Showing 120001 words to 122205 words out of 122205 words

Chapter 41 - BUZU BOOK2 COMPLETE 2

18 Jan 2026

629

Asibiti"

Ya buɗe idonsa ya kalle shi ya ce "Babu abin da yake damuna Sultan, ba sai na je Asibiti ba"

Cikin damuwa ya ce "Me yasa ka yi hawan bayan ka san ba cikakkiyar Lafiya ce da kai ba? Kuma da ka ji ba za ka iya ba ai sai ka haƙura"

"Lokacin da na yi ba na jin komai a jikina, amma tuba nake ba zan sake ba"

Sultan ya ce "Ka tabattar ba ka jin komai a jikinka ba sai mun je Asibiti ba?"

"Ba na jin komai Abie, ka kwantar da hankalinka"

Ya jinjina kai ya ce "To shikenan, Allah ya tsare gaba ka kwanta ka huta sosai"

Ya jinjina masa kai, suka yi sallama ya tafi.

Duk yadda Nana ta so sanin halin da yake ciki, haka ta haƙura, sai dai bacci mai daɗi ya gagara ɗaukan ta.
Da sassafe ta fita ta hau gyaran sashen, tana jira ko za ta ji motsin Asal, duk yadda za a yi ta tambaye ta, ya jikinsa sai dai ta ji shiru, haka ta ajiye Abincin kari ta koma ɗakin da aka ba ta.
Sai wajen sha daya da rabi, ta ji motsi a falon, ta fito ta leƙa.
Shiru ta yi tana kallon mutumin da ya zo, kamar shi ta taɓa gani a gidan cin abincin su Al Hussain. Yana tare da Imam Asad.
Sayyid yana zaune a ƙasan Carfet, shi kuma yana saman kujera.

Allah ya taimaki Nana da Hausa suke magana, ba yarensu ba.

"Kai ya aka yi ka faɗo daga kan taguwa, ko ka fara shan wani abu ne ba mu sani ba?"

Asal ta ce "A'a Imam ba ya shan komai, dama ba shi da cikakkiyar lafiya ai"

"Ina magana kina sanya baki?" Asal ta ja bakinta ta tsuke.

Ya mayar da idanunsa kan Hammad ya ci gaba da cewa "Allah ya sauwwaƙe ya kuma kiyaye gaba. Amma ka din ga kulawa dai"
Bai ko ɗaga kansa ba, balle ya tanka masa, sai dai jikin Asal ya yi sanyi. Ba ta ji daɗin yadda Tafawa ya zarge shi da shaye-shaye ba.
Wuni aka yi zuwa duba Imam Hammad, sai dai ds Yamma Nana na tsaka da gyaran falon ta ga wannan takardar, mai ƙwarangwal ɗin nan yana ci da wuta.
Gaban Nana ya faɗi, ta yi shiru tana kallon takardar.
Jikinta ya ba ta kowaye yake yi masa wannan aika-aika yana cikin waɗanda suka zo dubiya yau.
Nana tana aiki a kitchen, Asal ta same ta, ta miƙa mata wani ƙulli ta ce "Ga shi nan, ki dafa wa Imam a shayi, maganinsa ne"
Nana ta karɓa ta amsa da to. Ba ta yi tunanin komai ba, ta dafa shayin ta je ta ajiye a falo.
Asal tana zaune tana jiranta a falo.
Ta tashi ta karɓa, Nana ta ce "A yi wa shugaba sannu, ina fatan Allah ya ba shi lafiya ya kiyaye gaba"
Asal ta amsa da Amin a ciki, ta nufi ɗakin baccinsu.
Yau Nana kamar ta fasa ihu, ta cika wata guda a gidan Asal, yau gaba ɗaya hankalinta yana kan ɗan jaririnta.
Ga shi tun da ta zo ba su yi waya ba ko sau ɗaya ba.
Haka kwanaki suka ci gaba da shuɗewa, kwana uku Asal na ba wa Nana maganin Sayyid tana dafa masa.
Sai a na ukun yake fitowa ya zauna a falon, amma ba ya fita.
A kai Abincin safiyar kwana na uku, Nana ta haɗu da shi.
Cikin girmamawa ta ce "Barka da safiya Sayyid, ashe tsautsayin da ya faru kenan, Ubangiji Allah ya kiyaye gaba."

"Ba ki yi mini sannu ba sai yanzu?"

Ta ɗaga kai ta kalle shi, duk ta ji abin wani banbarakwai, amma har cikin ranta ta ji dadin maganar da ya yi mata.
Ta ɗan juya idanunta ta risunar da kanta ta ce "Tuba nake Shugabana, ban samu damar ganinka ba ne, duk da na yi ƙoƙarin hakan, ba na son uwar gijiyata ta ce na zaƙe ne, amma tuba nake Ubangiji Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana mai amfani "

"Amin na gode sosai. Ina ganin ƙoƙarin da ki ke ta yi, ina yabawa, ki yi haƙuri da Asal kar ki tsane ta, duk da na san tana takura miki wasu lokutan"

"Babu takura a ciki, matuƙar hidima taka ce shugabana"

Ya ce "Madalla na gode sosai"

Ta tashi ta bar falon, a ranta tana cewa ina Asal ta ga kirki, shi da yake hangenta daga nesa ma, ya san tana ƙoƙari, ita kuwa ban da jaraba da uwar hantara da nuna mata ƙyama babu abin da take yi.
Asal ta shirya ta fita tun safe, dan haka Imam ne kawai a sashen.
Da Nana ta tashi kai masa abincin rana, ta sha kwalliya cikin doguwar rigar Atamfa.
Duk yadda yake jin jikinsa babu daɗi, yana motsa shi da kyar, amma bai hana shi satar kallon Nana ba.
Ba ƙaramin kyau ta yi ba, ga ƙamshin turaren sa da yake tashi a jikinta.
Ta kalli idanunsa da suka yi jawur, tamkar jini zai zubo daga cikin su.

"Sayyid lafiya kuwa?" Kai kawai ya jinjina ya mayar da idonsa ya lumshe, yana jin wannan ƙarar mara daɗin ji a kunnensa.
Haka Nana ta tashi ta bar shi a gurin, saboda tsoron abin da ka iya biyo baya.
Sai dare Asal ta dawo, kuma itakaɗai Nana ta ga ta ci Abincin dare.

Misalin ƙarfe ɗaya da rabi na dare, Nana ta gabatar da sallolinta na dare. Ta zauna tana karanta Alqur'ani, a hankali sai ta daina ganewa.
Ziiiiiiiiii ta fara jin ƙarar guguwar iskar sahara tana tasowa. Ta rufe Alqur'anin a hankali ta ajiye, sannu a hankali sanyi ya fara ratsa ta.
Ji ta yi tamkar an buga wani abu da ƙarfi, ta zabura ta miƙe tsaye.
Cikin hanzari ta buɗe ƙofar ɗakin da take ciki ta fito corridor da ɗakinta yake ta tsaya.
"Imam mene ne haka? Meye haka ka ke yi wai?"
Sautin kakarinsa ya daki kunnuwan Nana. Gaba ɗaya ta kasa zaune ta kasa tsaye.
Asal ta gani ta fito da gudu daga ɗakin, ta yi waje ta fice daga falon, ta ja ƙofar falon da karfi ta rufe.
Gaba ɗaya sai kan Nana ya kulle ta rasa abin yi, ta bi bayan Asal, amma ta ji ƙofar a rufe gam.
Ta juya a hankali ta kalli hanyar bedroom ɗin da sautin kakarinsa yake ta fitowa.
A hankali ta fara takawa tana tunkarar hanyar ɗakin, duk da ba ta taɓa zuwa ko daf da gurin ba.
Zuciyarta na bugawa cike da tsoro ta buɗe ƙofar ɗakin.
Wani irin sanyin na'urar sanyaya ɗaki ta dake ta, hakan ya ƙara ninka sanyin da take ji. Wani ni'imtaccen ƙamshi ya ziyarci hancinta.
Girman ɗakin baccin har tsoro ya ba wa Nana, ita dai tana mamakin yadda suke abubuwan su kamar babu lissafi, ɗakin kwana kawai an yi shi gari guda.
Idanunta ya sauka a kan Sayyid da yake shirin faɗowa daga kan gadon yana jijjiga. Ta ƙarasa da sauri daidai lokacin ya faɗo ƙasa.
Ta ɗaukko pillow za ta saka masa, kawai ta ga wannan hoton a ƙasan fulonsa. Cikin mamaki take kallon hoton, tare da mamakin yaya aka yi ya zo kan shimfiɗarsa.
Ta durƙusa a kansa, ta kalli jikinsa duk wata jijiya da take jikinsa ta miƙe ta kumbura.
Ƙwayar idonsa ta koma fara ƙal, gashin kansa ya hargitse, gaba ɗaya ya koma abin tsoro tamkar wani dodo.
Ta yi Bismillah ta zauna, tare da jin sai dai komai zai faru ya faru, ko a mutu ko a yi rai, ko da za a zo a kama ta gara balli ya tashi ko za su ƙaryatata gara duk abin da zai faru ya faru, da bar shi a wannan yanayin da bayan shi kansa babu wanda ya kai ta sanin mawuyacin halin da yake shiga.
Tamkar mayen ƙarfe haka ya riƙe ta gam, bakinsa yana karkarwa yana furta "Wuta! Zafi!"
Ya danneta a ƙasa ya ƙanƙameta, bakinsa na fitar za kumfa.
A hankali ta fara karanto suratul Saffat, ta sanya hannunta a cikin gashin kansa tana shafawa a hankali.
Sannu a hankali ya daina wannan gurnanin da yake yi ya yi shiru, sanyin jikinta ya fara ɗibarsa. Ya yin da ita kuma take jin tamkar ana gasa ta a tukuba saboda zafin Jikinsa.
Sosai Nana ta ƙanƙame shi ita ma, cike da matsananciyar kewarsa, wasu hawaye da ita kanta ba ta san na mene ne ba, suka din ga sintiri a kan fuskarta.

"Sai ki tashi ki tafi tun da ya samu bacci, tun da ke dai a rayuwarki ba kya tsoron matsala, tarar aradu kawai ki ke yi da ka. Maimakon ki bari mutumin nan ya gane ki, a yi duk wadda za a yi, amma sai ƙoƙarin kunno wa kan ki matsala ki ke yi" Ƙaisar ya yi maganar cike da takaici yana harar ta.

Nana ta ce "Wasu lokutan nasara ns buƙatar sadsukarwa, da kuma tarar aradu da ka. Mu da ku ba irin zubin halittarmu ɗaya ba, ba zan iya jure ganinsa a wannan mawuyacin halin ba. Ina tausaya masa a yanzu fiye da a lokacin da na san shi bai kan sa ba, yake ce mini yana ji a jikinsa rayuwar da yake da ni ya fi wadda ya manta aminci da kwanciyar hankali, ga shi kuma yanzu ina gani. Sai na ƙyale shi a haka?"

Ƙaisar ya yi tsaki ya ce "Allah ya sa shi zai iya yin abin da ki ke yi a kan sa"

Nana ta numfasa ta ce "Dama ba dan ya rama mini nake yi ba"

Sai gefen asuba jikinsa ya saki, ya ci gaba da nannauyan bacci. Ta saka masa filo ta tashi, sai dai jikinta tamkar ana karyata haka take ji, saboda azabar riƙon da ya yi mata.
Bayan ta idar da sallar asuba, ta yi adduo'inta ta shiga kitchen.
Kafin ƙarfe tara har ta kammala komai, ciki har da gyaran katafaren falon Imam Hammad. Tana son sanin halin da yake ciki, ya farfaɗo ko kuwa bai farfaɗo ba.
Tana can tana tunani, shi kuwa tuni ya fito ras da shi, ya hau buɗe-buɗen kwanuka. Har wani murmushi ya yi ganin ƙosai a cikin kayan karyawarsa.
Shiru ya yi yana kallon kofin madarar raƙumin da ke gabansa, bayan da ya buɗe ya ga 'ya'yan habbatussauda a kan madarar.
Ya ciro wayarsa ya daddana, ya kara a kunnensa.

"Al Hussain"

"Allah ya taimaki Imam Hammad adalin shugaba abin koyi"

"Barka da wannan lokaci ya aiki?"

"Alhamdillah, ina nan tafe cikin Agadez a wannan satin, tun da an ce mini yanzu ana ganin ka"

Imam ya ce "Eh, ammm tambayarka nake son yi"

"Ok Imam, Allah ya sanya ba wani abun aka ce na yi ba"

"Akwai yarinya da Asal ta zo da ita, ta ce a nan gurin cin abinci na Maraɗi ta ɗaukko ta, wata 'yar Nigeria"

Al Hussain ya ce "Haka ne, sai dai ba na nan suka tursasata Gimbiya Asal ta tafi da ita, na ɗauka ma nan  gidan cin abinci na Agadez za ta dawo da ita"

"A ina ku ka samo ta?"

Al Hussain ya ji gabansa ya faɗi cike da tsoron, ko wani abin ne ya faru.

"Wani kamfani ne suka kawo ta, da muke neman ma'aikata masu ƙwarewa a fannin girki"

"A nemo kamfanin, da shugaban kamfanin"

"To in sha Allah, amma ina fatan ba wani abin ne ya faru ba?"

Imam ya ce "Sarkin ruɗewa, babu abin da ya faru, ina sauraren ka" Daga haka ya ajiye wayar daidai lokacin da Asal ta shigo.

Ya ɗaga kai ya kalle ta ya ce "Ke ina ki ka tafi ne? Na yi zaton ma ko ki na sashenki ne?"

Ba ta ba shi amsa ba, Sultan ya shigo a rikice. Da mamaki yake kallon su.

Sultan ya ƙaraso cikin hanzari ya ce "Hammad ka na lafiya ya jikin naka?"

Imam ya ce "Ai ni lafiyata ƙalau, tun ranar da na faɗo fa babu abin da ya same ni"

Sultan ya kalli Asal, a rikice ta ce "Wallahi Sultan ba shi da lafiya, ba ka ga riƙon da ya yi mini jiya ba, wasu abubuwa ya din ga yi masu ban tsoro".

Imam ya ɗaga kai ya yi mata wani irin kallo, da sai da hantar cikinta ta kaɗa. Ya gyaɗa kai ya ce "Ni ban san me take magana a kai ba, lafiya ƙalau na kwanta kawai dai ba na jin daɗi kaina yana yi mini ciwo, ban sani ba ko ciwon haukan ne ya motsa mini ba"

Sultan ya ce "A'a ba ka da wani ciwon hauka, kawai dai rashin fahimta ne, ka san ba ka da cikakkiyar lafiya"

Hammad ya miƙe riƙe da kofin madararsa, yana sha a hankali ya ce "Abie zan je na shirya, zan ɗan fita ne"

Ya nufi ɗakin sa.

Asal ta kalli Sultan ta ce "Wallahi Sultan ba ƙarya nake yi ba"

"Na sani, na san ba ƙarya ki ke yi ba, ki yi haƙuri. Dan Allah ki yi shiru da bakinki kar ki gaya wa kowa. Zan san abin da zan yi a kai"

Nana kuwa burgima ta din ga yi a ɗaki, saboda azabar ciwon da jikinta yake yi mata, kamar ta saka ihu haka take ji.
Tun da ta jiyo muryar sa sama-sama a falo, hankalinta ya kwanta ta san jikinsa da sauƙi.

Sai dai wunin yau ma ba su haɗu ba, Asal ta ce mata ta ajiye masa Abincin, za a ɗauka a kai masa inda yake.

Ruwan zafi Nana ta dafa, ta shiga ta ya wanka da shi, ko za ta samu afuwa, ta gyara jikinta ta fita. Gidan ya yi shiru saboda dare ne, kowa ya kwanta. Ta shiga kitchen ɗin ta tabbatar komai lafiya ƙalau, sannan ta koma ɗakinta.

Tana shiga ɗakin ta ga duhu an kashe fitila, ta nufi gurin kunna fitilar ta ji an mayar da ƙofar ɗakin an rufe.

Ayshercool
08081012143
1K NE VIA 0069685771
Aisha Adam stanbic bank
💃💃💃


























Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login