Showing 165001 words to 168000 words out of 202729 words

Chapter 56 - MAZAN KO MATAN HAUSA NOVEL

M SHAKUR   

17 Feb 2025

8971

sanyi sosai taja bargo tarufa, tsoro mai tsananin gaske ya shigeta daman ance duk mazinaci sai ya haifi mazinaci, tasan ta tuba, takama Allah sannan tarufe past nata, what is happening yanzu? Tayi abubuwa da dama ada, tun tana budurwa kafin tai aure she sleeps around gaskiya with big men sabida tanada kyau Mamanta shuwa ce yan Maiduguri, she’s from poor home but ambition nata nason tayi kudin takuma zama babban mutum a Nigeria da sunanta zai shiga current affairs has always been her dream, bayan a while tasami wani mai kudi ta aura wani bafulatani Nijar but dan Nigeria ne, ta haifa mai Raheena da Hameeda da auren ta hadu da wani attajiri sundanyi abu tazo tarabu da mijinta lurada tayi tana dauke da cikin attajirin tagudu tabar kasan that’s how ta haifi Layla kusan duka yaranta basu da Baba, sai akan Alawiyya shima taje wani course da aka turata daga office na Alhaji taje tayi a Qatar, 2yrs course tahadu da wani yaron masu kudi a campanin news channel da take internship aciki, yaron irin sangartaccen bad Arab rich boy din nan ne, he was 16 then, ita tana 26yrs, just sabida kudi tamai wayau ganin yanda yake yawan kallonta yana bata green light, tanada wani irin baiwan maza nayin kome takeso suyimata, nan da nan tai convincing nashi sukai secret wedding, yabata some properties yamata cikin Alawiyya, daga bayadai akazo aka gano sunyi auren sirri da Ammi aka koreta daga wajen Ammi tai fushi sabida bai iya yahana family shi ba tarabu dashi tahanashi tabar garin ta tafi Dubai, anan ta haifi Alawiyya bayan ta haifeta kodaya mata maganan Babyn tacemai ta mutu wajen haihuwa, abinda yasa yahakura yatura mata manyan kudade yagayamata zaije Australia karatu.
She knows Alawiyya sleep with wani sabida tayi rayuwan itama and batason Alawiyya tai kalan rayuwan ko kadan, kuma tasan koda wasa Alhaji yana gano AJ akwai babban matsala da tashin hankali wlh, balle kuma yagano dashi Alawiyya ta gudu and ya kwantamai da mata bala’i, mesa Alawiyya ke dauko dabi’unta da taurinkanta da kafiyanta duk haka itama take, data sama kanta saitayi kudi saida tayi by fire by force, data sama kanta saitai mulki a gwamnatin Nigeria saida tayi by fire by force.
Yanzu how will she solve this matsalan? Yaya zatayi da yarinyar nan? How can she deal with wacce keda exact halinta? Innalillahi wannan wani kalan jarabawa Allah kemata! Yazatayi da Alhaji? Mema zata gayamai? Wani explanation zatamai na how Alawiyya ends up in Abuja? Ga yarinyar ta tada rigima kan bazata komamai ba the moment Alhaji yagano batada wani power ko influence akan Alawiyya bazata iya tankwarata tayi abu ba koda bataso ai amfaninta da darajanta da kimatan yagama karewa awajen Alhaji kenan, what will she do now? How can she solve this matter? What strings and ropes zatai pulling? How will she deal with this? Yarinyar nan ta shirya tozartata aduniya yaya zatayi yanzu??.





*MATAN KO MAZAN*



EPISODE 1️⃣5️⃣


Yanzu dai have you bought laces, bags, and shoes naki from ASMEEYAMIN COLLECTION?? have you seen what that amazing woman is selling kuwa??? Ohh my my, join her group now and loot kayanta kudi kwasha kwasha.

https://chat.whatsapp.com/Fvbu8FNZxXTIA5oHt26Daj






Duk wacce takaranta min book without paying ita da Allah, I no forgive you ooooo!
Har dare Ammi takasa runtsawa zazzabi ma saiya rufeta sosai da kyar ta tashi ta debo kwayoyi ta watsa abaki tasamu tai bacci gari na wayewa wajajen 10 aka shigo dakin aka sanar da ita tayi baki, wani babban mayafi tadauka tayafa tafito tasauka kasa, wani babban Malami ne yana sanye da malum malum da rawani aka ga katon charbi a hannunshi yana ja, shigowa falon Ammi tayi tasami kujeran dake facing nashi tazauna, cikeda kamala tace “ina kwana Akaramakallahu nagode dakazo” dan murmushi yayi cikin natsuwa da haiba yace “naga sakon ki Fateema Bintu so ai dole nataho” daidai nan aka wadata gabanshi da kayan ci da sha, Ammi takalli yan aikin tace “kufita kuje bayan gida zanyi magana” amsawa yan aikin sukayi suka fice, Malam yace “meke faruwa ne? Kika turamin sakon tashin hankalin nan”? Shiru Ammi tayi sai chan tace “Malam Alawiyya ce fa Auta na, yarinyar na neman tasamin ciwon zuciya, tana neman kunyatani ta tozarta n…..” tai shiru maganan na makalemata sabida yanda zuciya ke dibanta tana sauke ijiyan zuciya sannan tacigaba tace “Malam duk cikin yarana kasani ai babu wanda yake iya kallona ya kalli tsabar kwayar idanuna ya maidamin magana wlh kuwa amman Alawiyya narasa yanda zanyi da ita, ayanda nake ganinta tana gab da ta dauramin mari ma” tayi shiru chan tace “jiya lamarinta ya girgizani ainun, kaga rashin kunyan da hayagagan data mini kuwa, tana neman taki tankwaruwan mini, nai dukan nai zagi nai ihu amman cemini tayi ko kasheta zanyi tagama zaman aure da Alhaji mai Makamashi, hankalina inyay dubu yatashi Malam yazanyi da ita? Mezan gayama Makamashi bayan shine ubangidana eh? Alhaji Makamashi shine gatana shine wanda ya tsayamini agarin nan ai kasani ban boyemaka komi akan lamurana, ya takeso nayi? Malam narasa yanda zanyi, gabaki daya idanunta sun juya bata damu da damuwar da abinda tace zai iya jefaniba, wlh nakasa bacci tun jiya, abinci nan nan nakasa jefawa abakina, narasa wanda zan gayamawa? Narasa yanda zanyi, Malam ka taimakamini banson sanadın Alawiyya na tozartu nasha kunya, duniya tanin dariya ana nunani, nadamu sosai, yau aka cireni a minister yan adawa da zasumin dariya dayawa suke” Ammi takarashe maganan tanajan bakin lullubin datayi tana goge hawayen daya zubo daga idanu, Malam yace “assha ashha wannan lamari baiyi kyawu ba, amman ya isa kada kidamu akwai abinda za’a mata” kallonshi Ammi tayi tace “mene za’amata? Zai karkatomin da hankalinta”? Dan gyaran murya yayi yace “kwarai, ai kaman addu’an dana miki abaya babu wani abokin adawa dazai tunkareki ya kalli tsabar idanunki yamiki maganan banza hakama akwai addu’a damukema yara kangararru fitinannu dake gallabar iyaye” gyara zama Ammi tayi dasauri tanajin wani karfi Malam yace “ire iren yara irinsu Alawiyya masu ma iyayensu gardama da taurinkai yaradai dake bama iyaye ciwon kai, zakiga dazaran munyi addu’an Allah zai dauraka kan yaran, Allah zai dauraki akanta, zuciyanta zaiyi sanyi yayi lugub, duk fitinanta takalli kwayan idanunki rasa bakin zatayi kuma dole tayi abinda kikeso and komi zai tafi yanda kikeso bazata sa kiji kunyan duniya ba da izinin Ta’ala” wani irin dadi da Ammi taji batasan lokacin data fashe da kuka ba tace “wayyooo Allah na Malam, nagode nagode, Allah kara kara muku fahimta, nawa ake bukata ko nawa ne zan biya eh”? Anatse Malam yace “bijimayen shanaye kawai nakeso guda uku da buhun shinkafa da kudin girki, za’ama Almajirai abinci da naman, asakasu farin ciki sai ayi addu’an kibani kwana bakwai zakiga abin Al’ajabi, Alawiyya tayi kadan taja dake da izinin Al Quddusu” dasauri Ammi tace “Malam na yarda dakai da rayuwata gabaki daya dari bisa dari, ai tun addu’an dakamin kafin nazama minister nan nazo nazama na kara yarda da addu’anka Malam” jinjina kai Malam yayi yace “bana bokanci ni Allah nake taya mutane roka yabiya musu bukatan su, kuma ana dacewa sosai, dan haka karki damu kema kitashi tsaye akanta kina addu’a da izinin ubangiji bazakiji kunyan duniya sabida abinda kika haifo zuwa duniyan nan da cikinki ba amman dai ko menene kwana bakwai nake bukata sai bayan nan zakiga chanji” dasauri Ammi tace “to godiya nake Alaramma, bari na dauko kudin komi da komi a sama” sama tawuce bata wani dade ba tadawo da rapa rapa na yan dubu dubu guda ishirin ta zuba a Leda tabashi tace “Malam zanyi transfers bansan shikenan cash danake dashi agidaba Wallahi” karba yayi yana tashi yace “bakida matsala sai najiki sai anjima” har waje Ammi ta rakashi yashiga wata mota yawuce itakuma takoma ciki ta zauna tai shiru tana tunani how will she stop investigation da Alhaji yakeyi a Kaduna? Koda wasa bataso agano gaskiya har agano AJ hakan nada mugun matsala kuma tasan babu yanda zatayi ta gayamai anga Alawiyya tana nan dabazai zo da gudunshi ba, so what will she do now, she wants to deal with AJ on her own idan Alhaji yasani abin will be messy ayanda yakeson Alawiyyan nan, to yazatayi?



Shiru tayi tana karkada kafa tana tunanin how can she kill two birds da one stone? Tayaya zatasa Alhaji ya dakatar da investigation dinnan batare daya zo nan Abuja yaga Alawiyya ba? Ta tambayi kanta still shaking legs nata tadaura hannu kan bakinta, sai channnn ahankali tadena kada kafanta tareda sauke hannunta daga saman bakinta sabida wani idea daya fado mata arai dasauri ta tashi tawuce sama zuwa dakinta waya tadauka tazauna akan gado taciro number Alhaji ta kalla tareda gyaran murya sosai gudun karya dago wani abu sannan tai dialing number sa, ringing one two yadauka muryanshi sounds so weak yace “Hello Binta kun sauka a Kadunan ne”? Dasauri Ammi tace “a’a Yallabai ina kwana, kai kadaine akwai wata yar magana dazan maka”? Dan yunkurowa yayi ya jingina da kujera yace “na’am? Eh ni kadaine ina dakin Lawi gani nan kwance rungume da tufafinta ya akayi?” Ijiyan zuciya Ammi tasauke tace “Alhaji inaso you should calm down da abinda zan fadamaka don’t panic and kabani hadinkai, katuna ai jiya kafin mutaho na sanar dakai Raheena ce takira akan akwai matsala nataho yanzun nan” Alhaji yace “kwarai kin gayamin, Meya faru mecece matsalan?” Dan ijiyan zuciya Ammi tasauke tace “Alhaji dan Allah don’t panic ka natsu ka saurareni” gabanshi na faduwa sosai yace “ina jinki menene fadamin Binta” ahankali Ammi tace “Alawiyya tadawo!” “Mene! Alawiyya! Lawi….Lawi na…. Wayyooo Allah zuciyana, Lawi Lawi Lawii……” maganan shi ta daburce kaman yana kuka kai kaman yazare, Ammi tace “Alhaji wannan ne abinda banso this is the good part of the story, listen to the main thing dazan fadi” yana ijiyan zuciya sama sama yace “ina jinki” ahankali Ammi tace “Alawiyya ba lafiya sosai fa, tuburan tuburan” zabura Alhaji yayi yatashi zaune yana sakin tulin kayan Alawiyya daya rungume a kirji yamike tsaye yace “meya sami Baby na? Meya sameta gani nan zuwa right away, wayyoo Lawi na” dasauri itama Ammi tace “Alhaji dakata kaji bazaka iya ganin Alawiyya yanzu ba, yanzu haka mun dawo daga gidan Malami ne shine nace bari nakiraka kasan meka faruwa” gaban Alhaji na bugawa dum dum dum yace “ina jinki, meke faruwa? Meya sami Lawi?” Dan ijiyan zuciya Ammi tasauke cikin muryan tsantsan tashin hankali tace “Malam yace jifa aka mata!” “Mene? Jifa? Wani dan kutumar durun uwa ne ya jefi Lawi na? Wlh wlh ko uban waye sai inda karfina yakare, Jifa fa kikace Bintu” cikin tashin hankali Ammi tace “eh, to Alhaji Malam dai yace ana zargin daya daga cikin kishiyoyinta ne wato matanyen ka!” Yanda jikin Alhaji yafara rawa zaka dauka shocking yataba yama kasa magana, Ammi cikeda makirci tace “ashe wai tun fitan nan datayi daga gidanka alokacin sihirin ya bugeta ba’a cikin hayyacinta tafita ba, anyi asiri akan ta tsaneka sosai, ta kijininka ta tsaneka sosai ko kallonka bazata kaunaci yi ba, sannan ta shiga duniya, duk wannan haukan datayi bata sani ba, infact batamasan ina take for 7days ba, kawai Raheena taga Alawiyya agaban gate na gidanta gabaki daya yarinya tadawo mahaukaciya Alhaji, Malam yace kada abari tahada idanu dakai harsai an karya sihirin sabida zata iya kasheka kota jimaka dan haihata haihata aka muku, yace 7days yake bukata ya karya sihirin”.


Yanda gaban Alhaji ke bugawa zaka dauka zai fashene kaman wanda zaiyi kuka yace “Innalillahi wa Innalillahi raji’un! Wattaba’u ma tatalu shayadini ala mulki sulaimanu, me Babyna tamusu? Yarinyar dako kasamata hannu abaki bazata iya ciza ba, yaushe aka haifeta sunfayi jikoki da ita, ubanme Babyna ta musu? Yarinyar da bama tasan suna rayuwaba, ni mesa basu jefeni ba zasu jefi abinda nafi komi so aduniya iyye? Metamusu akan mene zasu jefeta sukasa tanata garari aduniya da gatanta da komi” Ammi tace “hmmm I tell you, dana ganta saida na fashe da kuka kaga yanda ta rame ta lalace ba kyan gani? Ta rame? Tai duhu, tun kayan data fita dasu sune ajikinta for good 7days, ihu kawai take tana kururuwa wai she hates you she hates you tagama aurenka” cikeda damuwa Alhaji yace “la’ilaha illallahu! Ya Allah kamini barra’u da kowacece tamin wannan mugun abu, da Lawi ta tsaneni ai gwara duka duniya su tsaneni zan jure but nata ina samsam” Ammi tace “Malam yace ka kira ayi sauka a gidan nan” Alhaji cikeda damuwa gwanin ban tausayi yace “to na aiko mata dasu Hassan ne ko zataji dadi”? Shiru Ammi tayi idan aka kawo yaran zata kara gyara zama taki komawa idanko sunachan she can use the kids and blackmail her to go back dasauri tace “a’a kabarsu ni banjin ko yaran yanzu zata ganesu ba, Alhaji kaima katashi tsaye fa amaka tsari da sauransu” dasauri yace “yanzun nan zan kira Malamina amana addu’an kariya harda yaran, akuma mini kaikayi koma kan mashekiya, yanzu nawa ake bukata for magungunan ta” dasauri Ammi tace “yanzu nabama Malamin 20M” Dasauri Alhaji yace “I will transfer 100M to account naki yanzu kome ake bukata ki gayamini, sukuma zan dauki mummunan mataki akansu billahil azim, ina Lawi na yanzu ko hotonta ne ki dauka ki turamin” Dasauri Ammi tace “ai kasan nima bata gidana gidan Yayanta Raheena take, Raheena kadai yanzu takeso take kuma yarda da ita, kaman ita kawai ta gane amman zan koma gidan anjima zan maka hotonta kada ka damu, inaga ka kira yan sandan nan ba adena bincinken tunda an ganta” dasauri Alhaji yace “yanzu zan kira inspector, dan Allah ki kulamin da Lawi Binta, ku kulamin da ita da kyau, ku kulamin da yarinya na, kome akeso, kome akeso asanar dani, dan girman Allah Binta, zan hakura kwana bakwai idan ba cigaba zan taho da nawa malaman” dasauri Ammi tace “shikenan bari naje namata girki” ta katse wayan tana sauke ijiyan zuciya tana kallon wayanta, tace “I love duka yarana I can give them kome sukeso, suma kuma saina sami abinda nakeso dasu, Alawiyya ko kinaso ko bakiso Alhaji na zaba miki as miji sai kin zaunadashi Wallahi! Zan nuna miki nina haifeki bake kika haifeni ba, sabida dan iskan soyayyan ki bazan rasa seat dina ba and zanyi maganin yaron nan, badai kina gida yanzu ba, in this life zakisan cewa soyayya is not for the riches! Ga soyayyan but bazaki taba yinta ba dan ubanki!”.


Do you really think Ammi zatabar yarinyar nan tahakura tabar auren Alhaji???
Well my people in this book I want to show you the power of a mother😂 A mother can f*ck you Up idan tanaso! A mother can either help you archive dream naki or shatter your dream!!

In this chapter natabo iyaye badan rashin kunya ko cin mutunci ba but to let parent know cewa decisions naku can actually kill yaranku ya hallaka yaranku.

Why are some parents stubborn?? Mulki da dadi babu maison impeachment but amman look at that child naki dakike killing in that process.

Ammi is just showing you reality of some yan sayasa.
Dearest Parents be guided okay! And May Allah bless all our mothers.

Now my question.
Ammi zata sadaukar da soyayyanta ga Mulki for Alawiyya diyarta, ko Alawiyya ce zata sadaukar da soyayyanta for Mahaifiyarta sabida kartai loosing Mulki????

A mother and daughter WAR 🤯





EPISODE 1️⃣6️⃣





ASMEEYAMIN COLLECTION ASMEEYAMIN COLLECTION ASMEEYAMIN COLLECTION ahhh kunsan mesa naketa kiran sunan this brand?? Sabida is one of the best wajen saida laces takalma and bags, wayanda suka saya kaya daga wajenta can testify now rush and join WhatsApp group nata kuma kusayi kaya💃
https://chat.whatsapp.com/Fvbu8FNZxXTIA5oHt26Daj





Hana kowa yamata magana Ya Raheena tayi hakan yasa duk suka tafi da kanta ta kula da Alawiyyan ta shafa mata hot balm a waist nata da Ammi tabuga a table ta share mata baki tabata pain killers sannan ta kwantar da ita akan gado tana shafa kanta kawai tana kallonta, mugun tausayi Alawiyyan ke bata bini bini yarinyar tai kuka, ta juya tai chan, tai nan ahaka bacci yayi awon gaba da ita.
Wajajen 4 ta tashi da kyar ta mike bayi taje da zumin yin fitsari da alwala kawai saitaga blood, ajiyan zuciya ta sauke, tayi deep down kuma feeling relief batason tayi cikin AJ batare da sunyi aure ba, fitowa tayi jin hayanyiyan yaran Ya Raheena hakan yasa tafito suna chan falon kasa, hango wayan Bobo akan gadon dakinsu dayake a bude tayi hakan yasa taje dakin dasauri ta dauko wayan kawai saita kashe ta tura karkashin gado, yaran banda wayoyi sunada İPad sunmafi damuwa da iPad dinsu sabida game, Teddy gadon tadauka ta rungume she misses AJ so much, she miss kamshin turaren shi, she miss his touch, his smile, his hands a jikinta, she misses yanda yake magana da ita, yanda yake lallashinta, he is the only person aduniya daya damu da farin cikinta da bakin cikinta duka, idan har Allah yabata AJ batajin akwai wani abu dazata kara damun Allah akai yabata ba, tanason AJ sama da rayuwanta, tun ranan haryau basuyi waya ba kawai saita hau kuka ahaka Ya Raheena tashigo dauke da tray na abinci taganta ijiye mata abincin tayi tace “eat Cookie” batare data kalli Yayan nata ba tace “I want pad” juyawa kawai tayi yafice takawo mata pads da disposable pants a kwali karba tayi tawuce bathroom itama Ya Raheena tafice she don’t wanna talk to her yanzu harsai yadawo daidai.
**

Waiwaye Baya Kadan!
Wuraren 10 nadare AJ yakai gidanshi, sauka yayi yabude gate yashigo da motan yakoma yarufe yajuyo tun kafin yakai kofa yaga Khairat tafito da gudunta da bala’in farin ciki tayo wajenshi, chak ya tsaya dan baiso tai hugging nashi hakan yasa itama ta dakatar da kanta ta tsaya dab da shi jiki asanyaye ganin ko bude mata hannu baiyiba alamun she can hug him, ahankali tace “sannu da zuwa, ya aiki? Kadawo lpy”? Kai ya gyadamata yace “fine ya kuke Ya princess”? Yayi maganan yayi gaba tabiyoshi abaya feeling so happy ganinshi direct dakinta yashiga dudda Alawiyya na bacci saida ya dauketa ya rungumeta tsamtsam ajikinshi yana motsi, tsayawa Khairat tayi jikin kofa tana kallonsu bata taba sanin is
possible kaso yaro kaki uwarsa ba sai akan AJ, son Alawiyya

25, August 2025
Saadatu Ali

Yes

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login