Showing 15001 words to 18000 words out of 202729 words
Ameena sosai” Hajiya data washe baki tace “nima inason d’ana sosai” Ameena ta turo baki tace “Hajiya nifa” dan dariya Hajiya tayi tace “Inason ku duka akwai wanda ma yasamu soyayyata irinki Auta na” ahaka suna family hira sukakai gida Nura yace “specialist danai consulting yace zai ganmu by 12 yanzu zakici abinci kihuta anjima saimuje asibitin ko” yayi maganan tareda yin Parking yafito da ita sabida dakali da kafanta tayi tafiya tana rikeda shi suna tafiya ahankali Ameena biye dasu tana kallon hadadden gidan, bude kofa sukayi suka shiga ciki wani lafiyayyen kamshi yamusu sallama dasauri Ummi tafito daga kitchen tazo har tsakiyan falon ta duka tace “sannu da zuwa Mama, ya hanya ya jiki, Allah yabaki lafiya Mama, Allah yasa kaffara ne” washe baki Hajiya tayi tana kallon Ummi tace “waye wannan yarinyar mai ladabi ba irin su Auta ba da basu gaida mutane da kyau, ga iya addu’a, waye ita”? Dan murmushi kadan Nura yayi yace “Ummi sunanta” daidai Hajiya na zama, Hajiya tasauke ijiyan zuciya tace “jiki Alhamdulillah Ummi, sannu kinji Allah miki albarka tashi tashi ki zauna, ina Hadiza? Nasan jikoki na ana makaranta ina Hadiza?” Hajiya takara tambayan da zuciya daya tana waige waige neman Hadiza, cikeda hikima Ummi tace “tadanje tadawo wani uzuri yakamata amman tace na kula dake da kyau kome kikeso namiki” sosai Nura ke kallon Ummi yanda yarinyar keda hikima baitaba sanin zata iya fadan magana hakaba, dariya Hajiya tayi tace “ayyooo” kallon Amina data shigo da jaka Ummi tayi gateman biye da ita da kayansu da sauri ta tashi tace “kawo nakai miki daki jeki zauna kihuta kinsha hanya” murmushi Meena tayi tace “thanks” kai kayan sukayi sama sannan Ummi tadawo tashiga kitchen a tray tajera abincin Hajiya da ruwa a bowl mai kyau na wanke hannu tafito takawo har gaban Hajiya, Hajiya tace “Ayyah sannu da aiki Ummi, Allah dai yasa cimata ne dan yanzu bakomi nakeci ba, cuta batayi ba” tai maganan tana bude kulan ganin tuwon Alkama da miyan zogale dayaji ganye yasa Hajiya tace “laaaaaaa Hadiza tamin girkin nan kafin tafice” dasauri Ummi tabude baki zatace eh Nura yace “Ummi ta dafa miki Hajiya” kara kallon Ummi Hajiya tayi saikuma ta nunawa Meena Ummi tace “kinga girkin sa’onninki ko ke sai shegen kiwuya, wai wannan kamshi haka bari naci abincin nan akasa zan zauna ma” da taimakon Nura tazauna akasa ta wanke hannu takai abincin baki saita kalli Nura takuma kalli Ummi takara kallon Nura again tace “Ummin nan dai danake gani tai girkin nan”? Gyadamata kai Nura yayi sai kawai Hajiya tace “Allahu Akbar wlh tayi girkin yanda nakeso, kaga ba gishiri ba magi, sannan bata sakamin jan nama ba hanta da Koda kadai ne amiyan, cimata tamin kuma yanda nakeso, bani jakana Meena kigani” bata jakanta Meena tayi Nura ya karba, dasauri Hajiya tace “ciro duka kudin dake purse dina” murmushi yayi ba musu yaciro dubu goma da dari biyar ne ta karba tamikama Ummi tace “ga tukuicin ki dan kin dadada mini rai kinsa natuna na diyata Aisha mai bin Nura tana aure a eygpt ita kadai kemini abinci irin wannan taste din wannan tarban da akamin bazan taba mancewa da ita ba, nagode ko Ummi amshi kudinki” akunyace tace “Mama kibar shi ni nadafa miki ne kawai wlh” Hajiya tace “laaaa ungo amshi nace” dan satan kallon Nura tayi shima kallonta yake ahankali yace “bazaki amsa kudin Hajiya ba kinsan kalan makon Hajiya kuwa? Ba kasafai akecin kudinta ba, ke kinyi sa’a tabaki” dariya duka sukayi harda Ameena, Hajiya tace “atoh dan haka karbi abinki” gently Ummi tasa hannu ta amsa ahankali tace “nagode Mama Allah ya ninka miki dubun su” Hajiya tace “Ameeen Ameeen” Ummi na murmushi takalli Ameena tace “nadafa miki shinkafa dafa duka dakuma taliya na manja wanne zan kawo miki” dasauri Ameena tace “taliyan manja” harzata tashi saikuma tadan kalli Nura dake kallonta kasa kasa tace “Alhaji mezan kawo maka bakayi breakfast ba kaima” abincin Hajiya yakalla yace “zanci abincin Hajiya” gyadamai kai tayi tawuce kitchen karaf akan idanun Hajiya yanda Nura ke kallon yarinyar amman batace komi ba, saida sukaci sukai kat Ummi takawo mata juice na cucumber kadai data mata Hajiya tasha sosai sannan Nura yakaita sama dakinsu dakin dake kusada na Hadiza inda Hadiza ta kwana ranan ta gyara Hajiya ma sai complain take ita batason sama Nura yace yafiso ta kwana inda zai dinga jin motsinta hakanan ta hakura.
Wuraren 12 suka fice asibiti Ummi tasake gyara gidan.
Sai wajajen shidda saura suka suka shigo gidan da gudu daga Aman har Amal sukazo suka rungume kakansu abinci Ummi takawo, tama Hajiya unripe plantain porridge datasa shuwaka da bushashen kifi da daddawa aciki shima ba maggi ba gishiri sai kamshi daddawa da kifi sun bama abincin taste, tayi jellof rice da naman rago ma sauran mutane, duk suka baje harda Nura za’aci abinci anan falo, Ummi takoma gefe ta duka Hajiya tace “kema taho nan kici, an taba haka ki mana girki saiki koma gefe, tahonan” dan satan kallon Nura tayi shi harya faracin faten Hajiya ma, da idanu yamata tazo nan, hakanan taje tashiga cikinsu suka faracin abinci, ita da Ameena da su Aman shinkafa sukeci, tunda tafara aiki yaune rana na farko data ji kaman tana gidansu Hajiya ne Gwaggon ta Amina kuma yan uwanta, sai hayaniya su Amal keyi anacin abinci, no wonder Alhaji keda kirki mahaifiyar shi batada matsala at all. Nura yace “Hajiya dan ban juice din cucumber dinki nasha” jug din Hajiya ta kalla tace “kai Nura na tsammaka na tsammaka harna gaji da sammaka wai kaine mara lafiyan nan ne”? Dariya akayi Ummi itama dan boye dariya ta tayi ganin yanda Hajiya keda barkwanci, takalli Nura tace “inje inmaka kaima Alhaji”? Batare daya kalleta ba yace “a’a kihuta zansha na Hajiya” kofi Hajiya ta dauka ta tsiyaya mai rabi ya karbe ita ta shanye rabin tace “Allah miki albarka Ummi zaki koyama wannan shashashan Autan nawa kafin mu koma” gyadama Hajiya kai tayi, Hajiya tace “Auta dukta cinye ke bakici komiba” dasauri Ummi tace “naci sosai wlh” kashigo falon ji zakayi inama haka farin ciki zai dawwama agidan, Nura yana lura da yanda bini bini Ummi kecin abincin tana duba Amal da Aman, chan kuma saita debo tai feeding Amal da mostly wasa take da abincin at this point bazaiyi karyaba yarinyar ta shiga ranshi sosai barinma dayaji labarinta dazu, yaji ta taba aure har ta haihu dudda pre matured birth tayi amma saiyaji yakara natsuwa da ita, wato saisa takeson yaranshi kuma saisa takeda hankali koba komi tanada experience, baison yayi mu’amala da yara masu danyan kai that knows nothing akan aure koba komi tasan menene aure kuma tayi zaman aure, tayi rainon ciki, sannan tayi nakuda, hakan is perfect for him.
Sake lura da yanda yake satan kallonta Hajiya tayi daidai nan aka bude kofa aka shigo dukansu suka dago kai cikeda fara’a Hajiya tace “oyoyo oyoyoo, sannu da dawowa Hadiza” tundaga inda Hadiza ke tsaye tabi kowa na falon da kallo da yanda falon yayi kacha kacha dudda bawai kacha kachan yayi ba kayansu ne jaka da gyaluluwa dasuka zuba akan kujera dan dawowansu kenan Ummi ta taresu da abinci sai abincin da Amal da zuzzubar a falon rice din, daidai nan idanunta yasauka akan Ummi dake cin abinci tareda Amina dakuma yaranta akasa tana kokarin bama Amal abinci abaki hankalinta kwance dan akasa take zaune technically batayi laifi ba yau. “Ke menene aikinki? Jibi yanda gidana yayi kacha kacha zama kikayi kinacin abinci? Kina yar aiki waya gayamiki kinada darajan zama inda mijina yake kici abinci eh”? Yunkurawa Ummi tayi jikinta yayi sanyi zata tashi dasauri Hajiya tace “dakata Ummi” takalli Hadiza dake tsaye awajen da taje tace “ninace taci abinc……” “Hajiya dan Allah kidakata badake nake magana ba” Hadiza tayi maganan rai abace dasauri daga Nura har Ameena suka juyo suka kalleta da mugun mamaki itama Hajiya tayi tsuri tana kallonta dan batasan haka Hadiza tazama tasan ta dai da rashin son aiki ko sunzo babban salla Kano dama ba zama take agidanta ba saidai ta gudu gidansu so bata wani zauna da Hadiza one on one na dogon lokaci ba, ganin abun zai zama wani kala yasa dasauri Ummi ta tashi zata juya strictly Nura yace “dawo ki zauna kicigaba da cin abincin ki” cikeda tsoro Ummi takalli Nura gabanta na faduwa tadan kalli Hadiza dake kallonta rai abace ahankali takoma ta zauna abun ya mugun mugun yima Hadiza ciwo dan yaune rana na farko daya nuna bata isaba agaban yar aikin yawanci ba agaban idanunta suke tsiyansu ba, zuciyanta wani kalan baki yayi takalli Nura tace “muzuba nidakai badai anzo har cikin gidana ana nema ajuyamaka kai ba tun yanzu an fara kulla kisisina da shairi ko da sunan rashin lafiya amman bakin mutum rass yazauna yana zakalkalan abinci to wlh muzuba dani dakai” Ameena jitayi kirjinta na tafarfasa badan Ya Nura na zaune wajen ba da wlh saita durama Hadiza ashar wucewa tayi fuuuu tayi sama kunyan duniya rufe Nura yayi abinda matarshi tama Hajiya jiyayi ma abincin ya isheshi kowama hatta yaran jisukayi abincin ya ishesu Hajiya ta kalli Ameena tace “tashi keda Ummi ku gyara wurin” kunya yasa Nura yamike yama kasa kallon kwayan idanun Hajiya yajuya yace “bari nazo Hajiya” baima jira amsanta ba yafice dasauri Hajiya tabishi da kallo saitaji dan nata yabata tausayi.
Kayan daya sayo dazu yasa mai gadi ya kwashe yakaima Ummi sannan yaja mota yabar gidan.
Abin yama Hajiya ciwo sosai, ya sosa mata rai, ta haifi yaran dasuka girmi Hadiza, yaranta mata uku biyu sunyi aure saura daya, ita Hadiza zatama rashin kunya haka. Dawowa daga kitchen Meena tayi ganin ba Yayanta awajen tazauna kusada Hajiya tace “Hajiya Hadizan nan yar iska ce kuma wlh wlh ta ijiye iskancin ta a inda tasabayi let her not try that nonsense da ke inba hakaba ni kadai na isheta wlh dan idan nakira su Ya Aisha har gida zasuzo sumata shegen duka ba Egypt ba Ya Aisha zata iya barin ko’ina take aduniya tazo muma duk wacce ta zageki shegen duka……” hannu Hajiya tadaga mata tace “banson maganan nan Auta, Matar yayanki ne” cikin fushi Meena tace “koma waye dama nasha gayamiki halinta tunda kika fara rashin lafiya sau daya bata taba kiranki taji yajikinki ba, yar iska kawai mahaukaciya wacce batasan darajan iyaye ba idanma kinci abinci na kanin ubanta kikaci kona danki, okay saitaga kina shurin mutuwa ne zatasan baki da lafiya dakikiya kawai” Hadiza dataji duka maganganun Meena dan saukowa tayi zataci abinci takoma sama saikuma gobe, takarasa saukowa takalli Ameena dabama ta lurada itaba tace “did u just call me dakikiya Ameena”? Dasauri daga Hajiya har Meena suka juyo suka kalleta Meeena zatai magana Hajiya taja hannunta cikeda hikima irin na manya tace “a’a badake takeba Hadiza wani labari take bani daya faru a kano” kwafa Hadiza tayi tace “gwara dan wlh dasaita bar gidan nan yanzun nan kema kibita” fizge hannunta Meena tayi daga hannun Hajiya tamike tsaye tai wajen Hadizan dan rainin wayon ta yayi yawa ta nunata da hannu tace “an kiraki dakikiya dake nake Hadiza idan baki koreni daga gidan nan ba baki cika yar halas ba” Hajiya datake daga zaune tahau yunkurin tashi tana kwalama Meena kira itama Ummi tafito daga kitchen da gudu tazo wajen yaran ma haka daidai Hadiza na nuna Hajiya tace “kinga dakikiya chan not me” Meena batai wata wata ba ta daurama Hadiza mari abaki jikake tasss!!!! Haba sai jini Hadiza ta kurma ihu tadaura hannunta kan bakinta dataji lema lema tacire hannu taga jini ahaukace tace “ni kika mara”? Ta chakume gaban rigan Meena da karfi, dambe sukahauyi ba kama hannun yaro Hajiya tafashe da kuka sosai Ummi tashiga rabasu amman ina basa rabuwa, dukan juna suke sosai bana wasa ba, Meena ta fizge ribbon din gashin nan taja gashin kaman zata cire mata su daga tushen kwakwalwa, da gudu Ummi tayi waje Mai gadin su takira yazo da kyar aka iya rabasu aiko Meena ta bala’in lallasa Hadiza bakinta sai jini yake ta yayyakusheta a wuya da hannu, dudda itama Meena ta daku a hannun Hadizan amman bata sami any ciwo ba kaman yanda tama Hadiza kowa sai nishi yake, shiga tsakaninsu gateman yayi Ummi tarike Meena tace “dan Allah kuyakuri” cikide zuciya Meena tace “kada kice na yakuri Ummi ba’a haifi wacce zata zagan mini uwa agabana banyi wani abu ba, am I even my mother’s daughter idan agabana za’ahau zagin Mamana nai yi shiru eh? Is she mad? Ba’a bata tarbiya agidan su bane? Idan ba’a bataba ni I will give u, dagayau kowace uwa kika tashi zagi zaki tuna diyar wata ta taba miki duka dakika zagan mata uwa, you are very very very stupid to insult Hajiya kinji, shegiya mai halin matan da iyayensu sukama baki” cikin ihu da kururuwa Hadiza tace “wlh, wlh, wlh yau saina kulleki a police station na rantse da Allah, ni kika daka kin san wacece ni anan Abuja? Number one, the most successful business owner anan Abuja, kinsan award guda nawa ke cikin office dina? BBC waye waye duk anyi hira dani, nizaki zo har gidana ki daka? Wlh wlh u are a small girl yau zan nuna miki your place” tana maganan tayi kofa bayan ta fincike key nata awajen tray na car key ta shiga motanta tafice dasauri Ummi tasaki Meena tayi wajen Hajiya dake kuka shikuma gateman yace “ayi hakuri ayi hakuri” yawuce yafita.
Dukawa Ummi tayi takai hannunta tana sharema Hajiya fuska tace “Hajiya kiyakuri” da kyar Hajiya ke iya magana tace “Ummi kiramini Nura gobe goben nan zan koma gida Meena batajin magana nasha gayamata zuciya batakai mutum ko’ina, kowani zagi Hadiza tamini sai mene ita ta zaga basaita bartaba akanme zatai dambe da Matar yayanta eh akan mene daga zuwa na garin nan yau yau din nan? To ko warakata na nan nahakura kiramin Nura idan akwai jirgi yanzun yanzun nan ma komawata zanyi kano” yanda Hajiya ke kuka tana bama Ummi wayanta yasa takira Nura, yana dauka yace “Hajiya” ahankali tace “nice kazo gida Hajiya na nemanka” hakanan jikinshi yabashi wani abu daman baiyi nisa ba duka duka yana ta gaban estate nasu fruits yaje saya yasan yanda Hadiza tadawo saitai rashin mutunci saisa baiyi nisa ba at all dasauri ya katse wayan, ijiye wayan Ummi tayi tadauki Amal dake kuka sosai ta goya Aman ma ta lallasheshi dan duk kuka suke sunga anci uwar Maman su, taje wajen Meena dake wajen dinning zaune akasa yanda Hajiya ke kuka yasa she’s feeling so guilty dan yanzun nan hawan jininta zakaga yatashi, yana isowa gidan ko parking baiyi da kyau ba yafito yashigo gidan Hajiya yagani tana kuka sosai yaranshi suma kuka Ummi sai jijjiga Amal take ga Meena akasan dinning idanunta sunyi jazur kayanta ya chukurkude kaman wani abu yafaru dasauri yayi wajen Hajiya ya duka yace “subhanallahi hajiya menene haka?” Cikin kuka tace “kaga Ameenatu yarinyar chan bazata taba daina jamini bala’i aduniya ba, duba jirgi yanzun nan idan an samu mukoma kano nahakura da asibitin Nura bazan iyaba bazan iya da tashin hankali ba” rungume Hajiya yayi yace “ya isa Hajiya ya isa daina kuka muje ki kwanta gobe da sassafe saiki koma” yay maganan trying to just calm her down, yace “ya isa ko I’m here now, everything is gonna be fine”.
Sama yakaita yana zuwa wani allura yamata a hannu da Dr yace adinga mata idan anga hankalinta yatashi nan da nan bacci yadauketa yasauko kasa yazo inda Meena take zaune yace “Meya faru?” Baki tabude zatayi magana saikuma tafashe da kuka cikin kuka tafada mai duka abinda yafaru batai karyaba zaiyi magana daidai an bugo kofa an shigo Ummi ce dawasu yan sanda guda biyu ta nuna Meena tace “officer ga tachan” tashi da sauri Nura yayi yana kallon Hadiza da yan sandan guda biyu wanda ganin Nura yasa basu karasa shigowa falon ba duk suka tsaya anan mini parlor dasauri yakaraso inda suke ya mike musu hannu yace “officer lafiya”? Mutumin yace “Madam dinka ne tashigar da kara kan mother Inlaw ta da sister Inlaw sunzo har gidanta sun mata taron dangi anmata duka, kuma munga shaida bakinta da wuyanta saisa muka biyota muyi arresting sai amusu sulhu a police station” ijiyan zuciya yasauke yajuyo yakalli Ummi dake faman jijjiga Amal tana kuka tarike hannun Aman yace “ku tafi sama keda Meena dakin Hajiya ku rufo kofa” dan yasan Hadiza zata iya kamasu da duka kuma, gyadamai kai tayi tawuce takama Meena duk sukai sama, Hadiza tace “ba sama ba ko lahira kukaje sai anyi arresting naku yau wlh” officers din duk suka kalli Hadiza Nura yace “bismillah ku muje waje” binshi sukai waje Hadiza tabiyosu officer da kanshi yace “ki barmu maza muyi magana mana Madam” tsayawa tayi saikuma ta buga tsaki takoma daki, explaining komi Nura yamusu yama nuna musu some magungunan Hajiya dake motanshi yabasu hakuri kan kada suyi arresting kanwarshi, ganin kamalan shi da natsuwan shi duba kuma da babban mutum ne, a well known businessman anan Abuja kuma ba yaro ba sannan sunga yanda Hadizan keyi itama borkonon kanta ce yasa sukai Na’am dudda haka saida suka amshi 20k a hannunshi kafin su tafi, suna tafiya ya tsaya ya jingina da mota yadan sauke ijiyan zuciya baiso ya yanke decision cikin fushi yakai 5min awajen sannan yakoma ciki afalo yaga Hadiza jikin window tana ganinshi ta taho tana ihu tana tafi tace “u bribe them and send them away sabida kar ayi arresting sister ka da Maman ka ko? To rest assure wlh wlh I will so deal with them, wlh saisun barmin gida, babu wani mahaluki dazai shigo gidana and snatched my peace of mind for me to menene amfanin karatun danayi? Ina zaman zamana wata Maman miji ta dawo gidana da zama is that even fair? Ba manyan asibitoci ne a Kano? Why here why Abuja? Let’s be fair fa Nuri, lokacin da Maman ka ke gidan mijinta mother inlaw dinta tazo ta tare mata
25, August 2025
Saadatu Ali
Yes