Showing 36001 words to 39000 words out of 202729 words
wanke, the next day nine da wanke wanke kene da shara same goes for girki, Hadiza Baba da Mama nada rufin asiri mun taso bamu rasa komiba but we were trained muma kanmu komi muke wanki, muje aike bamu da yar aiki Hadiza, mun taso munga yanda Mama kema Baban mu girki tabashi, tamishi komi, Nura ya nuna shi girkin ki yakeso yaci how many minutes zai daukeki kimai? Is just breakfast and dinner da rana yana office, Hadiza Nura ba dan Abuja bane that’s wat nakeso ki gane bazamfare ne girman kano, ya nunamiki he doesn’t want the Abuja lifestyle dole ne saikinyi lifestyle din to please your friends and co? This is peer pressure Hadiza, must u do abinda kikaga anayi agarinku? Anyi magana kice feminism you know your rights Nura yafiki sanin rights naki tunda har mutumin nan zai bude miki kasuwanci ya daukeki kuje garuruwa ki samo contact na suppliers ki saro kaya, Hadiza Nura na mugun sonki how many men zasu iya ma matansu abinda Nura yamiki yet baki da wanda zaki cima mutunci sai shi sabida kinganshi shiru shiru baida hayaniya kuma yana sonki saikikai abusing simplicity nashi” hawaye Hadiza ta share cikin muryan kuka tace “Anty idan baka rikema maza wuta ba cin ubanka suke, ga Baraka nan mijinta juyata yake kaman lagwani, yahanata business kudi sai wanda yaga dama zai dan yammata, gashi da mata ihu agaban kowa haka kikeso Nura yamaidani? Ya takani duk sanda yaso? Noo bazan yarda ba wlh, fire for fire yanzu shine new system na zaman lafiya tsakanin mata da miji agidan aure” Anty Jamila tace “Noo fire for fire is never option, look at you yanzu jibi yanda kike kuka kina bala’in son mijinki but girman kai da al’adan yahudu da nasara yasa you are gradually loosing him” dasauri Hadiza tace “I reject it Anty Jams, bazan taba loosing Nuri na ba, yana bala’in sona, duk yan uwanshi ne da Mamanshi suka gama zugashi, Nuri baitabamin hakaba, Nuri kome zanmai baya fushi dani, baida riko ko ijiye mutum azuciya, he will still come back to me and talk to me and call me, Nuri na baitaba shareni ba, wlh all this aikin Maman shi ne da kanwarsa kuma muzuba da ni da su” girgiza kai Anty Jamila tayi zatai magana Hadiza ta tareta tace “karki damu you’ve said enough Anty Jams ko’ina Nuri yaje zaizo har nan har gidan nan yasameni bawai ina kukane sabida abin yawani dameni ba, kukan danakeyi na bakin ciki ne cus nine yakamata na dinga cusama namiji kalan bakincikin nan ba namiji ya dinga cusamin ba ninefa Anty Jams is still me Hadiza bakatakani bama nabaka hot-hot balle kuma katakani, wlh Nuri zai gane ni yagasama aya a heart, saida safe” bama ta jira amsan Anty jams ba ta katse wayan ta ijiye wayan tanabin dakinta da kallo gidan gabaki daya bayamata dadi sabida yanda ba kowa ciki, mutum rahama ne hayaniyan yaranta is something, kawai she’s not enjoying komi, mamaki take take kuma karayi itane Nuri bazai returning call nataba, lallai Nuri don get liver, tasaba saidai ita ta katsemai waya amman wai itane ya katsema waya tun ranan yaki kiranta back, yaki replying messege nata, hmmm takasa yarda ita Nuri zaima haka cus baitaba mata iskancin maza haka ba tunda sukai aure sai yau, da wannan abin har gwara ya mareta ma eh tasan mari ne bakaramin shiganta wannan silent da ignoring attitude din da Nura yamata ke damun zuciyanta ba.
****
Bayan 2weeks
Cur Nura yabuga two weeks yana gogan lafiyayyen amarci shida Ummi, yaki kiran Hadiza ko returning calls nata but yana kiran mai gadinshi everyweek yaturamai kudi ayi cefene wanda dama haka yakeyi dudda yasan ba girkawa zatayiba Mamanshi da yaranshi kusan kullum sai sunyi waya daman.
Lafiyayyen soyayya yake bugawa shida Ummi jinshi yake kaman wani sarki ko shugaban kasa ne ma zai fadi, baitaba sanin yar kauye can give him this much respect, affection, peace and love ba saida ya aureta, wlh ayanda Ummi kemai da ace an halasta a addini cewa mata ta bautama mijinta da Ummi zata bautamai ba tantama that girl is just an Angel, saisa shima he became like a fool kome takeso koda batace tanamaso ba zai mata.
Yau zasu koma Abuja jirginsu is by 1, yadan fita haka yabarta tana yima su Amal wasu kayan zaki a kitchen, dudda she’s hiding it but he could see fear a idanunta.
Tana zaune a kitchen tana kallon wasu cute robobi data jera su Iloka, kwakumeti, tuwon madara, tsami gaye, gullisuwa data musu tayi shiru tana tunani, bini bini gabanta na fadi batasan yaya zata kalli Anty ba, ita tunanin ta kenan danta dauka Nura ya sanar da Hadiza, baitaba mata maganan Hadiza ba ko yace any bad thing about her kullum abunsu suke baya kawo sunan matarshi aciki. Tana zaune taji an manna mata kiss dasauri ta dago kanta Nura ne, robobin ya kwasa dagakan kujeran yazauna yana facing nata yace “ya akayi Hajiya Ummi tunanin me kike”? Murmushi tamai cikeda wayincewa tace “bakomi kawo naje nayi parking a akwati” tai maganan tana mikewa dasauri tajuyar da kanta zata tafi karaf Nura ya kamo hannunta tsayawa tayi batare daya juyoba robobin ya kalla yace “baki amsaba zaki tafi kuma gashi” dasauri takai hannunta tashare hawayen daya zubomata sannan tajuyo Nura yabi kwayan idanunta da kallo hannu tamikamai ahankali tace “kawo” kin bata yayi ya ijiye robobin a gefe ya mike yakai hannunshi kan fuskanta yace “menene? Meke damunki? Talk to me menene damuwanki Ummi”? Girgizamai kai tayi dasauri tana kokarin kauda kanta tanaso ta ture hannunshi saikuma kuka ya kufce mata dasauri ta fizge kanta ta juya tareda kifa kanta a bangon kitchen din yanda yara keyi tafashe da kuka sosai tace “ni banso nakoma Abuja kabarni anan naci amanar Anty bazan iya kallonta ba, nasan tunda ka sanar da ita zancen Auren nan zuciyanta bazai mata dadi ba babu wacce keson kishiya barinma yar aikin ka, wlh wlh Allah ma yaga zuciyana bantaba so na aurema Anty Miji ba Auren kaman amafarki haka nima naga yafaru, banda kirki My Noor, ban kyautama Anty ba” Nura yadade yana kallonta all he sees is tsantsan childishness da rashin wayau, tahowa yayi ahankali wajen yajuyo da ita hannunshi yakai kan fuskanta yana sharemata yace “jibi yanda kika bata kwalliyan dakikamin eh” ahankali tace “kayakuri” murmushi yayi this is one reason dayasa yake kara sonta she apologize to him ko bataimai laifi ba, ahankali tana jikinshi yace “bazan taba iya barin matata awani gari ba ni ina wani gari, maza dayawa na haka but ni baya cikin tsarina Inason duk inda nake iyalina na wajen kinajina” gyadamai kai tayi ahankali, anatse yace “bakici amanan Hadiza ba ni mijin mata hudu ne, nan gaba still idan naji inada bukatan kara aure still zanyi Ummi, so bakiyi laifiba” yayi maganan kai tsaye yace “dake da Hadiza dukanku matayena ne daya kuke awajena babu wacce tafi wata and dukanku kuna karkashina ne, nina aureki bake kika aure ni ba, inma laifine aure kinga kenan nine nai laaifin bakeba dan nine na aureki, idan mun koma gida ki bata girmanta amatsayinta na wacce ta girmeki sannan mahaifiyar su Aman da Amal ban yarda ki mata rashin kunya or anything ba dudda nasan ba halinki bane kada ki shiga harkanta kome zatace idan kinga bazaki iyaba ki shiga daki ki kulle kofa ki kirani muyi waya idan bananan but kada kiyi fada da ita okay” gyadamai kai tayi, ahankali ya manna mata kiss a goshi yace “Ummi ina sonki sabida kina bani kwanciyan hankali kada ki chanza daga hakan okay” gyadamai kai tayi, idanunta dasuka cika da hawaye ya kalla yanda fuskanta ya kwabe sai kawai yaji sha’awanta yakamashi hannunshi yadaga yakalli Rolex dake daure a writs nashi yace “akwai sauran time zoki bani hakkina daman jiya da daddare sau biyu kawai nayi kikahau bacci raguwa” murmushi tayi tana turamai baki kaman yar yarinya cikeda so tace “nan fa kitchen ne” yana daga riganta sama yace “eh nima ilokan wajen zan dafa a kitchen inci tunda ni bancin na roba ba” dariya Ummi tayi tace “saina cinye bakinka yau” kawomata bakin yayi yace “ai nace nabaki tunda ke kinfi son kiss kan komi kin sa lips dina sun kara pink tsabagen tsotsa oya sumbaceni” kaman jira take dasauri tayi grabbing lips nashi tashiga kissing nashi ya mannata abango yana kissing nata back yana warware wando yana ja kasa……
Saura kadan suyi missing flight nasu amman Alhamdulillah sunkai on time daman business class yabiya nan da nan sukai boarding, ashe ranan nan data daure sabida mutane ne yau harsuka sauka Abuja tana rungume ajikinshi sunyi kyau daga ita harshi ruwan amarci yasa Nura yakara haske yana sheki yadan kara kiba sabida abincin dayake samu akai akai itakuma Ummi kaman ba itaba fatanta ya goge tana sheki hannunta rikeda Samsung Z-flip dan kaita shago yayi yace ta zaba shita zaba wai sabida yanda yake budewa yana rufewa ya saya mata shikuma yana rike da hannunta suka fito suka shiga jeep dake jiransu wanda yaron Nura ne na office ya gaida Ummi akunyace ya amsa dudda tana shakkan zuwa su gida amman daurewa tayi ga mamakinta wani gida daban sukaje Nura yace “muje Muga Hajiya ko sai mu dauko yaran mu anjima saimu tafi gida” gyadamai kai tayi parking sukayi gidane babba mai kyau suka shiga suna sallama a babban falon inda su Aman da Amal ke wasa da guje guja dawata karaman yarinya dasu Hajiya da Meena da Matar Baffan shi yaran suka juyo wani irin ihu da Amal da Aman sukayi suka taho dagudu bude hannu Nura dake gabansu yayi suka taho aguje ga mamakinshi wucewa sukayi suka rungume Ummi Amal sai kawai tafashe da kuka shima Aman haka Ummi kawai ta yarda handbag da wayanta ta rungume yaran itama saiga hawaye shiru daga Nura har duka yan dakin sukayi suna kallonsu Nura saiyaji yakara jin dadi da natsuwa dakuma hamdala da auren Ummi dayayi da kyar Ummi ta iya sakinsu cikeda dabara tace “ga Dadyn ku bakumai oyoyo ba” sakin Ummi sukayi da sauri sukai wajen Dadyn su Ummi kuma tazo wajensu Hajiya ta duka ta gaishesu bayan anyi gaishe gaishe aka kawo abinci sukai nak Nura yafita sallan la’asar itama Hajiya tace bari nayi, Ummi taje ta cewa Meena pls Meena je mota ki bude akwatina akwai wani leda shine a saman kayana ki kawomini abin Hajiyane” murmushi Meena tayi tace “nifa” dasauri tace “naki na handbag dina” wucewa Meena tayi tafita bata wani jimaba takawoma Ummi ummi ta karba Meena tace “je daki ki kaimata mana kina kuma jin kunya ni natafi kitchen” wucewa Meena kitchen tayi Ummi tawuce dakin, Hajiya na zaune kan dadduma Ummi tayi sallama Hajiya tace “shigo mana Ummi aiba saikin jira nace ki shigo ba shigo shigo maza” dakin Ummi tashiga har gaban Hajiya ta duka akunyace tabama Hajiya ledan tace “Hajiya ga tsaraban dana yo miki ba yawa” dasauri Hajiya tazaro idanu tace “laaaaaa Ummi harda wani yimini tsaraba ikon Allah, toooo Allah yayi Albarka Ummi, Allah yakawo kazantar daki” bude ledan tayi wasu manyan atampopi ne guda biyu akwatin nan da Nura yakawo gida ranan kayanta ne daya sayomata su kafin yamata proper akwati, an dinka wasu some baa dinka ba amman tadauko atampopi wayanda sukafi kyau aciki guda biyu, tasama Hajiya wani soft silipas dan madina blue da ake saidawa akauyensu tasayo, da irin dankwalayen nan na tsofaffi kallabi masu kyau guda uku daban daban, ga mamakin Ummi sai kawai Hajiya tafashe da kuka sosai tana kallon kayan tace “Ummi ni kikasiyoma duka abubuwan nan”? Adan tsorace Ummi ta kalleta danta tsorata kartaga kaman ta rainata tanada yara masu kudi yarta na Egypt amman tazo tana mata kyautan danmadina, sai kawai taga Hajiya tahau kwalama Meena da matan baffansu kira dasauri suka shigo cikeda kukan farin ciki tace “Karime, Meena ku kalli abinda yarinyar nan tasayo mini, babu wanda yataba siyamini tsaraba irin wannan daya faranta mini rai haka, nadade ina neman dan madina sabida ciwon kafana kinsan takalmin da laushi duk silipas da ake sayomini saidai nasa ba yanda zanyi, jibi kalluba ku kalli atampopi na, Allah miki albarka Ummi, yanda kika faranta mini ubangiji Allah ya fara tamiki” sai kawai sukahau yima Ummi godiya akunyace ta tashi tafita Meena tabiyota sukaje dakin da Meena ke kwana sai Meena taji takara sonta sabida yanda tasaka Hajiya farin ciki kuma tai alkawari zata kira su Ya Aisha dukta fadi musu dudda tasan ma Hajiya zata fadi, dan babu wanda bazaiji labarin kyautan nan ba yau haka Hajiya taje bata boye abin arziki.
Nura na shigowa gidan Hajiya tace “Nura kalli tsaraban da matanka tayomini ohhh Nura yarinyar nan Ummi saidai Allah ya yimata albarka kawai, kasan yanda silipas din nan da kalluban nan sukamin dadi kuwa, gashi yamin chass akafa, achan achan Masha Allah kaga kiramini kanwarka Aishaa nagaya mata abinda matarka tamin” yana xaune nan yana taya Hajiya dialing numbers saida takira yaranta uku mata ta gayamusu sukace asa Meena ta tura musu lomban amaryan Ya Nura duk zasu kira sunata godiya.
Yanda Hajiya ke murna tana fadama kowa kyautan nan sai shiwa Ummi albarka take bakaramin dadi Nura yaji aranshi ba yana kallon atampopin, shine yasayo su anan Adamawa abinda yafi bashi mamaki yanda sunfi kowani atampa kyau cikin kayan daya sayo mata, design nasu is so beautiful but suta dauka tabawa Hajiya kuma wlh bata fadamai ba, baimasan tana tareda takalman nan ko kallbin nan ba that means tun akuayensu tasayo, kawai saiyaji yakara respecting yarinyar imagine ko shi baisayo musu tsaraba ba shi dama ansanshi baya tsaraba bai iya riko tsarababa amman yatashi sayo abu zai shiga super market ya jido kaya, abin really touched him bazaima iya misilta dadin dayaji ba, duk wanda zai tayashi da Hajiyan shi farin ciki babu abinda bazaima mutumin ba cus Hajiya number 1 ce arayuwanshi.
Zama yayi abinshi tareda Hajiya anan dakin nata sunata hira bini bini ta shiwa Ummi albarka har abin yasa yasomajin kishi maisa shima bai kawo tsaraba ba yasami kalan addu’an nan da Hajiya kema Ummi haka? Kawai abin saiya zama kaman eye opener dagayau duk yayi tafiya kobaiso saiya sayo tsaraba yakawo shima In sha Allah Ummi takoyamai something in this his old age.
“Ka sanarda Hadiza kayi aure Nura?” Dasauri yadago kanshi daga katifa yakalli Hajiya jin tambayanta ganin yayi shiru yasa tace “baka kyautaba Nura ai kome Hadiza tamaka ba’a haka, bai dace kawai taga mata daga sama ba dan haka ka sanar da ita yau, sannan ka kira kanwarka Aisha ko ita ko Maimuna ko Matar Baffan ka Karemi kabasu kudi ahadoma Ummi da Hadiza akwati, sannan kaji tsoron Allah kayi adalci atsakanin su dan rashin yinsa zai kaika wuta, ka manta duka halin Hadiza na baya ka bude sabon chapter yanzu and treat them equally kada ka cutar da Hadiza sannan kada ka bari ta cutar da Ummi dubada tafita wayewa dakuma shekaru, sannan kada kabari Ummi ta raina Hadiza ganin itace amarya ko ka nuna mata kafifitata kan Hadiza, kada ka kuskura ka rike matanka ahaka kowacce ka rike sirrinta azuciyanka kada ka sanar da Hadiza kanada matsala da Ummi haka kada kasanar da Ummi kanada matsala da Hadiza, ka kama girmanka kayi tsayin daka akansu, ka tsare hakki dakuma mutuncin kowa kanajina Nura” Gyadamata kai yayi ahankali yace “naji Hajiya” kanshi ta shafa tace “kayafema Hadiza kome tamaka kada ka riketa da laifinta please sannan yau karaba musu kwana, tunda baka gari kuma duk kana tareda Ummi ne lokacin yau kashiga dakin Hadiza kajini”? Gyadamata kai yayi yace “naji” ahankali tace “Allah yamaka Albarka Nura, yanda kake kulawa dani dinnan ka tsaya akan lamarina, kabani ci kabani sha kamin duk abinda nakeso sannan kaji magana ta Nura ubangiji Allah ya saka mata da aljanna” murmushi yamata yace “Ameen Hajiya nagode” murmushi tamai tace “idan naji sauki komi ya tabbata saika gana da yaron dake neman Auren Auta ko”? Gyadamata kai yayi yace “eh Hajiya amman tana aure xakibar kano ki dawo gidana da zama bazan barki ki zauna ke kadaiba gaskiya” dasauri Hajiya tace “kai barni da Abujan nan wlh ba sonta nake ba nafison kano” dasauri yace “Hajiya akwai flat dinki daban agidana, nan da wata biyu za’a gama komi bazaki zauna ke kadaiba a kano gaskiya” ahankali tace “to baridai lokacin yayi sai muyi wannan maganan, tashi kaje masallaci an tada salla leka min Meena da Ummi kagani Allah sa sun tuna sun hada kayan su Amal ba sun tsaya hira ba” wucewa tayi yafita dakin da Meena take yaje yadaga labule yayi Ummi kadaice adakin tana shirya kayan su Aman bama tasan da zuwanshi ba sai aikin take harta ga Amal zaune gefenta hannunta da tuwon madara tanasha dan murmushi yayi akan Ummi yasoma sanin akwai wacce zata iyaso yaranka tsakani ga Allah koda ba ita ta haifesu ba saidai basu da yawa a duniya, gyaran murya yayi dasauri Ummi tadago kanta ta kalleshi folding hannu yayi akirji yace “awanki nawa baki sani a ido ba”? Murmushi tayi kaman mai tunani tace “uhmmmm awa biyu da minti ashirin da uku da sakan shidda kenan bansa Dadyn Amal a idona ba” dasauri yace “shine kuma kike murmushi” hadiye murmushin tayi tace “tuba nake nadaina Yallabai” kwafa yayi yace “kinci sa’a akwai Princess anan” dasauri tajuya taja hancin Amal tace “ai princess zaki dinga cetona koda yaushe ko?” Amal tace “yesssss Anty Ummi na” dariya tayi takalleshi tace “kaji ko” hararanta yayi yana murmushi yace “kuyi salla ku shirya nadawo zamu tafi” gyadamai kai tayi tace “to mijina, adawo lafiya asamu a addu’a fa idan kana cikin jam’in nan kaji” juyawa yayi yace “naji matata” yayi murmushi yawuce Meena tazo da gudu tace “ke Ummi haka kuke soyewa keda Yayana, zona koya miki zama da Hadiza……..”
Yana dawowa aka zuba komi a mota harda abincin dare Hajiya tasa Meena tazuba musu a babban kula dantasan matan gidan bata dafaba kuma bazatazo Ummi tahau aiki da daddaren nan ba suka musu sallama suka
25, August 2025
Saadatu Ali
Yes