Showing 111001 words to 114000 words out of 202729 words
mata yakara samata tsoron Allah da tsantsan nadama aranta kullum sallan darenta saitayi addu’a kan Nura yakomar da ita dakinta, aurenta da rufin asirinta dan duk business da kudi is all trash idan ba namiji.
Yauma kaman kullum ta tashi tayi duka abubuwan datakeyi ta daura ruwa awuta taji da kanta da cikinta na ciwo wanda tun jiya da daddare taji hakan amman datai bacci ta tashi bata karaji ba sai kuma yanzu datake kitchen din nan.
Iza ruwan tayi tamike tsaye ahankali saitaji maranta ya rike sosai mamaki tayi period zatayi ne to ko shine ai bata ciwon mara haka, daurewa tayi tana dafa bango ta lallaba tafito daga kitchen din tana fitowa kaman ance oya kara tafiya mugani kawai kafanta ya rike tana ganin jiri d next thing kawai ta zube awajen daidai Baba da Amadu na shigowa gidan tana landing akasa akan idanunsu, Baba yace “Subhanallahi Khadija” da gudu yayi wajen ya tallabo kanta tana bude idanunta kadan kadan tana kallon su, Baba Amadu ne yafara ganin jinin dakebin kafanta dasauri yace “Yaya kalli” dasauri Baba yakalli kafanta yace “Subhanallahi, je tada mota” daidai Mama nafitowa jin hayaniya ganin Hadiza zube akasa ga jini a kafanta yasa dagudu tazo wajen hankalinta tashe abinku da uwa Baba yace “Hadiza nada ciki ne?” Arude Mama tace “ciki?! Ciki kuma, Wlh bantaba sani ba, ko miyar bata taba tofarwa ba, balle zazzabi ko amai, banganta ma da alaman mai ciki ba kwata kwata, bari na dauko hijabi” wucewa tayi aguje ta dauko hijabi akasa Hadiza amota Amadu yarufo gidan sai asibiti wani madaidaicin private asibiti Baba yakaita daidai kudinshi ba irin na yan gayun nan ba, karbanta akayi akai ciki chan Dr yafito ya nuna Amadu yace “kaine mijinta”? Dasauri ya kalli Baba yace “a’a lafiya meya faru”? Dasauri yace “ina mijinta yake?” Anatse Baba yace “likita meya sami diyata nine mahaifinta? Meya faru take bleeding”? Cikeda damuwa likita yace “Baba ko’ina mijinta yake just call him yazo maza maza, bari nakoma ciki, ya iso kwaji ko menene” yawuce yakoma ciki, Mama da hankalinta inyay dubu yatashi tace “kira Nuran Malam, Allah ubangiji yasa yana kano” dan Jim Baba yayi saiya wuce yafita waje yaciro number Nura yayi dialing.
Cikin wani bacci mai shegen dadi sun gama watsewansu da Ummi yaji wayanshi na ringing hakan yasa da kyar ya iya yabude idanunshi, jaye Ummi yayi daga jikinshi ahankali yasa hannunshi yadauki wayan ganin Father Inlaw saida yayi dan jim har wayan ya katse bai dauka ba sannan yayi dialing number back cikeda girmamawa yace “Assalamu Alaykum Baba” dan ijiyan zuciya Baba yasauke yace “Nura ya gaji?” Ahankali Nura yace “Alhamdulillah Baba” anatse Baba yace “gamu a asibitin sangu yanzun nan muka shigo, kawai Hadiza ta sume gaban kitchen saiga jini ya balle mata” dasauri Nura ya yunkura ya tashi daga bakin gadon dayake zaune, anatse Baba yace “sunki gayamana komi Likita yace lallai lallai saina kira mijinta, ana nemanka saisa nakiraka dudda nasan kana Abuja maybe saina yasaka da Likitan awaya ko”?
Anatse Nura yace “ina kano Baba gani nan zuwa” ahankali Baba yasauke ijiyan zuciya feeling calm jin yana kano yace “toh” ijiye wayan Nura yayi yakalli Ummi dake bacci dukowa yayi yaja bargo ya rufanata yana kallon kirjinta da kullum kara girma suke yarasa dalili maybe dan yana matsasu ne oho yawuce bayi wanka yayi yafito ya shirya cikin wata farra yadi mai kyau yana cikin fesa turare Ummi tabude idanu kallonta yayi yace “kin tashi baby girl”? Gyadamai kai tayi ahankali saka agogo yayi yazo bakin gadon ya duko ya manna mata kiss agoshi cikeda so yace “zan fita me zan kawo miki idan zan dawo”? Murmushi tamai tace “babu abinda yakaika dadi ni kadawo da wuri kada in kewanka, me zakaci na dafa maka?” Murmushi yayi cikeda so yace “yau nama nakeso naci but bansan ko Hajiya nada naman rago ba idan akwai kimin farfesu idan babu call me zan kira akawo” gyadamai kai tayi tace “saika dawo Allah karemin Baban Amali” “Ameen Maman Amali” yafadi yanajan hancinta ya mike tareda daukan wayanshi yafita dakin Hajiya yaje ya sanar da ita tace “imaxa kaje Allah yasa lafiya” ahankali yace “Ameen” yawuce tareda shiga mota yaja yasan hospital din hakan yasa yaje yayi parking ya sauka tareda wucewa ciki yana shiga yaga su Baba da Mama gaban wani daki hakan yasa yakara sa wajen cikeda girmamawa ya gaisa dasu akunyace yana kallon dakin daya hango Hadiza da likitoci akanta ta glass door din idanunta lumshe, tsayawa yayi yay jim yana kallonta, kusan 10min yayi awajen saiga likitan da nurses din sunfito ya kalli Nura yace “kaine mijinta”? Danjim kadan yayi kafin yace “yes” “come with me please” Dr yayi magana yana tafiya Nura yabi bayanshi zuwa office nashi suka zazzauna Dr yace “why was parent nata skeptical about calling you danake nemanka?” Dan shiru Nura yayi sai chan yace “bana tareda ita ne yanzu” kallonshi Dr yayi yace “dudda haka dai cus na tabbata cikin dake jikinta nakane” kallonshi Nura yayi dasauri, gyadamai kai Dr yayi yace “yes matan ka na dauke da cikin kimanin 2month da sati biyu but unfortunately……” yadanyi shiru kafin ahankali yace “yafita cikin tayi barinshi!” shiru Nura yayi kaman ruwa ya cinyeshi awajen, arayuwanshi yanason yara, shifa baiki yaga yanada 20kids ba wlh cus he just love kids, da kyar ya hadiye abinda yaji awuya har saida Dr yaga yanda Adam Apple dinshi yayi motsi, ahankali Nura yace “Dr are you sure Babyna yafita? Inace ba yanzun nan tafadi aka kawota ba kunyi scanning ne? Taya kuka tantance cikin yafita”? Yayi maganan cikeda damuwa, dan murmushi kadan Dr yayi ganin mutumin nada son yara from maganan shi dukya rude ya dimauce, dan ijiyan zuciya ya fuzar yace “that’s even the reason yasa nace a nemoka inaso kayi signing this document, tana bukatan wankin ciki cus cikin ya zuba but bai gama ficewa tatas ba” dasauri Nura yadagamai hannu yace “nooooo!” sai kawai ya mike tsaye dasauri jin yanada hope yace “just give me bill let’s pay zan maidata hospital na Abokina” yayi maganan yana kiran Dr Tanimu instantly, ringing daya yadaga yace “kana hospital? Zan kawo Hadiza yanzun nan” kawai ya katse wayan duk Dr na kallonshi yajuya yafita nan da nan duk su Baba na kallonshi yabiya kudin komi yataho dakin da Hadizan take shida wasu nurses suka daurata kan wheelchair duk she’s unconscious suka fito su Baba suka biyosu, wajen motanshi Nura yawuce dasu duk su Baba na kallonshi, da taimakonshi suka dagata daga kujeran sukasa abaya sai a lokacin yajuyo arude ya kallo Mama dake tsaye taredasu Baba yace “Mama zoki zauna da ita anan saisu Baba su biyomu” Toh Mama tafadi ta taho ta shiga su Baba suma suka shiga tasu sukabar asibitin, sosai Nura ke sharara gudu bini bini yana juyowa yana kallon Hadiza da Mama tadaura kanta kan lap dinta, nan da nan suka kai wani babban private hospital na masu kudi already Dr Tanimu ya shirya daki da komi aka karbi Hadiza kawai Nura yasami waje ya zauna yana bug buga kafanshi akasa looking so worried, he’s just praying Dr Tanimu zai fito yagayamai nothing happens to babyshi yana cikin tommy Maman shi alive and health, Mama da Baba duk tana kallon Nura suke kusan yamafisu iyayenta damuwa har ranta Mama take addu’a Allah ya daidaita Nura da Hadiza dan Nura care about Hadiza alot, jibi yanda duk yadamu, kusan 20min Dr Tanimu yadauka adakin yafito dasauri Nura yatashi ganinshi yabi shi zuwa office kasa zama ma yayi yace “tell me babu abinda yasami baby na pls”.
There this connection tsakanin Nura da Hadiza i don’t know am i the only one seeing it ko kuma kuna gani???
Is this real love koko kawai affection ne as per anyi zaman tare da??
Hadiza Nura yakeso ko babyn shi dake cikinta???
💫 MATAN?? Ko MAZAN??💫
✍🏻M SHAKUR
EPISODE 3️⃣5️⃣
Wae har yanxu bakije shagon Habisma Underwears ba?
Kode bakya Maiduguri ne?
To shin kinje shafinta na Instagram ko TikTok?
To yaude ki leqa Instagram, base kinyi following dinta ba, kawae kije Kisha kallo, in akwae wani abinda kike buqata Baki gani bama kitambayeta, wasu abubuwan basa samun dama suyi posting dinsu!
@habisma_underwears. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=11rv83nzhagn6&utm_content=i5wy1kf
***
Yau I need to get somethings off my chest.
So a lot of people nata zagina, (M Shakur baki da hankali, me Hadiza tamiki kodai sunan kishiyanki Hadiza ne, akwai wata Hadiza data taba offending naki ne, the hate you have for Hadiza is too much, this writer don’t know what she’s doing, this writer is selfish, she’s bias, Haba abubuwa sunma Hadiza yawa bakida tausayine, wannan littafin baida ma’ana idan naji wasu zasu karanta ma zan hanasu, M Shakur I hate you) hmmm my people babu abinda ke bracket din nan da ba’a gayamin ba and more all because of this book MATAN KO MAZAN???
Now listen!
If you can’t take this book kidena karantawa! Allah yasan ni banjinma family mu akwai me sunan Hadiza ba or wata Hadiza ta tabamin wani abuba, abubuwan nan dakuka gayamin all because I am trying to create awareness and still teach something on top of that kesa ake cema mata munada brain din KIFI!
Are you even blind to think this book is about kishiya??? My dear this book is about feminism, are you too blind to see abinda nakeyi in this book?? Book din danai involving full circle na zamantakewa Mata, Miji, and Familyn su da iyayensu!
Kun dauka inayin this book to downgrade first wife ko second wife ne?? Ask yourself Maisa nakawo Hajiya, Kannen Nura, Hadiza, Baba and yan uwan ta, Su Zeenah and co just ask kanki.
I write this book to tell you what feminism is! To tell you how feminism are affecting our homes! To show you the implications of feminism! Abinda feminism kesa ki loosing, and to show you the end result of feminism, banda haka to show you how yan uwa, friends and family suma suke taka rawan gani in everything.
I am hurt da all the insult but it’s okay! Allah knows best!
Just remember one thing ko kina team Hadiza ko Ummi ko Nura your judgement doesn’t influence my writeup sakon danakeso na isar saina isar da shi!
Idan bakiso ki karanta karkiyi as simple as that!
35
Shigowa office din Mama da Baba suma sukayi hankali adan tashe, cikeda damuwa jin har lokacin Dr Tanimu bai bashi amsa ba yace “tell me, did you save my baby”? Dr Tanimu na kallon Nura a natse ya girgizamai kai cike da damuwa ahankali Nura ya dafe kanshi tareda zama akan kujeran gaban table din dabas, Mama da Baba sukai salati, ahankali Dr na kallon Nura da har lokacin ya dafe kanshi yace “I am so sorry Nura, the thing is cikin yadan kwan biyu da lalacewa ajikinta kawaidai yau ne Allah ya kaddara zai fita, sorry Abokina, Allah yasa mai ceton kune” su Baba suka amsa Ameen, Nura yadade ahaka shi mutum ne mai tsananin son yara, he loves children, he loves children, dafashi Baba yayi yace “ya isa Nura Allah sa mai ceton ku ne” gently Nura yadago kanshi idanunshi sunyi ja ya kalli Baba tareda gyadamai kai, Baba yace “saika fito” shida Mama suka wuce suka fita, da kyar ya iya signing amata wankin cikin, yaciro wayanshi ya sanar da Hajiya, ita Hajiya ko kadan bataji dadi ba dan tanason jinin danta kodako daga jikin waye zai fito kuma tasan yanda Nura keson yara yawanci yana yawan gayamata yanaso Hadiza takara haihuwa amman ita tanason spacing yara so she really felt bad itama addu’a tamai suka katse wayan.
Fitowa yayi daga office din da tuntuni Dr Tanimu yafito yabarshi shi kadai, wucewa yayi inda su Baba suke zazzaune a reception din, sai kuma yakasa zama yawuce hanyar dakin tiyata din dayagani an wuce da ita, yakasa tsaye yakasa zaune sai zagaye yake awajen, chan yaji ihun Hadiza wlh saida kanshi yasara dasauri yayi wajen dakin da aka shigar da ita wanda yake kusa da dakin tiyata room, wata Nurse yagani zata shiga ciki tace “Sir you are not allowed to be here” cikeda damuwa sosai Nura yana kallon kofan dakin yace “why is she screaming like that please? Ba amata alluran kashe zafi bane?” Ganin yanda yadamu Nurse din tace “Sir trust me ahankali ake mata nan da 10min angama baya daukan lokaci jeka zauna please” Gyadamata kai Nura yayi yawuce jin yakasa standing ihun sai kawai yawuce fuuu yafita.
Duk su Mama da Baba na kallonshi chan saiga Anty Jams tashigo asibitin hankali tashe tawuce wajensu Mama.
Nura na tsaye jingine da motanshi wayanshi yahau ringing daga wayan yayi ganin Baba ne yasa yamaida wayan aljihu yawuce ciki dasauri, Baba yagani yana kokarin fitowa yace “angama an fito da ita anma kaita dakinta idanunta biyu Alhamdulillah” Dan ijiyan zuciya Nura yasauke, suka wuce shida Baba ciki har zuwa dakinta, ahankali Baba yabude kofan Nura na biyeda shi abaya private room ne na mutum daya idanunshi kyur kan Hadiza da idanunta biyu sun kumbura sosai sunyi jaaa ga zufa agoshinta gashin idanunta sun tartare alamun tasha kuka tana kokarin kurban ruwan dumi da Anty Jams ke bata babu wanda yagaya mata Nura na asibitin but kawai kamshin turaren shi ne yadaki hancinta da sauri tajuyo da kanta ta kallo wajen kofan, hada idanu tayi da Nuran dake kallonta bayako kyafta idanu yana kokarin shigowa dakin biyeda Baba gabanta yawani kalan fadi ganinshi, dauke idanunshi yafara yi daga kallonta yatura kofan bayan yashigo ya rufe ya tsaya daga wajen Baba yakarasa gaban gadon ya kalli Hadiza dake kallon Nura takasa cire idanunta daga kanshi yace “sannu sannu kinji Khadija, yaya jikin?” Ahankali tace “Alhamdulillah Baba” Baba yace “meke miki ciwo yanzu”? Wajen maranta ta nuna tace “nan ne kawai amman kadan” hannunshi Baba yadaura awajen ya tofa mata addu’a yace “zai daina yanzun nan, bari naje nazo” yakalli Amadu kafin yakalli Nura yace “bari nadanje nazo Nura ai kana nan ko”? Gyadama Baba kai yayi, bawai Baba nada wajen zuwa bane kawai yanason yabasu space ne sun rasa dansu yanzun nan is only right suyi magana akai, Mama itama ta dauki nufin abinda Baba yayi ta kalli Jams tace “muje muhado mata shayin akawo wani riga ko Jamila” Anty Jams tace “to Mama” suka wuce suka fice dakin yarage daga Nura sai Hadiza dake kallonshi kaman yau tafara ganinshi yakara mata wani irin kyau a ido kaman tai shekara bata ganshi ba haka takeji, fatanshi yakara haske yanda kasan wani balarabe, she feels kaman yazo ya rungumeta and just talk to her kotaji dadi, bata tabajin ciwon rasa abu kaman yanda taji na cikin nan ba, da kyar cikin muryan mara lafiya dake a bala’in kwance sounding so weak tace “ina yini Baban Amali” dan kallonta Nura yayi kaman bazai karasa gaban gadonba saikuma yadaga kafa atsanake yakarasa gaban gadon ya tsaya tareda folding hannunshi a kirji yana kallonta kaman yanda take kallonshi heart dinta na racing kinship very close to her duka kamshin turarenshi na shiga hancinta, asanyaye akuma taushashe yace “are you having any pains?” Har cikin jijiyoyin dake zuciyanta taji tambayan dayasa zuciyanta yayi wani irin melting, girgizamai kai tayi ahankali, duk yanda take kokarin danne hawayen yakasa, she just wanna cry and cry and cry for him, she just wants to cry for her Nuri, hawaye ne masu bala’in dumi suka zubo daga idanunta takai hannunta da sauri tashare cikin wani kalan sanyin murya tace “I have no idea wlh inada ciki Nuri, nida from day one na sami ciki nake laulayi, but this is different banji komi ba, I lost our Baby Nuri, wlh koda wasa bansan inada ciki ba, I lost my baby, it’s hurts” tafashe da kuka sosai mai tsuma rai, he knows Hadiza so well she hardly tell lies, hakan yasa tana fadin batasan tanada ciki ba ya yarda without a doubt, cikin kuka sosai taga an miko mata handky hakan yasa tadago rinannun idanunta ta kalleshi hada idanu sukayi takasa tantance exact reaction dake kan fuskanshi but she’s happy yayi offering handkerchief nashi for her, hakan yasa tasa hannun ta ahankali tana kallon fuskanshi kaman bata taba ganinshi ba ta karba asanyaye tace “thank you” kai handkerchief din tayi kan fuskanta kamshin Nuri da warmth dake jikin handky din na jikinshi saitaji yakara tsumata tafashe da kuka sosai wanda yamafi nada, why will she make this coolest Man to hate her harya rabu da ita? Why did she pushed him to the wall, dan lumshe idanu Nura yayi yabude su ya daura akanta ahankali yace “stop crying please haka Allah ya kaddara, Allah yasa mai ceton mune, stop crying okay” yafada warming kaman yana lallashinta gyadamai kai Hadiza tayi ahankali tana goge fuskanta kukan yaki tsayamata she just wanna hug him, ahankali yace “bari naje naga Dr Tanimu” gyadamai kai tayi yajuya da sauri zai fice haryakai kofa tace “Nuri!” Tsayawa chak yayi batare daya juyoba dan lumshe idanu yayi ahankali yace “Nura dai” tsinkewa Hadiza taji zuciyanta yayi cikin murya dake dauke da tsananin shaukin so tace “I love you Nuri! I still very much do, I can never ever love anyone like you, Nuri forgiv…..” dasauri Nura yabude kofan yafice batare daya gamajin maganan ta ba Hadiza tafashe dawani kalan kuka kaman ranta zai fita.
Office na Dr Tanimu yawuce, zama yayi Dr Tanimu yakalleshi yace “sorry about your Baby Nura” gyadamai kai Nura yayi yay shiruuuu sai chan ya fuzarda iska yadago idanunshi da suka danyi jaa ya kalleshi yace “is something else wrong with her ne”? Dasauri Dr Tanimu yace “nope kaga wani abune”? Dan lumshe idanu Nura yayi kaman baiso yayi magana sai chan ahankali yace “tayi duhu sosai, ta rame dik ta kode please kamata proper check up Dr Tanimu, she once had heart issue please kadubamin ita” ahankali Dr Tanimu yace “I think she’s stressed ne, stress din nema yaja mata barin nan, but dudda haka zan mata proper checkup idan yaso gobe sai ayi discharging nata daman anjima nake shirin nai discharging nata” gyadamai kai Nura yayi sai chan
25, August 2025
Saadatu Ali
Yes