Showing 69001 words to 72000 words out of 122205 words

Chapter 24 - BUZU BOOK2 COMPLETE 2

18 Jan 2026

581

Allah ki yi mini ko flashing ne, hankalina na matuƙar tashe dan Allah ki ɗaga wayata"
Ya tura mata saƙon, tare da ajiye wayar.
Hajjya Sa'a ce ta shiga ɗakin nasa, ta iske shi a kan kujera. Yana ganinta ya tashi zaune. Daga tsaye ta ce "Abba ba zaka fita bane? Baka fito ka karya ba, kuma baka fita kasuwa ba meyafaru ne?"

Ya girgiza mata kai ya ce "Babu komai fa"

"A'a akwai wani abu, na kasa gane kan ka 'yan kwanakin nan, hatta shirin bikinka nikaɗai nake abina, me yake damunka? Duk saboda Jamila ne?"

Ya girgiza kai ya ce "Ba kin ce ba kya son alaƙarmu ba, ni kawai ba ni da lafiya ne" ta yi shiru tana nazartarsa, kawai ta yi ƙwafa ta fice daga ɗakin.
Ya koma ya jingina, ya lumshe idanunsa, sai kiran Jamila. Ya ɗauka ya katse kiran ya kira ta cikin azarɓaɓi ya ce "Ƙanwata lafiya kuwa? Ba kya ɗaga wayata ko haryanzu kina fushin ne?"

Cikin numfarfashi ta ce "A'a Yaya Abba, ba ni da lafiya ne haryanzu"

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ya aka yi ba ki gaya mini ba? Kina gida ne?"

"Eh" ta amsa muryarta ƙasa-ƙasa.

"To shirya gani nan, bari na zo mu je Asibiti"

"To Yaya Abba, na gode" ta ajiye wayar da ƙyar. Hankalinsa ya yi mummunan tashi, a zatonsa aika-aikar da ya yi ce, ta sanya mata rashin lafiya har haka.
Da sauri ya zura kaya, ya ɗauki mukullin motarsa ya yi waje ya tafi gidansu Jamila.

Yanayin yadda Jamila ta fito, tamkar ya je ya ɗaukko ta, fuskarta duk ta kumbura, da alama tana jin jiki sosai da sosai.
Ya buɗe mata gaban motar ta shiga. Cikin tausayawa ya ce "Sannu ƙanwata, haka jikin naki ya yi ba ki gaya mini ba?"
"Ba na son tayar maka da hankali ne, kai ma ba ka da lafiya, amma Mama fa ta kai ni Asibiti" Gabansa ya faɗi ya ce "Allah ya sa ba ta gane komai ba"

Ta girgiza kai ta ce "Babu abin da ta gane, zazzaɓi ne fa kawai"

A tsorace ya ce "Jamila ko ciki ne?"

Ta kalle shi, sai da ta ji kamar ta yi dariya, duk da halin da take ciki. "Tun kan hakan ta faru ai nake rashin lafiya, ba wannan ba ne ba, ba wani ciki".

Ya sake cewa "Amma duk da haka kamar ya assasa miki ciwon, amma bari mu je Asibitin" haka ya ja motarsa su ka bar layin.

Safiyya ce ta tarar da Hajiya Sa'a ta cika ta yi fam, tana zaune a falonta.
Da kyar Hajiya Sa'a ta iya amsa mata sallamarta. Ta zauna a kusa da Hajiya Sa'a ta ce "Mummynmu maganin kukanmu, lafiya kuwa na ga ranki a ɓace?"

"Ba dole ki ganni a haka ba? Da gaske fa Abba son Jamila yake yi, nema yake ya bujire mini, kin ga yadda duk ya damu saboda na raba su. Ga bikinsa na ƙaratowa da Yasmin.

Maman Khairat ta tuntsure da dariya ta ce "To meye a ciki, idan tana son sa ki bar su mana"

Hajiya Sa'a ta kalle ta ta ce "Amma ba ki da hankali, yarinyar da shugaban ƙungiya suka kwanta da ita, sai Abba ya auri ragowa? Ba ma wannan ba, kar ki manta idan ƙungiya ta buƙaci ta bayar da jininsa fa, shikenan ta bayar da jinin tilon ɗan nawa?"

Maman Khairat ta ce "Na fahimce ki Mummy, da wasa nake yi miki, amma maganar gaskiya yanzu haka kan na taho ma, na ga motar Abba a unguwarmu, kuma na san ba ku da kowa a unguwar, dan haka gurin Jamila ya je"

Cikin matsanancin ɓacin rai ta ce "Gurin Jamila kuma? Yarinyar nan ta zame mini masifa da bala'i ko? Maganinta zan yi, wallahi sai ta rabu da Abba, ko ita ta haifar mini shi"

Maman Khairat ta ce "Ki yi dai a hankali, kin san halin yaran zamanin nan" Hajiya Sa'a ta ci gaba da huci, tamkar macijiya saboda takaici.

Maman Khairat ta ce "Ina dai ƙara gaya miki, ki bi komai a sannu, kin san halin yaran zamanin nan, sai su baki mamaki. Shi kansa Abban duk yadda yake yi miki biyayya, idan ba ki yi wasa ba, a wannan karon tsaf zai bujire miki".

"Ai ga alamu nan ina gani, amma ni zan sanya wa Abba doka, na hana shi abu, amma ya zagaye ya je ya aikata? Shikenan, na san matakin da zan ɗauka. Da ni suke zancen.

Alhaji Fatuhu ne zaune a harabar gidan sa, a kan kujera, ya kan ɗan iya dogara sanda ya tashi tsaye yanzu. Idan aka taimaka masa har harabar gidan yake iya fitowa, duk da idan jikin ya tashi kuma, sai ba ya iya hakan ko kaɗan.
Yana zaune a harabar gidan, yana kallon ƙaramin ɗan sa na gurin Fadila, yana ta wasa da Ball, yana jin yadda ƙaunar ɗan ke ratsa masa zuciya. Gefe guda yana tausayin yaron nasa, dan bai taɓa iya saya masa abin naira biyar ba da kuɗinsa. Hatta abincin da suke ci, 'yan uwa da abokan arziki ne suke kawo musu, ga shi wanda ya sai gidansa ya ba du aronsa suke zaune a ciki, ya fara ƙishin-ƙishin ɗin yana buƙatar gidan.

Fadila ce ta ƙaraso tana murmushi ta ce "Daddy kallon Ball ka ke yi?"

Ya yi murmushi ya ce "Eh mana, yana ta in tashi mu yi tare, ina ma zan iya da ko sau ɗaya mun yi tare, no na saka shi farinciki"

Ta zauna a ɗaya daga cikin fararen kujerun, ta ce "A hakan ma, ka na sanya shi farin ciki ai"

"Fadila"

Ta tattara masa nutsuwarta ta ce "Na'am Daddy"

"Kin san wani abu?"

Ta ce "A'a sai ka faɗa"

"Ina yarinyar nan Nana?"

"Wace Nanan?"

Ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Malamar Muhsin, da yake faɗa"

Ta ce "Ohh Allah sarki, na tuna ta"

"Mafarkinta nake yi"

Ta ɗan yi saroro ta ce "Mafarki kuma?"

"Eh Fadila, har aikawa na yi gidansu, a yi mini alfarmar a faɗa mini inda gidanta yake, wani abu nake gani da ya fara damuna"

Ta danne kishinta ta ce "To ka yi mini bayani mana"

"Kin dai san ni ba ma'abocin, biye-biye ba ne ba, da yarda da harkokin shirme da zai sanya na ji wani zai iya cutar da ni ba, amma a jere sau kusan biyar ina mafarki da ita".

Cikin ƙosawa ta ce "Daddy ka yi mini bayani, ka na ta kwana-kwana da ni"

"Ganinta nake yi a mafarki, tana ce mini an yi mini sihiri, karo kusan biyar fa"

Fadila ta yi ajiyar zuciya ta ce "Kuma ka yarda?"

"Ba ma son na yarda na gazgata hakan, amma na ji kamar na fara amincewa, saboda yadda nake ganinta abin ya yi yawa, ya wuce a ce shirmen mafarki ne kawai."

Fadila ta numfasa ta ce "Ai ni tuntuni na zargi hakan, amma sanin halinka na rashin son irin wannan abubuwan, ya sanya ba na yi maka maganar. Ko wannan sauƙin da ka ke samu, na san tasirin addu'a ne. Dan kuwa Umma kuɗi take bayarwa ana sauke karatun Alqur'ani."

Cikin mamaki ya ce "Amma ke kina ganin, akwai wanda zai damu da ni, har ya iya yi mini sihiri? Ina azkar ɗina da addu'oina, gani nake sun wadace ni, babu wanda zai damu da ni ya yi mini wani sihiri."

Ta gyara zamanta sosai ta ce "A duk Duniya waye ya koyar da mu azkar ɗin? Na san za ka ce manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam, amma an yi wa fiyayyen halitta sihiri, kuma ya kama shi.
Daddy ka yi haƙuri da abin da zan faɗa maka. Kana ibadarka ta farilla daidai gwargwado, amma ba ka damu da nafilfili ba, da tsananta addu'a. Kana ganin Allah ya baka duk abin da ka ke buƙata, ba ka fiye tsananta addu'a da neman kariyar Allah ba.
Sannan azkar da ka ke yi, kuma a yi shiri ya kama ka, ba ya nufin Allah baya kare ka, amma wataƙila jarrabawa ce daga gare shi, kamar yadda ya ce zai jarrabe mu, ba a fasa jarraba mai imani, kuma jarrabawa alama ce ta soyayyar Ubangiji. Allah ya jarrabe ka da cuta, ka nemi magani shi ma a cikin jarrabawa ne, amma Daddy ka naɗe ka dage, kai sai na Asibiti kawai, bayan akwai magungunan musulunci da suke na halal babu kauce hanya, idan an jarraba ba a san inda za a dace ba, amma ka ƙi ka ce kai sai na bature, na baturen kuma ba a gano komai ba, kame-kame kawai ake yi."

Ya yi shiru yana nazarin kalaman Fadila, ya numfasa ya ce "To yanzu mene ne abin yi? Kin ga yanzu bani da kuɗi, kuma irin wannan abubuwan sai da kuɗi".

"Kar ka damu, zan yi wa Kawu magana, shi ma ranar da ya zo duba ka, ai ya ce a yi na islamic, Alhaji Zailani ya ce ba za a yi ba. Da haka za tuntuɓe shi, in sha Allah ba zai gagara ba"

Alhaji Fatuhu ya ce "Allah ya sa, dama duk ina tsoron, kar a aikata abin da zai kauce wa hanya ne, amma na amince yanzu a yi ɗin"

Ta yi murmushi ta ce "To shikenan, yaya ita yarinyar an gano ta ɗin?"
Ya girgiza kai ya ce "Ina fa, an ce wai ba ma ta ƙasar nan, amma ina ta mamakin dalilin da ya sanya nake mafarinta, kuma idan na farka sai na ji kamar a zahiri, shi ya sanya ma na fara yarda"

Fadila ta ce "To Allah ya sanya a dace" ya amsa da "Amin"

*****

Ɓangaren Nana kuwa, gaba ɗaya kanta ya kulle a kan lamarin nan, kawai sai ta dasa addu'a, a kan idan da alkhairi a tafiyarta, Ubangiji Allah ya sanya mata son tafiyar, ya tsare mata Muhsin, idan kuma babu, Allah ya cire mata abin daga zuciyarta.

Kamar yadda ta saba ji haka ma wannan karon, ta ji muryarsa, da gudu ta ajiye abin da take yi, ta nufi taga ta leƙa sai ta hango giftwarsa da doguwar riga baƙa a jikinsa.
Da gudu ta fita daga gurin, ta nufe shi tana ƙwala masa kira, amma ya ɓace mata.
Cike da takaici ta yi juyi, tare da jan guntun tsaki, kawai ta ji hancinta ya fara shinshino mata, ƙamshin wannan ɗakin na cikin dutse, da take ganinsi tare da Sayyid.
Ta buɗe idonta a hankali, ta ji ana shafar cikinta a hankali, tare da yi mata numfashi a wuyanta.
"Sayyid" ta furta a ɗan tsorace.
"Asmyna, ina kewarki da yawa, gangar jikina na ta kewarki. Idan ina jin zafi babu mai bani sanyin da ki ke bani, babu wanda yake iya fahimtar kurman baƙin rayuwata, ki ƙaraso gare ni Please" ya yi maganar yana shafa wuyanta, tare da yin maganar ƙasa-ƙasa.
Ta saka hannu ta shafa gashinsa ta ce "Ina ta gaya wa Allah Sayyid, ya san lokacin da ya dace ya haɗa mu, amma jikina yana ba ni, ina daf da kai in sha Allah"
"Ki ƙaraso da wuri Asmyna, ina cikin matsananciyar buƙatarki"
"Ina ta ƙoƙari Sayyid, kuma ina gaya wa Allah, na san zai haɗa mu a nan kusa, kuma ina roƙonsa ya kare mini kai a duk inda ka ke, na san kuma yana ji ya kuma amsa in sha Allah"

"Nana, wai ba kya salla ne, gari ya fara haske fa" ta ji muryar Nene. Ta tashi tana mustustuke idonta, hancinta na ci gaba da jiyo mata sauran ƙamshin turaren nan.
Da ta yi salla ta idar, ta je ta samu Nene a ɗakinta, suka gaisa.

Ta ce "Nene na amince"

"Da me?"

"Zan tafi gurin yin girkin nan"

Nene ta ce "Ina fatan ba wani ne ya matsa miki ba? Ko kuma kunyata ki ka ji ba ki ka ce za ki je?"

Nana ta girgiza kai ta ce "A'a, wa ma na sani na saba da shi, da zai ziga ni na ɗauka? Babu wanda ya ziga ni"

Nene ta ce "To shikenan, zan kira ta a waya na ji, idan ba a samu wata ba, sai ki je. Sai mu je gurin jami'an tsaro mu yi yarjejeniya mu yi rubutu, mu je a yi a gaban su Auwwalu ma da Hajara"

Nana ta girgiza kai ta ce "A'a Nene, na yarda da ke, abin duk bai kai haka ba ai"

Nene ta ce "A'a, haka kurum wani irin ki ka yarda da ni, ɗan mutum fa zan riƙe miki, a'a, mu je mu yi a rubuce, yadda jami'an tsaro ma za su din ga sanya ido, kar wani abu ya faru ma. Sai dai abin da Allah ya aiko na ƙaddara wannan ba yadda muka iya, kuma na san za ki yi mini uzuri a wannan. Amma idan aka yi haka kema sai kin fi sakewa, hankalinki ya kwanta.

Nana ta jinjina kai ta ce "Ni dai, bakin da zan yi miki godiya ba ni da shi, amma ina fatan Allah ya yi miki tukuici da abu mafi dacewa da abin da ki ka yi mini na alkhairi, a duniya da kuma Lahira"

"Amin Nana, ai ɗa na kowa ne, Allah ya tabattar mana da alkhairinsa, ya kuma bayyana miki mijinki da ahalinsa cikin aminci".

"Amin uwata ta kaina" ta yi maganar tana murmushi.

Sai dai tun da Nana ta amince za ta bar wa Nene Muhsin, ta fara jin kewar ɗan nata, ta din ga jin kamar ta ce ta fasa. Saboda kallonsa kawai na sanya mata matsanancin farinciki da nishaɗi, idan ta tuna mallakinta ne shi ɗin. Tana jin ko ba ta ga Sayyid ba tana da ƙaramin Sayyid, duk da tana fatan ta gan shi ɗin, ko ba komai al'umma sa kalli ɗan nata da kima da daraja.

Ko da Nene ta kira matar, Matar ta tabbatar wa Nene, akwai sauran space ɗin da Nana, za ta yi musu aiki, sai dai a saka ranar da za su tafi ta kai ta.

Haka nan fargabar Nana ta ƙaru, ta rasa murna take ko tsoro, duk da abu mafi rinjaye kewar ɗan jaririn ɗanta ne, da yanzu take ƙara shaƙuwa da shi,ƙaunarsa take ƙara shiga ranta. Tana jin tamkar ta fasa tafiyar nan, amma ƙasan zuciyarta tana jin tafiyar ta ta alkhairi ne.

*****

Ɓangaren Abba kuwa, sai da aka yi wa Jamila ƙarin ruwa, typhoid ne ya yi mata mummunan kamu.
Sai kuma damuwa da take ciki, jininta ya ɗan hau. Abba ya biya duk bills ɗin, ya janyo kujerar ɗakin, ya zauna a gaban gadonta, ruwan da aka saka yana shiga jikinta.

"Ko a kira Mama a waya a sanar mata ne?" Ya yi maganar cikin kulawa.

Ta ce "A'a, na gaya mata Asibiti zan je, ana gamawa sai ka mayar da ni gida"

Ya ce "To shikenan, mai zan sayo miki ki samu ki ci?"

"Ba na son cin komai, kawai kar ka matsa daga kusa da ni, ka zauna a nan" ta yi maganar tana riƙe hannunsa a cikin nata.
Ji ya yi zuciyarsa ta narke, da matsanancin tausayin kan su, ya ce "Ina tare da ke matata, har abada in sha Allah" ta yi murmushi tana ƙara riƙe hannunsa. A hankali kuma ta saki hannun nasa, da tuna rashin dacewar hakan, sai dai wani irin abu mai wuyar fassara take ji, game da Abban.
Yana kallon kiran Hajiya Sa'a, amma ya ƙi ɗagawa, kawai ya din ga jin zafinta.
Har azahar sannan ruwan da ake saka mata ya ƙare, ya ɗauke ta a motarsa, ya yi mata sayayya sannan ya mayar da ita gida.

Sai da ya tabattar ta shiga gida, sannan ya kira Mummy.

"Sai yanzu ka ga damar ɗaga wayar tawa?"

"A'a caji take yi ne, ki yi haƙuri?"

"Kana ina ne?"

Ya ce "Na ɗan je wani uzuri ne, na zo ne?"

"A'a shikenan" ta ƙyale shi, bayan tuna shawarar da Safiyya ta bata, wato maman Khairat.

*****

Kamar yadda Nene ta buƙata, sai da suka je gurin jami'an tsaro, suka yi yarjejeniya, aka rubuta da yaren hausa, French da kuma turanci, duk suka sanya hannu, a gaban su Auwwalu da jami'an tsaro.

Daga nan suka dawo gida Nene ta ba wa Nana wata 'yar madaidaiciyar Jaka, da za ta haɗa kayanta da za ta buƙata a ciki.

Ta kalli Nana ta ce "Nana dan Allah ki kula da kan ki, duk da na san ke kamammiyar yarinya ce, ba mutuniyar banza ba, amma tunatar da mumini abu ne mai kyau, ki riƙe mutuncinki, ki kiyaye hakkin aurenki. Idan ki ka ga wani abu na ba dai-dai ba, ko wanda ya saɓawa addininki, a haƙura da sabgar nan. Kuma cikin hikima za ki din ga bincikawar,ba sai kowa ya fuskanci ainihin abin da ya nai ki gurin bax

Nana ta jinjina kai ta ce "In sha Allah Nene zan kula da kaina, ba zan ba ki kunya ba, ki taya ni da addu'a, Ubangiji Allah ya sanya zuwana ya zame mana alkhairi baki ɗaya"

"In sha Allah, addu'a ina nan zan ci gaba da yi miki ita da yardar Allah."

Nana ta haɗa kayanta, amma ji take kamar ta fasa tafiyar, amma ta ƙarfafi zuciyarta, ta hana hakan yin tasiri a ranta.
Ranar Asabar, da safe matar ta zo domin tafiya tare da Nana.

Nene ta ce mata "Dan Allah gata nan amana, Hansatu, kar ki kai ta idan za a cutar da ita, kin ga yaro ne da ita ƙarami, dan Allah idan akwai matsala a gurin nan, gara ki saka a sallamo ta ta dawo gida."

Hansatu ta ce "Haba Nene, ya ki ke haka kamar ba ki yarda da ni ba ne?"

"A'a ba rashin yarda ba ne ba, 'yar amana ce shi yasa nake jadda da miki, ga kuma ƙaramin yaro da take da shi"

"Ba ki da matsala fa, ki kwantar da hankalinki"

Nana ta kalli Muhsin, da yake jikin Nene, yana wasansa, idanun Nana fal hawaye ta ce "My little Sayyid, zo ka yi sallama da Umminka" ya taso daga jikin Nene ya nufo Nana.

Hatta dogayen gaɓoɓin jikinsa, irin na Sayyid ne sak.

Ta rungume shi a jikinta, hawaye na zuba daga idanunta "Allah ka kula mini da ɗa na, Allah kar ka saka wani abin cutarwa ya same shi, Ubangiji Allah ka sanya na je na dawo na tarar da shi lafiya" ta furta a hankali ƙasa-ƙasa.

Ta ɗago ta kalle shi ta ga yana yi mata murmushi, ta sumbaci goshinsa, ta miƙe ta ɗauki jakar kayan nata, Nene ta rako su har bakin ƙofa, suka hau abin hawan da Hansatu ta zo da shi, suka tafi.

08081012143

68

Nana ta din ga waige, tana hango su Nene tare da Muhsin, har suka ɓacewa ganinta gaba ɗaya.

Hansatu su na tafe su na ta  hira da direban motar, aka biya gidanta, aka ɗauki wasu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login