Showing 57001 words to 60000 words out of 122205 words

Chapter 20 - BUZU BOOK2 COMPLETE 2

18 Jan 2026

580

daban.
Hoton wata alƙarya ce, da ke tsakanin duwatsu, da aka rarake aka samar da katafariyar daula.
Ta buɗe littafin shafin farko, ta fara karantawa.

"Tushiya..." Shi ne abin da ke rubuce a shafin farko na littafin.

"Ka sani,har abada da ɗan Gari a kan ci gari. Kuma ba a cimma buri da tausayi ko jin ƙai. Wannan mataki na farko kawai ka cimma, na sharar fagen cimma nasararka.
Ka na buƙatar sanya wa mutane tsoronka, da shakkarka domin cimma burinka, kuma hakan ba zai taɓa yiwuwa ba sai ka zubar da jini, duk wanda ya biyo ta hanyarka ka datse rayuwarsa, kar ka damu da adadin rayukan da za a rasa, ka zubar da jini ba ƙaƙƙautawa har sai mutane sun fara jin fitsari a duk lokacin da aka ambaci sunanka.
Ka kame mutanen gefen alƙaryar nan, ka mayar da su bayi, matansu ka mayar da su naka, mazansu su zama bayinka, ka yi amfani da ƙarfinsu da fikirarsu ka gina alƙaryar da babu wani mahaluki da zai iya ɗaga maka yatsa, kar ka gushe kana aikata hakan, har sai buƙata ta biya.
Zaka kasance cikin sanyawar albarkar Aljanu, za su baka dukkanin goyon bayan da ka ke buƙata kar ka saurarwa kowa"

Cikin damuwa mutumin ya kalli mai maganar ya ce "Ka sanya ni na kashe mahaifina da hannuna, yanzu ga wani abin ka sake zuwar mini da shi, kar ka manta ina da 'yan uwa maza, ba za su zuba mini ido, duk na yi wannan ba, na ɗauki abin da ba nawa ba, alhalin su na gaba da ni ba"
Ji ta yi mudubin gurin yana wata irin ƙara tamkar zai tsage, a take ta ajiye littafin ta nufi mudubin tana kallonsa.
Wata irin wuta ta gani tana ci a cikin mudubin. Wutar mai matuƙar ban tsoro saboda yadda take ci. Wani mashi ta gani a soke a jikin wani ƙwarangwal, ɗaya gefen mashin an yi rubutu a jikin wani abu mai kama da takarda. Ta ƙara matsawa domin karanta mene ne a jikin takardar amma ta ga mudubin yana hayaƙi yana baƙi yana washewa.
A kusa da wutar ta ga wani abu mai kama da mutum, a lulluɓe da wani mayafi yana zuba wani abu a cikin wutar wanda yake ƙara sanya wutar ƙara balbala.
Imam... ta iya gani a rubuce a jikin abin, mai kama da takarda, a gaban Imam ɗin akwai wani sunan, sai dai ba ta iya karanta sunan ba. A jikin wutar ta ga taswirar fuskar Sayyid yana jijjiga jikinsa na ƙonewa yana kururuwa yana kiran sunanta.
Wata irin zabura ta yi ta kuma tunkarar mudubin gadan-gadan, mudubin ya yi wata irin tsawa ta ja da baya ta faɗi ƙasa.
A gigice Nana ta farka, ta haɗa uban gumi ta yi sharkaf, ga wata irin ƙullewa da cikinta ya yi haɗi da mararta. Ta yinƙura da ƙyar ta tashi ta tafi banɗaki, a zatonta fitsari take ji, ko kuma bayan gida, amma ta ji ba bayan gida take ji ba, ta fitsarin amma still mararta kamar an saka wani abu an ɗaure mata. Ta yi alawala ta koma ɗakinta.
A zaune take salla saboda yanayin girma da nauyin da cikin ya yi. Ta kasa tuna abin da ta gani, sai iya wutar nan da wannan tsawar da mudubin ya yi su kawai take iya tunawa.
"Allahumma ajirni mina narr"
Ta maimaita da tuno yadda ta ga wutar nan. Ta ji sam mafarkin nan bai yi mata daɗi ba, ko mene ne babu Alkhairi a tattare da shi sam.
Sai da gari ya waye, sannan ta samu afuwa daga wannan ɗaurewar da mararta ta yi da bayanta. Jikinta babu daɗi, haka nan take lallaɓawa ta daure kar Nene ta fuskanci wani abu.
Nana ta dama kunu da kanta, ta tashi tana tafe da kyar, Nene ta ce "Nana wai cikin nan naki wata nawa ne?"

Ta ɗan yi shiru ta ce "Ina ga bakwai ne"

"Anya kuwa Nana, kalli yadda ya cure guri ɗaya ya yi ƙasa sosai a ce cikin nan na watanni bakwai ne kawai? Amma ban sani ba ko biyu ne. Yakamata ma mu je Asibiti a duba ki, ni wallahi na ma manta shaf ana zuwa awo. Ko danmu lokacinmu ba awon ake yi ba oho" Nana dai ta yi murmushi kawai tana jin yadda ɗan yake ta motsi yana danno ta.

Da ba rufe cikakken sati, mijin Hajara bai zo gidan ba, dama yana fargabar kar Nana ta kasa zama da Nene, saboda faɗanta, kuma cikin ikon Allah ya ga lafiya kalau suke zaune. Dan haka ya rage zuwa sosai.
Tun da Nana ta je gidan, Neme ba ta barin ta ta fita, saboda ta ce mata tana da aure, kuma tana yawan gaya mata, ba a son mace mai ciki ta din ga yawo jama'a su na kallonta, saboda baki da ido.
Ma'aikatan Nene duk sun saba da Nana, duk a tunaninsu 'yar uwatta ce, sai dai sukan tambayi Nana, ya aka yi hausarta ba irin tasu ba.
Wasu lokutan sai Nene ta cewa Nana ta zauna a ɗaki kar ta fito, dan haka babu inda Nana ta sani a garin.
Nana ta kwana huɗu, tana fama da wannan ciwon a tsaitsaye.
Sai dai na yau ya fi na kullum, dan sam ba ta yi bacci ba, kuma ba ta gaya wa Nene ba.
Da safe kan Nene ta fito, Nana ta yi shara ta wanke banɗaki, ta ɗora abin karin kumallo.
Ta kuwa sha faɗa a gurin Nenen, sai dai ita ko a jikinta.
Sun gama karyawa, Nene ta shiga ɗaki, ta ji Nana na kiran sunanta, cikin mawuyacin hali.
Nene ta fito da sauri ta ce "Nana lafiya?"

"Nene yoyon fitsari nake yi, ba na iya riƙe fitsari" gaban Nene ya faɗi ta ce "Kamar yaya?"

"Ji na yi kawai fitsari yana bin ƙafata, kin ga" ta yi maganar tana ɗaga wa Nene doguwar rigarta, ruwa na ta bin ƙafafuwanta".

"Nana wannan ai kamar naƙuda ki ke yi, anya ba ruwan mahaufa ba ne?"

Duk da ƙoƙarin da ta yi, za ta yi magana, sai ta kasa saboda wani irin gigitaccen ciwo da ta ji.

Har Nene ta fita suka samo abin hawa, Nana na cikin halin ciwo, ba ta iya gane komai.
Nene ta ɗaukko wa Nana wasu kayan, su ka fita suka tafi Asibiti.
A Asibitin ma, da aka tambayi Nana, cewa ta yi cikinta wata bakwai ne, sai dai da aka yi hoton cikin, ya nuna satin cikinta arba'in da biyu.
Likitan ya yi mata tambayoyi, yaushe ta yi al'ada na ƙarshe, ta ce ita ba za ta iya ganewa ba, saboda ɓari kawai take yi a jere.
Ya tabattar mata a cikin ɓarin da ta din ga yi, tun da ba Asibiti take zuwa a duba ba, akwai wanda bai fita ba ya ci gaba da girma, dan haka naƙuda take yi.

Gaba ɗaya Nene ta rikice, kamar 'yar ta ce za ta haihu, sai a lokacin ta fita, ta sayo kayan jariri da ba ta san ma na wani jinsi ba ne, da ɗan abin da za a buƙata.
Ma'aikata na tsaye a kan Nana, su na ƙoƙari, duk ta galabaita ma ta kasa nishin can ta ce "Ya hayyu ya ƙayyum" ta yi yinƙuri sai ga kan ɗan ya fito. Ita dai ba ta san yadda aka ƙarasa ba, ta ji kukan jariri ya cika ɗakin.

Likita ta ɗago mata jaririn ta ce "Kalli me ki ka haifa?"

Nana haushi ya kama ta, ta gama shan wannan uwar wahalar ga ɗan a hannunta, kuma a din ga tambayarta me ta haifa.
Ta kalli yaron namiji ne, ta ga wani irin shirgegen ɗa, kamar ɗan wata biyu, sai ta hau mamakin yanzu wannan ɗan duk girmansa a jikinta ya rayu, kuma ta ɗan wannan gurin ya fito?
Wata irin zabura ta yi ganin fuskar yaron, ta miƙa hannunta gaba ɗaya tana ƙoƙarin karɓe yaron daga hannun Likitar a kiɗime.

Yana kan gadonsa na marasa lafiya a kwance, su ka ga ya yi wata jijjiga sai da gadon ya girgiza kamar an jona masa wani abu, kawai suka ga ya buɗe idonsa.
A rikice suka kewaye shi, su na kiran sunansa, sai dai babu wanda ya amsawa sai bin su da yake da ido, kamar ya ga baƙin halittu.
Sultan ya riƙo hannunsa ya ce "Imam ka gane mu kuwa?"
Ya yi shiru yana bin Sultan da kallo.
Abduou ya ce "Ikon Allah, ka ga wannan karon bai tashi da ihun ba, sannu Imam"
Kawai ya yi shiru kamar saƙago, sai ƙwayar idonsa da yake juyawa.

Ayshercool
08081012143
65
Nana kuwa da sauri wata ma'aikaciya ta mayar da ita ta kwantar, ta ce "Kar ki tashi, ai miƙo miki shi za a yi"
Abin da ya razanata kuwa, bai wuce yadda ta ga fuskar Sayyid sak, a jikin ƙaton jaririn nata ba, ga sumar kansa a cike har goshinsa. Ga shi jariri amma hatta girar sa da gashi, haka jikinsa ma akwai gashi sosai.
Aka ɗora mata shi a ƙirjinta, ta yi wata nannauyar ajiyar zuciya, tare da furta Alhamdillah.

Ta sanya hannayenta, ta zagaye shi, ta ɗora hannunta a kansa ta din ga karanto masa addu'oi.
Ta din ga hasko irin murnar da Sayyid zai yi, da ya na nan aka haifi jaririn nan. Hawaye ya din ga gagangarowa ta gefen idonta.
Tana jin Likitan tana tsokanarta da har da kukan daɗi, ba za ta bayar da jaririn ba sai an ba ta tukuici mai tsoka. Nana dai ta lumshe idanunta tana murmushi. Aka ɗauke jaririn aka gyara ta, aka yi mata ɗinki, sannan aka kai ta ɗakin hutu.
Bakin Nene ya ƙi rufuwa, ta din ga kallon jaririn. Ta kira wayar su Hajara, ta gaya musu baƙuwar su Nana ta haihu.
Nana ta din ga kallon Nene, da mamakin yadda take ta murnar haihuwar nan, tamkar ita ta haihu.
Sai dai da Nana ta kalli fuskar jaririn sai jikinta ya yi sanyi, ta rasa abin da yake yi mata daɗi, tana tsoron idan ba ta haɗu da Sayyid ko 'yan uwansa ba, yaya za ta yi mene ne makomar yaron kenan? Ga fargaba da tsoron kar su Ƙaisar su yi masa wani abu, kar shi ma ya yi mummunan gado kamar yadda ta yi.
Haka dai ta ɗan saki fuska babu yabo ba fallasa. Bayan awanni shida aka sallame ta daga Asibitin suka koma gida. Aka bata magungunan da suka dace ta yi amfani da su, duk Nene ta biya komai.
Nene ta shiga hidima da Nana sosai, ruwan wankanta da na jariri. Ga lafiyayyen Abinci, Hajara kanta idan za ta zo, sai ta yi girki.
Kowa ya ɗauki jaririn Nana, sai ya burge shi.
Ita kanta Nana tasirin Addu'a ne ya sanya Allah ya kawo mata wannan ɗaukin da gaggawa, mutanen da ta haɗu da su suke sonta.

Kwana na biyar da haihuwarta, ta ɗebo kuɗi a cikin jakar gurin Sarkin baka, ta samu Nene ta ce "Nene kuɗin nan za su isa a sai wa yaron nan abin yanka?"

Nene ta ce "Kar ki damu, mun yi magana da Auwwalu za a samo abin yanka in sha Allah"

Nana ta ce "A'a Nene, ko ke ki ka haife ni, wahalar da za ku yi mini kenan, kuɗinki na sana'a ne. Ina son a saya masa kaya, a saya masa abin yanka, ko ba za su isa ba, a karɓa a ƙara irin kuɗin mahaifinsa ne, dan Allah kar ki ce a'a" Da ƙyar Nene ta karɓa.
Dan kuɗin da yawa, aka sayo ƙaton rago, Nene har da ɗawainiyar yin girki, ta gayyaci maƙwabtanta suna.
Muhammad Muhsin, shi ne sunan da Nana ta sanya wa jaririn, Muhsin saboda sunan ɗan gidan Alhaji Fatuhu da har abada ba za ta manta da mutuwarsa ba.

Maƙwabtan Nene da ma'aikatanta sun yi wa Nene kara, sosai suka tara mata abin alheri na kuɗi, da kayan sakawa kasancewar Nene duk masifarta akwai kyauta, shi yasa take shiri da mutane.

Da daddare Nene ta yi wa Muhsin wanka, Nana ma ta yi ta ba ta jaririn ta shayar da shi. Ta fita tsakar gida ta ƙarasa aikace-aikacenta. Kukan jaririn ta din ga ji, Nene ta ce "Nana ya ne, ki kula da shi mana"
Amma Nana ba ta amsa ba, sai kukan jaririn da ta ci gaba da ji. Ta koma ɗakin ta ɗaga labule, kawai ta tarar da Nana, ta saka jaririn a gaba tana ta uban kuka.
Hankali tashe ta shiga ɗakin cikin damuwa ta ce "Ke lafiya, kukan me ki ke yi?" Nana ta kasa magana, ta ci gaba da kuka, ga jaririn a kan cinyarta amma ta kasa riƙe shi. Nene ta ƙarasa ta ɗauke jaririn ta ce "Ba za ki illata ɗan mutane ba, maza yi ta kukan, idan kin gama kya kula da shi" Nene ta goye shi a bayan ta, ta ci gaba da sabgoginta ta ƙyale Nana.
Ba ta sake kula Nana ba, sai da ta yi kuka mai isarta ta gaji.
Nene ta gyara shimfiɗarta, ta kwantar da Muhsin da ya yi bacci.
Ta koma gurin Nana, ta zauna. "Nana" ta kira sunanta.
Nana ta ɗaga kai ta kalle ta.
"Ki gaya mini tsakaninki da Allah, yaron nan ta hanyar aure ki ka haife shi ko kuwa? Na san tambayar nan tana baƙanta miki rai, amma haƙuri za ki yi da ni"

Nana ta share hawayenta ta ce "Nene ni ba ƙarya na yi miki ba, ina da aure wallahi ɗan sunna ne"

"To Alhamdillah, dama jira nake Allah ya sauke ki lafiya, idan ta kama da kaina sai na je Nigeria, na mayar da ke gaban iyayenki Nana, wannan zaman naki kina yarinyar mace, ba kamace ki ba"

"A'a ba zan koma ba Nene"

"To saboda me?"

Hawaye na ambaliya a fuskar Nana ta ce "Sai na haɗu da Babansa, ko danginsa. Ai sun san na taho neman sa"

Nene ta ce "To a wane garin baban nasa yake?"
Ta girgiza kai ta ce "Nima ban sani ba"

"Kamar yaya? Meye sunansa da garin da yake ko hotonsa, sai a taya ki cigiyarsa" Nana ta sake girgiza kanta ta ce "Ban sani ba"

"Wacce daga cikin tambayar ce ba ki sani ba?"

"Nene ban san garin su ba, ban san sunansa ba, kuma ba ni da hotonsa"

Nene ta ce "Ke kar ki raina mini wayo mana, na kwaɗe ki, ta yaya za ki auri mutum ba ki san sunansa ba, ba ki san sunan garinsu ba kawai ki ka kamo hanya ki ka taho? Me ki ke ɓoye mini ne?"

Nana ta ɗan yi shiru ta numfasa ta ce "Ƙaddara ce ta haɗa ni da shi muka yi aure, ban san sunansa na gaskiya ba, ni ba shi sunan Sayyid. Ba shi da cikakkiyar lafiyar ƙwaƙwalwa kuma." Nan Nana ta warware mata komai da ya danganci aurenta da shi, duk da ba komai ta gaya mata ba.
Nene ta yi shiru sannan ta jinjina kai ta ce "Ikon Allah, dama shi ne Sayyid ɗin da ki ke ambata idan kina bacci? Amma Nana iyayenki sun yi ganganci. Ke yanzu ko hotonsa ba ki da shi.
Kawai Nana ta ɗaga mata kai alamar eh.
"To ai Nana zama guri ɗaya a haka, ba zai sanya a gano shi ba, dole sai an taɓuka wani abin, wane ƙabilar ne ko shi ma ba ki sani ba?" Nana ta yi shiru ta rasa ma me za ta cewa Nene.

Nene ta ce "To shikenan, amma ba kya ganin yakamata gidanku su san kin haihu?"

"Nene babu buƙata goben jaririn nan nake hange"

"Haka ne, to Ubangiji Allah ya kyauta, amma wannan lamarin naki akwai sarƙaƙiya Nana. Amma ba komai Allah ya taƙaita"

Nana ta amsa da Amin.

****
Baba yana tsakar gida yana shan kunu, sai ga Suwaiba ta fito, gaba ɗaya ta zama wata iri kamar shiri-shiri. Ta kalli Baba ta cake a ƙofar ɗaki ta ce "Nana fa ta haihu" ba shiri ya ajiye ludayin kunun ya kalli Suwaiba ya ce "In ji wa? Waye ya gaya miki?"

"Nanan ce ta gaya mini"

"Ke a ina ki ka ganta?"

"Ina bacci a ɗaki, na ganta da jaririn, ta ce mini haihuwa ta yi"

Wani uban tsaki Baba ya ja, saboda jin shiritar da Suwaiban take faɗa. Dan da fari ya zata ma da gaske take yi.

Alhaji Zailani ne tare da Malam Gambo, su na zaune fuskarsa ɗauke da damuwa.
Malam Gambo ya ce "Wai duk me yasa ka damu ne har haka? Ka na tsoron ƙungiya ta sake cewa ka kawo jininka ne?"
Alhaji Zailani ya numfsa ya ce "Abu na farko burukana biyu, ɗaya ya cika na durƙusar da Fatuhu. Amma samun yarinyar nan ya zame mini bala'i, ƙarewa ma da yake azzaluma ce mai baƙin hali, wai ta tafi Nijar. Ban kuma san ta yadda zan yi na same ta ba.
Babu yadda ban yi na samu yarinyar nan ba, amma duk lokacin da na yi wani yinƙuri a kanta, sai hankalina ya gushe. Yanzu babban tashin hankalina wannan jarababbiyar Sa'a, ashe ita ma ƙoƙari take yi, ta mallaki jinin yarinyar nan.
Ga shi na rasa dalilin da ya sanya Shukura take ta zargin likitan da yake yi mini aiki, da kisan jaririnta."

Malam Gambo ya numfasa ya ce "Ka tattara nutsuwarka guri guda, nasara na buƙatar kasada a kowane lokaci. Ita waccan yarinyar ka jingine batunta a yanzu tukuna, tun a wancan lokacin ai na gaya maka tana ɗauke da wani shu'umin aljani ne mai taurin kai a kanta ba zai taɓa barin burinka ya cika ta daɗin rai a kanta ba. Ba kai kaɗai ba koma waye kuwa. Sannan ƙungiya idan ta sake buƙatar jini, sai ka bayar da na ɗaya daga 'ya'yanka ko namijin, ko kuma ita yarinyar taka a bar jaririn nata ba shikenan ba. Kawai ya zuba wa Malam Gambo ido, idanunsa suka yi jawur sai dai bai ce komai ba ya tashi ya fita.

****
Ɓangaren Sagir kuwa, sosai yake sintiri tsakanin Kano da Abuja, saboda Yusra, saboda soyayyar da suke yi ma a yanzu, ba su yi ta a lokacin da suke saurayi da budurwa ba.
Wata irin muguwar shaƙuwa suka yi, da shaiɗan ke barazanar shiga cikin lamarin nasu, ga shi ya rasa ta inda zai tunkari Hajiyarsa da batun, domin ba son Yusra suke yi ba. Shukura tuni ta daɗe da gano inda ya dosa, amma ta zuba masa ido ta ga ina ne ƙarshen alewar zai kasance.

****
Kwanci tashi asarar mai rai, Nana ta yi wata guda da haihuwa, Nene ta tattara ta daina fita gurin sana'arta.
Sai aikin kula da Nana, ga shi kullum da sassafe kan ta ci komai, ake kawo nonon raƙumi fresh Nana ta sha, sannan ta ci

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login