Showing 114001 words to 117000 words out of 122205 words

Chapter 39 - BUZU BOOK2 COMPLETE 2

18 Jan 2026

617

ƙamshin turaren da ya cika gurin ne ya sanya ta farga ta waiwaya, sai ta ga a kan hanya ta tsaya.
Ta yi taku biyu ta ba shi guri, ya saci kallonta, zuciyarsa ta din ga raya masa son sanin wace ce ita, sanin na sosai ya yi mata tambayoyi game da wasu abubuwa.
Ya haɗiye yawu ya zo zai gifta ta, wani irin daddaɗan sanyi ya ratsa shi, sanyin da zai yi fatan dauwwama a cikin sa, saboda yadda ya saba da zafin jikinsa, wanda duk sanyin da yake guri, a cikin jikinsa yake jin wannan zafin.
Sai dai wannan sanyin da ya ratsa shi, har cikin ƙashinsa ya ji sanyin.
Ya sake waiwayawa ya kalli Nana, amma ya ga shi take kallo. Ji yake tamkar ya koma da baya ya ƙara samun kusanci da ita, sai ya fi jin sanyin sosai da sosai. Tun da Allah ya jarrabe shi da ciwon nan, bai taɓa jin sanyi mai daɗin wannan ya ratsa shi ba, kuma ya yi imani da Allah daga jikinta wannan sanyin yake, saboda sun samu kusanci sosai da sosai da zai gifta ta.
"Allah ya sa ba wani abin ake kuma shirya mini ko wani tarkon ake shirin yi mini da ke ba" Ya yi maganar a zuciyarsa.
Nana ta yi mamakin dalilin da ya sanya shi tsayawa haka.
Zuciyarsa ta din ga raya masa ya koma da baya, daf da Nana, ko zai fi kin sanyin yadda yake so.




AREWABOOKS

Nana ta ce "Sayyid ko wani abu ka ke buƙata ne?"
Sai da ta yi maganar sannan ya farga, bai ce mata komai ba kawai ya fice ya bar gurin.
****
Shukura ce a zaune ta takure jikinta, tana kallon kwanon abincin da aka kawo mata, Abinci mai rai da lafiya sai dai ko sha'awar kai wa bakinta ba ta yi ba, duk da uwar yunwar da take ji, tamkar ta ci babu.
Shiru ta yi tana tuna yadda bayan fitowarta daga Asibiti suka yi karo da wani mai adaidaita sahu.
Ya fito yana jarabar sai ta biya shi, duk da shi ne da laifi, amma ta kasa fitowa daga motar, ta sauke gilas ta ce ya gaya mata dammage ɗin nawa ta yi masa ta biya shi. Daga sauke glass ɗin nan ba ta sake sanin inda kanta yake ba, sai farkawa da ta yi ta ganta a wannan ɗakin, da sai dai a zuro mata abinci kawai.
Ba ta iya banbance adadin lokacin da ta kwashe a gurin ba, sai dai ta kintaci lokacin salla ta yi.

Babu tsammani ta ji an buɗe ƙofar ɗakin, hakan ya sanya ta kalli ƙofar da sauri.
Sai dai hasken fitilar mai wayarya haske mata ido, ba ta iya gane waye ba.
Sannu a hankali ya jingine wayar hannunsa ya zura mata ido.
Duk da ta ɗan razana amma abin bai wani ba ta mamaki sosai ba.

Ya zuba mata ido sannan ya ce "Kin yi mamaki ko?"

Ta girgiza kai ta ce "Ba sosai ba"

"Ko me yasa?"

"Saboda jikina ya daɗe da bani hakan"

"Ta yaya kenan?"

"Na daɗe ina zarginka ne, sai dai ana ta dankwafe ni, an hanani"

"Gaskiya ne, ban so ki zurfafa ki takura da son sanin abin da bai kamata ki yi ta bibiya sai kin gano ba, amma ban san me ki ka gani ki ka dage kina bin diddigina ba"

"Zarginka nake yi da kai da doctor Sharif na kasa yadda ɗa na mutuwa ya yi, saboda har yau ina ji a jikina, mafarkin da na yi gaskiya ne"

Alhaji Zailani ya ce "Haka ne, lokuta da dama mafarki ishara ne, duk da ban san abin da ki ka gani ba, amma zarginki gaskiya ne duk da na yi iya yi na a kan na ɓoye komai, sai dai kashi kin zaƙe Shukura, soyayyar da nake yi miki ba za ta hana ni ɗaukar matakin da ya dace a kan ki ba"

Shukura ta yi ajiyar zuciya ta ce "Da gaske ka na da masaniya a kan batun mahaifar Mami?"

"Ina da ita, haka zalika ina da masaniya a kan jaririnki ma da ki ke ta zargina da Sharif a kai, duk da ban san me ki ka gani a mafarkin ba"
Shukura ta yi masa wani irin kallo, zuciyarta na bugawa da sauri da sauri.

"Tabbas mafarkinki ishara ne. Amma kafin na yi miki wannan bayanin ina son ki sani, talauci bala'i ne Shukura, babu yadda ban yi a kan na yi yaƙi da shi ba, amma abu ya gagara. Na faɗi na tashi na yi iya yi na amma na kasa nasara a rayuwata. Burina ya gaza cika na mallakar manyan motoci da gidaje da tara manyan kuɗaɗe yadda zan yi nesa da talauci.
'yar makarantar da nake taƙama da ita, abubuwa suka nemi ƙwace mini, bayan faɗuwa a jarrabbawa. A taƙaice dai a makaranta na samu ƙungiyar asiri na shiga, cike da burin na gama makaranta cikin sa'a da fatan cikar burikana na yin arziki mai yawan gaske ta hanya mai matuƙar sauƙi.
Bayan na auri mahaifiyarku, ta haifi Sadik, ƙungiya ta fara neman jini a gurina. Na bayar da babban ɗa na Sadik, na kaɗu na shiga tashin hankali, sai dai hakan ne zai ba ni damar taka babban matsayi a ƙungiyar, duk da na bayar da waɗanda ba jinina ba a ƙungiyar amma na ji zafin bayar da Sadik. Aka haifi Yusuf, aka haife ki, ba a sake neman kowa ba, sai da wata buƙata ta sake taso mini, wadda biyan buƙatar na buƙatar na ƙara taka wani matsayi a ƙungiyar.
Haka na bayar da matata ta fari, Hafsat da tsohon ciki, na saka mata ƙyallen jini a ƙasan shimfiɗarta ta tashi da ciwon naƙuda ta mutu a gurin haihuwa.
Hakan ya sanya dukiyata ƙara haɓaka, na yi kuɗi na yi suna. Duk fafutukar kasuwanci da muke yi tare da Fatuhu, shikaɗai yake abin sa, ni fakewa kawai nake yi da kasuwanci amma ta ƙungiyar asiri nake samun kuɗina.
Duk da ina samu ta kasuwancin ma, amma ga mamakina Fatuhu da baya ƙungiyar asiri, ya fi ni samun kuɗi, kuma duk inda muka je an fi son sa.
Bayan na auri Amina, aka buƙaci duk wani ɗa da za ta haifa, zan din ga ba wa dodon ƙungiya. Lamarin ya yi mini nauyi, saboda ina jin ɗacin rabuwa da iyalina. Na nemi sassauci, sai aka dasa wa Amina wani jaririn aljani a cikin mahaifarta, duk cikin da ta samu ba ma ta sani yake cinyewa. Sai dai kawai ta wayi gari tana zubar da jini, babu ƙaƙƙautawa. Karo shida na shidan saura ƙiris ta rasa ranta, saboda jini take zubarwa ba kaɗan ba, sai dai a yi ta saka mata jini.
Ba a taɓa gane ɓari take yi ba, an zata larura ce kawai,  Asibiti aka kasa gane abin da yake damunta, na kuma hana a yi mata na hausa, tana zaune lafiya kawai sai ta hau zubar da jini babu ƙaƙƙautawa.
Ta damu ta damu da matsalar rashin haihuwa, amma na hana ta zuwa Asibiti ta ci gaba da bibiyar lafiyarta.
Ni kaina na damu da wahalar da take sha, sai aka nemi na sadaukar da mahaifarta gaba ɗaya ga wannan jaririn aljani, yadda ba sai ta ci gaba da samun ciki ba, cinyewar da yake tana azabtar da ita ba.
Haka na amince, cikin dare ta farka tana ihu da buge-bige, ina kunna fitila na haska, na ganmu a cikin jini male-male.
Na rirriƙe ta, amma ta fita daga hayyacinta, ihu kawai take tana riƙe mararta, a dole  na ɗauke ta muka yi Asibiti, ganin za ta rasa ranta saboda zubar jinin nan. Ta fi kwana uku ba ta hayyacinta, jini kawai ake saka mata.
Aka tura mu scanic, domin a gano musababbin zubar jinin.
Na takurawa mai scanic ɗin ya gaya mini me ya gani. Ya sanar da ni babu mahaifa ma a jikinta gaba ɗaya, dan haka bai ma gano daga inda bleeding ɗin yake ba a scanic ɗin, sai dai a ci gaba da bincike.
Abin ya bani mamaki, duk da a cikin ƙungiyar asiri nake, ban taɓa tunanin za a ga abin a zahiri a yi scan a ga babu mahaifa ba.
Na biya mai scannnic kuɗi, ya rubuta sakamakon da ba daidai ba.
Muka koma gurin likita, aka din ga bincike ba a gane komai ba. Ita kuwa sai da ta shafe kwana goma ba ta tantance wanda yake kanta, har an fitar da rai da ita sai kuma ta warke.
Na daɗe ina tunanin abin da na yi mata saboda son da nake yi mata. Muka tattauna da malamina, da mamakin yadda a scanic ɗin aka gane bata da mahaifa ma zata a zahiri bs a za a gane ba.
Sai ya ce mini idan na ce haka na ƙaryata kungiyar asiri gaskiya ce kenan, amma ya aka yi na yadda da kuɗin da nake samu a cikinta, har nake kashe su a zahiri? Ya ce mini dole na san duk yadda zan yi na ci gaba da rufe mata ba ta da mahaifa, dan kar ta ce za ta bi diddigi duk da ko ta bi diddigin babu abin da za ta iya ganowa.
Wannan aljani haryanzu yana rayuwa a cikin Amina, gurbin da mahaifarta take, kan addabe ta da ciwo wasu lokutan, sannan wannan aljani shi ne yake saka ta zubar da jini lokaci zuwa lokaci da take tunanin Al'ada take yi. Wasu lokutan ta zubar da jini fiye da kima wanda take tunanin duk su ne dalilin rashin haihuwarta."

Cikin matuƙar tsoro da matsanancin mamakin yadda ya zauna ya wassafa mata wannan mummunan labarin da tun da ta buɗe ido a duniya ba ta taɓa jin labari mai razanarwa da tashin hankali ba.

Cikin matuƙar tsoro da matsanancin mamakin yadda ya zauna ya wassafa mata wannan mummunan labarin da tun da ta buɗe ido a duniya ba ta taɓa jin labari mai razanarwa da tashin hankali ba.
Da ƙyar ta harhaɗo kalmomin da ta ce "Kai ka kashe Mummy, kuma ka bayar da mahaifar Mami? Da..da.dama aljani duk zai iya yin irin wannan abin?"

Yayi dariya ya ce "Ki na mamaki ne? Kodayake mutane duk abin da ba a kanmu ya faru ba, bamu fiye yarda ba, nima da fari kasa yarda na yi, abin ya ɗaure mini kai. Sai dai idan ki ka duba, ba a taɓa yi wa Amina aiki ba, kuma babu alamar tabo na tiyata a jikinta, dan haka ta yaya za ta rasa mahaifarta? Aljani muddin za ka yi masa biyayya, ka yi abin da yake so, to zai zama mai biya maka dukkanin buƙatunka. Da su ake sihiri, da su ake jifa, neman shugabanci, ɗaukaka kungiyoyin asiri da makamantansu. Duk wani siddabaru da za a ce miki sun yi ba abin mamaki ba ne ba" Ya yi maganar yana wata 'yar guntuwar dariya.
Shukura ta ƙara rikicewa ta kiɗime. Ta ce "Yanzu Daddy, duk son da mahaifiyarmu ta yi maka kai ka kashe ta? Ga amanarmu da Mami ta riƙe ta kula da mu, ashe dama rashin haihuwarta da ciwon nan na zubar da jini da take yi babu gaira babu dalili, kai ne sila? Kai ka haddassa mata? Yanzu tayaya zaka nemi yafiyar su? Ka rasa imaninka saboda abin Duniya? Kai fa ka kashe su"

Ya ce "No in ji wa? Ai ban rasa imanina ba, ai annabi ya ce duk wanda ya ce La'ila ha illalahu zai shiga aljanna"

Cikin kuka ta ce "La'ila ha illalahu ba ta fatar baki ba Daddy, tayaya za ka shiga aljanna bayan ka kai buƙatarka gurin wanin Allah da ya buƙaci ka saɓa wa mahaliccinka dan ya biya maka buƙata. Me yasa ka ga buƙatar ka ta yi girman da ta gagari Ubangijinka ka dangana ga waninsa"

"Wannan wa'azin naki kin riga kin makara Shukura. Ina da yaƙinin zan tuba kan na mutu, kuma Allah zai yafe mini"

"Wa ya baka garantin ganin nan da awa ɗaya ma?" Ta yi maganar tana kuka mai tsuma zuciya.

"Ina da shi, dan ko ciwon kai sai na shekara ban yi ba"
Ya miƙe tsaye yana faɗin "Ki mayar da hankali ki din ga cin abinci, saboda ke da abin cikinki nake sanya ran ku zama sadsukarwar ƙarshe da zan yi a ƙungiya. Sai dai kafin nan, ina roƙon afuwarki ko ba komai ke ma kin ci albarkacin dukiyata. Ɗanki da ki ka rasa ni na yi amfani da shi" Daga nan ya ɗauki wayarsa ya yi gaba abin sa hankalinsa a kwance, kamar bai aikata komai ba.
Wani irin gunji Shukura ta din ga yi tana kuka mai tsuma zuciya, ta din ga fatan ina ma mafarki ne ba gaske ba. Tabbas wannan babbar jarrabawa ce, a ce mutum irin mahaifinta shi ne mahaifinka, gara a ce an haife ka ba ta hanyar aure ba, ko makamancin haka. Amma uba irin Alhaji Zailani ba shi da wani amfani. Duk wata gwagwarmayar sa da faɗi tashinsa a kan iyalinsa ya zama na banza, a dalilin wannan mummunar hanyar mara ɓullewa.
Abubuwan da ya gaya mata sun shallake tunaninta, yanzu yadda ya tafi haka zai je ya ci gaba da rayuwa da Hajiya Amina duk da zaluncin da ya yi mata. Ta ji dama ta ba wa Sagir damar kai ta Asibiti wataƙila da ba a samu damar sace ta ba. Cikin kuka take roƙon Ubangiji Allah ya tona wa mahaifinta asiri, saboda a yadda zuciyarsa ta ƙeƙashe ɗin nan, babu wani abu na rashin imani da zalunci da ba zai iya aikatawa ba.

Can gida Sagir ko abinci ba ya iya ci. Yusra kuwa abin ka da ba cikakkiyar lafiya ce da ita ba, sai ta kwanta rashin lafiya, saboda yadda ta addabi kanta da ɗorawa kanta alhakin ɓatan Shukura, dan cewa take saboda ta dawo gidan Sagir Shukura ta tafi.
Haka Hajiya Amina ma, Addu'a kawai take yi a kan Ubangiji Allah ya bayyana Shukura a duk inda take. Sosai take jin tamkar 'yar cikinta ce ta ɓata, tun tana daurewa har ta kasa ta fara zubar da hawaye, kasancewar babu wani labari mai daɗin ji da zai nuna an kusa gano inda Shukura take.

****

Asal ta na tsaye a banɗakin cikin ɗakinta, bayan tabattar da Imam baya ɗakin, ta danna wata lamba ta kira.
Can aka ɗauka mutumin ya ce "Na'am ina jin ki"

"Ina da labari ne"

"Ina sauraren ki"

Ta numfasa ta ce "Hannun Imam babu zobensa na tambari, na tambaye shi ya ce mini karyewa ya yi ya kai gyara, daga bisani kuma ya ce mini bai san inda yake ba"
"Kin tabattar da hakan, ba kuma ɓoye shi ya yi a wani gurin ba?"
Asal ta ce "Eh na tabattar ai zobe ne da ba ya cire shi, tun da ya dawo babu zoben a tare da shi"
Mutumin ya numfasa ya ce "Madalla, ki ci gaba da sanya ido da sanar da ni duk wani abu da yakamata na sani"
Ta jinjina kai tamkar yana ganinta ta kashe wayar ta fita.
Jikin Nana tamkar an yi mata duka, saboda azabar gajiya da ta yi. Ta kammala aikinta tana ta gyaran kitchen, sai ga Balaraba ta shigo da ƙatuwar jarka. Ta ajiye ta ta ce "Gashi nan madarar raƙumi ce da Imam yake sha"

"To sannu da ƙoƙari Mama Balaraba"

Ta ce "Yauwwa kukun Imam, Allah ya taimake ki"

Nana ta yi murmushi ta ce "Kar ki ba ni kunya mana"

"Ba kunya zan ba ki ba, ai ke yanzu duk wata kuku a gidan nan a ƙarƙashinki take, ke kaɗai ki ke dafa abincin da zai ci, dole mu girmama ki saboda kema shugabarmu ce"

"A'a ni ba shugabarku ba ce ba, ni da nake bare ma a cikinku. Amma dan Allah Mama Balaraba wai su wa ake cewa Imam ɗin nan ne? Dan na ga wanda ake kira da hakan da yawa"

"Eh su Biyar ne, galibinsu jikoki ne na gidan sarauta, su na cikin jerin waɗanda za su iya gadon kujerar Sultan. Shi Imam Hammad a gidansu su biyu ne  da shi da Imam Abdallah, sai Imam Zahradeen shi ma jikan marigayi Sultan ne, akwai Imam Asadullah yayan Asal, sai Imam Omar, waɗannan su ne jerin waɗanda ake sanya ran za su gaji kujerar Sultan. Duk da su na ganin cewa Sultan na yanzu nuna son kai ƙarara na son Imam Hammad ya gaje shi a cikin yaransa. Imam Hammad yana da 'yan uwa da suke uba ɗaya amma su biyu ne suka cika ƙa'idojin zama Imam.
A ƙasar nan ana girmama duk wani Imam fiye da zatonki, mu na ƙasa mu na son Imam Hammad sosai mussaman baƙaƙen buzaye da fararen ke  yi mana kallon kamar ba 'yan uwansu ne mu ba, bayinsu ne kawai.
Idan kin lura galibi hadiman gidan nan baƙaƙen buzaye ne, fararen kaɗan ne ƙarara yake ƙoƙarin yaƙi da kyamar da fararen buzaye suke yi mana, yana ta fafutukar nema mana 'yanci, da ƙoƙarin mu ma a din ga bamu dama a cikin shugabanci, bai kamata iyayenmu sun ƙare a bauta mu ma mu ƙare a haka ba. Amma manyan nan ba sa son shi sam, gani suke yana ƙoƙarin hana su rawar gaban hantsi. Ni tun da ya dawo ma duk ya canza mutum ne mai sanyin hali, amma kaifi ɗaya ne, ba sani babu sabo.
Shi ne shugaban majalisar duk Imam ɗin ƙasar nan. Duk da a cikin su akwai wanda suka girme masa, amma a haka dole su girmama shi kamar yadda yake a dokar ƙasar nan.
Tarihin masarautar Agadez yana da yawa da kuma faɗi Nana, bari na tafi na je na ci gaba da aikina.
Nana ta jinjina kai ta ce "To shikenan na gode sosai da sosai"
Bayan fitar Balaraba Nana ta naɗe hannunta a ƙirjinta, tana nazari da tunani.

Jiki a sanyaye ta koma ɗakinta, ta duba kayanta ta lalubo takardar nan da aka kawo saƙon aka ce a ba wa Sayyid. Ta ƙare wa takardar kallo.
"Ko a cikin Imams ɗin nan ne wani ya aiko da wannan takardar?" Ta yi maganar tana tuna maganganun da ta ji suna yi ranar da aka kai su yin girki a gidan Sultan. Ta koma ta lalubo zoben gurin Sayyid ta din ga jujjuya zoben ta ce "Ko kai a ke nema ne? Idan kai ne ta yaya zan ba shi abin sa, tun da ban san iya adadin muhimmancin sa a gare ka ba, idan na baka ka manta ni ta yaya zan yi bayani a yarda da ni?" Ta din ga surutai ita kaɗai ta gaji ta nannaɗe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login