Showing 126001 words to 129000 words out of 202729 words
ake mata ba ki barta anan Gwaggo” cikeda masifa tace “kai kaga jikin jikana ne, yooo asibiti da alluran nan nasu kara mata karfin ciwo zasuji, dauji ne ciwon nan muna zuwa kauye dakaina zan shiga daji na samo mata sassake assake na magungunan na jika dana sha dana shafawa kafin kace mene zata warke” cikeda lallabawa Alhaji Musa yace “Gwaggo to shikenan ki bari agama na nan saiki tafi da ita kauyen” fashewa da kuka Gwaggo tayi Tana nuna Ummi dake kallonta da kyar tace “yarinyar nan haka ciki ke wahalar da ita, kubani ita natafi da ita kauye nasama mata magana iyye, Shatu keda Zakkiya kuzo ku cicciba mini ita abaya na goyata mutafi tasha ai Alhamdulillah nayo guzurin kudina, kuzo ku cicciba mini ita abaya” zasu fara tahowa da sauri Hadiza tasa baki hannun Gwaggo takama cikeda lallashi tana magana ahankali kaman mai whispering but zaka iyaji tace “Gwaggo kiyakuri kinga kukanki zai kara tadama Ummi hankali hakan baida kyau agareta, yanzu kiyakuri tadanji sauki koda kadan ne saiki tafi da ita, yanzu kinga ayanda take zaman mota kona jirgi zai mata wuya ko Nuri” dasauri Nura shima cikeda lallashi yace “eh Gwaggo kiyakuri kinji, yanzu kiyi magana da ita tun jiya ketaketa nema” juyawa Gwaggo tayi takalli Ummi tana kuka sosai Hadiza tasaki hannunta, bayan riganta tasa ta share idanunta tass sannan tazo gaban gadon ta duka ta shafa fuskan Ummi cikeda so tace “gani nan nazo, Gwaggon ki na nan dake Ummi zakiji sauki kinji, me kikeso ciki gayamini nizan miki dakaina” tai maganan tanakai kunnenta saitin bakin Ummi, ahankali Ummi tace “Gassashen dankalin hausa amurza kulikuli akai” dasauri Gwaggo tadago takalli su Shatu daduk ke tsaye tace “buhun tsaraban damukazo dashi nasa dankalin hausa? Kaina yayi chaji na manta nasaka Shatu”? Whispering Alhaji Musa yama Nura akunne yace “kai kaga zabgegen buhun tsarabane saida nabiya extra luggage fee a airport” dasauri Zakiyya tace “eh akwai” dasauri Gwaggo ta zame lullubin dake kanta taci dammara dashi aciki takalli Alhaji Musa tace “Zakiyya ta bika kabude buhun, ke Shatu samomin manyan duwatsu da makamashi na gasa mata dan kali” takalli Hadiza tace “zan sami mai” Nura dafe kanshi yayi Hadiza ma tsoron rigiman tsohuwan yahanata magana Alhaji Musa ne cikin dabata yace “Gwaggo nan asibiti ne” “yo masallaci ne dabazan iya hada makamashi ba naga ba girki zanyi ba gasa dankali zanyi” gefen Gwaggo Nura yabi yazo gaban gadon yakalli Ummi kaman yar babyn shi yace “dankali zakici gashashe?” Gyadamai kai tayi Gwaggo tace “da murjajjen kulkuli da man gyada” kallon Gwaggo yayi yace “Gwaggo saidai aje gida ayi baza’a bari ayi anan ba” dasauri tace “kaga nabar dakin nan jikata tabar shi ne su Shatu dai akaisu gidan suyi” dasauri Alhaji Musa yace “kuzo duk muje gidan sai Gwaggon tazauna” cikin turenci Nura yace “someone needs to stay what if Doctors needs anything” ahankali Hadiza tace “kaje kai inyaso saikai wanka i will stay with them” Gyadamata Kai yayi ahankali yace “thank you” shima murmushi Alhaji Musa yayı ganin changes from Hadiza, sake dukawa yayi ya shafa fuskan Ummi yace “bari muje gida okay” Gyadamai kai tayi takalli kannanta da ido hakan yasa Nura yace “Shatu kuzo” Kaman jira suke dasauri sukazo gaban gadon rungume Ummi sukayi duka sai kuka Gwaggo tace “mehaka kuka nace kuzo kuyi?” Wannan karan kowa na dakin saida yayi dariya har Nura saida ya murmusa wacce tagama kukanta yanzun nan ne take Hana wasu tashi sukayi duk suka tafi Alhaji Musa yatukasu har zuwa gidansu dasukakai gidan baki suka büfe suna kallo har flat na Ummi yakaisu gateman ya shigo da tsaraban shidai yabasu grill nashi da charcoal aciki a bayan gida shida Alhaji Musa suka fito da kayanshi da Hadiza takawomai asibiti flat nata yawuce yabude kanshi ko ina tsaf tsaf yatafi sama kaman ba gidan Hadiza ba wanka yayi ya shirya ya sauko shida Alhaji Musa sukaci abincin dake nan dinning a warmer yaşandı ba laifi sannan yatafi duba su Shatu abubku da charcoal harya gama gasawa Shatu ta daka kuli tasa maggi da dan yaji Nura yabasu kul da kanshi suka zuba yakawo musu abinci daga side din Hadiza da drinks tass sukacinye sannan yadaukesu Alhaji Musa yawuce dasu asibiti shikuma yadauki wani mota dan zuwa dauko Hajiya da Meena a airport.
💫MATAN?? Ko MAZAN??💫
✍🏻M SHAKUR
EPISODE 4️⃣1️⃣
Kina neman class na matan aure da akeyi da turenci??? To look no more ga MAJAL WELLNESS nakawo muku💃
Indai class ne da ake tafarfasa karatu kan harkan abenga da turenci trust me bazaki taba samin a class better than SAMOHHACK by Majal ba so hurry and join her waitlist group ko kiyi chatting nata up now now now!!!
Check out her IG page @majalwellness💃
You will come thank me later oo💃
https://chat.whatsapp.com/H50w7C7Lrbv8ZiPKzKxm5l
Yana daukan su suka wuce asibitin Alhaji Musa yatafi daga Gwaggo dake bama Ummi dankalin tanaci ahankali sai Hadiza data rike mata bottle water a hannu Nura da Hajiya suka shigo dan faduwa gaban Hadiza yayi ahankali tamike tsaye tace “sannu da zuwa Hajiya” ga mamaki ta kaman bata taba samun matsala da Hajiya ba Hajiya tace “sannu Hadiza, sannu da kokari kinji Allah miki albarka” takalli Gwaggo cikeda Fara’s tace “maraba lale Gwaggo” Gwaggo itama cikin fara’a tace “Barka da zuwa Hajiya” Hajiya tabi Ummi da kallon tsantsan so da tausayi tace “ya diyata da jikinta”? Gwaggo tace “lpy lau” Kan Ummi Hajiya ta shafa saita shiga tofa mata addu’a da babu wanda keji sai bakinta dake motsi Nura ya jingina da bango kawai yana kallonsu, gamamakin Hadiza karasowa Meena tayi kusada ita kaman basu taba samin misunderstanding ba tace “ina yini Anty Hadiza” mamakin da Hadiza taji saida ya bayyana a idanunta, Meena tace “thanks for everything Yaya told us yanda kiketa dawainiya dasu mungode” murmushi Hadiza tayi tace “bakomi ai an zama daya” Gyadamata Kai Meena tayi saita wuce wajen kannen Ummi data saba dasu kusan wuni sukayi sai around 3 Hadiza takoma gida sabida su Aman dazasu dawo dağa school tareda Hajiya da Meena da kannin Ummi akabar Nura da Hajiya, sai hira sukeyi itada Hajiya tun bata sakin jiki harta saki jiki abinta a flat din Ummi suka sauka itakuma Hadiza tawuce nata tasan dama da wuya su sauka anata dudda taso hakan but bakomi with time komi zai daidaita.
Sai around 11 Gwaggo takado Nura da karfi da yaji yabar asibitin badan yasoba flat din Ummi yawuce duk idanunsu Hajiya biyu basuyi bacci ba yadan zauna yana hira dasu Hajiya tace “tashi kaje ka kwanta kahuta Nura” baiyi musu ba yawuce bayan yamusu sallama yafita yawuce flat din Hadiza falon a gyare tsaf, Hadizan yagani zaune afalon ga laptop dinta tasaka reading glasses sai yau take duba harkan shagonta tana ganinshi ta ijiye laptop din ta mike saikuma ta tsaya tace “sannu da zuwa” dan murmushi yamata ya maida kofan yarufe yatako anatse zuwa inda take ahankali yace “lemme hug my wife da warin asibiti” sai kawai ya rungumeta murmushi tamai tace “my husband smells good” yadanyi one minutes ahaka sannan yasaketa zai wuce sama da sauri tace “akwai dinner zakaci ko zakasha tea”? Ahankali yace “make tea for me cus it’s late ki kawomin dakina bari na watsa ruwa” sama yawuce direct dakinshi dan kowani flat yanada dakinshi yafada bayi wanka yayi damuwa yamai yawa daurewa kawai yake fitowa yayi daure da towel yaga Hadiza takawo tea pajamas yasaka ya feffesa turare sannan yataho gently yazauna kusada ita yadauki mug na tea din yace “thank you Didi” murmushi tamai tana kallonshi yanashan tea ahankali harya gama tashi tayi tace “bari nakai kitchen” shima tashi yayi yace “bari naduba yarana” tare suka fito dakin Aman yafara shiga dake bacci ya duddubashi yamai addu’a sannan yawuce na Amali itama yamata addu’a yafito saiya bude dakin Hadiza ganinta yayi ta kwanta agado ahankali yace “taso muje mu kwanta” batai musu ba tasowa tayi tana tafiya yana binta da kallo har saida tazo dab da shi hannunta yakama yatayata kashe wutan dakin sannan suka wuce dakinshi kashe wuta yayi ita tafara shiga cikin gadon shima yahayo ya kwanta tareda jawota jikinshi faduwa gabanta yayi tanaso tayi gyara kafin wani abu ya shiga tsakanin su she prays bazai mata komiba.
Ijiyan zuciya yasauke ahankali kafin yakai hannunshi yasa a tsakiyan nata suka hade murya Chan kasa yace “my Didi” ahankali itama tace “my Nuri, menene? Meke damunka? Menene matsalan Mijina? Talk to me”? Dan ijiyan zuciya yasauke yasake shigewa cikin jikinta da kyau kaman bazaice komiba chan yace “I haven’t told anyone but inaso nakai Ummi either Egypt ko India duk Wanda yarıga fitowa what do you think?” Ahankali tace “yes nima zanso hakan sabida a dubata da kyau and manage her harta haihu” Ijiyan zuciya yasauke yace “zaki dagamin kafa?” Dasauri tace “of course Nuri” murmushi yayi yace “I love you my stubborn wife” dan murmushi tayi tace “ai ka horani bazan karaba” saitai dan shiru kafin chan tace “Nuri” ahankali shima yace “Didi”. Labarin Zeenah tabashi tundaga kan case na kotu har karshe tace “Nuri I’ve been a fool, is just like abinda Anty Jams tace I am just a fool wawiya mara wayau all abinda na iya is ihu da zagi Zeenah ta cutardani Nuri she made me believe in feminism kaman an juyamin brain na zauna kan abin kaman nina kawo feminizm duniya amman nida feminizm har abada Nuri I sincerely apologize for all the pains I’ve caused you can u find a place in your heart to forgive me?” Ahankali yakai hannunshi saman fuskanta dudda baiji karan kuka a yasan hawaye yazubo dağa idanunta ahankali yace “komi daya faru between us is destiny, haka Allah ya kaddara, duk Wanda zaiyi kuskure yagane ya gyara mutum ne, babu wanda yafi karfin jarabawan ubangiji nayafe miki itakuma Zeenah Allah zaiyi maganinta ki barta da halinta delete her number bansonki da any kawa again, and your business kicigaba but anything 3 daga yanzu nakeso ki dinga dawowa gida, and weekends that’s Saturday and Sundays is for me nawane banso kina zuwa shago ranan kinji you can hire more staff to handle your work, and yarana give them your time and affection I wants Aman and Amali su soki sama da yanda suke sona make up for your mistake ki gyara tsakaninki dasu kija yaranki ajiki kinji Hadiza” gyadamai kai tayi ahankali, tace “thank you Nuri you are the best husband” ahankali yace “u are the best wife” hamma yayi, ahaka yana manne da ita bacci yayi awon gaba dashi.
Almost 1months Ummi tayi anan asibitin aka gama processing komi cikin kannin Nura Ya Aisha ne kawai bata zoba itama sabida Egypt za’a kawo Ummin nan but duka kannen Nura sunzo nan da nan aka saman ma Ummi da Gwaggo komi suka wuce Egypt itakuma Hajiya tawuce kano da kannin Ummi da Meena Nura yarığa ya barmata kudi yanaso takai yaran boarding school mai kyau yama gayama Gwaggo bazai yarda ta aurar dasu yanzu ba washe garin ranan dasukaje Kano Hajiya takaisu school hadadde akai komi suka dawo gida dan amusu shopping akaisu school zasu fara JSS1 dan Gwaggo da Ummi bazasu kara dawowa Nigeria ba sai bayan Ummi ta haihu.
Gidan Abuja yarage Hadiza kadai da yaranta.
Dudda Nura baiso yasauka gidan kanwarshi ba but mijin Ya Aisha yace bai isaba daka shi ma yadaukosu airport Gwaggo idanunta sun kuşa faduwa akasa.
Sosai Ummi tasami kulawaa asibitin da aka kaita nan ma wata daya tayi tasoma motsi da kafa da hannun ba sosai ba aka sallameta lokacin cikinta na wata biyar aka hadasu da home nurse dake managing Ummi agida 2/4/7 ga Gwaggo ga Ya Aisha shikuma Nura yabarosu yadawo Nigeria yasan Hadiza tai kokari haryau babu abinda ya shiga tsakaninsu rashin lafiya Ummi kaman ya ciremai sha’awa gabaki daya ajiki abinshi ma bai aiki yanzu dayaga tadan Soma miydi da kafa har an sallamesu yasa hankalinshi yadan kwanta.
7:30 na bayan magrib jirginsu yasauka a Nigeria Hadiza da kanta da yaran sukazo daukoshi dan yaranshi sunyi missing Babansu basu tabayin one whole month basu ganshi ba, itama Hadiza takosa taga mijinta dan tasha gyara bana wasaba har vagina rejuvenating aka mata duk suna tsaye a arrival Aman yafara hargo Babanshi da cabin size LV trolley nashi hadadde wani ihu yaron yayi yace “Daddyyyy” dasauri Nura ya kallo wajen dan ana duba bag nashi ne Amali ta fanfale da güdü tana dady Dady tai wajen Hadiza na kwala mata kira ina batasan wannan ba Aman shima ya bita wani tsalle Amali tayi. “Oyoyooo Dady” Nura yadauketa yana murmushi sosai yace “oyoyooo my princess, Amannnnn” yafadi daidai Aman na zuwa shima yadaga shi duk suka rungume Baban su saikuma sukahau kuka airport authority yace “to baga Dady yadawo ba menene kuma na kuka” ashagwabe Amali tace “I’ve missed my Dady a lot” kiss Nura yashiga manna mata a kumatu daidai an gamamai komi yafito yasauke Aman yaja jakan da hannu yaran na murna Hadiza sai murmushi take akwai wani joy da fulfillment da mata keji idan mijinta nason yaranta cus bakowani maza ke nunama yaranshi so kaman Nura ba, dan tsayawa Nura yayi nesa da Hadizan yabude hannunshi daya yace “baza’amin oyoyo ba” dasauri Hadiza ta taho akunyace ta rungume Nura Aman yayı tsalle yace “Mommy I’m right here carry me let’s hug Dady together” sakın Nura tayi tana murmushi tadauki Aman suka rungumeshi duka yanda kasan yayı shekara baya tareda su (Omoh maza is good to be a good Man oo duk randa kai tafiya aji kaman kayi shekara dari).
Sakinsu sukayi suka wuce Amali na jikinshi har lokacin har zuwa wajen motan Hadiza, boot yabude yasa bag nashi yabude baya yasa yaran Hadiza ta zata mazaunin wanda ba driba ba ta kalleshi cikeda so tace “I will be your driver just for today” cikeda tsokana yana murmushi yace “thank you direba” dariya Hadiza tayi tace “Allah ko you will pay fine” ta maida kofan tarufe tazaga ta zauna mazaunin direba taja motan sai hira yaran kema babansu suna tambayan ya jikin Anty Ummi, kusan duka hiran abinda yafaru da baya nan saida sukamai amotan nan shima yabiye musu har Sauda sukakai gida.
Nan ma har dakinshi suka bishi zaiyi wanka Hadiza zata hanasu yace “tabarsu shima yayi kewan yaranshi” zama sukai akan gadon shi suna jiranshi yawuce bayi dan wanka itakuma Hadiza ta tsaya a dinning tana kara gyara abinciccikan datamai daban daban saukowa sukai shiga yaran abincin ma anan kasan carpet na falo yazauna yaci barbecue chicken da Hadiza tamai ga lasagna, ga Chinese rice da salad ga fresh juice abincin duka sunyi dadi yaci sosai hakama yaranshi dan duk sunkicin abinci wai sai Dady yazo sannan yasa Hadiza tabude jakanshi takawo tsarabansu toys masu kyau yasayo musu yabasu da wasu cute kids slippers da ribbon for Amali Hadiza kuma yabata wani gold bangle mai shegen kyau sai murmushi take yaran suna murna nan fa suka dingama Dadyn su hira Amali anan jikinshi tai bacci Aman kuma anan kan carpet gefen Baban Hadiza tace “finally! Some peace” dan murmushi Nura yayi yace “zoki dauki Amali” zuwa tayi tadauki Amali shikuma yadauki Aman duk suka wuce sama suka kwantar dasu yasauko kasa ya kulle kofa ya kashe tv ya kashe wuta yawuce sama ahankali, dakin Hadiza yawuce but bata ciki tana bayi wanka take ahankali ya maida kofan yafito yawuce dakinshi ya zauna tareda daukan wayanshi dake gaban mirror dan kiran Ummi saiyaga text message nata tace “ka sauka lpy Baban Amalily? Yasu Aman da Amali? Ya kasamı Maman su? Please ka gaishemin dasu, Baban Amali inaso kahuta ka kula da kanki the past 2months kawahala da dawainiyata kaje nan kaje chan duk sabida ni, Allah yabiyaka da Aljanna nagode dakomi My Noor, inamaka so na hakika! Inason ka amiji har aljannatul Firdaus” murmushi yayi saiyay dialing number ta yaji akashe yasan da gangan takashe, Aisha yakira tana dauka tace “Yaya kasauka lpy” ahankali yace “Lpy lau kaima Ummi wayan” dasauri tace “to” kusan 1min tace “gata” tabama Ummi wayan tafice kai tsaye yace “wa yace ki kashe waya?” Kasa magana tayi yace “kinason nahadaki da Gwaggo bakisan nakira naji wayanki akashe hankalina zai tashi ba”? Ahankali tace “kayakuri” dasauri yace “noo bazan hakura ba saina hukuntaki nadawo” dan murmushi tayi murya ciki ciki tace “ka manta kan lokacin””bazan manta ba zansa a reminder” yafadi dasauri ta zaro idanu dan bata dauka yajiba yace “ya hannun da kafan”? Ahankali tace “hannuna na komi yau kawai kafan ne shima Alhamdulillah” ahankali yace “Babyna fa” dan cikinta daya Soma girma takalla tace “gashinan uhmmm munyi kewanka yau tun safe rabon damuga Dadyn Amalily” dan murmushi yayi cikeda so yace “ki kula da kanki kome kikeso kice abaki kada ki gwada tafiya idan nurse bata taredake and again kome kikeso ki kira ki sanar dani okay” gyadamai kai tayi ahankali hawaye yazubo mata daga idanu wlh mugun kewanshi take kaman taita ihu dudda babu sauti but jikinshi yabashi kuka takeyi yasan kewanshi take cikeda lallashi yace “Ummi na” murya Chan kasa tace “uhn” ahankali yace “stop crying dudda ina nan but am still there with you, zan dawo soon kaman gobe ne kinji, kidena kuka kar babyn mu yafara kuka, goge fuskanki” hannu tasa ta goge fuskanta yace “good girl ina Gwaggo bata wayan” Gwaggo dake chan falo zata kashe mijin Ya Aisha da dariya dan yanda kukasan ita ta haifeshi ta kealama kira tazo ta gaisa da Nura tace “wai yaushe ka bata Ummi haka kaga kukan datamini yau bayan katafi kuwa saida zuciya ta debeni nacema sani nima yakaini ma shiga jirgi natafi tunda ni ba mutum bane gani amman tanama miji kuka danya tafi nan fa aka dinga rokana nahakura” dan dariya Nura yayi yace “Gwaggo nidai kidena ma matana fada banso” dasauri Gwaggo tace “kaci mai garinku Nura ungo wayanki nafasa magana tunda shakiyanci yake mini” sallama yayi da Ummi sannan ya ijiye wayan yatashi yafito dakin Hadiza yatafi hartazo taji yana waya hakan yasa takoma dakinta batason takatse shi kuma bataso taji abinda zaisa kishinta yatashi.
Tana zaune gaban mirror tana shafa lips sleeping mask na
25, August 2025
Saadatu Ali
Yes