Showing 171001 words to 174000 words out of 202729 words
ki gaida Alhaji har aka baki kudi da sauransu daga ranan dai ni bansan ko shine ba but dai yace ke da Ammi ku koma Dubai ki secondary school naki daganan baki kara dawowa ba sai bayan kin gama, Alhaji shine gatan rayuwan Ammi, he’s her best friend, Alawiyya listen to me very well duk duniyan nan bazaki taba samun wanda zai soki tun kina small baby da akema komi kawowa this age ba irin Alhaji” baki Alawiyya tabude dasauri zatai magana Ya Raheena tadaga mata hannu tace “wait lemme finish bawai cewa nake kisoshi ba and ba gardama nace kimin ba” anatse Ya Raheena tace “as mace you have to be a critical and logical thinker, karki kalli abubuwa from just love angle Cookie look at things from other parts, now bawai ina cewa kibani amsan tambayiyin nan dazan miki yanzu bane but I want you to analyze it azuciyanki, first question kina ganin Ammi zata taba yarda duk runtsi ki rabu da Alhaji wanda yamata komi all labarin nan dana baki ki auri wani??” Tai maganan tana kallon Alawiyya dake kallonta tace “kinsan everything da Ammi ta mallaka ta sanadin aurenki ne? Takuma sanadin Alhaji ne, Ammi had a dream of becoming politician but bata da means din Alhaji made that possible, Kinsan kashe auren nan zaisa Ammi tarasa duk wani mukaminta aduniya? Muma yaranta mu rasa namu cus duk Alhaji ya sama mana this work, sannan ayi publishing family news namu a news channel, jaridu, social media ke ko’ina ma, do you want family ki and your mother to go through this mess sabida nonsense feelings din da you called love???” Ya Raheena tai shiru tace “now mu dauka kin bata relationship din tsakanin Ammi da Alhaji an raba auren, what if Ammi tace bazata taba yafemiki ba sannan ita ba mahaifiyar ki bace sannan mu sauran yaranta tarabamu dake ta hanyar yimana Allah ya isa duk wanda ya kara kulaki a rayuwarsa??” Ya Raheena tadanyi shiru tace “that’s my second question and again, kina ganin abangaren Alhaji zai barki? Sannan zai bar duk koma wani yaro ne daya shigo rayuwanki yasa kika rabu dashi? Alawiyya did you even know who you are married too? Kintabajin wayanda ake cewa su they’re above law??” Ya Raheena tadanyi murmushi tace “irinsu Alhaji ne ake cema they’re above law cus gwamnatin dake ruling yanzu a Nigeria tasa ce, dan gidanshi ne shine ubangidan shugaban kasan mu, ke bari kiji Alawiyya Alhaji zai iya hadama koma waye saurayin naki tarkon dahar yamutu yana gidan yari bazai fito ba ko anan kadai bakiyi 2 zero ba? Kega Mamanki ta yafeki sanma tarabaki da yan uwanki, saurayin da sabidashi kike haukan nan kuma yatafi gidan yari da bama’a barinki kiganshi tell me Alawiyya bakiyi asara ba? Baki zama stupid and gullible foolish girl ba?” Ya Raheena ta sauke ijiyan zuciya tace “well that’s my third question now bari muje kan Oga kwata kwata shi yaron ko saurayin ko who ever he is dayasa kike mana iskanci da hauka da hayagaga, first abu dazan tambayeki akanshi is how sure are you yana sonki 100 over 100 Cookie?? Cookie kinsan maza kuwa?” Ya Raheena tace “is he worth risking everything and everyone dakike dashi aduniya for him Alawiyya!”? Tai maganan da karfi tace “how sure are you bayan kin bata relationship naki dana family naki he will remain loyal to you har abada? Idan yazo yajuya miki baya fa nan gaba wazaki tunkara cikinmu? Alawiyya sorry to say this but am sure kin riga kin bashi jikinki cus is obvious tun haukan dakikazo kina mana, ya bude miki baki yakoya miki kima mamanki da yan uwnaki rashin kunya, ya nuna miki kaman aduniya yafi kowa na duniya sonki, kin bude kafa tun awaje kin bashi yaci to mekuma yarage? Meyarage ajikin naki dabai sani ba? Ko bayan kunyi auren dokin me zaiyi? What again? Koda yayi marmarin ki bayan kwana biyu ne he will start looking at you like a normal mace that is idan ma yayi trusting naki kenan cus inhar xaki iya da aurenki ki gudu kije wani waje ki kwana da wanda ba mijinki ba har 7days kuna shagali simply means zaki iya hakan da kowa, that guy will never trust u, any namiji dazai ganki dashi ko zaki rantse bazai taba yarda dake ba, Alawiyya love is NONSENSE! kinada tabbacin gayen nan da kike ihu kina fada da kowa na rayuwanki akanshi zai iya miki the same shima a bangaren shi? What if iyayyenshi sukace basu yarda ya auroki ba matan Alhaji Makamashi ce ke basuson matsala did you think of that? Maza nada wayau sunajin maganan iyayensu kina ganin mamanshi ta hanashi aurenki zai aureki still?? Kina nunamai kinyi fada da iyayenki bakisan abin kunya bane indai namiji ne he will use that to insult you wata rana duk dare dadewa yamiki gori da hakan, you call this drama dakikeyi fighting for soyayya the same man dakikayin all this sabida shi one day zai miki dariya and call you wawiya maima Mamanta rashin kunya sabida namiji, Alawiyya are you thinking outside the box kinsan me kikeyi eh? Is the guy worth you? Is he worth fadan dakikeyi da mahaifiyarki da mijinki da yan uwanki ehhhhh?” Gyadama Ya Raheena kai Alawiyya ke kokarin yi idanunta sunyi jazur Ya Raheena tamika hannunta tadaura saman kanta tace “don’t stress yourself, bana bukatan amsanki” ahankali tace “I called Hamida here without Ammi ta sani cus I wanted us to talk to you sabida muna sonki and we care about you, da ace bama sonki ayanda kike tunani bazan taba gayamiki all this thing ba, and I want to tell you one final thing, I am ready to support you Alawiyya, Hameeda is ready to support you all of us sisters naki are ready to support you, dukan mu mun hakura da aikin namu, idan Alhaji yasa akore mu fine, idan baisaba fine zamu hadu muma Ammi magana on behalf of sister namu, but just know one thing, Ammi trained all of us as yara adilai masu biyayya idan nan gaba Ammi tamana iyaka dake dole zamuyi!” Hawaye ne yazubo daga idanun Alawiyya, Ya Raheena tace “your life your call and your rule, mu sisters naki munbaki daman nan to set your standards ke ba yarinya bace and bazamu kara miki kallon yarinya ba now that we tell you everything kan rayuwa think about it today ki gayamun amsanki gobe, dukanmu harda ke zamu hadu collectively muje muma Ammi magana tabarki kifita daga auren nan tunda akwai cutarwa we will support you Alawiyya, we will! But think everything through ki auna komi and kisan kowani action nada consequence dan haka choose wisely! Let’s go Hameeda yamma nayi kitafi gida” tashi Hameeda tayi tazo har gaban Alawiyya sai kawai tai hugging nata ahankali tace “I love you soo much Cookie, make your decision and let us know I am ready to give up my work my everything ma for you wlh, kome kika zaba muna tareda ke, think through the decision is yours to make” sannan ta saketa ta tashi suka fita daga dakin.
If you ever find kanki a situation na Alawiyya what will you do???
*MATAN KO MAZAN*
EPISODE 1️⃣8️⃣
ASMEEYAMIN COLLECTION ASMEEYAMIN COLLECTION ASMEEYAMIN COLLECTION ahhh kunsan mesa naketa kiran sunan this brand?? Sabida is one of the best wajen saida laces takalma and bags, wayanda suka saya kaya daga wajenta can testify now rush and join WhatsApp group nata kuma kusayi kaya💃
https://chat.whatsapp.com/Fvbu8FNZxXTIA5oHt26Daj
Idan kika karanta this littafi baki biyaba ban yafeba! Wallahi ban yafemiki ba eh ke! Ban yafe makaba kaiba! This book subscription is 1k pay idan bazaki iyaba don’t read. Chat me up don saya by clicking on this link wa.me/+2347032934950
Alawiyya kasa motsi tayi daga inda take zaune, all her life ta taso batada problem, irin asalin rainon ajebota pikin akamata, asalin diyar masu kudi so technically zama ka iya kiranta mara wayau cus ta taso with so much love daga kowa datake tareda shi, yayyinta, Ammi and AJ, zancen aurenta da Alhaji was the first abu daya fara dagulamata lissafi arayuwa, gabaki dayan rayuwanta that smartness da wayau na yaran zamani ita bata saniba, bata dashine, Hamda is her only friend mace itama yar gatace yar masu kudi so kusan yanayinsu daya, banda shagwaba babu abinda ta iya so is as if maganganun da su Ya Raheena suka mata sun damamata lissafi sun hargitsa kanta ne, kanta kawai yadauki chaji, wlh ko 5mins basuyi da fita ba wani irin mugun zazzabi ya lullubeta, koda matan dake bata magani ta shigo da kyar tasamu tasha tsumin ahaka ta lallaba tayo Alawala tai salla azaune sannan ta kwanta akasa da abun yamata yawa kawai saitahau kuka, tsoro fargaba damuwa rashin kwanciyan hankali duka sun taru aranta she love AI but what if yazo ya yaudareta? Namiji baida tabbas kuma ba dan goyo bane? What if duk abinda su Ya Raheena suka fadi yazo yafaru? Wlh sosai zazzabi yarufe ta ahaka tai Isha’i, Ya Raheena tazo tamata good night ta tafi, wayanta ta kalla but takasa kiranshi sai kawai taji yau she don’t wanna even talk to him, different thoughts and fear azuciyanta, takasa bacci, kanta kaman zai fadi har 12 nadare idanunta biyu kaman shima AJ yagaji da jiran kiranta yakirata da kanshi dan yawanci saita kirashi sai yay maza ya katse yakirata amman har wayan yakatse taki dauka, normally akwai possibility da zai iya yuwa an kwace wayan a hannunta ne but hakanan ranshi yabashi wayan na wajenta, kira yacigaba da yi Amman yaki dauka har asuba tama tura wayan kasan gado tai tai kuka tai kuka idanunta sun kumbura kanta ya kulle tarasa mezatai tunani she don’t know what to do nor what to think, idanunta sun kumbura sunyi suntum yanda taga rana haka taga dare tarasa mezatai tunani damuwa yamata yawa, sai kawai tambayan kanta take mema takeyi aduniyan nan? Tashi tayi kanta kaman zai fadi tafada bayi tsayawa tayi tana kallon kanta amadubi tana tambayan kanta AJ zai iya yaudaranta? Zai iya wulakantata nan gaba? What if tagama fada dasu Ammi AJ yazo yana gana mata azaba sanın batada kowa sai shi? Yaya zatayi alokacin? Who will she run to? Zuciyanta is strongly telling her AJ bazai taba yaudaranta ba at the same time wani tiny little spot a zuciyanta na gayamata everything is possible AJ zai iya and she should better prepare for the worst, wani kalan dukawa tayi awajen tasaka hannunta cikin gashin kanta tawani kalan barbasa tana kuka da karfi Whyyyyy? Ta tambayi kanta? Tace banda rabon farin ciki arayuwana ne? Eh? Takai kusan 1hr kuka take abayin ta tashi da kyar tacire kayan jikinta tai wanka tayo brush tafito tana wani lafiyayyen kamshi fatanta na sheki sabida gyaran jiki, wani simple straight gown tasaka tasa hijabi tai salla shigowa dakin akayi aka kawomata farcesun kaza wanda na magani ta ne dawani shayin magani mai shegen dadi, kadan taci shima sabida batason zazzabi yakamata ne.
Wuraren 8 Ya Raheena tashigo dakin taci gayu sosai yanda taga idanun Alawiyyan saida gabanta yafadi dasauri tazo gabanta tace “Cookie what happened? Subhanallahi kinga idanunki kuwa did you even sleep at all eh?” Kankame hannun Ya Raheena Alawiyya tayi saiga wasu hawaye masu shegen dumi sun sauko daga idanunta cikin murya kaman na yar yarinya Alawiyya tace “Ya Raheena help me wallahi inason AJ, Ya Raheena AJ has my entire heart and soul, I don’t know what to think help me Ya Raheena” dasauri Ya Raheena ta rungumeta taba sata ajikinta tace “come here Cookie it’s okay stop crying ya isa” tai maganan tana patting bayanta ahankali tace “I’m glad kinyi tunani u sleep on abubuwan damuka fadamiki jiya, Alawiyya don’t gamble your life akan uncertainty, bakida tabbas idan AJ will forever be loyal to you so akanme zakiyi fanchakali da family naki kanshi, men come and go but family are there forever, duk runtse muna tareda ke but shi fa? Kina tunanin yanzu Alhaji Makamashi yasamo AJ yabashi 100M akan yahakura da soyayyanki bazai hakura da gudu ba? Whatever ke da AJ kukayi was a mistake cus I know kunyi wani abu and I will not judge you, it was a mistake, AJ took advantage na you were not in your right senses yakaiki wani waje and sleep with you, so koma mekikeji yanzu is side effects na abinda kukayi ne saisa kikeji kaman shi kadaine namiji aduniya, just forget about him kima mahaifiyarki biyayya duk wanda yabi iyaye baya tabewa har abada, I promise you zakiga tukuicin da Allah zai miki, and all of us are ready to support you throughout this journey okay” gyadamata kai Alawiyya tayi tana jikinta tana shaking daidai lokacin aka budo kofan dakin dasauri Ya Raheena tajuyo ganin Ammi saida mamaki yakamata dasauri tace “Ammi” dasauri itama Alawiyya tasaki Ya Raheena tadago kanta takalli Ammi Ya Raheena tace “muna shirin zuwa gidan ki ne yanzu haka fa Ammi, I’m sure su Hamida ma duk suna hanyan zuwa gidan ki” waje Ammi tasamu kan gado tana kallon fuskan Alawiyya dake kallonta tace “gaisuwa ma yanzu saina roka zakimin eh ishashiya”? Saukar da kanta kasa Alawiyya tayi ahankali tashiga wasa da yatsunta batasan mesa ba but haushin mahaifiyarta takeji yanzu, whenever she looks at Ammi all she sees is matan that is causing her so much pain and agony, matan data bata mata rayuwa, tabata da Ya Raheena tayi yasa Alawiyyan ahankali tace “ina kwana” shiru Ammi tayi bata amsaba takalli Raheena tace “excuse us I wanna to talk to her Raheena and ki kira su Hamida ki gayamusu ina nan” gyadama Ammi kai Raheena tayi tawuce tafita daga dakin Ammi takalli Alawiyyan dake zaune kan carpet ga breakfast nata bata wani ci ba, kanta akasa sai wasa take da fararen dogayen yatsunta, Ammi tadade tana bin yarinyar da kallo duk cikin yaranta Alawiyya tafisu kyau tafiso kyan jiki, tafisu sura da diri dudda suna kyau suma but Alawiyya daban ne, forget ta rame sabida rashin kwanciyan hankalin kwana biyun nan but dudda haka kaganta kaman ka saceta asalin balarabiya xakagani ka kalleta, ijiyan zuciya Ammi tasauke she needs to make peace da yarinyar nan yau dan gobe takeso ta maidama Alhaji ita a kaduna, ai Malam ya kirata kan yagama addu’a dan haka bari yau tanunama stubborn yarinyar nan itane ta haifeta takawota duniya ahankali ta sauko kasa ta zauna gaban Alawiyyan dab da ita, hannuwanta dataketa fidgeting Ammi takai hannunta takama ahankali cikin wata yar sansanyar murya tace “Cookie you hate me ko, ni Maman ki, Ammin ki kin tsaneni ko?” Shiru Alawiyya tayi batace komiba gabanta kawai na faduwa, muryan Ammi yayi wani kalan sanyi tace “Alawiyya imagine life da Hassan da Hussainin ki dakika haifi bayan kinsha wahala dawainiyan cikinsu su girma su tsaneki har yakaiga bama sason su dago fuska su kalleki, Alawiyya you hate Ammin ki kaman ki kasheni kikeji ko?” Wani kalan rawa zuciyan Alawiyya yafara barınma yanda Ammi ta kwatantan situation din da yaranta but still takasa magana, juyawa Ammi tayi sai kawai tasa hannu yadauko fork din dake cikin tray na breakfast nata tabude hannun Alawiyya tasamata fork din aciki tace “gashi kasheni Alawiyya sai kawai ki huta you don’t have to ever see me aduniya for ever” takai hannun Alawiyya da fork din ta daura da karfi awuyanta dayasa hannun Alawiyya yashiga rawa da bari dasauri ta kalli Ammi tace “Ammi!” Tsayawa chak Ammi tayi rikeda hannunta da fork din awuyanta tana kallon kwayar idanun Alawiyya kaman yanda Alawiyya ke kallonta da jajajyen idanunta wani kalan emotional tears ne suka sauko daga idanun Ammi suka gangaro kumatunta tana kallon Alawiyya kaman yanda Alawiyya ke kallonta Ammi tace “I thought kin tsaneni, you can’t stand the sight of me, matan datasa kika auri tsoho, you hate looking at me, mesa kika kasa ending life dina ki huta gabaki daya da ganina eh?” Sai kawai Ammi tafashe da kuka sosai ta sauke hannun Alawiyyan ta zare fork din ta maida kan tray tana kuka mai bala’in tsuma zuciya dayasa kawai jikin Alawiyya gabaki daya yahau bari gashi takasa magana haushin Ammi yacika mata wuya at the same time she’s feeling the cry of her mother in every part of her, duk Ammi na lura da ita ganin still yarinyar batai lugub tafara rokonta tayafe mata ba kaman ba Alawiyyanta data sani ba dakeda soft heart ga saurin kuka, ko ubanme shedanin yaron nan yamata oho, dare daya ya chanza mata Yarinya, Alawiyya is now strong hearted gata very stubborn but su zuba za’aga in this battle of saurayi da uwa wazaici, zata nunama dan durun uwan yaron nan ita tahaifi diyarta as long as she’s alive bazai taba samun diyarta a matsayin mata ba wlh, tsagaita kukan tayi tasa bakin tsadadden gyalenta tashare idanunta tass takalli Alawiyyan tai dan murmushi irin mai ciwo din nan tace “kina min kallo kaman nine ni mahaifiyarki the villain in your love story ko Cookie? Cookie do you really think ni mahaifiyarki don’t want what’s best for you? Are you that gullible dazaki tunanin bansonki ni mahaifiyarki? Banson abinda diyata keso? Tunda nake haihuwan yara bantaba yin cikin yarinyar dana wahala akanta na wulakanta akanta like you ba” tanuna Alawiyya tace “kinsan kalan wulakanta da larabawan nan sukamin kuwa”? Tai shiru tana kallon yarinyar da idajunta sukai jajir amman taki kuka sai kawai ga mamakin Alawiyya Ammi ta daga riganta sama tanunama Alawiyya wani long scar tace “all yarana babu wanda akamin operation sai akanki bayan long labour danayi akai juyin duniya ki juya kikaki, haka aka budeni Alawiyya aka ciroki only me a asibitin nan, ba Mama ba Baba ba yaya ba sister, aka yaga cikina aka ciroki” Ammi tafashe da kuka tace “I still remember every pain, every cry and sweat danayi ta sanadiyan haihuwanki, but yau ni diyar nan ta tsana Ya Allah!!!” Ammi tai shiru tace “baki barina baccin dare sabida ciwon cibiya, gaki da shan nono Alawiyya, I suffered sabida ke, still ban damuba it was all
25, August 2025
Saadatu Ali
Yes