Showing 24001 words to 27000 words out of 202729 words
dake kan fuskanta daya rufe yayi shiru, kamshin da Ummi taji na shiga hancinta yasa tadan ware two of her right fingers kaman munafuka tadan bude idanunta dan so take taga ina yake dan yanda takejin kamshin turaren nan nashi karaf suka hada ido ya leko fuskanta ta spice na yatsun ahaukace ta yunkura zata tashi karaf yariketa hannunshi daya yakai ta waist nata yarikota dasauri taboye kanta akirjinshi sosai takejin kunyanshi, yanda yaji fuskanta akirjinshi yasa ahankali yasaki hannunta yakai dayan hannunshi daman bayanta yaturata tashiga kirjinshi gabaki daya sannan yacire hannunshi daga waist nata yasa dukansu abayanta ya rungumeta da kyau tareda sauke ijiyan zuciya ataushashe yace “Assalamu Alaykum Matata Zainab” wani irin sanyin kunya Ummi taji tanaji takasa yarda jikin Alhaji take arungume haka, wlh kirjinshi bala’in taushi ga fadi kaman wani katifa, tun tanajin kunya taki sakin jiki hartai lamo tadaina motsi tanaji yanda kirjinshi ke beating ahankali, wayanshi ne yahau ringing batare daya saketa ba yazare hannunshi daya yaciro wayan yakai kunne Ummi bataji akace ba, amman da muryanshi dataji harya chanza launi yace “bari nagama sallama da iyalina nafito” yana maganan yacire wayan daga kunnenshi yamaida aljihu kafin ahankali yakai hannunshi daya yadago kanta daga kirjinshi maida kanta tayi da sauri, murmushi yayi cikin whispering yace “ina sonki Ummi, amman banji amsan soyayyata aranki ba aka daura mana aure kina sona”? Noke kanta tayi akafadanshi kaman yanama yarinya magana yace “kunyana kikeji?” Gyadamai kai tayi, ahankali yace “nazama mijinki yanzu babu ragowan kunya, yaushe zaki bani amsa?” Kanta yasake dagowa for the second time wannan karan batai musu ba ahankali ya manna mata peck agoshi batare daya cire bakinshi akan goshinta ba yace “zanbar miki Meena da some mopol anan ranan itiyau zan dawo na dauke, banda yawo, idan kinason wani abu ki kirani ki sanar dani kinji”? Gyadamai kai tayi ahankali yasa hannunshi a aljihu yakamo soft hannunta yasa bandir na 500 aciki yace “ki ijiye kudin nan tare dake kome kikeso kiyi dashi kinji”? Gyadamai kai tayi, har lokacin bakinshi nakan goshinta lips dinta ya kalla tanada a bit chubby soft bottom lips sai na saman is slightly thin a bit pinkish a bit dark he seriously wanna kiss her like right now but then yanason tazama comfortable dashi dan ijiyan zuciya yasauke kadan kafin ahankali yasaketa yace “zan tafi” dan komawa baya kadan tayi kaman kada tafita daga jikinshi tana sussunnar dakai tace “Allah maidaku gida lpy nagode da abubuwan daka kawoma su Gwaggo Allah kara budi mai albarka” Ameen yafadi yayi wajen kofa dan juyowa yayi yakalleta kaman yadauketa yakeji yadai daure yadaga labule yafita daga dakin.
Bin dakin Ummi tayi da kallo ganin littafai da byro akan wani dan table yasa taje wajen ta bude tsakiyan book yafalllontahsiga rubutu, dasauri take rubutun cikin 2min tagama tadaga takara karantawa sannan tashiga linke paper wani kalan linki tama paper kaman flower wow yarinyar is creative fitowa tayi daga dakin da sauri Aishan su tagani tabata tace “imaza kaima mijina Shatu maza kafin su tafi” da gudu Aisha ta fanfala sai alokacin Ummi tadaura hannunta kan bakinta jin tace mijinta, Aiaha nafita suna tafiya haba tabi motan da gudu tana ihu yaran anguwa suka bita suna tayata ihu ana. “Mota ku tsaya ku tsaya” abunku da yaran kauye, Musa yafara hangosu dasauri yace “Nura wanchan ba kanwar Ummi bace ke biyomu da gudu da tawaganta” lekawa Nura yayi ganin yanda yara ke gudu ana ku tsaya yacema driver ya tsaya parking sukayi da gudu su Aisha sukazo wajen 𝕄𝕦𝕤𝕒 dasauri yabude kofa dan daga Nura sai shi sai engineer Baffa na dayan motan, ana bude kofan Aisha da karfin muryanta tana haki tace “Yaya Ummi tace nabawa mijinta wasikar nan” tamikama Musa wasikar juyawa Musa yayi yakalli engineer dake murmushi sannan Nura daya hade rai Musa yamika hannu yace “to sannu da aiki Shatu kawo” hannu yasa zai amsa saiga hannun Nura ya fizge ya sa a aljihun gaban riga yabama yaran wasu kudi daya ciro daga aljihu yace “nagode” yaran suka kwasa aguje Musa yarufe kofa yace “jamuje direba” yakalli Nura yace “wowww Ango wlh soyayyan kauye tayi ne jibi wani wasika da aka aiko maka an mata wata kinmin fulawa kaga engineer billahillazi a kauyen nan zanzo nima na nemi amarya inaaa kai kaga yaransu ne sunsha kindirmo tun suna jarirai yanzu duk yakoma kirjinsu” dariya duk sukayi Engineer yace “kaidai kwarto ne Musa shegen gari, kai ranan kasa na kusan kashe madam wannan maganin basir ai bala’i ne” dariya Musa yayi suka cigaba da hira ganin haka yasa Nura yaciro wasikar yana yaban design da magic na maida sheet of paper into flower shape da Ummi tayi ya warware ahankali.
“Assalamu Alaykum Baban Amalily, wanda yazama mijina ayau rana uku ga watan maris.
Amsan tambayan kace awannan sakon”
Gyara zama Nura yayi yacigaba da karatu.
“Acikin wani bakin dare mai duhun duhu daban taba tunanin zanga haske awannan daren ba wani haske ya gauraye inda zuciyan Zainabu Ummi take, kasan haske nada zafi a ido dakuma fata sai wannan hasken ya kasance mara zafi, mai taushi ce dakuma da tsantsa kyawu, kyawu irin wanda bantaba sanin akwaishi ba awannan duniyan sunan hasken nan NOOR wato NURA! Ana haka wata kalan guguwa mai karfi ya taso dake dauke da kifiyoyi guda uku masu zafin rabasheshen dalman wutan kauna ce ke tashi daga jikinsu, suna zuwa chak! Chak!! Chak!!! Suka sossoki zuciyata, kifiyoyin nan guda uku na dauke da kalma guda uku ne na farkon yace I nabiyun yace LOBE na ukun yace YOU!!!, I lobe you My Noor Baban Amalily” Yihuhuuuu!!! Nura yabuga ihu kaman dan daba dayasa su Musa duka suka juyo suka kalleshi yace “wlh Yarinyar nan ta tashi kaina, billahillazi dauko matata zanyi, kai dereba juya kan motan nan kaga ku kusauka ku shiga dayan motan, ba’a taba gayama Nura irin wannan kalaman soyayyan ba, wayyoo zuciyata nima kifiyoyin dalman soyaya sun chakeni” tsayawa duk sukayi suna kallon Nura kaman kanshi ya kwance.
Hahahahah Guys rate sakon soyayyan yan kauyen M shakur naku, I crafted this on my own chaiii yayi making sense kuwa???😂😂😂😂😂
Ummi fa zata haukata mana Nura Hadiza sorry for you, just look at how Ummi ke feeding mijinki soyayyan kauye, soyayyan uneducated girl.
💫 MATAN?? Ko MAZAN??💫
✍🏻M SHAKUR
EPISODE 8️⃣
Adan birkice direba ya gangara zuwa gefen hanya yayi parking yin yanda Nura yabuga ihu, Nura yana murmushi sosai kaman wanda yaci lottery yakalli su Musa da duk suke kallonshi asankare irin ikon Allah din nan yace “kufita mana” dasauri Musa yace “ohhh Allah kana gwadamin halin Nura yau kaine haka kake rawan jiki kaman wani sabon shiga? Shekaran ka nawa yanzu kana buga odafere”? Kwashewa da dariya Engineer yayi yace “kai wlh dan iska ne Musa, mekuma Odafere” yakalli Nura yace “dan Allah kayakuri mutafi Nura, mukoma Abuja this one week Musa ya loda maka maganin basir kaga system dinka yayi refreshing afitar da toxins din ciki, sabon ruwa yazo yataru a buhu” dasauri Musa yace “itama bakasan da Gwaggon nata tace abarta abinda za’a mata ba kenan duk dadin kane fa, gyaramaka ita za’ayi fa, kuma ma ai da kunya kawani koma saikace wani saurayi, kawa Allah ka rungumi letter nan yarage maka zafi mutafi kai direba tada mota next week fa karenka zakaci ba babbaka” tada motan direba yayi badan yasoba yahakura cus yasan gaskiya suke fadi, koda suka shiga Abuja gidan engineer yaje yaci abinci yayi knack sukasha hira wuraren 11 yabaro gidan yakama hanya suwa gudanshi yakira Ummi amman wayanta akashe maybe ba chaji baiso yakira wayan Meena kuma around 11:30 yashigo gidan, yana bude kofan falon yasan Ummi bata gidan yau kaman ba falon da Ummi ta gyara dazu da safe ba.
Dakin gabaki daya a hargitse, school uniform din su Aman na nan falon da jakunkunan su da safa, dinning hargitse da plates ga ragowan abinci indomie yagani da egg is as if yaran basuci ba gadai cups na tea da ragowan slice bread da alamun abinda sukaci kenan, kitchen yaleka daganan dinning just indomie da Hadiza ta dafa tajuya kitchen din up side down kaman ba kitchen din daya shiga ya zauna aciki bane harya sha shayi rannan da Ummi ba, ijiyan zuciya yasauke yadawo falo da kanshi ya duka ya tattare kayansu na school sannan yabude baga nasu yaciro books nasu sunada homework ba’ayiba and wlh dudda Ummi is uneducated she manage ta koya musu homework duba ayyukan su nada yayi da Ummi ke tayasu duk sunci to menene ma amfanin auren Mai ilimi tunda bazata iya yima yaranta homework ba, kwasan komi yayi yawuce sama yakai kayan kowa dakinsu yana kallon yaran da ba’a musu wanka ba normal kayane ajikinsu bana bacci ba da Ummi tasaba saka musu, shiru yayi yanzu haka yaran nan zasuyi rayuwa, shi karan kanshi bazai iya kwatanta yanda yakeson yaranshi ba bazai dauki rashin kulan nan ba da rashin basu abincin nan ba ko kin musu homework ko uniform ma sabida yasan sunada wani set dazasu saka gobe ne amman what’s all this dakinshi yatashi yatafi yaje yayi wanka.
Da asuba as usual yafito harzai wuce yasauka kasa saikuma yajuyo dan yayadata tama yaran nan abincin school ta shiryasu gaban dakinta yaje tareda bude kofan yashiga ya kunna wutan dakin, bauu dakin yayi haske yatsine fuska Hadiza dake lafiyayyen bacci tayi jin haske, tadan bude idanunta kadan ganin Nura yasa cikin muryan bacci tace “Nuri am off salat ka tafiyan ka masallaci basaika tasheni ba” yana daga wajen yace “get up fix something for the kids and get them ready for school sannan basuyi home task nasuba, and arrange the house yayi datti gidan” wani kalan ware idanunta Hadiza tayi tasss takalli sama saikuma ta tashi zaune da sauri ta kakkalli gefe da gefenta dan she wanna be sure cewa bada ita Nuri yake ba ganin bakowa adakin yasa tanuna kanta da sauri tana kallonshi cikeda mamaki tace “Nuri ni kake bama order haka kake lissafo ma ayyuka haka?” Duk yanda taso kasa rike dariyan datakeji tayi tadan kyalkyala dariya tana nuna kanta tace “wait are u mistaking me for Ummi ne or wat dakake lissafo mini abubuwan da zanyi, idanunka gizo suke maka ne Nuri? Nayi kama da yar aikin mu ne? Wait ma kai what happen da u can’t do all of this abubuwan nan daka fadi are you not mahaifinsu? Can’t u cook for them? Can’t you bathe them and get them ready for school? Bazaka iya musu homework nasu ba? Who said shirya yara, basu abinci, getting them ready for school da gyaran gida responsibility mata ne kadai?” Babu wasa kan fuskan Nura yace “ki tabbatar kin tashi kin soma aikin dana fadi kafin nadawo gidan nan daga mosque” yana maganan yajuya yafita daga dakin mamaki yasa Hadiza tama kasa zama tashi tayi dasauri tasauko daga kan gado tafito daga dakin tabiyoshi abaya tace “Nuri ni kake commanding like that are you for real? Kalleni fa” tanuna kanta tana sanye dawasu arnaye kayan bacci tace “do I look like a house help? Listen fa Nuri lemme tell u something ko Allah yasan ni ba housewife bace, I have a business danake managing, I contacted agency masu kawo yan aiki babu wasu akasa za’a nemo mini, idanma zaka zauna and be attending to this children reschedule work naka do it tunda Ummi tatafi garinsu dankai ur company is big kaine CEO kanada manager dazasu iya managing komi niko banda manager, I manage everything about business dina nikadai banda sales girls danake dashi dake attending to customers namu but I do komi dakaina dan haka Nuri attend to ur kids, babu inda aka rubuta a musulunci cewa dolen dole mama ce zata dingama yara komi yaran nan na me and you get them, gaskiya I don’t have that tim…..” ganin Nuri yabude kofa yafita yasa Hadiza ta tsaya turus da mamaki, Nuri just walk out on her tanamai magana irin baida lokacin ta wow! Tana kallon kofan kirjinta na tafarfasa, da tayi niyan ko falon ne tadan tattare suyi sharing work din amman wlh tafasa tayaya zaiki girmamata ita ta girmamashi, wani disrespect ne hakan? Wannan sabon confidence din da Nuri yake mata kodan sabida yaga yasaketa tadawo gidan da next day ne yasa yake mata Iskanci haka, ta inama zata fara all this ayyuka Allah ma yasan bazata iyaba wlh, rabon datayi aikin gida harta manta to tariga tawuce wannan level din nayin aiki dakanta agidanta Allah ma yasani, idan tayi aiki agidan mijinta menene banbancin gidan ubanta da gidan mijinta? Kana gidan iyaye ne u must work, abaka umarni kabi, but your husband house suppose to be your paradise that’s the beauty of aure, kiyi duk yanda kikaga dama agidanki, kici karenki ba babbaka, tanada kudi mijinta nada kudi maisa zata tsaya da kanta tana all this silly household chores? No Nuri u can’t subject to into doing abinda zuciyana baiso yayi, itama shegiyan yarinyar nan akan wani dalili zata sakani in this tight spot, that stupid Ummi datawani tafi shegen kauyensu wai wajen kakanta, juyowa Hadiza tayi tarike waist nata tabi falon da kallo yanda yayi datti ga kwanukan abinci tsaki da ragowan food a dinning tayi tai ihuuu. “Wayyyooooo, Goddddd! A ina zan sami yar aiki yaune ni Hadiza? Ohhhh I can’t do this, how can I start doing this chores haba dan Allah, ai abin kunya ne, niba yar aiki bace ba I can’t do this wlh, ni nama manta yaya ake girki ma, indomie nan koni nakasa ci dana dafa jiya ewww, yuck” ta yatsine fuska, komawa sama tayi dakinta tawuce bayi abinta.
Dawowa gidan yayi around 7 yanda yabar falon haka yazo yasami falon sama yawuce Aman yagani da Amal duk sun zauna anan falon sama sunyi zugum kaman marasa lafiya, ganin babansu dasauri suka tashi sukai wajenshi Aman yace “Dady where’s Anty Ummi”? Amal kuma sai kawai tafashe da kuka tace “Daddy ina Anty Ummi tun jiya banganta ba she’s not in her room” tausayin yaran yaji dasauri yadauki Amal yakama hannun Aman yawuce dakin Amal yarufo kofa yace “Anty Ummi taje garinsu amman zata dawo next week I promise” dasauri Aman yace “daddy ka kaimu wajenta” shiru yayi yana kallon yaran saikuma yaga sun fashemai da kuka dukansu biyun atare dasauri yashiga lallashin su wayanshi yaciro yayi dialing number Ummi yana addu’a Allah sa akunne, kafinma wayan yayi ringin Aman ya karbi wayan yahau kan gadon Amali itama Amal tahau gadon kusa da Aman ta zauna wayan na ringing daya biyu Ummi tadauka cikin sweet voice nata data wani lankwasa ganin number mijinta tace “hello” atare yaran sukace “Anty Ummi” saikuma suka fashe da kuka atare, cikin kuka Aman yace “why did u go to kauye baki gayamana ba”? Amali tace “bakince zakije damu duk randa zaki kauyeba” Ummi jitayi zuciyanta ya tsinke dasauri cikin dabara tace “Aman wait one by one” a cartoon nasu ta koyi kalman, cikin kuka suma yaran sukace “one by one” ahankali tace “Aman daina kuka bari nafara magana da Amal” gyadamata kai yayi kaman yana gabanta cikeda lallashi Ummi jin yanda Amal ke kuka sosai tace “Amalily na, Amalily Dadynta, Yarinyar datafi duka yaran duniya kyau, ga gashi, gata yar fara, baturiya, balarabiya, Princess Amal Nura Wambai ammatana” wani kalan murmushi Amal tayi tana turo baki da saida abin yasa Nura yasaki baki yana kallon ikon Allah yarinyar dake kukane yanzun nan hartai murmushi sabida taji kirari ana cemata Ammata wai tafi duka yaran duniya kyau, gyara zama yayi yana kallonsu cikeda so. Ummi tace “banson Mudi yagane mini ke ne saisa ban gayamiki ba nazo amman zan dawo next week zan kawo miki goruba da aduwa da hanjin ligidi” dasauri Amal tace “tuwon madara fa”? Dariya Ummi tayi tace “harda tuwon madara Amal dina” wani ihu tayi tana tafi Ummi tace “tom jeki brush ba Aman wayan” bawa Aman wayan tayi tasauka dagudu tawuce bayi Ummi tace “takawanka lafiya d’a guda kuma daya tilo ga Baban shi, Mr Aman gogan zamani, matashin saurayi, dogo, yaro ga ilimi ga tausayi, yaron dayafi kowani yaro jin magana da hakuri kaman Baban shi, Amanu Aman babban yaya ga Amalily, haba ama Anty Ummi hakuri mana eh Yaya Aman” dan turobaki Aman yayi yana murmushi sosai yana juya idanu looking super cute ahankali yace “to nayi amman idan kinzo zaki mini Oumu Oumu mai cheese a tsakiya” dasauri Ummi tace “zanyi” murmushi yamata yace “bye bari naje nai brush” yana maganan yabawa babanshi waya yatafi bayinshi cire wayan Nura yayi daga Speaker yakai kunnenshi yadan lumshe idanu yace “nikuma mezan samu nida nafi kowa yin hakuri”? Dan murmushi Ummi tayi cikin wata narkakkiyan murya tace “barka da safiya Baban Aman da Amalily mijin Ummi kuma, ina kwana My Noor” wlh ko baitabajin sanyin dayakeji irin wannan dayakeji ba da gaisuwan nan datamai sai kawai yaji kanshi na kumbura, ahankali yace “Alhamdulillah ya darenki? Yasu Gwaggo? Meya sami wayanki jiya akashe” “Kowa lafiya lau, ba chaji ne, ya jikin Hajiya kuma yau zakuje asibiti?” Gyadamata kai yayi yace “eh zanje nakaita taga Dr” murmushi tayi tace “tom bari na barka kaduba Amal nasan wasa da ruwa take yanzu haka” dudda baiso ba haka yace “to zan kiraki anjima, kema kije kiyi breakfast, agaida mutanen gida” to katse wayan yayi yatashi yawuce bayin Amal shiyama yaran wanka ya shiryasu yadauki akwatin su yazuba musu kaya aciki komi dasuke bukata, yajawo suka fito falo Hadiza na zaune afalo taci uban gayu tasaka hill takada ma kanta tea tanaci da bread kadai anan kan kujera ganinsu duka da akwati yasa tace “ina zaka kaisu naga akwatinan su”? Batare daya kalleta ba yace “inda za’a kulamin dasu tunda bakida lokacin su” kofa yayi tabisu da kallo yaron ko kallonta basuyi ba, saikuma ta tabe baki ita adadinta ma atleast yau zatai zamanta ashigo without tunani su, amota ya lodasu straight gidan Baffan shi yayi dan Hajiya tacema yakawo su nan dan da ita ya tsaya yayi magana awaje kafin ya shigo gidan, akwai kananun yara agidan, anan
25, August 2025
Saadatu Ali
Yes