bakin ƙofa ya yi zamansa.
Da kyar ta sake lallaɓa shi, ya koma ya kwanta. Ita ba ta sake komawa bacci ba, ta yi alwala ta zauna tana tasbihi har aka yi sallar asuba. Sai dai fafur ya yi salla ya ƙi yi. Ya nemi guri ya zauna ƙyam yana kallon ta.
Ta dama masa kunu, ta soya fanke, ta zo ɗaki ta zauna a gaban sa. Ta ce "Ga kunu ka sha, amma dan Allah kar ka zubar Sayyid ka ji?" Ta yi maganar tana miƙa masa kofin kunun. Sai ya miƙo hannun hagu zai karɓa. Ta janye kofin ta ce "Hannun dama dai, wannan hannun za ka bani" Ta yi maganar tana nuna hannun damansa, amma bai miƙo mata ba, ya zura mata ido.
Ta kai hannu ta janyo hannun nasa, dan ta damƙa masa kofin kunun, amma ta ji hannun a ƙame ƙam. Ta sake ƙoƙarin janyowa, amma ta ji tamkar tana jan itace.
Ta kalli hannun sosai, sai ta ga shanyewa ya yi.
Gabanta ya yi wata irin mummunar faɗuwa, ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Sayyid me ya same ka haka? Me ya samu hannunka? Ya Allah!" Ta yi maganar tana kuma ƙoƙarin ganin ta miƙar da hannun nasa, amma hannun yana maƙale, kamar an tsotse shi.
Ya sunkuyar da kai ya yi shiru, fuskarsa ɗauke da damuwa. Ta aro jarumta, ta matsa daf da shi, ta ɗebo kunun ta kai bakinsa. Amma ya tsaya yana kallonta, bai buɗe bakinsa ba.
"Buɗe baninka na baka" Ta yi maganar tana ƙoƙarin danne hawayen da ke ƙoƙarin ƙwace mata.
A hankali ya buɗe bakin, sai ta ga shi ma bakin ya karkace, yawu na ƙoƙarin zubowa. Kawai ya rufe bakin hawaye ya fara