Showing 99001 words to 102000 words out of 122205 words

Chapter 34 - BUZU BOOK2 COMPLETE 2

18 Jan 2026

624

na kira gida ne, na ji halin da yarona yake ciki"

Balaraba ba ta bata amsa ba, ta ji Muryar Asal ta ce "Babu wannan damar, sai dai idan kina buƙata ki zo gurina ki karɓi wayar ki kira"
Nana ta ɗan yi shiru sai kuma ta girgiza kai ta ce "A'a ki bar shi na gode"

"Me yasa ki ka ce haka? Kina tunanin wani abu a ranki ne?"

"Bana tunanin komai, kawai dai na fasa ne"

Ta yi murmushi ta ce "Shikenan, ga saƙo can daga gidan Sultan, tukuicin aikin da ku ka yi na girki"

Balaraba ta risuna tana yi wa Asal magana da yarensu, Nana kuma ta cigaba da aikinta, tana sane ta cewa Asal ba ta so, dan ba ta gama gane ina Asal ɗin ta saka gaba ba, da kuma cikakkiyar manufarta a kanta ba. Tana tsoron ta yi amfani da wata dama da za ta samu ta cutar da ita.

Katafaren ɗakin bacci ne, mai ɗauke da kayan alatun more rayuwa irin na masu mulki.
Duhun dare ne, sai dai hasken fitilun ɗakin ya gauraye ko ina, kai ba ka ce dare ne ba.
Yana zaune a gefen gadon, tare da dattijon. Cikin kamala dattijon ya ce "Imam, ina ƙara yi maka gargaɗi da jan kunne a kan ka ƙara kula da kan ka. Kar ka ɗauka kowane murmushi ne na soyayya, wani murmushin na babu yadda aka iya da kai ne. Kar ka kuskura ka faɗi wani abu da zai rusa shirinmu, mun ɓoye abubuwa da dama a game da kai, duk abin da baka fahimta ba, ka tambaye ni, kar ka wani ya buƙaci sanin wani abu daga gare ka, ka sanar masa kawai jinya ka yi tsawon wannan lokacin.

"Abii"

"Na'am abin ƙaunata" Imam Hammad ya yi murmushi ya ce "Me ka ke ɓoye mini ne, akwai abubuwan da suka hargitse a rayuwata, tsawon wani lokaci na ɗauka ina jinya ba a hayyacina ba?"

"Ka na ji na? Haryanzu ba ka warke ba, ka na buƙatar hutu mussaman a ƙwaƙwalwarka, kar ka takurawa kanka da tunanin abubuwan da suka faru. Jita-jitar da ake yaɗawa a kan ka, da surutai daban-daban shi ne dalilin da ya sanya muka dawo da kai ƙasar nan, a shaida dai kana raye, cikin ƙoshin lafiya"

"Mahaukaci ne ni kenan? Tun da ina iya tuna yadda ciwon nawa ya fara, amma ban san yaya ya ƙare ba"

Sultan ya tsuke fuska ya ce "Ya ishe ka haka. Kar ka kuskura na ji labarin nan ya fita, waye ya ce kai mahaukaci ne? Larurar zuciya ce take damun ka, babu daɗi babu ƙari daga haka. Babu wata larurar hauka a tattare da kai".

"Amma Sultan ko zaka saka na ɓoye wa duniya, yakamata na san matsayin lafiyata...

"Hammad!" Tilas ya ja bakinsa ya yi shiru, ganin yadda ya fusata Sultan ɗin.

*****

Tun da garin Allah ya waye, Nana take jin faɗuwar gaba da matsananciyar fargaba, ga sanyin da take jin yana ratasa ta, ta san ba na lafiya ne kawai ba. Dan haka ta ɗaura alwala take ta addu'a.
Bayan fitowarta ta cika da mamakin ganin yadda ma'aikatan gidan, suke ta aiki tuƙuru suke gyara gidan duk da ko ina a gyare yake.
Ko ta ina ƙamshin turaruka ne ke tashi daban-daban. Har sun so su yi yawa ma.
Ɓangaren da take aiki, sai azalzalarsu ake yi, ta fahimci dai wani baƙo ne mai muhimmanci zai sauka a gidan.
Har mamaki take yi yadda suke ba wa abinci muhimmanci, baƙo ɗaya sai a saka a yi masa abinci biyar, kuma duk da an san ba iya cinyewa zai yi ba.

Ta fito kenan ta ci karo da Asal, ta sanya zani da doguwar riga na shadda baƙar shadda, kanta babu ɗan kwali, hannayenta da yatsunta duk zobunan gwal ne, uwa uba wata irin sarƙa da ta saka ta zinari tun daga wuyanta har cikinta. Gashinta ya sha ado, ta sake shi har kafaɗarta, shi ma ta sanya masa wata siririyar sarƙa da ta kwanto har goshinta.
Duk hassadar mai hassada babu yadda za a yi ka kalle ta ka kushe ta, jawur da ita a cikin baƙar shaddar sai ta haska shaddar.

Ita dai Nana tun da ta zo gidan, ba ta taɓa ganin Asal da miji ko 'yan uwa ba, sai tarkacen ƙawayenta, su ma a wancan gidan ne, wannan gidan ba sa biyo ta su zo. Kuma duk abin nan Nana ba ta taɓa bin diddigi ta ji wace ce Asal ba, me yasa kuma take rayuwa a gidan daga ita sai masu yi mata hidima ba.

Da daddare Nana ta ji su Balaraba su na yare, su na faɗin sunan Imam, lokaci lokaci su na haɗa wa da Hausa, sai dai ta manta a inda ta taɓa jin Imam ɗin.

Babban abin da ya ɗaurewa Imam kai, bai wuce yadda a faransa yake jin sa garau, ba shi da wata damuwa ko wani ciwo da yake ji ba. Amma tun da ya sanya ƙafarsa a Agadez tsawon kwanaki huɗu, ko sau ɗaya zuciyarsa ba ta saurara da bugun da take yi cikin sauri babu ƙaƙƙautawa ba.

Nana na ta kai komo a kitchen, ta kammala duk wani aiki da ya shafe ta, tana shirin tafiya ta je ta kwanta. Balaraba ta ce "Saurin me ki ke yi ne Nana?"

"Ina son na je na yi wanka na kwanta ne"

"Ki je ki yi wankan, nan da mintuna talatin za ki kai wa Gimbiya Asal bunu da madara sashinta"

Har Nana za ta yi magana, dan ba ta shiga sashin Asal sai sau ɗaya, ta taɓa zuwa idan sun yi girki akwai waɗanda suke kaɗai suke iya zuwa sashen su kai. Ta fasa maganar ta ce "To"

A gurguje Nana ta kintsa, ta koma ta ɗauki kayan za ta yi gaba, Balaraba ta ce "Ai ba sashinta za a kai ba, Ramata raka ta"

Ramata ta kalli Nana ta yi mata kallon banza, ta ɗan kwaɓe baki sannan ta yi gaba Nana ta bi bayanta.
Duk yadda Nana ta so sarrafa kanta ta kasa, ta ɗaga kai ta din ga kallon ƙawataccen gurin tare da jinjina yadda masu gidan suka ƙware a iya almubazzaranci. Dan ba za ta kira shi ado ba kawai sai dai almubazzaranci.

Tana saka ƙafarta a cikin falon, ta ji tamkar an jona mata shocking, saboda rawar da jikinta ya yi, sai da farantin hannunta ma ya girgiza tamkar zai ɓare. Ramata ta kalle ta, ta yi tsaki kawai.
Nana ta ajiye kayan a hankali a kan carfet ɗin ɗakin.
Bayan ta ajiye ta yi taku huɗu zuwa biyar, ta ji yadda adadin sanyin da take ji yana ƙara yawa. Ta sauke idanunta a kan ƙaton frame da hotonsa a jiki. Danƙarewa ta yi a guri ɗaya, ta kasa motsa ko da ƙafarta.
Taku ta fara ji a bayanta, ana tahowa, muryar Asal ta ji tana magana da faransanci cikin shagwaɓa.
Ɗan ja ya yi ya tsaya, jin yadda jikinsa ya yi wata girgiza.

"Lafiya dai ko?"

Ya jinjina mata kai alamar eh.

"Amm me ku ke yi a tsaye a gurin nan ne?"

Ramata ta ce "Abinci muka kawo"

"Waye ya yi?"

Ta nuna Nana da ba ta juyo ba.

"Zo" ta kira Nana sai dai Nanan ta ƙame ba ta juyo ba. A wulaƙance Ramata ta taɓa ta ta ce "Ana yi miki magana"
"Tana ji na rainin hankalin za ta yi mini"
Sannu a hankali Nana ta juyo, idonsa na kan wayar hannunsa.
Yanzu ta tabattar da mafarki ta yi ba, Sayyid ta gani, sai dai ganinsa bai razana ta ya kiɗimata ba, kamar yadda alamu suka nuna Asal matarsa ce ba.
Ta sunkuyar da kanta ƙasa, tana jan ƙafafuwanta a hankali.

"Me ya same ki ne?"

Ta girgiza kai alamar ba komai.

"Ki yi mini magana kina girgiza kai kawai"

"Ba ni da lafiya"

Asal ta ja tsaki ta ce "Je ki kar ki ɓata mini rai"

Ta zuba masa shayin a kofi, ta zuba masa madara, ya ɗauka a hankali ya kai bakinsa yana sha.

Nana kuwa a ɗakinta, gaba ɗaya ta burkice, tamkar za ta yi hauka ta ce "Dama abin da ka ke gargaɗina a kai kenan Ƙaisar? Sayyid me yasa za ka yi mini haka, dama ka na da wata matar ka aure ni? Yanzu ka na nufin ka manta ni, Sayyid anya alƙawari ya ce haka? Na haƙura zan ɗauki ɗa na na koma gida, ganinka da wata kawai ya isa ya yi ajalina. Wataƙila alhakin iyayena ne ma da na taho ba da izininsu ba. Yadda ka ke a cikin daular nan, yaya za a yi na ce ina da alaƙa da kai ma a yarda da ni?" Ka ce Ruhina da naka su na rayuwa a tare, kowannenmu yana ɗauke da ruhin ɗan uwansa, ni na yi dakon soyayyarka ashe ka na da matar da ta fi ni komai" Ta yi maganar cikin matsanancin kuka tamkar za ta fita daga hayyacinta.

Yana tsaye yana jin yadda ruwan yake ratsa shi daga cikin gashin kansa zuwa jikinsa.
Wani irin zafi yake ji a cikin ƙwaƙwalwarsa, tamkar kansa zai tarwatse.
Karo biyu yana jin jikinsa ya yi girgiza.
Ya yi wankan ya lulluɓo jikinsa da towel.
Asal ta sha kwalliya cikin baƙaƙen kaya na bacci.
Ta nufo shi tana rangwaɗa, ta cire towel ɗin da ya lulluɓa da shi. Ya ɗan lumshe idanunsa saboda ƙamshin turaren da Asal take yi mai jan hankali.
Ta shige jikinsa ta rungume shi, ta ce "Na yi kewarka sosai Imam"
"Nima ina jin kewar abin da ban san mene ba, bayan kewarki da na yi"

"Akwai abin da ya fi ni muhimmanci dama, da har ka ke kewarsa fiye da ni?"

"A'a ban ma san mene ba, kawai dai ina jin akwai wani abu da ba daidai ba"

Ya yi maganar yana shafa gefen wuyanta, yana son tambayarta wace ce yarinyar nan, amma ya haɗiye ya fasa.
Ya fara ƙoƙarin sumbatar ta, sai dai ya ja da baya da sauri yana dafe kansa, da yake jin wani sauti mara daɗin ji a cikin sa.

"Imam jikin ne dai?"

Bai yi magana ba, ya hau kan gadon ya kwanta ya lumshe idanunsa.

Washegari da safe, idanun Nana sun kumbura suntum, saboda ba ta rintsa ba ko kaɗan.
Ta saba da wuri take tashi, ta fara gudanar da aikinta, amma sai da aka zo aka kira ta, ta ce ba za ta yi aikin ba.

Bayan mintuna talatin sai ga Asal a ɗakin, ta kalli Nana a wulaƙance cikin isa da gadara ta ce "Ki ka ce ba za ki yi aiki ba yau? Saboda gidanki ne ko zaman kan ki ki ke yi a gidan? An kai wa Imam shayi ya ƙi sha ya ce ba irin na jiya ba ne"

"Eh ba zan yi girki ba, kuma barin gidan nan zan yi, na gaji da wannan aikin, zan je na ga yarona"

Asal ta yi dariya ta ce "Ai kuma ƙarya ki ke yi. Na ɗaukko ki gidan nan saboda nesanta mijin da waɗanann munafukan hadiman, na kawo bare da baki san komai a kan harkar gidan mulki ba. Kuma ba kya cikin kalar matan da za su iya ɗaukar hankalinsa. Dan haka na kawo ki ne dan ki din ga kula da abin da Imam zai ci aikin da ki ka zo yi gidan nan kenan.
Nana ta yi wa Asal wani irin kallo mai cike da tsana, ji take tamkar ta kama Asal ta yi ta jibgarta har sai ta ji ta huce.

"Gimbiya Asal, ai an bar kari tun ran tubani. Ba zan yi girki ba sai dai yunwa ta kashe Imam ɗin, ke da yake aure idan ba za ki girka masa ba, to kar Allah ya sa ci, sai na bar gidan nan ba zan zauna ba" Ta yi maganar cikin ɗaga murya da zazzaro ido.

Asal ta yi taku biyu, ta hankaɗa Nana baya ta ce "Ki kiyaye harshenki a kan abin da zai din ga fitowa daga bakinki, a kan mijina. Biyan buƙatata ce kawai ta sanya nake ƙyale ki, ki daina ƙoƙarin ƙetare iyaka. Tafiya kuma ga hanya nan maza ki tafi mu gani, idan kina tunanin da ka na kawo ki gidan nan na ajiye"

Ayshercool
08081012143
74

Wata irin tafasa zuciyar Nana ta din ga yi, ta din ga jin tamkar za ta tsaga ƙirjinta ta fito.
Asal ta yi wani shu'umin murmushi ta ce "Ko za ki dake ni ne? Na ga kina ta huci tamkar macijiya. Sannan ina mai ƙara jaddada miki, muddin mijina ya ci wani abu da ya samar masa da matsala a dalilin abincinki da rayuwarki za ki biya. Babu tsautsayi babu ƙaddara a gidan nan. Dan haka sai ki tattara dukkanin nutsuwarki ki san abin da ya kamace ki.
Sannan babu ruwanki da yi masa magana, ko yi masa shishshigi, ki dafa abinci ki kai sashensa kawai, babu wanda yake da damar zuwa sashen kai tsaye, ke kawai ki ke da wannan damar a cikin bayin gidan nan, dan haka ina ƙara gargaɗinki a kan ki iya kan ki a zaman gidan nan"

Kalmar Bayin da Asal ta faɗa, sai da Nana ta ji kamar ta fashe. A gidan uban wa ta zama baiwarta. Za ta yi magana ta ji tamkar an saka abu a danne mata maƙogwaronta, ta kasa magana.
Tana ji tana gani Asal ta gama caɓa mata baƙaƙen maganganu, ta fice.
Nana ta fashe da wani irin matsanancin kuka, ta rasa wani tunani ma za ta yi, kanta ya kulle ta zauna tana ci gaba da kuka mai sauti da ratsa zuciya. Ta kasa samun sukunin da za ta yi tunanin mafita ma.

Asal na komawa sashen Imam, ta tarar da shi ya shirya tsaf da alamar fita zai yi.
"Imam, fita kuma zaka yi?" Ya jinjina mata kai.

"To ai ba ka karya ba, kuma mu ɗauki tsawon wannan lokacin ba ma tare baka nan, kuma yanzu ka ce fita za ka yi?"

Ya ci gaba da ƙoƙarin fita, amma ta tare shi.
"Haba Imam, ko kewata ba ka yi ba? Ba ka yi farin ciki da ganina ba ne? ka ke shirin ficewa ka bar ni?"

Ya tsaya yana ƙarewa fuskarta kallo ya yi murmushin gefen baki ya ce "Abincin ne ban ji daɗin sa kamar na jiya ba. Sannan Gimbiya Bilkisu zan je na gaisar".

Noƙe masa kafa ta yi tana riƙe rigarsa.
Ya ajiye agogonsa ya nemi guri ya zauna, hakan ya sanya ita ma ta zauna tana murmushi.

Nana kuwa tana tsaka da kuka ta ji an dafa ta, ta ɗaga kanta a hankali ta ganta a ɗakin karatun Ƙaisar.
Sai dai wannan karon tsawonsa daidai da ita, ya zauna sosai ya fuskance ta.

Ta sunkuyar da kanta hawaye na ci gaba da kwararowa daga cikin idanunta.

"Uwar gijiyata" Nana ta ɗaga idanunta a hankali ta dube shi, ta mayar da kanta ta sunkuyar.

"Bai kamata ki nuna karaya a wannan gaɓar ba, duk da ina jin zafin yadda ki ka yi burus da ni, da buƙatata da gargaɗin da na din ga yi miki a baya, amma wannan kamar ita ce gaɓa ta ƙarshe mai kuma matuƙar wahala, idan ki ka sare a yanzu wahalar da ki ka yi tuƙuru a baya za ta tashi a banza kenan.
Ba ki da tabbacin ya gane ki? Ko kuma bai gane ki ba, sai dai komai ya zo da sauƙi. Ita wannan matar sauƙaƙa miki aiki ta yi, tun da ta kawo ki kusa da shi, ta kawo ki har inda yake, godiya ma yakamata ki yi mata.
Ki kawar da kai daga kan duk wani abu na wulaƙanci da za ta yi miki a yanzu, a ƙarshe ke ce da riba, ki fara tantance halin da yake ciki, kafin ki ɗauki mataki na ƙarshe"

Cikin kuka Nana ta ce "Ƙaisar na karaya, na sare ba zan iya ba, wa zai yarda da ni matarsa ce, banbancim da ke tsakanina da shi tazara ce mai nisan gaske.
Ba na buƙatar ya gane ni, gida zan koma na nemi gafarar iyayena na kula da yarona"

"Ba za ki koma gida yanzu ba, yaronki yana hannu na gari a yanzu duk ban san gaba ba. Na daɗe ban ga bil'adama mai juriya sadaukarwa da tsantsar juriya kamar ki ba. Imaninki da Allah ina da tabbacin ba zaki wulaƙanta ba kamar yadda ki ke yawan faɗa mini. Kar ki karaya ki tsaya ki karɓi abin da yake naki ne, idan ki ka karaya ki ka tafi kin yi biyu babu, wahalarki kuma ta tashi a banza"
Da wannan maganganun ta buɗe idonta, tana sauke numfashi a hankali.
Daki-daki ta din ga jin maganganun Ƙaisar na dawo mata. Ta yi shiru tana nazari, ta tashi zaune a hankali.
"Abin da yake nawa? Eh Ƙaisar, Sayyid nawa ne, bai kamata na karaya a wannan gaɓar ba" ta furta idanunta na sake cika da hawaye bayan tuna Asal matarsa ce.
Ta din ga tunanin suwaye suka tafi da shi lokacin suna Buda? Ko dai da kansa ya gudu ya bar ta? Ina su Habu, ta gan shi shikaɗai? Da gaske taɓin hankali ya yi a baya ya manta wace ce ita, ko kuwa dai raina mata hankali ya yi, ko kuwa dai duk wannan abin ba Sayyid ɗin ta ba ne?"
Wata zuciyar ta ce "Haba dai, ko na makance na shafa na san Sayyid, ko za a ajiye irin sa dubu zan fitar da Sayyid a cikin su. Ina zan samu amsoshin tambayoyina ne?" Ta yi maganar tana dafe kanta da yake yi mata wani irin ciwo.

Ƙaisar kuwa yana sakin Nana, ɗakin karatunsa ya gauraye da sautin dariyar Giyaz, dariya ta rashin imani mara daɗin ji.

Ƙaisar ya waiwaya, yana kallon inda Giyaz yake shawagi a sama yana ƙyaƙyata dariyar, hakan ya tabattar masa da Giyaz ya gama jinyar abin da Nana ta yi masa.
Ya yi wata irin girgiza ya bayyana a gaban Ƙaisar, ya din ga zagaye Ƙaisar yana ci gaba da dariyar cike da mugunta, daga bisani ya tsahirta da dariyar ya ce "'yan samari, yaushe imaninka ya ƙaru haka, har ka ke yi wa uwar gijiyar da ba ta ɗauke a bakin komai ba, nasiha da ba ta shawara?"

Ƙaisar ya tsuke fuska ya ce "Ban yi maka iyaka da zuwa inda nake ba?"

Giyaz ya ce "Daɗin abin har gori ta yi maka a kan butulcin ka yi mini, amma da yake ba zuciya ce da kai ba, ka na liƙe da ita. To bari na gaya maka abin da ba ka sani ba, ni ne na sake juye tunaninsa na shafe masa wancan tunanin, yadda abin zai yi mata ciwo, dama na gaya mata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login