Showing 90001 words to 93000 words out of 202729 words
haka ko glass cup yayi ihu yace “ubanwa yace ki kawo mini wata kawarki gidana I don’t care if she’s squatting here sabida mijinta yasaketa, are you deaf? Are you stupid, gidan ki ne? Is this house yours? Who do you think you are Zeenatu dazaki dinga shigo da mutane ba tareda kin sanar da ni ba? Oya go and call her ta tattara yinata yinata tabarmin gidana inba hakaba wlh kema koranki zanyi yanzun nan” zaro idanu Hadiza tayi saikuma ta dafa kirjinta Zeenah ne da mijinta ke fada haka akanta ake magana ko wata kawan daban? Tashi tayi ahankali tabude kofan dakinta tafito tayi tafiya tadan leka downstairs ta yanda basa ganinta Zeenah tagani tayi kneeling awajen dinning da duk an faffasa plates tahada hannunta biyu harda kuka tana rokon wani attajirin mutum dabai wani tsufa ba kaman Nurin ta yake, murya kasa kasa tana cewa “dan Allah karufamin asiri kada ka tozar ta ni kabarta ta kwana gobe zata tafi i promise” kana ganinshi kaga masifaffe har zufa ke keto mai a hanci da goshi, ga takalman ta dataga an wawwatsar a falo mutuwan tsaye Hadiza tayi dataga yadauki cup yakara bugawa a katsa ita kanta Hadizan saida ta firgita kaman glass zaizo nan sama inda take ya shiga jikinta cikin fushi yace “stop begging me useless woman who are you dazaki dingayi yanda kikaga dama agidana, jeki kira kawar naki kubar gidana dagake har ita” hannu Hadiza tasa ta taushe bakinta mamaki sai kawai ta juya fuuu cikeda zuciya dan tafi karfin wulakanci akan wannan kurkukun gidan tawuce dakin datake tadauki handbag nata kawai tashiga saukowa jin tafiya yasa dukansu suka juyo dasauri Zeenah ta mike tana goge fuskanta ta kakalo murmushi cike da duniyanci tace “Hadiza zoki gaisa da Baby hala karan plate ya tadaki daga bacci ko dan dazu na leko naga kinyi bacci, wlh bari mukayi yanzun nan” wani kallo Hadiza kema Zeenah yanda tayi just now kaman hawainiya sai kawai ta tsinke da lamarinta batace komiba tace “ina key motata”? Center table Zeenah ta nuna mata Hadiza na tsallake tsallake kwallaben dakenan har falon tawuce tadauki key motanta ta kwashi takalmanta tai wajen kofa cikeda zuciya Mijin Zeenah ya nuna Hadiza da hannu yace “jibi mara kunyan da kike cewa ta kwana agidana taganni bata iya gaidani ba” azuciye Hadiza ta juyo tace “anki agaidakan mata mutuncin mahaukac…….” “Hadizaaaaaaa!!!!!!” Zeenah tama Hadiza wani kalan ihu kaman zata tsaga gidan tace “karki kuskura ki zagin mijina wallahi cus zakiga other side of me” baki Hadiza tabude completely flabbergasted tana kallon Zeenah, saikuma chan ta nuna kanta tace “Zeenah you, me!” For the first time in history the chatterbox Hadiza was speechless tama kasa constructing sentence tsabagen shock tana kallon camellion Zeenah, Zeenah tace “yes zaki shigo har gidana ki zagi mijina are you okay an gayamiki irin ex mijinki ne shi Nura”? Shiru Hadiza tayi tana kallon Zeenah, zata sake maganan mijin Zeenah yace “kneel down ki gayamin wace jakace wannan mara tarbiya kika kawomin gida, and you leave my house kafin nakira bodyguards dina a kulleki” ya nuna Hadiza da yatsa cike da wulakanci kaman kashi yakema magana, Hadiza ga mamakinta kneeling taga Zeenah tayi agabanshi kaman baiwa sai kawai tajuya da gudu sosai fa tawuce motanta da dazu Zeenah tayi parking achan bayan gida sai yanzu tagane mesa tai parking awajen ashe batason mijin yasan takawo wata gida ne tashiga motan da sauri ta tuki tafito around 12:15Am nadare kawai tahau kuka cus from just little abinda tagani dudda mijin Zeenah is a minister tafi Zeenah enjoying rayuwa in every aspect starting from gidama, maybe halan ya ijiye Zeenah a wannan gidan sabida itane Amarya kuma batada yara but still she expect gidan minister yafi gidan mijinta that is into real estate girma da komi amman gidan ta yafi gidan nan da girma da komu har interiors na gidan ta yafi na Zeenah kyau, not to talk of babban gidan da Nura ke gina mata da ba’a gamaba lokacin daya kaita gidan ita kanta saida tai ihu wani kalan design na gini yake da bata taba ganin kalanshi a abujan nan ba, look at yanda Zeenah ke living in fear tun a kotu data cemata zata kwana agidan ta ta lura da wani abu, look at yanda take baiwa in her own house kneeling agaban miji yana fashe fasten utensils agabanki what if tasami injury, sannan bataga yar aiki ko guda daya ba halama batada yan aiki, jibi yanda mijin keta ihu akan me zata kawo wata gidanshi batare data fadamai ba ita look at yanda take kawo kowa gidanta ba ruwan Nura itanema Nura bai isa yakawo kowa bai fadamata ba, Zeenah has been lying to them all this while tana zuga ita da Baraka suci uban mijinsu yanda takeyi so dama karya take, imagine Zeenah data gama zugata dazu harda cemata she’s a disgrace to all feminist out there, look at Zeenah miji ke bossing around yana sata kneeling kaman student, Zeenah dake gayamata taji kunya tana kuka kan namiji look at Zeenah da life datakeyi! Ya Allah! Daidai Hadiza na parking acikin Hilton hotel tadade a mota tai kuka harta godema Allah gash Anty Jams sun kirata bata dauka ba, bawai tana nadaman abinda tayi bane for slapping her da Nura yayi he deserves to be thought a lesson but she’s just hurt yanda Zeenah made her look so stupid and a fool bayan tafita more gidan miji in every aspect dudda tana auren minister, but Zeenah made her look kaman itace the unluckiest wife in history, koda yaushe ji take she wants to be rulling her house kaman yanda Zeenah ke gaya musu tanayi, and abinda ke faruwa is bata cika zuwa gidansu ba cus kullum tana shago kawancen su is suzo shagonta ayi hira a fita, sudanje occasion ko outing that is it, Hadiza batada yawon zuwa gidan kawaye business nata baya barinta saisa batasan actual condition na gidan Zeenah ba, mesa Zeenah zata zugata bayan itane ke facing abuse ma agidanta not she dan Nura bai taba fasa plates a inda take ba, Zeenah lied to her and betray her, tazugata and made her look so stupid, fool, and immature.
Hadiza taci kuka ta koshi sannan tafito taje tai booking daki jin kanta na sarawa ta tsani karya da yaudara dan ita kozata mutu bata karya, bata yaudara, bata pretending to be who she’s not, she’s just herself aduk inda zataje a duniya be it to mijinta, relatives nata ko friends natama, ganin kanta zai tsage yasa taje ta kwanta.
BECAREFUL WITH FRIENDS MATAN AURE!!!!
SOME FRIENDS ARE EVIL!! SNITCH!! ENVIOUS!! WISE!! AND CROOKS!!!
Zeenah is just one!!! Now ku fadamin mesa Zeenah tama Hadiza what she did to her??? Please kubani amsan nan!
MATAN AURE KUDENA FADAMA KAWAYEN KU MATSALOLIN KU wani zubin daka fadama friends your issues gwara stranger na rantse, bawai ina cewa all friends are bad bane no! But some friends basason suga progress arayuwanki ko cigaba.
Dan Allah kubarni nayi this book yanda na tsara nace zan muku magana akan major abubuwan dake kashe aure ayau which the most common one is FEMINISM wanda shine nake nuna muku abubuwan dayake causing arayuwan mu na yau, look at inda Feminism yayi landing Hadiza, this book is not for enjoyment or catching fun novel nope! Idan irin wannan kukeso I have them very tantalizing ma ga dadi check my wattpad page Mshakurworld. This novel is an educating novel dayake nuna illolin of some actions na both side, look at how nake rubuta this book any action na mutum ina nuna how that person thinks and see things, still ina nuna muku idan kina kaza it can leads to this and this and this, this novel is about auren mutum biyu Nura and Hadiza, life nasu, origin na problem din, kaza kaza kaza, I break everything down for you, and I can tell you for free Nura is the origin na this issues for not teaching Hadiza and guiding her as her leader, ya saki Hadiza dayawa, yabata freedom da yawa, saisa hakuri ma da shiru shiru idan yayi yawa is a disease, lokacin dazakace okay bari nafara gyara karfen yariga yanuna harma ya nika, please masu cewa am bias am this and that look at this book from different perspectives and you will see abinda nake kokarin yi.
This is a wake up call to all of us mata cewa mu gyara, and this is a wake up call to maza na idan matanku nayi ba daidai ba correct them dan ba soyayya bane dan kayi letting go of mistake na mata infact cutar da ita ma kakeyi indirectly.
Anata cewa shi mutum baya chanza wa menene menene, kowa aduniya na da tendency chanza wa either from good to bad or from bad to good, wasu they just have to experience life outside the box kafin suyi tunani, look at Hadiza yanzu just few minutes datayi agidan Zeenah she saw rayuwan wasu couples and tafara tunani this that and this, Hadiza will change guys I know abinda nakeyi but mubarta tayi rayuwan da babu Nura aciki muga how things goes and I sincerely hope you will understand cewa littafin nan nayi shi ne for the betterment of our society in general both daga bangaren mata da bangaren maza Thank you.
Allah yamana albarka gabaki daya, yau nabude layina you can either call me or drop a message kota whatsapp kota text 07012181461.
Zaku shiga shiga group na matan aure na with just 2k. Chat me up idan kinaso.
THANK YOU ❤️
💫MATAN?? Ko MAZAN??💫
✍🏻M SHAKUR
EPISODE 2️⃣7️⃣
KUJE AGUJE🏃🏾♀️🏃🏾♀️ KU KOYI HARKAN KITCHEN🏃🏻♂️🏃🏻♂️
Great news for the people outside jos who are eagerly want to become pastry chefs and bakers.
BAKE N’ FROST
is bringing you it’s first online class and the class will come with alot of benefits. 🥰🥰🥰
Make sure you join us today. 🤩
Believe me, you won’t regret it because we will be teaching you everything from scratch 💃🏽
Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/Hs8bU0RnXpLA5Lvr1o4qDe
Hadiza tajuya nan tajuya chan takasa bacci hakan yasa ta mike tawuce bayi ta tsaya gaban mirror ta wanke fuskanta tana kallon kanta idanunta sunyi jazur, takasa wrapping head nata around abinda Zeenah ta mata, wani kalan daura hannayen ta biyu tayi akan bakinta tafashe da kuka da kyar ta lallashi kanta tafito tadawo daki, wayanta tadauka takira Barakah amman harya katse bata dauka ba hakura tayi ta ijiye wayan ta lumshe idanunta, da ace Zeenah bata ambato zancen court ba da batasa Nuri a kotu ba wlh dudda tasan saitayi bura’uba dashi dan bai isa ya mareta bane ta hakura ba but bazata taba tunanin kotu ba. Zama tayi ta gaban gado tayi shiruu tanaji kaman an daura mata dutse akirji saikuma ta mike tsaye taje gaban wardobe tabude she’s feeling so angry da kanta, duk wacce tace zata iya maka bayanın the feeling after been divorce daga mijinka is just lying dan the feeling is just unexplainable, she’s having different emotions, She’s angry da abu biyu yanda Nura yasaketa yakuma mata iyaka da gidanshi and his life gabaki daya, yanzu fa idan tashiga rayuwanshi yanada hujjan yimata kome yaga dama dakuma abinda Zeenah tamata, takasa gathering courage na kiran gidansu dudda taga kiran Anty Jams takasa dauka takasa kiranta she don’t even know what she’s doing, all abinda tasani is zataci durun uban da uwar Zeenah gobe before she even think of anything dan idan bataci uban Zeena ba bazata sami kwanciyan hankali ba.
Komawa gado tayi ta kwanta tasake daga wayanta batasan metake ba but kawai samin kanta tayi da shiga gallery taciro hoton Nura yana sanye da suit da cake agabanshi ranan dayay lunching real esatate company nashi na a Abuja tamai hoton yana murmushi sosai yayi kyau da fararen hakoranshi, Nura is very very handsome, dudda shekaru sun ja but few furfura gareshi kodan yanada kudi ne kuma yana kula da kanshi ga yawan shan fruits but he’s super cute, kuma he’s still very fit bai ijiye wannan pot belly ba. Kuka Hadiza takejinyi tana kallon hoton but tahana kanta yi takasa yardanma kanta tayi kuka sabida wani yasaketa da sauri cikin karfin hali tana kallon hoton nashi cikin wani kalan murya da kasan she’s so hurt tace “ni zaka saka Nuri har kanace amaka shamaki dani who do you think you are? Kana tunanin zanyi kuka ne or I will be hurt sabida kamın haka to nima I don’t want you” tana maganan kuka yazo mata wuya tarike kukan gam tasa yatsanta ta nunashi tace “yesss I said nima I don’t want you, nima amin shamaki dakai, I don’t wanna ever see you” tai maza tai shiru jin kuka na neman kufcemata chan tace “I don’t even know why nake wani tunaka what’s so special about you Nura akwai thousands of men that are way cooler than you’re, sun fika kyau, sun fika kudi sun fika komi so why am I sad? With or without you Nura I will always be Hadiza Mangal Haruna! Babana yabani sunan nan and I will always be that, I have my money, I can give kaina anything danakeso and sponsor any trip danakeso naje so barina dakayi baida any effect akaina kuma kadade baka sakeni ba kaine kai rashi, i promise you bazaka taba samin mata as Preety as I am ba, as loving as I am ba, kuma bazaka taba samin wacce zata baka yara kyawawa kaman wanda na haifamaka ba and lastly Nura saikayi nadaman sakk…….” Kuka ne ya kufcemata da sauri ta ijiye wayan ta daura duka hannayen ta kan fuskanta tace “why am I crying now I hate you Nura I hate you, mugu azzalumi narasa meyake ma mace dayake sa so much effects on her, get out of my heart Nura, get the f*ck outtt already” tafashe da kuka sosai ita kanta batasan why takema Nura wani cool so, he’s just so adorable ne, gentle and cool guys has always been her spec, she loves Nura cus he’s so gently da ita, despite abubuwan dazatamai he will always treat her with so much love and affection kaman batamai komi ba Nura ko is just something else ne kawai a maza, bata taba ganin forgiving man like him ba, baida bakin ciki sannan zai iya sadaukar da rayuwanshi just to see you happy, dudda tanamai iskancin datakemai bata taba fatan ya chanza ba saisa bazatai karya ba daya saketa yau ta girgiza! Bata taba sanin zancen kotun nan zaisa ya saketa ba, abinda yafi jinjigata shamakin daya musu, wato yakai karshe yanzu he’s done with her ohhh no no her heart arching in agony wlh batasan sanda bacci yayi awon gaba da itaba.
Wuraren 7 ta farka tashi tayi ahankali tawuce bayi wanka tayi tayo alwala tazo ta maida kayanta tai salla sannan tai order abinci shima tsakura kawai tayi tasake dannama Baraka kira wajajen 8, Baraka na dauka Hadiza tashiga koramata abinda yafaru Baraka tace “mu hadu a shagon ki zan kira Zeenah sai a maida maganan” sukai sallama tashi Hadiza tayi ta shirya wajajen 8:30 tabar hotel room din tana kallon Anty Jams da Mama duk sun kirata taki dauka but taki dauka still hada handbag nata tayi tafito tai checking out ta tafi wajen motarta tabar hotel din zuwa shagonta da har sales girl dinta tabude amsa gaisuwansu tayi ta tsaya ta zabi abaya daya mai shegen kyau tawuce sama office nata dashi tana zuwa ta shirya tsaf ta zauna bata wani dade da zamaba saiga Baraka ta shigo tace “Hadiza” tashi Hadiza tayi cikin fushi tace “ni Zeenah zata yaudara” da sauri Baraka tace “kinga daina ihu Hadiza staff naki na nan” cikin fushi tace “bura’uban staff” fuuuu tawuce kofa tafita tasami yammatan guda biyu tace “kutafi gida nabaku off today” cikeda mamaki suka kalleta ganin da gaske take yasa suka tafi bayan sun mata godiya takoma sama, Baraka tace “Hadiza calm down explain it to me Zeenah tana hanya kinga baban yaran nan nafita nafito nima wlh sabida banma gane maganan dakikemin ba ta waya” Hadiza na kallonta tace “Baraka kinsan halina, ke da Zeenah are my only two close friends duk duniya, Baraka kinsan banda gulma arayuwana tunda nake dake nabata kawo miki maganan wata ko wani?” Baraka tace “a’a zan shaideki awannan Hadiza bakida time din nan” Hadiza tace “bana karya, sannan bana munafuntan mutum wlh yanda abu yake araina haka nake juyeta da bakina, bantaba samin wani naje nabada labarin ki ba, Baraka you and Zeenah are the closest associates danake da shi aduniyan nan banda family na akan me Zeenah zata yaudareni ta ha’inceni” daidai ana bude kofan Zeenah na shigowa tai shigan alfarma tace “kaman ya na yaudareki ko na ha’inceki”? Azuciye Hadiza tajuyo tashi Baraka tayi tace “dan Allah dukanku biyun calm down ku tsaya bari naje na kulle shagon kar customers suzo bamu sani ba” Baraka ta fice da sauri Hadiza da Zeenah sukahau kallon kallo Zeenah ko dar babu tattare da ita saima cingum datake tauna wa Baraka ta dawo ciki kai tsaye Zeenah tace “Baraka kinsan ina mugun ganin mutuncin ki saisa nazo wlh wlh dan banga abinda zai fito dani yau ba dan yau ake zuwa mini full body massage har gida, so why did you call me”? Anatse Baraka tace “Zeenah zauna” takama hannunta ta zaunar da ita akan kujera, Hadiza kuma taja kujeran gaban desk nata ta zaunar da ita tace “Hadiza you too sit please” itama ta zauna Zeena ta zauna kan center table more like tana tsakiyansu tace “we three are friends tun secondary school days namu a college munada n fadan mu da hargowa na yarinta but so far so good tunda mukai aure mukai hankali bamu kara tada ba, please what is happening, Zeenah Hadiza takirani this morning akan kin yaudareta kin ha’inceta, kin kuma cuceta meya faru? Talk to me Zeenah” wani kalan karkada kafa Zeenah tayi ta kalli Hadiza tace “Hadiza ni ne na yaudareki na ha’inceki how? Yan
25, August 2025
Saadatu Ali
Yes