Showing 96001 words to 99000 words out of 202729 words
tafashe da kuka tace “Aisha Hadiza zata kashemini yaro wannan wani kalan abune me d’a yamata? Aisha cikinku babu wacce kema mijinta yanda Hadiza kema Nura, kunama mazanku girki, kuna girmamasu, why is my son so unlucky da mata eh? Kashemin yaro takeso tayi? Zata haifamin waninshi ne eh? Yarona sai kuka yake all because of her, why are so women so heartless? I know babu excuse na marin mace, Nura was very very wrong daya mari Hadiza, mari ba kyau musulunci yahana amman akwai forgiveness a aure, tsakanin mata da miji yakamata akwai yafiya, jinkai tausayi wanda duka naga Nura nama Hadiza, what’s the point na makashi a kotu uban yaran dakika haifa aduniya fa, sabida ya mareki? Idan ma so take abimata hakkinta for marin daya mata she can call me wlh saina sabamai, zata iya kiran mahaifinta takai karan Nura akira amai kashedi kada ya kara taba lafiyanta, kotu all sabida mari is too harsh, so take Nura ya wulakanta aduniya dayau beda kudin bail da yana gidan yari yanzu haka, ga yarinya mai ladabi da biyayya ya aura amman hankali shi baya kanta yafison wacce ke bashi kashi wai yaya kan maza yake ne mesa sun fison abinda ke cutarda su? Hadiza ce kadai mace aduniya akan wani dalili zata dinga wulakanta min da shirun dataga nayi ta dauka tsoron ta nakeji koko ta dauka bansan darajan dan cikina bane”? Cikeda lallashi ganin ran Hajiya na tafarfasa Ya Aisha tace “Hajiya please stop crying is not good for you kada su Meena su jiki suzo suna kuka suna duk hankalinsu yatashi” cikin kuka Hajiya tace “basanan sun tafi lesson din da Meena keyi da ita da Ummi, Aisha I don’t care Nura ya haihu da Hadiza sunada yara all I know shine ko yau Allah zai dauki yara koda Ummi bata karbesu ba ku zaku amshesu bazasu taba wulakanta ba Aman da Amali, wlh wlh idan yarinyar chan takaini bango karshen auren su kenan koda Nura zai maidata saina hanashi, if she’s not ready ta zauna da yarona let her go gabaki daya” calming Hajiya down Aisha tayi sosai, tadinga bata hakuri da kyar tashawo kan Hajiya ta huce tayimata hira har saida su Meena suka dawo gida sannan tabarta tamata sallama.
Saida sukai magrib suka wuce gida, Nura na sallama su Amal da Aman dake wasa da yaran Alhaji Musa afalo suka taho da gudu suka rungumeshi suna oyoyo Dady, yaran Musa ma haka boye duk wata damuwarshi yayi yayi murmsuhi suka daddauki yaran suka shigo gidan cikeda girmamawa Maman Humaira ta gaida Nura ya amsa Humaira ma ta gaidashi cikeda girmamawa Nura ya shafa kanta yace “Humaira is now a big girl fa yaushe aka haifi Humaira nazo na dauketa a baby showel a hospital” akunyace Humaira ta rufe fuskanta duk akai dariya, abinci Maman Humaira takawo akaci suka fice dan yin isha’i Humaira ta wanke komi da sukai amfani dashi suna dawowa daga mosque suka tafi gidan yarage daga Nura saisu Aman dake wasa da toys akan rug, dago kanshi Aman yayi yakalli Babanshi saikuma yabar toys din yahayo kan kujeran yazauna kusadashi ahankali yace “Daddy are you fine?” Dasauri Nura yakalleshi saikuma yamai murmushi ganin yanda yaron ke kallonshi yace “yes Dady is fine” dasauri Amal itama tabar wasan ta hayo kujeran ta zauna kan cinyanshi takai hannunta ta taba fuskanshi tace “Dady you look very sad today right Ya Aman?” Gyadamata kai Aman yayi yana kallon Baban nashi shima, murmushi Nura yamusu baice komaiba sai kawai ya kama kansu ya manna musu peck cikeda so, ahankali Aman yace “Dady where is Mom? Bata dawoba” shiru Nura yayi yana kallonsu they have the right susan meke faruwa dudda yarane, anatse yana kallonsu duka biyun dake kallonshi kur kaman tv saikuma yakama hannunsu cikin tsantsan so da kamanta magana ta yanda yara zasu fahimta yace “Mommy will not be living with us again, Daddy is not together with Mommy” Sosai yaran ke kallonshi sukai shiruu dukansu biyun suna kallon fuskanshi chan Aman yace “Momy started doing those bad things again right Dad? Is that why your eyes are read”? Dasauri Amal abunku da yarinyar takai duka hannayenta kan kumatun Babanta tajuyo da fuskanshi saitin nata tawani leka idanunshi kaman wacce ke leka rijiya, cikin muryan yara tace “Mommy hurt my Dad, Aman daddy eyes are red like he criedddddd” taja cried din tana sakin kuncinshi tai kwaba kwaba da fuska zatai kuka da sauri Nura yace “no Amali don’t cry ni banyi kuka ba, Dady ai baya kuka, idanuna na ciwo ne saisa sukai ja” ahankali Aman yakama hannun Babanshi shima kaman zai fashe da kuka yace “Dady I promise I will never hurt you like Mommy does, and we will never ever yelled at you or scream or be stubborn ko Amali”? Gyadamai kai Amali tayi ashagawabe tace “I love my Dady very much Ya Aman I hate seeing my Daddy looking sad” ta rungumeshi, Aman shima ya rungumeshi yace “Dady you are my superhero and I love you alot Dad, you are the best Dady don’t be angry kaji Dady, kayakuri, Anty Ummi said Innallaha….” Dasauri Amali ta taso daga jikin Baban tace “ma’a sabireen” atare suka hada baki sukace “lalle Allah yana tare da mai hakuri, Dady kayakuri kaji” gyadamusu kai Nura yayi yanaji kaman yayi kuka maganansu ya mugun sosamai zuciya kawai ya rungume yaranshi kowanne side side gam gam, arayuwanshi yanason yaran nan, su biyun nan are his soul, yaranshi are just so adorable and sweet kuma suna sonshi sosai, sai yaji Ummi takara shiga ranshi, akwai some small small abubuwa datake koyama yaran da he so much appreciates, kaman son junansu tanunama yaran su biyu are one and Aman should always take care of Amali, wlh dawuya kaga Aman da Amal nafada ko sunyi sharp sharp zakaga Aman ya rungume Amali ya lallasheta he’s so protective of little sister nashi and is all thanks to Ummi da yan tatsuniya da labaran datake basu. Banda haka kana ganin kaman basusan meke faruwa ba they understand everything, saisa ko fada bayaso yanayi da Hadiza agabansu especially Aman dan yaron is very smart.
Sun dade ahaka saida yaji dukansu sunyi bacci sannan ya daddaukesu yaje ya kwantar da su adakinsu, wanka yayi anan bayin Aman yafito yaje dakin Ummi yadauko wani jallabiya yasaka yadawo dakin Aman ya kwanta yayi shiruuu sai chan hawaye ya gangaro daga gefen idanunshi dasauri yasa hannu ya share tareda fuzar da iska yace “enough!” Tashi yayi yadauki wayanshi yaciro number Hadiza yayi deleting, yashiga files nashi yashiga deleting komi nata messages, pics, yashiga whatsapp yayi blocking nata ta ko’ina, ya maida settings na wayanshi ta yanda unknown number bazai iya kiranshi ba, yanaso from daren yau yarufe babin Hadiza gabaki daya and just move on with his life, harga Allah he wish her well koba komi itane mahaifiyar yaranshi he wants her to get everything datakeso in this life to tayi rayuwan datakeso, he wants her to excel and attain success in business nata, but for him ya yafe Hadiza koda zai mutu he don’t wanna ever be together da mace kalan Hadiza ma balle Hadiza, he just wanna live his life yanzu da wacce keda opposite of all abubuwan da Hadiza kedashi.
Washegari as usual da wuri ya tashi yana dawowa tea yashiga kitchen yamusu yayi microwaving abincin da Maman Humaira ta dafa yayi arranging komi a dinning yaje sama yatadasu ya musu wanka brush yasa sukai salla yafito yabasu abinci tsaf suka cinye daidai wata babban mota na zuwa gaban gidan, sama yakai yaran dakinsu yabasu iPad nasu sannan yafito ya shigo da maza su 7 aka shiga kwashe kayan gidan ana fitar da su, dudda duka kayan gidan na Nura ne, dasukai aure da kayanta aka kawota gidan su na Kano dazasu dawo Abuja yasa ta kyautar da komi yamata komi sabo but he wants her to have it dan Allah yasani da sunanta yasai everything agidan kap, kayan dakin Ummi da gadajen dakin yaran ne kawai ba’a taba ba but hatta kujerun falon sama tass aka fitarda komi gidan looks empty yar kayan kitchen, frames menene menene, address na gidan iyayen Hadiza yabasu a kano yariga yabiyasu kudinsu aka tafi sosai ya tsaya yana kallon gidan da babu komi ciki banda pentin bango, kawai yawuce sama dakin yaran ya shiga yahada kayansu tsaf a akwatinan su dan idan yabar gidan nan sabon gidanshi zasu koma next time, shima ya tattara kayanshi awani akwati yasauka kasa shida mai gadi suka ijiye a boot already yaran sun gama exam badai suyi closing school ba tukunna amman yakira school nasu yagayamusu tafiya takamashi yadawo yadaukesu suka sauko yasasu amota ya kulle gidan yashiga mota office yaje yayi some ayyuka da komi yabarma manager shi aikin sannan by 2:00 suka tafi airport dan 2:45pm jirgin zai daga, yaran were so happy zasuyi tafiya they’ve missed traveling daganan sukai flying sai kano inda direban Hajiya ke jiransu already.
Kuna ganin Nura made the right decision na rufe chapter Hadiza gabaki daya in his life??
Koko kuna ganin is not the right decision daya kamata yadauka??
Me aganinku yakamata yayi??
In his statement “I want mace complete opposite na Hadiza” yana nufin wacce is not as educated as Hadiza, expose as Hadiza dadai sauran su, kuna ganin that’s the best thing for him??
What are the perks na auren educated independent woman??🤗
And what are the perks na auren uneducated uncivilized lady???🤗
Don’t forget ku shigo class dina na matan Aure with just 2k chat me up today wa.me/+2347012181461
💫 MATAN?? Ko MAZAN??💫
✍🏻M SHAKUR
EPISODE 2️⃣9️⃣
https://chat.whatsapp.com/JgukZW7wzUHL8lbg9IraqN
INDAI KAYAN SAWAN YARANE TO GA KANKAT NAKAWO MUKU❤️
Do you want your kids to look like those yan gayu kids you admire on instagram? Definitely yes, Eshamin kiddies got you covered. mun shiga mun fita mun tattaro the best for your kids, with chikini money zamu fito muku da yaran ku tass. We make beautiful dresses (rtw and bespoke) headbands and turbans. When it comes to kids fashion you know I no get no 2
You can also check us on IG
https://instagram.com/eshamin_kiddies?igshid=OGQ5ZDc2ODk2ZA==
29
Mota suka shiga instead instead sutafi gidan Hajiya direct super market yasa driver yafara kaishi, tsaraba ya kwasa dayawa yakai wajen kayan zaki tsayawa yayi yana kallon roban mentos cingum Ummi ne tafado ranshi sanin tanaci, ahankali yasa hannunshi yadauki roba daya yasa a cart su Aman ma suka kwashi abubuwan dasukeso dukansu yaran were so happy sukaje suka biya direba ya deba yasa a boot suka wuce gidan Hajiya.
Yaran sunsan gidan Hajiya sosai ko sunzo salla anan suke zama sai idan Mommy su tazo takan dauke su suje gidan su adawo dasu wajen Hajiya da yamma.
Suna shiga gidan Hajiya da gudu suka sauko daga mota sukai ciki, matan dake taya Hajiya aikatu na kayan abinci sai sannu da zuwa sukema Nura dayayi kyau gaidasu yayi cikeda girmamawa ya ciro ragowan cash na aljihunshi yamikama babban ciki su raba sai godiya suke yawuce ciki daidai bakin kofa yaga Hajiya tabude mai hannu rungumeta yayi warmly yace “Hajiyaaaaa” “barka da zuwa Nura, sannu sannu, maraba lale” sakinshi tayi sabida Aman da Amali dasukace “Grandma where’s Aunt”? Gwaggo na murmushi tace “sunje school amman sun kusan dawowa” shiga falon sukayi Nura yasami waje ya zauna yana kallon yanda Aman da Amal ke guje guje suna fadawa kan lumtsa lumtsan kujerun Hajiya falon a gyare sai kamshin turaren wuta yake, sosai Hajiya ke kallonshi yadan rame yafada, yama danyi duhu kadan, kusadashi ta zauna tareda shafa kanshi cikeda so tace “ya kake”? Murmushi yamata yace “I’m fine Hajiya kada ki ramu I’ve moved on” sosai Hajiya ke kallonshi feeling at ease da yanda yayi maganan kanshi ta shafa tace “Madallah, to jeka wanke hannu kazo kaci abinci da kaina namaka girki yau” cikeda kulawa yace “Hajiya bana hanaki aiki ba, me Meena keyi da Um…….” Saiyay dan shiru kafin dasauri yace “all this matan dake tare da ke ai zaki iya sasu koda ace Meena na school” murmushi tamai tace “I cooked for my son, Oya tashi ka wanko hannu kazo, na gyara maka side dinka, idan kuma gidanka zaka sai shima nasa aje a gyara” yatsine fuska yayi yace “banson naje gidan nan Hajiya ina nan, maybe dai naje Adamawa” Hajiya na kallonshi cikeda gamsuwa tace “yakamata kaje kaga Gwaggon Ummi kam” Gyadamata kai yayi kaman ya tambaya ina Ummi yadai shiru yatashi hannu yaje ya wanke duk Hajiya na lurada shi yanda yake kalle kalle he’s just dying to see her, yadawo sosai dagashi har yaranshi sukaci abincin Hajiya kaman wayanda suka fito daga yunwa tass yagama ya mike yace “bari naje na watsa ruwa a side dina” Hajiya dake bawa su Aman abinci abaki da hannunta tace “toh” wucewa yayi yafita yataka zuwa wani side dake dan nesa dana Hajiya babba ne flat din, bude kofa yayi yashiga an gyara falon dayaji komi sai kamshi yake yawuce bedroom ga akwatinshi har ankai ciki, ruwa ya watsa yafito ya tsaya ta window yana goge jikinshi daidai nan yaji yaranshi na ihu ihunsu yacika gidan. “Anty Ummiiiiiii” dasauri yasa hannunshi yadan dage labulen ya leka, Ummi yagani sanye da dogon rigan abaya black mai shegen kyau ta yane gyalen akai dayadan zamiye baya ana ganin kitson datayi ma shuku yan kanana masu kyau hannunta dayasha jan lalle rikeda jaka haka dayaga books aciki tawani daga Amal da bala’in mamaki takasa yarda yaran ne kaman Hajiya bata sanarda ita zuwansu ba.
Tsayawa Nura yayi chak yana kallonta she look peng, way prettier than before, black skin nata nawani kalan sheki though idanunta sun fada ciki but she looks thicker than yanda ya santa, dan lumshe idanu yayi yana kallonta yanda harta daura Amal abayanta ta rungume Aman ta gaba suna juwa juwa matan gidan na musu dariya, jiyayi zuciyanshi ya buga! Kasa daina kallonta yayi she looks sooo happy da ganin yaran suma yaran haka, saida yaga da ita da su sun wuce dakin Hajiya sannan yasaki labulen window idanunshi kaman zasubi Ummi falon.
Suna shiga falon Ummi ta gaida Hajiya tace “Hajiya yaushe su Amali sukazo”? Murmushi Hajiya tayi tace “dazun nan da Baban su sukazo yana bangaren shi, yaje yadan watsa ruwa” faduwa gaban Ummi yayi daman zuwanshi yasa Hajiya takira aka mata kitso da lalle kuma tabata wasu magunguna jiya da daddare tasha dabata san na me ba, yayma da safe har wani farfesun kaza aka bata taci da wani maganin, amugun kunyace takama hannun Amali tace “kuzo muje dakina” itama Hajiya cikeda hikima tace “jeki ajiye abubuwan school kizo kici abinci ku shiga kitchen ko, mijinki yazo gari ke zakimai girki” gimtse dariya Meena tayi Ummi kuma akunyace tace “tohh” tawuce dakinta su Aman na biyeda ita kaman bindi, deep down jitayi takosa tadaura Nura a ido amman kuma fushi take dashi, but she’s just so happy yazo kanon, she missed him alot, salla tayi ta chanza kaya zuwa wani atampa mai shegen kyau sabo ne ma am mata gown fitted daidai jikinta shape nata yafito sosai tasa dan kunne tana kokarin yin dauri Meena ta shigo dakin saikuma ta saki baki cikeda tsokana tace “biki zaki ne Ummi”? Cikeda rashin gane tsokanan tace “bikin ina”? Murmushi Meena tayi tace “ohh kenan duk yayana akema kwalliyan nan ai na dauka fushi kike dashi”? Akunyace Ummi ta nuna su Amal dake wasa da wayanta tace “me haka Meena yara na nan fa” hararanta Meena tayi tace “ni zauna namiki daurin” zama tayi tamata daurin tai kyau sosai kaman ba kitchen zata shigaba ta shafa turaruka, takalli kanta amadubi saitaji tanama kunyan Hajiya ta ganta ahaka Meena tace “muje” dasauri Ummi tace “Meena mesa nai gayu haka girki fa zanje nayi ai Hajiya saitamin wani kall……” “Ummiiiii” Hajiya ta kwala mata kira da sauri tace “na’am” tabi gefen Meena tabude kofa da gudu tafito kawai taci karo da mutum zata fadi yariketa da sauri ajikinshi suka tsaya chak suna kallon fuskan juna but jikinsu amanne da juna, sosai Nura ke kallonta yana sanye dawata soft milk yadi mai shegen kyau yazo kiran Aman suje masallaci Hajiya tace “yaje yana ciki” yawuto nan, da gangan Hajiya ta kwalama Ummi kira dan so take su hadu, lumshe idanu Nura yayi jin wani la’anannen ni’imantaccen kamshin datakeyi dayamai sallama a hanci feeling her soft skin da hannunshi daya na waist nata daya nakan hannunta ta wajajen muscles, he miss every part na jikinta kaman yar baby yarike ajikinshi haka yaji yakasa koda kwakkwaran motsi sai zuciyanshi dake bugawa, almost 30secs sukayi ahaka suna kallon juna babu wanda ya iya magana cikinsu, da kyar Ummi ta iya samun natsuwan fita daga jikinshi cikin wata yar muryan da ita kanta batasan tanada shi ba dakeda kaudi asirace tace “iiiishhhh sorry Baban Aman ban ganka ba” bata jira amsanshi ba tabi ta gefenshi tawuce tana wani irin cat work dake juya ass dinta, wani kalan automatic baci alwalan Nura yayi wow! Yafadi cikeda mamaki irin is this Ummi yanda tamai magana casually kaman ita dashi basu taba sharing any relationship ba, kaman irin ta yafeshi arayuwanta din nan wai sorry Baban Aman ban ganka ba, kaman banda shi Baban Aman ne batasan wani matsayi nashi ba awajenta, fitowa daga dakin da Meena tayi yasa yajuyo da kanshi dasauri yakalleta tace “Yaya kaine” “call Aman” Nura yafadi kai tsaye, dasauri Meena tace “sunachan suna wasa da wayan Ummi bari na kirasu” dasauri yace “don’t worry jeki” yawuce yashiga dakin wayan Ummi ya karba daga hannunsu yasa a aljihu sannan yace “suje” saida yakara komawa side nashi ya dauro alwala sannan suka tafi, basu sake shigowa gidan ba shida Aman sai bayan sallan isha’i.
Around 9, yana shigowa dakin Hajiya yabi dakin da kallo ganin baiga Ummi ba sai yaji ranshi yadan baci, gaida Hajiya yayi, Hajiya tace “akawo abinci Nura”? Dudda bayajin yunwa at all dan yaci abinci dazun din nan dayawa but ahankali yajuya dan baiso yahada ido da Hajiya yace “akawo side dina Hajiya kaina ciwo yake zan kwanta” yana maganan yafice murmushi kawai Hajiya tayi kasa
25, August 2025
Saadatu Ali
Yes