Showing 69001 words to 72000 words out of 202729 words
my life partner, Ya Allah nasan tayi kuskure da dama but please give her a second chance please give her a second chance to amend all her mistakes ya Allah ka taimakamin” wayanshi ne yashiga ringing hakan yasa ya tattaba Aljihunshi yaciro ganin Ummi ne yasa arude yadauki wayan yakai kunne cikeda tashin hankali yace “Ummi” cikeda damuwa Ummi tace “Ya jikin Anty naga ayanda kafita saisa nakira naji ko kunkai lpy, su Amal nata kuka meya sami, Mommy su bansan mezan gayamusu ba” arude Nura yace “Ummi kutaya Hadiza addu’a ki gayama su Aman suma Maman su addu’a, Ummi banson Hadiza tamutu, she means a lot to me, Maman yarana, nariga nafaro rayuwana da ita, tayaya zan cigaba da rayuwa babu ita eh Ummi?” Yanda Nura ke magana zakasan bemasan meyake fadiba cikeda so dakuma tausayin mijinta tace “in sha Allah babu abinda zai sami Anty kaji Baban Amali, Allah ubangiji yatada kafadanta, ka koma wajensu kada anemeka, kada kadamu zan kula da kowa na gida kaji Mijina” cikeda so yace “nagode Ummi ki tayani bawa Hajiya kulawa kar jininta yahau” gyadamai kai tayi tace “to Mijina zanyi, ka manta damu anan ka maida hankalinka wajen Anty tafi bukatarka, Allah yabawa Anty Lpy” ta katse wayan, komawa gaban kofan yayi daidai ana bude kofan Dr daya yafito dasauri Nura yace “doc…..” anatse Doctor yace “she’s alive!”.
Wani kalan rungume Dr Nura yayi saikuma yasake shi da sauri yaxube awajen yayi sujjada yatashi sauran likitocin duk suka fito da Nurses sai godiya yake musu head Dr yace “zaka iya shiga ka dubata but kada ka tadata kafin ka sameni a office” dasauri cikeda farin ciki yace “to, to, nagode Dr” dasauri yashiga ciro wayanshi yayi dialing number Ummi dasauri ringing daya tadaga cikeda farin ciki yace “Ummi Hadiza na raye! Tafarfado” dasauri Ummi tace “Alhamdulillah Alhamdulilah!” tahau fadama su Hajiya akan wayan duk sai hamdalasuke, ahankali Nura yana jinsu yace “ina Amal da Aman”? Ita tama dauka ya katse wayan da sauri tace “Amal na kuka gatanan na goyata tayi bacci, shikuma Aman gashinan kan cinyana idanunshi biyu yayi shiru kanason kaga Mommy ka ko”? Tai maganan a tana shafakan Aman, Gyadamata kai Aman yayi ahankali, “bashi wayan” Dasauri Ummi tabama Aman wayan cikin sanyin murya yaron yace “what happen to my Mom Dady?” Murmushi sosai Nura yayi yanzu yakara tabbatar yes Allah ne yabama Hadiza second chance tunda gashi yau Aman ne ke wannan damuwan kan mamanshi yaron da is always angry with her, cikeda so da lallashi yace “Momy was a bit sick but yanzu she’s fine, tana bacci anjima zanzo gida na kwaso ku kuzo ku ganta kaji” gyadamai kai Aman yayi Nura yace “you are the only man in the house, bana nan kaine incharge so promise me you will take care of your Grandma, Aunt, Anty Ummi and little Amali, promise me zaka kula da kowa” ahankali Aman yace “I promise Dad, take care of my Mom” murmushi Nura yayi yace “to zanyi, Daddy loves you and Amali a lot ko kada kadamu anjima zanzo gida ok” “okay Dady” katse wayan Nura yayi yawuce yabude dakin ahankali ya shiga, Hadiza na kwance kan gado da kayan patient an saka mata oxygen mask a hancı har lokacin she’s still connected to some machines zuwa yayi gaban gadon ya zaune tareda kama hannunta da sauri yakai bakinshi yayi kissing yana kallonta yayi shiru, she looks so peaceful tana baccin nan babu wanda zai ganta yace fitinanniyan mata ce, sake kissing hannunta Nura yayi murya chan kasa yace “thanks for pulling through, you scare the hell out of me today Hadiza” yayi shiru yana kallonta saikuma ya rungume hannunta akirjinshi yace “I love you very very much Hadiza despite all your crazy and annoying attitude but still ina sonki that’s why I’ve been putting up with your shit all this years, ni kaina I wonder why nakeson stubborn mata irin ki, but yazanyi the love is just unconditional kada ki karamin abinda kikamin yau okay! Kin tsorata Nurin ki sosai Hadiza” yayi shiru saikuma yasake kai hannunta kan bakinshi ya manna mata kiss yana kallon fuskanta yace “bantaba tsanan kiba for once duk kalan abinda zakimini, infact sometime nakan gayama kaina ma I should be grateful inada matan da will always say what’s on her mind the way it is, babu kwana kwana that’s you Hadiza, you are so real ba kaman sauran mata ba that use to be cunny and sly, nasan halinki tsaf ciki da waje saidai na gayama mutane who u are, you are just stubborn, gaki da anger issue but u are not wicked Hadiza, and u are not evil, u don’t even have that time, baki cikin sahun matan dake bin malamai ko bokaye so sometimes I feel kome zakiyi I can put you with it because bakida mugun nufi azuciyanki kuma baki shirka and idan akwai soyayya kome zakimin zan iya hadiyewa and be the man saisa ake ganin kaman nina bataki” yayi shiru yana kallon fuskanta yace “I just want you happy, I want you to enjoy your self saisa I gave you all that u desire, Hadiza banyi aure dan to hurt you ba infact I did it for you, I did it for my children and for myself, you were not willing to change and I don’t wanna force you, danaga kin aminta da Ummi, keda baki yabon kowa but kika yabama Ummi not once, not twice yasa I looked at the girl to see menene in this girl da matane the whole Hadiza ke yaba” yadanyi shiru ahankali yace “ke kikamin auren nan Hadiza and I was still considerate to marry the girl wacce keda yaranmu kukai approving sabida karna saba miki, I don’t think akwai a man that can love his wife this much kaman ni” yayi shiru yace “I thought bana gabanki cus u don’t value me Hadiza, u don’t look at me with love and affection dakikemin kafin muyi aure, rather koda yaushe kallona kike like your mate, bantaba sanin u will react this way da auren nan ba cus banga soyayyan dakikemin ba is as if yayi disappearing, to my biggest suprise naga auren yasa kin dawo dumu dumu kinasona saisa danaga haka I always give you my attention, and my love cus I don’t wanna hurt you, I took care of you, pamper you, always showing you how much u mean to me that babu abinda ya chanza a soyayyan danake miki eh Hadiza. I want you ki tashi mu rufe wannan chapter na fada kullum, mudawo kaman yanda muke da and forget everything and live as one okay happily ever after” yayi maganan yana tashi ya manna mata kiss a goshi sannan yakara gyaramata bargo yafito yawuce office na doctor.
Zama Nura yayi kan kujeran dake facing Doctor su dake duba file na Hadiza da glasses a idanu, saida yagama yadago yakalli Nura dake kallonshi yace “Alhaji what your wife had today was SCA, watto sudden cardiac arrest!” Sosai Nura ke kallonshi Dr yace “well all I can say miracle kawai yadawo da ita duba da lokacin daya daukeka da ganinta da bata CPR, dakuma kawota nan hospital still ta farfado is just God!” Ahankali Nura yace “Alhamdulillah Ya Allah, Hamdan Kaseeran Dayyiban Mubarakan fii” Dr yadan sauke ijiyan zuciya yace “zanyi managing nata a hospital for 7days dan I need to rule out daga ina wannan matsalan yafara cus this is her hospital bamu santa dawani matsalan zuciya ba nor hawan jini so inaso zan mata some test dazamu duba complete lafiyan zuciyanta tundaga kan arteries da veins da komi na zuciyan, zatayi EKG, MUGA, MRI, Exercise stress echocardiogram test, gashi u need to make payment” yabama Nura takarda ya karba dasauri yana dubawa Dr yace “Alhaji Nura” anatse Nura yace “na’am Dr” Doctor yace “so far so good we don’t know meya jawoma this issue and banso nayi digging into personal life dinku but ina ganin bayan munyi ruling out the heart issue I will refer her to a psychologist cus I think matanka is suicidal!” Dasauri Nura yace “no, no Dr, Hadiza musulma ce nasan we are having one or two issues but nasan bazata taba tunanin kashe kanta ba” Dr yace “yet kasameta abayi akasa ta kunnama kanta ruwa she knows the dangers of that, banda she’s risking jikinta ma cold that could result to pneumonia, she’s also an adult 32yrs da 2kids more of the reason why dole nayi referring nata to psychologist cus I believe batama san metakeyi ba duba da what’s at stake, what life nata means to you, to her kids and to her family” Shiru Nura yayi yakasa magana kana ganin fuskanshi kasan he’s feeling guilty he’s not just happy, ahankali Dr yace “it’s okay you have to be strong anan” gyadamai kai Nura yayi batare daya iya magana ba, Dr yace “I will suggest ka kira all family members nata, duk wani masoyanta should be here for her, koda wasa kada ku kara batamata rai for now, kutaru make her happy and show her how important she is to all of you, like I said bansan mene asalin problem din ba but I strongly believe your wife is depressed and suicidal dan haka you people should show her love” gyadamai kai Nura yayi, Dr yace “Alhaji Nura daga yanzu do kome zakayi kayi dan karta sake having this cardiac arrest dan believe me she might not be lucky the second time!” Gyadamai kai Nura yayi yace “İn sha Allah this is the first and last time” Dr yace “you can go” tashi Nura yayi yafice ahankali yafita waje wani dan dakali yasamu yazauna yayi shiru yana kallon paper expensive scans da test din zuciyan da za’amata sannan yaciro wayanshi yakira Jams ya sanar da ita komi da ake ciki yace “zai samata kudi tama kowa booking flight su taho da Mama da sisters dinta Hadiza needs love that she might be suicidal” katse wayan yayi yatura mata 1M sannan yakira Hajiya ya sanar da Hajiya ma komi, anatse Hajiya tace “Hadiza bazata taba kashe kanta ba Nura kasan likitoci da zancen banza wani zubin” Nura feeling so bad yace “Hajiya duk ni naja komiko”? Tashi Hajiya tayi daga falon ganin Ummi tafito daga kitchen tawuce dakinta ta zauna anatse tace “no Nura bakai bane kaddara ce” muryanshi na rawa yace “Hajiya I push Hadiza so hard da tana kokarin kashe kanta ko Allah yasan ban auri Ummi dan kuntata mata ba Hajiya u know me kinsan danda kika haifa am not a wicked person, inason mata ina kuma tausayinsu sabida matane kannina gabaki daya” cikeda so dakuma lallashi Hajiya tace “don’t beat yourself too hard Nura, mata munada zafin kishi, wasunmu sun iya handling kishi wasu kishin zai iya hallakasu stop blaming yourself Son, aure ba haram bane Alhamdulillah da ranta yanzu abinda zance maka is tundadai case din yakai haka karaba musu gida kaji” shiru yayi hakan yasa Hajiya tace “you have too nasan yanda kakeson yaranka su taso kansu daya but dole ka hakura dan at this point akwai cutarwa tunda Hadizan ba lafiya gwara yanzu ka dauke Ummi daga gidan nan ka kaita wani waje, idan kagama sabon gidan ka maida Hadiza chan saika ijiye Ummi anan kaji” gyadama Hajiya kai yayi yace “to” anatse Hadiza tace “kayı sallan asuba”? Sai a lokacin yaga gari yamadan soma haske ahankali yace “banyiba bari naje nayi” dasauri tace “tohhh” ta katse wayan.
Karfe goma family Hadiza na asibitin dan Max air suka samu na 7:30 shima dan anyi delay, da mahaifiyar Hadiza, da Anty Jams, da kannin Hadiza guda biyu dake binta Rabi da Hafsat dukansu kowa yayi aure duk jugum kowa yayi a asibitin har lokacin Hadiza bata tashiba, Mama dake kallon Nura dake rikeda hannun Hadiza tace “kaje gida kayi wanka ka kimtsa Nura” girgiza mata kai yayi yace “bazan iyaba Mama, bari saita tashi ai Dr yace nan da awa daya alluran zai saketa ta farfado” saikuma da sauri yakalli Anty Jams yace “ga car key na jeki dauko mata su Aman idan ta tashi ta gansu zataji dadi Batai musuba Anty Jams takarba key Rabi da Hafsatu sukace zamu biki bata hanasu ba duk motan Nura suka shiga ta tada Rabi tace “wlh sainaci kutumar uban yar aikin nan dan durun uwatta” wani kallo Anty Jams tamata tana tuki tace “kinsan Allah idan abinda kike shirin yi kenan zan iya kwana naje na saukeki a asibiti” cikin fushi Hafsat tace “Anty Jams waike mesa kike abu kaman Mama, inda mu Hadiza takira da tuni bamu zo mun tayata koran shedaniyan yarinyar ba takama takiraki bayan tasan u will just talk like Mama look at her yau, inda ta mutu shikenan fa mun rasa yar uwanmu Nura yacigaba da rayuwanshi like nothing happen mukuma fa? Munrasata har abada, duk yanda zaki kalli abin Nura yariga yaci amanar Hadiza daya auri yar aikinta, ai da kishiyan gida gwara ta waje, yarinyar da Ya Hadiza tadauka aiki tamata komi I remember lokacin da Ya Hadiza muna waya tana yaban yarinyar wai tanada kirki tanason su Aman saisa take biyan yarinyar 50k ni kaina saida nayi ihu nace yar aikin kike biya 50k abinda akano 5k ko 8k ake biya duk wata, tacemin yarinyar nada kirki ne but shine munafukar ta aure mata miji akanme Ya Hadiza bazata hadiyi zuciya ta nemi mutuwa ba is it easy? anty Jams are you even relating the pain Ya Hadiza is going through everyday agidan nan tana kallon yarinyan” ta share hawayen daya zubomata da sauri tace “Wlh sabida Nuran ma babba ne kuma akwai Mama awajen da bazan gaidashi ba, munafuki kawai mayaudari mugu sai yanzu dayaga takusan zuwa barzahu shine yaşan yana sonta” Rabi tace “bar munafuki ai maza! Maza! Wlh namiji ba dan goyo bane, namiji butulu! Namiji mayaudari! Maza yan duniya! Ba kunya ba tsoron Allah ba kawaici ya auremata yar aiki!!! Wlh kaman naita surfafamai zagi dana ganshi!” Anty jams kasa cemusu komi tayi dan itama bawai she’s happy bane she’s just feeling bad ganin kanwarta in that state saida sukakai gidan tayi parking tajuyo takallesu tace “Hafsat, Rabi’a na rokeku da girman Allah kada kuyi wani abu kungamai mahaifiyar Nura na gidan bawai kuma lafiya gareta ba please” da magana ciki ciki sukace “munji” duk suka sauko suka shiga cikin gidan, Hajiya ce ke zaune a falo ga Meena agefenta dake zuba mata kunu ganinsu yasa tace “a’a su Jamila ne”
Cikeda fara’a duk suka shiga gaigaisawa akayi anawa juna jaje, Anty Jams tace “ina yaran Baban su yace nazo na daukosu daganan zamu dan daukanma Hadiza kaya adaki” dasauri Hajiya tace “suna sama yanzun nan Ummi tahaura dasu dan yimusu wanka kuje kuhadama Hadiza kayan kafin nan tagama shiryasu nima ina ganin zan biku asibitin nan naje na ganota” Anty jams tace “Hajiya kina fama da kanki dakinyi zamanki agida wlh ai Alhamdulillah tunda she’s out of danger” Hajiya tace “ina kafana kafanku kuzo kuyi Kari nasan bakiyi ba” duk sukace Alhamdulillah suka wuce sama Meena tabisu da kallo zata mike Hajiya takama hannunta tace “me haka ina zaki saikace sata zasuyi agidan”? Dasauri murya chan kasa tace “wajen Ummi zani” girgiza mata kai Hajiya tayi tace “hakan zaiyi kaman munada wani manufa zuciya Jamila nada hankali ai yi zamanki anan” badan tasoba ta zauna.
Daidai Ummi tafito daga bayi dauke da Amal a hannunta Aman tariga tamai yana zaune bakin gado da towel yana jiranta tafito ta shafamai mai su Rabi suka bude kofa suka shigo chak Ummi ta tsaya dantama tsorata cikinsu Anty Jams kadai tasani da duk suke kallonta, tsayawa tayi gaban bayin ahankali tace “sannunku da zuwa ina kwana” azuciye Hafsa tataho gaban Ummi tasa hannu ta karbe Amal azuciye ta nuna Ummi da yatsa tace “kina nema ki kashe mahaifiyar su shine kuma kike nan nan da yaranta bakar munafuka” dasauri Rabi tai wajen ta nuna Ummi daga sama zuwa kasa awulakance tace “ke kina gani kin auremata miji ko hmmm je asibiti kiga menene soyayya wlh na tausayi miki dudda bakijin turenci but zan miki u mean nothing to Nura, keba komi bane awajen Nura ba, Hadiza Itace komi nashi, mata ta daukeki tabaki aiki, ta biyaki da kyau, tabaki ci sha sutura but kici amananta ta hanyar aure mata miji abinda kikama Hadiza Allah yasa ama yaranki! Ama kanninki! Ama jikokinki ke duk Wanda kika hada jini dasu Allah yasa amusu!” Dan lumshe idanu Anty Jams tayi tace “Rabi and Hafsat please ku dauki yaran nan kuzo mutafi dakin Hadiza” daukan Aman Rabi tayi suka kwashi kayansu dasuka gani akan gado wanda Ummi tafito dashi suka juya harsukai kofa Rabi tajuyo takalli Ummi da kanta ke kasa tace “kuma wlh idan kina Tuna’nın kin kwace mata miji kinyi kuskure ki rubuta ki ijiye saikin dawo abin tausayi kuma yar kallo agidan nan danko Nura kije asibiti kigani nadaman aurenki yake, mema yakaishi gashi yanzu kin zama sanadin matarshi uwar yaranshi dayakeso na neman ta mutu, duk wani addu’a da bokaye da malamanki gwara ki kirasu dan amiki addu’a Allah sa kar Nura ya koraki, tana maganan suka fice wasu hawaye masu zafi Ummi taji sun zubomata dasauri ta share tafito daga dakin tawuce ta shiga dakinta ta tafi bayi dasauri ta duka tafashe da kuka sosai.
Har suka gama abinda zasuyi sukabar gidan Hajiya har sawa Meena tayi taje takirata dantamata sallama zata bisu asibiti tace ma Meena taba bayan gida.
Ahankali take bude idanu dasuka mata nauyi sosai, dummmm kunnenta yakeyi kaman wacce ake kwalama kira daga mesa haka takeji taji ana. “Momy, Momy, Momy wake up” rawa rawa idanunta keyi dasauri jin muryan Aman and Amali daga nesa chan na gayamata ta tashi kafin tabude idanun nata a juye tana kallon sama ganin mutanen da idanunta basa gane mata su da kyau blurr blurr take gani saichan taji murya daga nesa ance “can you see me” sake runtse idanunta dasauri tayi sannan tabude su Dr tagani akanta saikuma taji an rike mata
25, August 2025
Saadatu Ali
Yes