Showing 87001 words to 90000 words out of 202729 words
yace “ba mistake bane ga sunana” yakalli secretary yace “you can go” tawuce tafita Nura yashiga bude file din, yaciro takardun ciki yashiga karantawa kaman wanda akacema yayi freeze kawai yayi freezing dasauri Alhaji Musa yace “lafiya menene?” Dasauri ya karbi file din gabaki daya daga hannun Nura yana karantawa dasauri yakalli Nura yace “ana nemanka gobe by 10:AM nasafe a kotu, Hadiza tayi suing you for domestic abuse!!” Sosai Alhaji Musa ke kallon Nura dayayi mutuwan zaune ranshi abace yace “meya faru kuma I thought kacemin kun shirya kun maida komi past, why is she suing you for domestic violence? Kasan hakan zai iya sa kaje prison for good 3yrs kuwa? Is Hadiza trying to ruin you and your career or what, meka mata?” Sai alokacin yasaki dan murmushi da zai nuna maka how hurt he’s deeply yakalli Alhaji Musa yace “I slapped her jiya!” Cikin tsananin fushi Alhaji Musa yace “wlh there’s nothing you can tell me Nura mata yar boko batayi bane aduniya sam sam! Allah ya wadaran matan I know my right, I know my right, kai!” Musa yayi ihu ranshi yayi matukar baci danko ba’a gayamai ba yasan waye Nura ba mutum mai dukan mata bane koda ya mari Hadiza jiya shi yasan wlh ba karamin abu bane zaisa Nura yadaga hannu ya Mari Hadiza ba.
Ganin yanda Nura yayi shiru yakasa motsin kirkima saiyaji yabashi tausayi, look at Hadizan daya wulakanta Ummi sabida ita thinking ta chanza yanzu zasu more rayuwa su dawo lovers din dasuke ada, dudda yaki admitting wulakanci yama Ummi but just look at abubuwan da Hadiza keyi, meke damun matan zamanin nan ne? Ta ina namiji da mace suka taba zama daya iyye? Wai what is wrong with matan yanzu ne haka iyayensu sukayi? Ba’a musu tarbiya bane agida? Iyayenmu mutane masu daraja mazajensu ne, kusan bauta musu ma suke, basu ganin yanda iyayen su ke rayuwa da mazajensu? ilimi haukane? What is keda mijinki dayane, ke kawai abarki kiyi komi yanda kikaga dama? Miji yace A, kice B har zuwa Z, ace kiyi kice bazakiyi ba, mesa wasu matan keda brain din fish??
Zama yayi kısada Nura ahankali yace “idan kaje goben just buy lawyer nata kawai akashe case awajen kafin alkali yazo, da kudinka a aljihu karka wahala abanza” murmushi Nura kawai yayi ahankali yama kasa cewa komi sai chan yace “Musa bani labari dan Allah” Musa jiyayi idanunshi sun cicciko da hawaye Nura yabashi tausayi ana wani zamani da kullum mata ake tausayama cus mata are weak waye, waye, waye but wlh idan akai looking deep akwai wasu matan da kawai sunfi karfin mazajensu ne duk ta yanda zaka kalli abin, infact matan ke soyama mazansu aya a hannu not the other way round, Hadiza na yanda taga dama da Nura kodan taganshi mutum mai hakuri ga yafiya sannan yana sonta, Nura is this type of person that hates hurting mutum baida riko that is just Nura, jibi dai abinda yamai jiya na ya saki Ummi ya aura da wanine yau bazai kulashi ba but because Nura is just Nura magana daya biyu sun shirya kuma har abada ya manta da maganan kenan, that is just Nura is his personality his nature bazaka iya chanza wa ba, ai shi kanshi wani zubin yakanji haushin Nuran for yanda yake barin Hadiza na getting away da so many things, haka kawai Allah ya yo shi, Nura hates hurting mutum, Nura nada hakuri, Nura nada yafiya, sannan Nura ya tsani takurama mutum inhar u are happy da abu zai barki kiyi, da ace zai iya zuga Nura dudda ba’a shiga tsakanin miji da mata dan just imagine abinda yama Ummi balle ma shi Aboki daya zugashi ya hakura da auren Hadiza kawai gabaki daya, taje ta auri namiji da baida matsala da mata maiyin feminism shikenan.
Amman banda jakanci da bahaggon tunani irin na Hadiza mutumin da yau shekara nawa kuna aure bai taba dukanki ba yau saiki makashi a kotu yana uban yaranki bazaku iya resolving issue din agidaba saikin tonamai asiri a duniya, and jahilcin da mata keyi is saisu dinga maka abi suga kaman kai sukema not knowing anything dazaiyi affecting Nura is affecting her as well koda ba directly ba, duk abinda yayi affecting Nura ayau will affect yaranta koda ace ma basa tare, if something affects yaranta ai yayi affecting nata as well so then menene riban tonama kanku asiri aduniya?? Sabida mijinki ya mareki sau daya in 10yrs kına tonama kanku da yaranku asiri wlh Hadiza is so shameless bamata da kunyan duniya.
Dafa Nura yayi ganin baison maganan yace “kasan Maman Humaira tasoma sakan mini gurasa fa dana nunata ke kinga nabi Alhaji Nura kauye yakaro aure nima fa auren nan nakeso nayi shine ta natsu”
Sosai Alhaji Musa yadinga ma Nura hira, office dinshi dabaije ba kenan har 1 nadare wlh suna tare just because baiso yanarshi shi kadai cikeda damuwa sannan suka koma gida.
Yauma adakin Aman ya kwana 4:30AM yatashi yayi wanka yasa kaya yabar gidan zuwa masallaci around 6 yadawo gidan zai bude mota ya shiga aka bude kofan falo Hadiza ne tafito tana sanye da bubu yana kokarin shiga mota tace “wato kaga sammaci bazama kazo ka rokeni, be on your feet and genuinely bag sabida nai withdraw the case ba” kallonta Nura yake daga head zuwa toe sai kawai ya shiga mota bai cemata uppan ba, abin ya masifar kular da Hadiza kaman ta kurma ihu wato ita zai maida mahaukaciya dasauri tazo wajen yana kokarin tada motan ta tsaya wajen kofan tabude cikeda rashin kunya dan yanda kasan zata makeshi tace “ohhh ni kakema girman kai imagine level na ignorance naka, don’t worry zakayi ladabi a prison yau stupid wicked man kawai mayaudari kawai” hannunshi yasa yakalleta yace “saki”ihu tamai da saida gateman yafito da gudu tace “bazan saki ba Nura!” Kallonta Nura yake idanunshi har sun kada sunyi ja, Hadiza tace “zanyi maganinka Nura, wlh zanyi maganinka dan kai karamin da duniya ne, muhadu by 10” tawani bugamai kofan motan Allah yasa hannunshi baya wajen da wlh saiyay sustaining injury jan motan Nura yayi batare yabar gidan, Hadiza jitayi ranta na baci har kasan zuciyanta bata wani so suje court dinba taso yazo ya lallasheta kawai ta kira ta janye case din saisama ganin bai biyota ba ita tazo nan tunda ta tashi take gadinshi yadawo daga mosque a window ta falo, tana ganin yadawo tafito with hope zaiyi sulhu da ita, koyadan mata magana mai kyau amman jibi yanda yamata banza ya mai data mahaukaciya sai taji gwarama data makashi kotun, juyawa tayi takoma ciki.
Karfe goma daidai motan Nura yayi parking gaban kotu inda Alhaji Musa ke tuki already Lawyer Nura na kotun, fitowa sukayi jiki asanyaye suka wuce ciki gaban court room din yaga lawyer shi tsaye yana ganinsu yace “yauwa muje ciki yanzu Alkali zai shigo”.
Ance a woman can make or break a man kun yarda???
Hadiza made this statement kana ganin karo aure shine zai baka peace din dakake nema to bazaka taba samun peace din nan ba, from abinda muke gani Nura ko yakasa samin peace din dayake craving right???
What action kuje ganin yakamata Nura yadauka akan Hadiza??
Yakokarin ya gyarata ta baki taki, yayi ta love taki, yayi ta family taki, Mezaima Hadiza ta gyaru????
But then again NURA yabani tausayi is not easy wacce ka keso tai hurting naka😭
Hadiza fans I have just one question danake so namuku, inhar Love bai chanza Hadiza ba, me kuke ganin zai iya cire wannan feminism din daga jininta???
Mata maza 🔊
Dukan mace ke jawo case din dambe between mata da miji, daganan kaga an kashe juna, ko mata ta kashe miji ko miji ya kashe mata, ko ajima juna rauni mai muni Allah ubangiji ya shirya damu.
💫 MATAN?? Ko MAZAN??💫
✍🏻M SHAKUR
EPISODE 2️⃣6️⃣
https://chat.whatsapp.com/KO6bdcXjxmh2l6pM6T0meI
In mutum yanason yayi register Kuma yayi siyayyar 🌟3 free registration ne
Kuma Ina adashen products din GHT in mutum beda halin Siya Nan take
08066136431
Note: Ni ba lawyer bace! Though I consulted some lawyers irin su Majal and co😍 Incase kunga mistakes no mind me, I be health personnel ejor❤️
26
Shiga cikin court room din sukayi hada ido yayi da Hadiza dataci gayu yanda kasan zataje gasan kyau tana sanye dawani vilisco embellish atampa maroon ta kafa daure tayi kyau gefenta kuma Zeenah ne zaune itama ta kallo Nuran, dauke kai yayi daga kallonta yawuce yazauna kusa da lawyer shi while Alhaji Musa yazauna a daya daga cikin kujeran dake row din bayansu, Hadiza itama tashi tayi tawuce tazauna kusa da lawyer ta wata attajiran mata ne haka taci glass Mrs Oyenyi Chichi Ebenezar, daidai nan Alkali ya shigo aka tashi akai introducing case din sannan aka kira Nura kanta yafito ya tsaya yayi rantsuwa Mrs Oyenyi ta mike taje gaban Nura ta tsaya tace “Mr Nura kaida Hadiza has been married for 10yrs 9month correct?” Anatse Nura yace “yes” anatse matan tace “describe relationship dinta dakai a tsawon shekarun” dan shiru Nura yayi saikuma ya kalli Hadiza dake kallonshi kyur, Mrs Oyenyi tajuya takalli abinda yake kallo tace “are you trying to blackmail my client Nura”? Dauke idanunshi yayi yace “no” Mrs Oyenyi tace “to bama kotu amsan tambayan da na maka” ahankali Nura yace “relationship dina da ita is just like relationship din any other couples, we live, we share good moments and we have arguments just like every other couples do” Mrs Oyenyi tace “babu any history of abuse ko molestation” Dasauri Lawyer Nura yace “objection my lord, mesa take sa magana abakin client dina is just kaman tariga tai concluding cewa client dina is an abuser” Alkali yace “objection overrule cigaba” Mrs Oyenyi tai murmushi tana kallon Nura tace “ina jinka Nura” Dan shiru Nura yayi sai chan yace “bantaba molesting Hadiza ba or abuse her banda ji…….” Mrs Oyenyi tai blocking nashi tace “matanka tace kasha molesting nata not once or twice ko bataso tai wani abu dakai kanayi” dafe kanshi Alhaji Musa yayi cikeda rashin jin dadi, dasauri Hadiza ta waiga ta kalli Zeenah cikin whispering tace “bancema Mrs Oyenyi yana molesting dina ba what is she saying?” Cikin whispering Zeenah tace “ni nace takara dashi sabida yaji ajikinsa ai kin gayamin abinda yamiki kenan daya auro Ummi” cikeda rashin jin dadi Hadiza zatai magana Alkali yace “silent” akai shiru, Mrs Oyenyi tajuya tadawo gaban bencinta tadauki wani file ta taho ta bayar tace “mai girma mai shari’a Nura yasha yima client dina fin karfi, ihu, harma yakai yana dukanta yanzu, cikin file din nan na dauke da evidence na farko hoton fuskan Cleint dina ne Hadiza da fuskanta dazaka ga yatsu biyar na Nura sunyi jazur a fuskanta wanda har yakaita ga asibiti aka dubata takarbi pain killers, sannan auren Nura yazama babban damuwa ga client dina bata da kwanciyan hankali da peace of mind agidanshi haryakai ga just about a weeek ago tana asibiti for case na heart sabida damuwan shi duk evidence na medical history nata is there, ina mai rokon kotu ta bima Hadiza hakkinta duba da irin fighting datayı for her life a hospital for the past two weeks duka duka yaushe akai discharging nata amman harya mata kalan wannan marin what if marin yayi leading nata takara samin cardiac arrest bayan yasan clearly an fadi a asibiti bazata kara surviving ba??”
Tashi lawyer Nura yayi zaiyi magana da sauri Nura yadagamai hannu alamun baiso yayi magana yazo dashi nan ne dan kawai yamai arranging bail da sauran formalities, ahankali Nura ya kalli Alkalin dake kallonshi ganin yahana lawyer magana yace “Yallabai I am guilty!” Dasauri daga Lawyer shi har Alhaji Musa har ita Hadizan suka kalli Nura dan bata taba tunanin Nura ko lawyer shi bazasuyi gardama ba, dan shiru Nura yayi chan yace “I let my emotions get the best of me, and I sincerely apologize for that” ahankali yadaga kanshi yakalli Hadiza yace “Hadiza am sorry for slapping you and for all d pains dakikace nai causing miki” Nura zai magana Lawyer shi yatashi da sauri yace “Mai girma mai shari’a client dina ya yarda yayi laifi kuma yabada hakuri muna pleading for mercy to pay fine na domestic violence din da duka charges dinma” dan hamdala Hadiza tayi tana karkada cinyoyinta dan feets nata are so cold batason akai Nuran ta gidan yari she’s just hoping ayarda ya biya fine din.
Tass Alkali yagama rubuce rubucen shi kafin yadago yace “kotu ta yaba da yanda Nura bai bawa kotu wahala ba, ya karbi laifin shi sannan yabada hakuri, duba da baida wani bad record kotu ta yanke hukuncin rike Nura harsai yabiya fine na naira dubu dari uku, 300,000!” Dasauri Alhaji Musa yace “Alhamdulillah” Alkali yace “idan akwai wanda keda wani magana cikin parties din zasu iyayi” hannu Nura yadaga hakan yasa Alkali yace “ina jinka” tashi Nura yayi ya kalli Alkali anatse yace “inason kotu ta shaida ni Nura na saki matata Hadiza SAKI DAYA!” Wani kalan dum! Dummmm! Hadiza taji azuciyanta yayi dawani kalan sauri tadaga kanta takalli Nura hannunta na rawa rawa, Nura na kallon Alkali yace “inason kotun nan tazama shamaki tsakanina da ita, kada Hadiza tasake daga kafa ta taka gidana! Duka wani abu nata na cikin gidana daidai da cokali zan tattara nasa a mota yau ba gobe ba na aika gidan iyayenta inda na aurota, sannan kada ta daukan mini yarana! Alkali inaso kamin katanga da ita!” Hawaye Hadiza taji zasu zubo daga idanunta tarikesu gam tana fuzgar da iska da baki kirjinta kaman ana barza masara dasauri Zeenah tazo ta bayanta tana mata whispering “kada ki kuskura ki nuna kinji wani abu dan dadi zaiji, abinda yakeso yagani kenan” daurewa Hadiza tayi ta rike hawayen Alkali yagama rubuce rubuce yace “you can sit” yakalli Hadiza yace “kaman yanda kikaji mijinki ya sakeki kuma yamiki shamaki da gida wanda yake nashi, dan haka kada ki kara sa kafa agidan shi kikai haka zai iya daukaka kara akanki, zancen yara kuma dake da shi zaku iya daukaka kara kuyi case na custody yara” cikeda karfin hali Hadiza tace “no need yara nawa ne ko suna hannunshi ko suna hannun uban idan inason ganinsu zan kirashi shiya kawominsu, kuma dama koda bai sakeni ba ni zancemai ya sakeni, me akeyi da namiji mai dukan mata” wani dadi Zeenah taji hardama Hadiza tafi kasa kasa Alkali yace “kotu tazo karshe” yatashi yafice police sukazo aka wuce da Nura lawyer shi da Alhaji Musa suka bisu, court room din yarage saura su Hadiza, hawayen da Hadiza ke rikewa ne suka zubomata wlh bazamata iya describing in words how she’s feeling right now ba, bata taba expecting Nura zai saketa ba sabida ta makashi a kotu, tunanin baimazo ranta ba yanzu Nura yamata saki biyu kenan, Mrs Oyenyi da bata wani san komiba ita she’s just a lawyer tace “why are you crying? You should be happy a man like this dayayi inflicting so much pain in you yasake ki infact this calls for celebration ma” Zeenah tace “owooo tell her oo Mrs Oyenyi, I don’t know why Hadiza base her whole life on this guy not knowing yanzu ne zaki fara cin rayuwanki da kyau dakuma tsinke, ni dayama miki biyu yacikashe” dasauri Hadiza tadago jajayen idanunta takalleta Zeenah tace “yes you should be free of this Nura for good haba yanzu kuma abin takaici kina wani zubar da precious hawayenki sabida namiji wlh tir Hadiza kinji kunya, you are a disgrace to mata damukasan ciwon kanmu, you are a disgrace to all feminist out there” hannu Hadiza tasa ta share fuskanta tass tai murmushi tace “ba ina kuka sabida Nura yasakeni bane Zeenah, kuka nayi sabida kalman saki feels somehow ajikin mata, but danya sakeni sai mene harda wani amini katanga da gidanshi tunda gidan dirhami gareshi ko gidan sarkin dubai ne dashi ko prince of Saudi useless Man gidan da I can buy like 10 of it” Zeenah tace “owooo, tashi mutafi jor let’s go and celebrate book hotel and sleep today kafin gobe muje house hunting” dasauri Hadiza tace “gidan ki fa? I thought anan zan kwana”? Dan murmushin yake Zeenah tayi tace “ohh my bad ni nama manta ba matsala saiki kwana agidana, muje let’s call Baraka and pick her up a hanya” tashi Mrs Oyenyi tayi sukai sallama daman sun gama biyanta suka wuce ahanya suka dauki Baraka wacce Sam bataji dadin labarin ba amman ina ruwanta, deep down Hadiza is so worried amman Zeenah taki bata room to show how worried she is kuma itama din batason suce tacika depending on a man ko she’s a disgrace to feminist.
Sai bayan magrib suka tafi gidan Zeenah, babban gidane mai kyau but baimakai gidan Hadiza girma da kyau dinba dudda matar minister ce, shiga sukayi ciki, Zeenah na murmushi tace “ai you are full ko kina bukatan abinci naga munci mun koshi a inda mukaje bari nabaki ruwa kinsan ni yan aiki na basa kwana da yamma suke tafiya saisa kikaga zan baki ruwa da kaina” Gyadamata kai Hadiza tayi Zeenah tadauko ruwa taba Hadiza tace “muje na kaiki dakinki” dan kallonta Hadiza tayi saitaga kaman she’s rushing ko ruwan fa bata budeba amman bata damuba ta tashi tabita sukaje sama takaita wani daki tace “to saida safe”gyadamata kai Hadiza tayi dudda she wanted su danyi hira har zuwa irin 12 din nan nadare but she guess tagaji tunda tun safe suna tare wucewa Zeena tayi agurguje ta sauko kasa ta kwashi takalmin Hadiza dake gaban kofa tashigo dasu da sauri ta wuce kitchen dinta taboye takalmin abaya shi kofa sannan tashiga kitchen agurguje fa tashiga hada girki.
Hadiza datagaji dan bayan tayi sallan isha’i bacci yayi awon gaba da ita cikin bacci mai nauyin gaske taji hayaniya da kaman karan fashewan abu hakan yasa ta bude idanunta ahankali baccin na fita daga idanunta muryan namiji taji yana cewa “takalmin waye wannan Zeenatu? Wakika kawo gidan nan bayan nagaya miki banason ana zuwa mini gidana?” muryan Zeenah taji kasa kasa bataji metake cewaba saikuma chan takarajin karan fashewa abu kaman plate
25, August 2025
Saadatu Ali
Yes