Showing 42001 words to 45000 words out of 202729 words
kishiya kaji, Nuri dan Allah wlh I can’t stand naganka da wata zan iya haukacewa barinma yar aiki na, dan Allah kaji Nuri mena maka zakamin kishiya da Ummi eh”? Yana bubbuga bayanta yace “Hadiza u are a very very stubborn woman, when I married u bahaka kikeba, I loved you kaman ba gobe you know, waye baisan kalan soyayyan damukayi ba, but everything changed damuka dawo garin nan, tunda na aureki baki taba cemin kinason kaza na hanaki ba, I change kayan daki anytime kikcemin kinason a chanza, I change cars for you, banwani damu da zuwa vacation ba but kinaso ke we go on vacation every year banda Umara da every now and then nake kaiki, have I ever wronged you kona hanaki abinda kikeso? Farko farko ai kinamin girki rana daya kawai kika ijiye, bakimin komi, baki damu dani ba nor my children wanda kinsan banda abinda nakeso aduniya kaman su, I can’t talk to you kafin nayi miki magana daya kinyi magana dari, kinamin ihu aka kaman yaron dakika haifa, bakiganin girmana ko darajata, Kona Hajiya, all I ask is for your attention and care, respect sannan kisa ido akan yarana but kin nuna ban isaba ban isa incemiki yi kazaba agaban idona zakice no, Bana iya tankwaraki ko kadan, u feel nidake daya ne, abu kadan kice feminism bazaki bari nayi demeaning naki ko belittling naki ba, you’ve been maltreating me doing as u wish, Hadiza ni ba yaro bane am 49 clocking 50 Allah yahoremini arziki da abinyi all I want yanzu is peace of mind and watch my kids grow na barmusu this company suyi taking over but kinki cooperating, u pushed me so hard and kinfi kowa sanina banda son mata banda biye biye, I’ve always been a one woman’s man but u made me look outside Alhamdulillah bantaba zina arayuwana ba and bazantabayi ba that’s the reason nakara aure don na sami kwanciyan hankali” cikin kuka sosai tana wani kalan sauke ijiyan zuciya tace “to saika auri yar aikina” Yana tapping bayanta har lokacin yace “Ummi ce the only macen dake rayuwana banda ke, kema kinsan ko kallo mata basu isheni ba, halinki made me notice the girl, yarinyar is a very good girl, she’s young, smart hardworking, she can cook and above all yarana na sonta sosai sais…….” jin zafin yanda Nura ke yabon Ummi yasa cikin kuka Hadiza tace “banson ji, toka saketa dagayau kome kace nayi zanyi please ka saketa na yarda ta kwana agidan nan yau gobe da sassafe tabar mana gidanmu I promise zan chanza kome kakeso zan maka amman kasaketa please Nuri karufamini asiri, I can cook nima, gani hardworking, smart, intelligent kuma I’m educated unlike yar aikin, kasaketa wlh zan chanza namaka alkawari” ahankali Nura yajaye jikinshi dagana Hadiza yakalleta batare dayace komiba, fashewa da kuka sosai tayi takai yatsanta ta taba harshenta tace “na rantse da Allah Wallahi Wallahi Nuri kaji na rantse ko kasaketa zan dawo sak Hadiza na nada, nadinga maka komi, bazan kara bata maka raiba, please karufamin asiri kada kasa duniya tamin dariya akaji ka auri yar aikina, please kasake ta kaji Nuri” dan lumshe idanu Nura yayi yabudesu yakalli Hadiza dake kallonshi tace “kaji Nuri kasaketa” girgiza mata kai yayi ahankali yace “bazan iya sakin Ummi ba Hadiza!” Dum! Gaban Hadiza yabuga dasauri harsaida takai duka hannayenta saman kirjinta wani sanyi na ratsata tace “mesa Nuri bayan nagaya maka zanyi komi infact nama gama daukan yar aiki har abada, dakaina zan dinga komi and take care of su Amal maisa bazaka saketa ba? U don’t need anything from her again, nice dama kuma nace zan chanza dagayau, maisa bazaka saketa ba”? Yana kallonta right in the eye yace “sabida nariga nakamu da sonta kaman yanda nake sonki!”
Tunda Allah ya hallito Hadiza bata tabajin wannan kalan pain din datakeji azuciyanta yanzu ba jin mijinta nagaya mata da bakinshi cewa yakamu da son wata kuma yana gayamata right before her eyes wai bazai iya rabuwa da itaba sabida yana sonta kaman yanda itama yake sonta wato harya soma raba musu komi equally irin ita da yar aikinta duka abu dayane yanzu azuciyanshi, kawai saitaji kaman zuciyanta ya buga kawai tai baya luuu bawai ta suma bane tanaji sarai yanda yake kiranta da yanda yariketa yana shafa ruwa a fuskanta kawai her energy is just on a zero level idanma akwai minus zero energy level nata na wajen, kaman ya lura da hakan hakan yasa Nura yadauketa ahankali yadaura kan gado ya kwanta gefenta tareda kashe wuta ahankali ya rungumeta cikeda lallashi yace “I still very much love you Hadiza don’t hurt yourself okay, you are my first love Hadiza, Maman yarana, yaran dasuka zame mini haske arayuwana, u gave me the most beautiful, adorable and sweet kids aduniyan nan no one yataba bani kalan gift din dakika bani Hadiza how can I even hate you eh my Didi”? Bakaramin tausayi tabashi ba, wlh yayi auren nan but ko kadan baimayi tunanin kalan wannan reaction din zatayi ba he was just expecting haukanta as usual baitaba sanin she will be this down ba and weak tana kuka haka having panic attack hakaba, so dama tana sonshi, batason taganshi da kowace mace but shine takemai all abubuwan datake, lallai kishi babban abune awajen mata.
Gently yadaura bakinshi kan nata hannunshi yana share hawayen dake fitowa daga idanunta yana kissing nata kafin ahankali yafara yunkurin making love da ita cikeda rashin karfi dakuma kuka cikin muryan bakin ciki tai ihuu tace “kada kasake ka sadu dani Nuri gabanka daya shiga jikin yar aikina bazai kara shiga jikina ba wlh kajini” hada bakinshi yayi da ita bai kara bari tayi magana ba dudda batada karfi saida tai kokawa dashi dan bataso yamata wani abuba but still saida yayi sexing nata da karfi da yaji she have no option but to succumb jikinta ya mutu gabaki daya kawai sai kuka takemai, dole ma Hadiza taso mijinta tayi kishinshi, Nura nada kirki ne sosai lallashinta yake bana wasaba yadinga shafa kanta duk uban bakin cikin datake ciki saida soyayyanshi yayi suppressing nashi bacci yayi awon gaba da ita sai ijiyan zuciya taje saukewa ajikinshi he cant lie is just soothing sex ne kawai wannan to calm her down dan sex na rage bakin ciki da damuwa, that fun da excitement dinnan ajikin Ummi kadai yakeji, lullubeta yayi da bargo yatashi bayinta yawuce yaje yayi wanka yafito kayanshi yasake maidawa yayi wajen kofa ahankali yabude yafita yaranshi yafara dubawa yayi mamaki ganin duk Ummi tamusu wanka sunsa kayan bacci tarufesu da bargo tarage musu AC addu’a yamusu yafito dakinshi wanda yake dakin Ummi yanzu yawuce ahankali yabude kofan tana kwance akan gado tai lamo dudda ba bacci takeba dan takasa bacci tun bude kofanshi taji, zama yayi ahankali bakin gadon yakalli fuskan Ummi feeling a bit bad cus baimata saida safe ba hannunshi yakai ya shafa kumatunta tareda dukowa ya manna mata kiss akai yace “good night Hajiya Ummi” sannan yamike yaje gaban wardrobe ya debi some clothes nashi yawuce yafito tareda rufe mata kofa yakoma dakin Hadiza hawaye Ummi taji sun gangaro mata daga ido kawai jitayi tana bama kanta tausayi most maganganun Hadiza tajisu dan maganan Hadiza ihu ne, maganganunshi ne batajiba but duk taji abinda Hadiza tafadi da cewa yasaketa datayi zata chanza shiyafi komi tada mata hankali saitaji takara raina kanta tana tunanin kodai Auren nan kuskurene, ita Allah yasani ba kwacema Hadiza miji tayiba babu wani mugunta aranta but tasan harga Allah dan bazata iyama Allah karyaba tanason Nura tana mutuwan sonshi, batajin zata iya rayuwa ba yasaketa ina! Tanason mijinta fa kome zatayi zatayi dan yazauna da ita karya rabu da ita, tuna yanda har kaman ya sadu ma da Hadizan dan taji Hadiza nacewa kada ka sake yasadu da ita da gabanka daka sadu da yar aikina, hawaye ne yazubo mata tasan ita yar kauyene bata waye kaman Hadiza ba sannan batai karatu ba but tanada hankali, sannan ta girma, ashirin da uku tana neman da hudu ba wasa bane, tasan menene miji sannan tasan banbancin miji mara kirki damai kirki, dan ta taba Auren mara kirki mugu yanzu yanda Allah yabata miji mai kirkin nan, wlh zatai kome dazatayi ta siye zuciyanshi takuma kara siye danginshi ta samanma kanta lafiyayyan wuri axuciyanshi, koda basuyi wani soyayya kafin aure ba yau alkawari takeyi zata samama kanta waje, bazata tabama Hadiza mugun abuba kawai dai bazata bari wani mahaluki aduniyan nan kap yarabata da Alhajinta bane, dan bata tabajin tanason abu kaman yanda takejin son Alhaji ba, yanda Allah yabata miji nagarin nan dare daya batare datai wani abuba bazata taba bari ya subuce mata ba tashigo rayuwan Alhaji tashigo kenan har abada Wallahi kuwa!.
Tai maganan tana goge idanunta tasake juyi agado takasa bacci, sati biyun nan datayi tana kwana ajikinshi saitaji yau baccin ya gagareta, tashi tayi tafada bayi tafito daure da alwala tahau kan dadduma tayi salla tafara addu’a kan soyayyan ta da aurenta da Nura.
Auuuucchhh I’m too emotional naso nacigaba but let’s take a moment of silence for our lioness Hadiza da Nura yay shattering ego nata today😎
Poor thing couldn’t hold back those tears 😭 ashe ta iya kuka😂
Auuu now I feel bad for HADIZA wlh, kishiya fa batada dadi but kuna ganin misali da Nura zai saki Ummi zata chanza????
Wai HADIZA ce ke kuka haka our strong fire for fire, feminist woman😂😂
Ummi dai tace taga miji, kuma tasamu gidan miji, zama daram injita mutuwa kadaice zata fitar da ita daga gidan mijinta Nura😂
Allah karabamu da kishiyoyi irin Ummi mayun maza😂😂😂
Anyway my people don’t forget to join MATAN AURE CLASS dina with just 1k today and tomorrow 💃
💫 MATAN?? Ko MAZAN??💫
✍🏻M SHAKUR
EPISODE 1️⃣3️⃣
My people wai kunji labarin BUKKISH FABRICS N MORE??
Ku saurara kunji bantaba ganin masu harkan Atampas, laces dakuma lafiyayyun gangariyan ready to wear kaya ba dake badawa akan sari kwashakwasha kaman BUKKISH FABRICS N MORE ba, both
wholesales n retails sunayi, sunefa akama taken PAY LESS STAY IN FASHION, wato ki biya kudi kadan amman ki saka kayan yayi adama dake, ku tura musu message now ku kwashi kaya with little kudi, danna link din nan kimusu magana👇🏼
wa.me/+2349034368170
Zaku iya duba shagonsu a TikTok- Bukkish fabrics n more
13
Wuraren 5 Nura yatashi daga bacci, Hadiza dake gefenshi yakalla har lokacin bacci take, sauka daga kangadon yayi yawuce bayi, wanka yafito ya shirya cikin wani jallabiya yana zuba kamshi yazo gaban gadon yadago Hadiza like a baby softly yace “jekiyi wanka kizo kiyi salla My Didi” bude idanunta tarr Hadiza tayi takalleshi yamata wani irin kyau yau saita ganshi yafi koda yaushe kyau dasauri takai hannunta tadaura kan fuskanshi tana kallonshi everything is coming back to her daya faru da ita jiya, cikin murya mai raunin gaske tace “Nuri mafarki nayi ko? Ai baka auri Ummi yar aiki na ba ko”? Dan murmushi kadan Nura yayi yakai hannunshi yacire hannunta dagakan fuskanshi yace “tashi kije kiyi wanka kiyi salla Hadiza” yana maganan yawuce yabude kofa yafito dakin Ummi yabude yashiga bata kan gadon harta gyara gadon, yabi dakin da kallo komi a gyare tsaf jin karan ruwa abayi yasa yaje gaban bayin ya tsaya tareda knocking cikin cool voice yace “wankan me kikeyi? Mafarkina kikayi?” Ummi nacikin bayin akunyace tace “wanka kawai nakeyi, ina kwana Mijina dafatan kayi bacci mai dadi kuma katashi lafiya?” Dan ijiyan zuciya Nura yasauke ahankali, he loves how Ummi always greet him, gaisuwa takemai not common gaisuwa but gaisuwa mai dauke da details, baki yabude zaiyi magana saikuma yace “ba’a magana abayi, maza kifito kiyi salla natafi masallaci” “uhm Uhm” tafadi amatsayin amsa hakan yasa yayi murmushi yace “naughty gurl” wucewa yayi yasauka kasa, yau monday he wants to see Hadiza ta chanza, he wants to be miji mai adalci, he just pray and hopes Hadiza will cooperate which he’s highly doubting it, dan yau girkin ta yakamata ita zatai girkin breakfast dasauransu, ijiyan zuciya kawai yasauke yatafi masallaci he’s just hoping zai dawo yaga tayi dama ga gidan na bukatan gyara.
Bayan Ummi tayi salla wani lafiyayen super tadauko tasaka cikin atampopin daya dinka mata dogon rigane fitted tazauna gaban madubi ta shafa hoda tasa kwalli tashafa wani pink janbaki sannan tayi dauri bayan tasaka dan kunne, shiru tayi tanason tafita taje ta daurama yaran nan girki zasuje school but tana shakkan Hadiza deep down kuma tasan idan tabari babu mai musu at the same time tana tsoron kada ace tayi shishigi bayan yau girkin Hadiza ne amman kuma tanaso tanunama Hadiza bawai dantaci mutuncin ta ta auri Nura ba ita kawai tanason Nura ne, kusan 3min tayi ahaka sanan tabude kofa kaman munafuka tafito ta maida kofan tarufe batare data bari yayi karaba tawuce tasauka kasa falo tafara gyarawa agurguje da dinning ta tattara duka kwanukan cokalan tawuce dasu kitchen tashiga hada abincin gida tanama Hajiya girki tana gyara kitchen din duka at the same time.
6 Nura yashigo gidan yau bai wani zauna a masallaci ba dan baiso Hajiya tafito daga daki ta nemi Ummi da bala’i, falon daya gani harya chanza kama yasa yayi shiru dan kawai ranshi yagayamai Ummi ne barin dayaji motsi a kitchen kitchen din yawuce a kofan ya tsaya yana kallonta tuwo take tukawa, ahankali yashiga cikin kitchen din dasauri Ummi tajuyo jin motsi ganin Nura ne yasa tayi murmushi tace “Sabahal khayri Baban Amanu” takowa yayi yazo inda take sai kawai ya rungumeta ta baya yana shakan kamshin datake yayi shiru itama saitai shiru tanajin saukan ijiyan zuciyanshi, bai damu dadan zufan datakeba ya goga gefen fuskanshi anata kaman mai whispering yace “maisa kika shiga kitchen yau ba girkin ki bane”? Dan shiru tayi kaman bazata ce komiba cikeda hikima tace “Anty tana zuwa aiki ni bana aiki, shine nace bari nafito nakama mata ta hanyar yin abincin kari saikuma inaso nama Hajiya girki dazataci kafin ta tafi asibiti, tunda nadawo nizan dinga mata abinci, ita nakema tuwon alkaman nan” shiru Nura yayi yana rungume da ita abayanta, akwai wani kalan hikima da Ummi kedashi da wlh ko educated mata dasaukai karatu daidaikune kedashi, yarinyar is good with words, Ummi is smart, tanada broad hikima kan zaman aure wanda yasan aikin Gwaggon tane, yanda ta tashi da safen nan tanama mahaifiyarshi girki abin warm his heart, dago kanshi yayi ya manna mata peck akumatu yace “godiya nake Hajiya Ummi” dasauri tace “nika dainamin godiya dan nama Mamana abinci” murmushi yasakeyi saikuma kawai yasaketa tareda juyoda ita yayi hugging nata so tight yace “thank you Hajiya Ummimy na” akunyace tazare jikinta daga nashi tace “tuwo zai kone” murmushi yamata sabida baiso tai wani abun yace “bari naje natada yaranki namusu wanka na shiryasu” dasauri Ummi tace “kabarshi zan musu zansa sanwan miyane nazo sama” girgizamata kai yayi yace “aikin zai miki yawa just do the cooking zan musu wankan” yawuce kofa saikuma yajuyo yace “kimini shayi” gyadamai kai tayi tace “angama maigidana” murmushi yayi yabita da kallo kaman yazo yamata wani abu saikuma dai yadaure yafita dan murmushi Ummi tayi dudda tanada damuwa tana cikin shakku da fargaban karya saketa bazata taba nunamai ba tama kanta alkawarkn nan.
Nura na zuwa sama baimaje dakin Hadiza ba dakin yaran yaje direct Aman yafara tarawa yakaishi bayi yasamai brush sannan yafito yaje dakin Amal yadauketa yakaita bayi yamata brush da wanka yafito da ita da towel yakoma dakin Aman yamai wanka shima wlh aikin yara is not easy yafito dashi da towel ya kwashi kayanshi sukazo dakin Amal anan yashiga shiryasu sunamai hira yana wasa dasu.
My people wai kunji labarin BUKKISH FABRICS N MORE??
Ku saurara kunji bantaba ganin masu harkan Atampas, laces dakuma lafiyayyun gangariyan ready to wear kaya ba dake badawa akan sari kwashakwasha kaman BUKKISH FABRICS N MORE ba, both
wholesales n retails sunayi, sunefa akama taken PAY LESS STAY IN FASHION, wato ki biya kudi kadan amman ki saka kayan yayi adama dake, ku tura musu message now ku kwashi kaya with little kudi, danna link din nan kimusu magana👇🏼
wa.me/+2349034368170
Zaku iya duba shagonsu a TikTok- Bukkish fabrics n more
Nan da nan Ummi tagama abincin Hajiya tahada breakfast tasoya chips ta sossoya eggs da sausage ta hadama su Amal abinci a lunch bag tadauko tafito zata ijiye a dinning tahada ido da Hadiza dake tsaye a dinning din tana sanye da riga da wani palazzo trouser mai shegen kyau na material pink tayi folding hannunta a kirji tana kallon Ummi da jajayen idanunta dasuka kumbura sukai jazur kaman mai ciwon ido abinku da faran fata, chak Ummi ta tsaya anan gaban kitchen din takasa karasowa dinning din ayanda zuciya ke diban Hadiza jitake kaman tazo ta shake Ummi tamutu gabaki daya, daga kafanta tayi tafara tafiya ahankali akuma zuciye tace “how dare you Ummi kika aure mini miji? Ni Hadiza kika aurama miji? Kin manta lokacin dana taimaka miki kina neman aiki ido rufe wayanda kikema aiki ada sunyi japa sun koma Canada anata gantali dake a Abuja ana nema miki gidan aiki baki samuba, na taimaki rayuwanki nabaki aiki nakuma biyaki da kyau, yan aiki da ake biya duba ashirin, dubu shabiya but ni nace zani dinga biyan ki dubu hamsin sabida duka gidana zaki kula dashi da yarana sabida bani zama ina fita aiki, sakkayan dazaki mini kenan ki aure mini miji, mijina Ummi? Nura na?” Ihu Hadiza tayi tana tafiya tace “ki daga fuska ki kalli kwayar idanuna bakar munafuka, algunguma, makira bakar mayya, butulu, shedaniya watsassiya, sai bayan kin aureshi zakizo ki kasa kallona kina sunnar da kanki kasa kaman baiwar Allah, dagakai ki kalleni Ummi, nace ki kalleni!” Hadiza tai maganan tana ihu daidai tana kaiwa gaban Ummi ta finciko gaban riganta gamgam tawani kalan jijjiga Ummi ta mugun makureta tana kallon fuskanta tace “wulakantacciyan yarinyar irinki harta isa ta aure mini miji, ni Ummi kina yar aiki na, sabida ina fita na barmiki gida kikai using opportunity nan kika auri miji na eh”? Hadiza tai maganan tana buga Ummi abango saida Ummi tasaki lunchbag din kasa tai
25, August 2025
Saadatu Ali
Yes