Showing 39001 words to 42000 words out of 122205 words
ta Adda Saude ba ta ɗaga ba. Ta nemi guri ta zauna, ta ci gaba da kiran wayar Adda Saude da ita kaɗai take shiga.
Sai dai still ba a ɗaga wayar, ga shi ba ta san daga garin, ina ce unguwar da za ta nufa ba.
Ta samu guri ta yi alwala, ta ciro sallaya a kayanta, ta shimfiɗa ta yi sallar azahar.
Bayan Azahar sosai, Adda Saude ta kira wayar Nana.
Nana ta ɗaga tare da yin sallama. Ta amsa mata ta ce "Nana yi haƙuri, caji na kai wayar ne aka kunna mini, ya ki ke ya gida?"
"Lafiya kalau Adda, kin ganni na zo Bauchi ne na sauka, sai dai ban san sunan unguwar da Mama take ba"
"Ke haba dai, da gaske ki na Bauchi Nana?"
"Eh Adda, na sauka ma tun ɗazu"
"Subhanallah, ai ba ki gaya mini za ki zo ba, da tuni an shirya karɓar ki, ban sani ba an bar ki ki na jira, dan Allah ki yi haƙuri yanzu ki na daidai ina, na zo na tafi da ke?"
Nana ta ce "Kar ki wahalar da kan ki dan Allah, ina garin ma, sunan Unguwar za ki gaya mini" Sai da Adda Saude ta ɗan ji dumm, amma ta maze ta cewa Nana ta samu abin hawa, ta haɗa ta da mai abin hawan ta yi mata kwatance.
Nana ta ce "To" ta samu abin hawa, ta haɗa su ta kwatanta masa, sannan ta hau.
Nana ba ta isa gidan da Mamanta take ba, sai ana kiraye-kirayen sallar la'asar.
Mama na tsakar gida tana ta fama da yara, kawai ta ji sallamar Nana. Ta ɗago da hanzari, sai dai ta kasa amsa sallamar ta nufi Nana da sauri suka rungume juna su na kuka.
Ta ɗago Nana ta ce "Nana ba ki yi fushi da ni ba?"
Nana ta girgiza kai ta ce "Ban yi ba"
Ta ja hannun Nana zuwa ɗaki, ta saka yaran su shigo mata da ƙatuwar jakarta.
"Sannu da zuwa, tare ku ke da mai gidan naki ne?" Nana ta sunkuyar da kai jikinta a sanyaye ta girgiza kai alamar a'a.
"To yana ina shi?" Nana ta yi shiru.
Cikin tashin hankali Mama ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Nana ba dai auren naki ne ya mutu ba?" Nan ma ta girgiza kai hawaye na bin fuskarta.
"Shikenan, yanzu nutsu. Bari na ɗora miki ruwa ki yi wanka, sai ki yi salla" Nana tana iya ganin tsantsar farinciki a kwance a fuskar mahaifiyarta. Ƙannenta suka kewaye ta, Nana ta din ga kallon su cike da so da ƙauna. Har gara Walida ta ɗan santa sauran kuwa duk ba su san Nana ba.
Ruwa mai ɗumi ta haɗa wa Nana, ta yi wanka, ta yi sallar la'asar.
Ta zubo wa Nana lafiyayyen Abinci, duk da yadda ranta ya biya a kan Abincin, amma ta kasa sakin jiki ta ci.
Mama ta din ga kaiwa tana komowa, tana ta ɗawainiya da Nana tamkar ta goya ta, sai ta ji ina ma tuntuni ta samu irin wannan kulawar ta uwa.
"Nana ina Imrana kuwa, ya daina zuwa gaba ɗaya"
Nana ta ce "Lagos yake tafiya neman kuɗi"
Ta yi ajiyar zuciya ta ce "Ai shikenan, ya aka yi ina mijin naki ne? Me ya faru?"
"Nemansa na yi na rasa"
Cikin rashin fahimta ta ce "Kamar yaya?"
Nana tana kuka ta yi mata bayani. Cikin mamaki ta ce "To ina 'yan uwansa? A ina yake a Nijar ɗin?" Sai a lokacin ta fayyace wa Maman komai, game da auren zuwa ɓatan sa.
"Nana, me yasa baki neme ni kin gaya mini ba? Yanzu duk wannan abin yake faruwa amma idan muka yi waya sai ki ce mini komai lafiya ƙalau? Ni kaina nan kina raina, ina ta fafutuka na ga yadda zan yi na zo na gan ki. Ba ki kyauta ba Nana, komai lalacewata, ni mahaifiyarki ce, yakamata a ce kin sanar da ni.
Yanzu dai ki zauna a nan, mu ga abin da Allah zai yi, kafin ki haihu mu gani ko Allah zai sanya a ga mijin naki. Amma na yi mamaki matuƙa da mahaifinki ya aura miki wanda bai san usulinsa ba? Yanzu ƙiyayyar da yake yi minin har ta kai haka?
Ko yana jin haushina amma ai ke 'yar sa ce, bai cancanci ya yi miki haka ba, amma babu komai.
Nana abin da nake so da ke, daga yanzu duk abin da ya faru Nana, ko ba zan yi miki komai ba, ki sanar da ni, ki bani dama na taka rawa ta ta uwa a rayuwar ki ko yaya ne" Ta yi maganar tana riƙe hannun Nana.
Sallamarsa ce ta tilastawa Nana haɗiye abin da take shirin furtawa, cike da tsoro.
Ba ita ba hatta Maijidda, sai da zuciyarta ta buga da ƙarfi cike da tsoro.
AYSHERCOOL
08081012143
61
Har zai gifta, zai shiga ɗaki ya hango Nana, cikin rawar baki, Nana ta gaishe shi, ya amsa mata sama-sama ya wuce, dan kallo ɗaya ya yi mata, ya gane ta.
Jiki a sanyaye Maijidda ta tashi ta bi shi ɗaki, tana ɗan sinne kai, tana jiran ta ji me zai ce, amma bai ce komai ba. Ta kawo masa Abinci, tana jiran ta ji me zai ce, ga hankalinta a kan Nana, tana so ta je ta yi hira da 'yar ta, su yi hira ta ji ɗuminta, amma ta haƙura.
Nana ma na ta gaban ne yake faɗuwa, tana tsoron abin da zai ce, saboda ba ta manta karan battarsu.
Haka dai a ɗarare suke hira da yaran gidan.
Maijidda na ta son yi masa magana, amma ta kasa.
Ya gama cin abincin ya fita, ba tare da ya ce komai ba.
Yana fita ta koma gurin Nana, suka ci gaba da hira, Nana ta kwanta a kan cinyar Mamanta, tana jin wani irin farinciki yana ratsa ta.
"Kin fara zuwa awo ne Nana?"
Wata irin kunya ta kama Nana, ta ɗan sinne kai ta girgiza mata kai. "Gaskiya yakamata, wata nawa ne cikin? Mu je a yi awo a duba, mu ga abin da zamu fara ajiyewa. Mu jira mu ga ikon Allah, idan an ga mijin naki shikenan, idan ba a gan shi ba kuma, ma san abin yi" Nana dai ta yi shiru, sai kuma ta ce "Mama ki yi mini addu'a, ki ce Allah ya bayyana shi cikin aminci"
Mama ta yi dariya, ta ce "Lallai kam, to shikenan, Ubangiji Allah ya bayyana mini sirikina cikin aminci"
Nana ta yi murmushi, dan kunya ce ta kama ta daga baya, da tuna katoɓarar da ta yi.
Da daddare Mai Jidda ta yi wa Nana shimfiɗa, ta saka nata net. Sannan ta tafi nata ɗakin gurin mijinta, har za su kwanta, Mai Jidda ta dubi Iliyasu, jiki a sanyaye cikin ladabi ta ce "Baban Walida, na ga ka dawo ka ga Nana a gidan nan, ba ka ce komai ba"
Ya dube ta ya ce "To me ki ke so na ce?"
"Ahh dama kar ka ce ban gaya maka ba ne, dama ta ɗan zo ta zauna da ni ne, duba da yadda...
"Kin ga dakata, na ɗaga miki ƙafa ne na yi shiru, na ga gudun ruwanki, kar ta wuce mini gobe a gida, ta wuce ta koma inda ta fito"
"Dan Allah ka yi haƙuri Baban Walida, Nana ta samu matsala a aurenta ne, dan Allah ka yi haƙuri ba za ta daɗe ba, amma dan Allah kar ka ce ta tafi yanzu. Ni ko ruwan gidanka ka ce ba za ta sha ba, na amince dan Allah"
"Ke Maijidda, bari ki ji na gaya miki, wallahi sai yarinyar nan ta bar gidan nan"
Ya nemi guri ya yi kwanciyar sa, takaici ya ishi Maijidda.
Nana kuwa tana jiyo hayaniyar su sama-sama, abin ya tsaye mata ta kasa bacci sam. Sai juye-juye, ga mararta ta ƙulle duk jikinta ma ciwo yake yi mata.
****
Kwance yake a kan gadon Asibiti, jikinsa babu riga, sai dogon wando an rufe iya ƙafafuwansa da koren yadi. Ƙirjinsa kuma an manna masa abin ECG. Sai gashin sa a rufe da hular Asibiti. Na'urorin gefen gadonsa sai sauti suke fitarwa.
Dattijo ne a tsaye a kansa, dogo fari tas, ya ɗaura hirami a iya kansa, ga gemunsa dogo duk farin gashin furfura a jiki.
Ya kalli mutumin da yake tsaye ya ce "médecin (Likita) yanzu mene ne abin yi?"
"Eh, gaskiya za a yi masa wannan allurar ne kamar yadda na yi maka bayani, idan kuma ba haka ba, gaskiya sai dai a saka masa na'ura a zuciyarsa wadda za ta din ga taimakawa bugun zuciyarsa"
Na kusa da Dattijon mai sanye da shuɗiyar shadda, da babbar riga, kansa ya yi naɗi da baƙin rawani ya ce "Ka gani ko Sultan, Allah kaɗai ya san abin da suka yi masa a Nigeria. Dole yaron nan ya ɗanɗana kuɗarsa a ci gaba da tsare shi, har sai ya yi bayanin abin da ya yi masa a Nigeria, da aka neme shi aka rasa tsawon wannan lokacin. Su kan su sauran da aka kama su tare, dole a killace su a guri ɗaya, haryanzu ban bari an sake su ba, saboda idan maganar nan ta fasu akwai matsala"
Sultan ya numfasa cikin damuwa ya ce "Ni wannan bai dame ni ba, na bar ragamar komai a hannunka, ni lafiyar sa ce a gabana yanzu. Likita ku yi duk abin da ya dace kawai. Lafiyarsa ce damuwata a halin yanzu"
Likitan ya ce "In sha Allah" Dattijon ya saka hannunsa a cikin na mara lafiyan,yana kallonsa cikin matsananciyar damuwa. Kamar mafarki ya ga yana motsawa a hankali, sai ya ƙara tattara hankalinsa a kansa yana kiran sunansa.
Wata irin miƙa ya yi, yana ƙoƙarin buɗe idanunsa, amma ya ji tamkar an cika masa idanun nasa da barkono.
"Imam..
Hannunsa ya ɗora a ka yayi wata irin kururuwa, jin yadda naman jikinsa yake yi masa wata irin azaba, tamkar ana cizgar naman jikin nasa. Ga wani irin zafi da raɗaɗi da yake ji kamar yana cikin wuta.
"Zafi! Wayyo wuta Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wuta zafi jikina"
Kansa suka yi gaba ɗaya cikin tashin hankali, su na ƙoƙarin rirriƙe shi, amma ya watsar da su ya diro daga kan gadon, yana girgiza kansa da yake yi masa wata irin azaba tamkar zai tarwatse. Tunaninsa ne ya hargitse gaba ɗaya, ƙwaƙwalwarsa na ta kokawar ƙwato wani abu daga cikin memories ɗin sa, amma abu ya kacame, gaba ɗaya tunaninsa ya hargitse, ya kasa tantance komai. Fizge-fizge ya din ga yi yana kururuwa jikinsa na rawa. Dattijon nan cikin jarumta da ƙarfin hali, ya bi shi da sauri ya damƙe shi iya ƙarfinsa.
Kokawa suka din ga yi, a rikice likita da ɗaya mutumin suka yo kansu, likitan ya haɗa wata allura ya yi masa. Jikinsa ya saki a hankali bacci ya ɗauke shi. Kan gadon suka mayar da shi suka kwantar. Ɗaya mutumin ya kalli likitan ya ce "Ka na ji na?" Likitan ya jinjina kai cikin nutsuwa.
"Ka san dai waye wannan, kuma ka san matsayinsa da girmansa ko?" Ya yi maganar yana nuna masa mara lafiyan.
Ya jinjina kai ya ce "Na sani"
"To muddin mu ka ji maganar abin nan da ya yi, ya fita waje, to ba wani ba ne ba kai ne, dole ka yi shiru da bakinka, kare sirrinsa wajibi ne a kan duk wani wanda yake yankin nan, idan kuma aka samu akasi ka furta wani abu, da rayuwarka za ka biya"
Likitan yana tsuma ya ce "In sha Allah ba zan faɗa ba"
****
Da safe mijin Maijidda ya shura takalmansa ya fice, bayan sun gama jayayya da ita, tana ta roƙonsa tana yi masa magiya. Gaba ɗaya Nana ta ji dana sanin zuwa Bauchi da ta yi.
Babban abin da ya bata mamaki, ƙatuwar kaza Maman ta saka aka yanka, ta gyare ta tsaf, ta yi wa Nana farfesunta, aka sayo mata ƙaton buredi ta haɗa mata shayi.
"Mama daga zuwana na ɗora miki ɗawainiya, ba ma na iya cin Abincin ni"
"Ɗawainiyar ƙaniyarki, da can na yi miki ne Nana? Dan Allah ki daure ki mayar da hankali ki ci ki ƙoshi, idan kuma ki na son cin wani abin, ki gaya mini sai na dafa miki"
"A'a ba na son cin komai, amma ki zo mu ci tare da su Walida"
Maijidda ta ce "A'a, babu wanda zai ci, da rana ma ci Abincin tare, wannan dai na ki ne" Haka ta takura Nana, ta karya.
Nana ta fito da nufin, ta kama musu ayyukan gida, amma Mama ta hana, ta dafa mata ruwa ta yi wanka. Ta fito ta tarar Mama tana wanke kayan da ta cire.
"Haba Mama dan Allah ki bari na wanke da kaina, ya za ki din ga yi mini wanki?"
"Tafi ɗaki ki je ki zauna ki huta, ga lemon fata can da rake, ki ɗan sha saboda ɗanɗanon bakinki. Akwai riɗi ma mai gishiri da mai suga, idan da wanda ki ke so" kawai Nana ta tsaya tana kallon ta, tana murmushi.
Maijidda ta ce "Ya dai?"
Ta girgiza kai ta ce "Ba komai Mama, na gode sosai"
Nana ta shirya ta canza kaya, Khadija da take 'yar autar Mama, Nana ta kama ta tana tsefe mata kai. Ta ɗauki wayar Nana tana kallon hotuna. Sai ta buɗe wani video da Nana ta yi wa Sayyid, ta yi masa kitso sai hararta yake yi tana cewa "Ka ga yadda ka yi kyau 'yan matana, yi murmushi mana" ya ɗago kansa ya hargitse idanunsa. Nana tana dariya. Sai da tsigar jikin Nana ta tashi, gani take kamar ta shiga cikin wayar ta ga Sayyid ɗin ta.
"Anty Waye wannan?"
"Mijina ne" ta ba ta amsa tana murmushi.
"Ya na gan shi da kitso, kuma fari?"
Nana ta yi dariya ta ce "Ni kuma baƙa ko?"
"Eh, kuma ba kyau maza su yi kitso fa"
"Wai in ji wa? Ba ki ga gashin nasa ne da yawa ba?"
Khadijah ta ce "Eh, to yana ina yanzu?"
"Ya je unguwa, zai dawo ya ɗauke ni mu tafi"
"To ki nuna mini shi idan ya zo" Nana ta ce "To in sha Allah"
Mama ta ce "Ke Khadijah, tashi ki bar ta ta huta, Nana kwanta ki huta, ki rabu da surutun yarinyar nan"
Khadijah ta tashi tana zumɓura baki, Nana ta ɗan kashingiɗa kawai wani abu mai kama da bacci ya yi awon gaba da ita, kasa tantance ma me take yi ta yi, bacci ne ko kuma ido biyu.
"Ma Vie" ta ji muryarsa a kunnenta. A razane ta waiwaya cikin damuwa. A tsakiyar sahara ta hange shi ta ce "Sayyid"
Ganinsa ta yi a tsaye a kanta, kayan jikinsa duk a yayyage, ya yi baƙi kamar ya ƙone, gashin kansa a hargitse jikinsa sai fitar da hayaƙi yake, ya ce "Ma Vie sun mayar da ni inda za su kashe ni, dan Allah ki zo kar su kashe miki ni." Yayi maganar yana hawaye.
Ta tashi cikin tashin hankali ta ce "Suwaye? Kuma a ina suke?"
"Dan Allah ki zo, ni ban san su ba, amma na san mutuwa zan yi, dan Allah Husnah ki zo gurina, za su kashe ni. Idan kuma sun kashe ni, ki kular mini da ɗa na"
"Sayyid, dan Allah kar ka tafi ka bar ni, dan Allah Sayyid ka dawo? Ka gaya mini kana ina, sai na zo na same ka na tafi da kai"
Guguwar Sahara ce, ta taso ta turnuƙe gurin.
Nana ta din ga tari, muryar Mama ta ji a kanta tana faɗin "Tari ki ke haka Nana?"
Kawai ta ga Nana ta tashi, ta yi waje. Ta riƙe ta ta ce "Ina za ki ke?"
Idanunta a rufe, fuskarta a murtuke ta ce "Ba ki ji Sayyid ne yake kirana ba?"
"Waye hakan?"
"Mijina mana" ta faɗa a fusace.
"A'a babu wanda ya kira ki fa"
Nana ta fara ƙoƙarin fizge hannunta ta ce "Yanzun nan fa ya fita daga ɗakin nan"
"Nana babu kowa fa a gurin nan, daga mu sai ke"
"Ni ki cika ni, na ji Muryar mijina gurinsa zan je yana kirana"
Tsawa ta daka wa Nana ta ce "Ina magana ki na ɗaga mini murya? Wuce ki zauna babu wani wanda yake kiran ki" Nana ta buɗe idanunta, ta kalli Mamanta, sai dai ba ta yi magana ba, kawai ta ga Nana ta yi baya za ta faɗi. Ta riƙe ta ta kwantar da ita. Jikin Nana ya hau karkarwa, idanunta na fitar da hawaye.
Cikin matsananciyar damuwa take kallon Nana, tana tunanin dama har zuwa yanzu, tana fama da larurar nan?.
Ta rungume Nana a jikinta, ta kama goshinta, ta fara karanta mata Suratul Jinn, tana tofa mata a fuskarta. A hankali jikin Nana ya saki ta fara bacci.
Ta yi shiru tana kallon fuskar Nana, tana tuna lokacin da take rungume da ita tana jaririya, cike da so da ƙauna. Tare da tuno irin soyayya da rawar ƙafar da Isa ya din ga yi lokacin da aka haifi Nana, ba ta taɓa tunanin zai yi wannan riƙon sakainar kashin da rayuwar Nana ba.
Adda Saude ce ta yi sallama, Mama ta amsa mata.
Ta ɗan yi turus ta ce "Ya dai Nanan ba ta da lafiya ne, na ganta a kwance a jikinki haka?"
"Wallahi kuwa, shigo daga ciki" ta zauna ta ajiye kayan da ta zo da su. Ta ce "Tun jiya na so zuwa, tun da muka yi waya da ita da ta ce mini tana garin nan, babansu ne baya nan bai dawo da wuri ba ga yara gidan babu kowa. Ikon Allah ciki ne ma da ita haka?"
"Ga shi nan dai, har ya yi girma ma"
"Ikon Allah, na yi mamaki da na ji zuwa ta yi babu sanarwa, tare da mijin suka zo?"
Maijidda ta numfasa ta ce "A'a, matsala ma aka samu, ba a san inda mijin nata yake ba"
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, garin yaya ina ya tafi?"
"Wallahi ban sani ba, na dai ce ta zauna a nan, kafin nu ga abin da Allah zai yi. Ashe rashin lafiya ya sha, yarinyar nan ba ta taɓa gaya mini ba. Ga babanta bai karɓe ta ba, ƙarshe ma sai Buda ta koma ta yi jinyarsa, kuma dai ma ya tafi ba a san inda yake ba"
Cikin jimami Saude ta ce "Kai subhanallah, abin nan bai yi daɗi ba, yanzu meya same ta haka?"
"Iska ne ya buge ta, na ba ta abinci ta karya, ta fara bacci kawai ta tashi wai mijin ne yake kiranta. Ashe haryanzu tana fama da wannan matsalar. Wallahi Adda na yi dana sanin biye wa Iliyasu na watsar da yaran nan." Ta yi maganar hawaye na cika mata ido.
"Ki yi haƙuri, amma