Showing 21001 words to 24000 words out of 202729 words
Babanka da wasu abokan naka, da Meena kuma Ubangiji Allah yasa albarka ni kaina na yaba da natsuwan yarinyar kuma ta kwanta mini arai.
Ba karamin fada mahaifiyar Hadiza tamataba kuma tace tabama Hajiya hakuri da Nura, washe gari ba dudda idanunta a kone suke amman kana ganinta tai zuru zuru sanda Mamanta tagaya mata Nura yace takoma har ijiyan zuciya tasauke aboye baro shagon tayi wajajen 8.
Around 9 takai gidansu tana parking motanta Nura na fitowa daga gidan rike da Hajiya da Meena suna hira suna dariya yayi wani irin kyau yana sanye da soft material milk yasa sunglasses a idanunshi, hada ido tayi dasu dasauri ta dauke kai haderai tayi tamau ta taho saida tazo dab dasu tace “sannu ya jiki” bata jira amsan Hajiya ba tawuce ciki tabude kofa ta shiga ta bugo kofan Nura yajuya yakalli kofan Hajiya tace “muje kaga 10 fa likita zai ganmu” wucewa sukayi suka tafi.
Tunda Ummi taga Hadiza tadawo ta shiga ta natsu tana gama aikinta ta tafi bayan gida a garden ta zauna akan kujeran lilon su Amal da wayanta a hannu tana buga game, ringing wayanta yayi dasauri ta kalla batasan number ba amman tadauka takai kunnenta ahankali tace “hello” anatse Nura yace “Hajiya Ummi” batasan lokacin datace “laaaaa Alhaji yakuri bansan kai bane, ina yini, Ya Hajiya kunkai asibitin? Wani abu kake bukata nayi?” Duk ta jero mishi tambayan atare, cikin kwantacciyan murya yace “Hajiya natare da Dr, tagama ganinshi kuma zan kaita chan Gwarimpa anan zata cigaba da zama gidan kannin Abba na” “okay” Ummi tafadi but zaka iyajin nuna jin dadin ta a muryanta, ahankali yace “kinada katinki na kasa? National identity card?” Dasauri tace “eh inada shi” shiru yasakeyi yace “kituramin hoton shi ta whatsapp sannan ki shirya kayanki gobe zan maidaki kauyenku Adamawa ko?” Maganan yazomata abazata dasauri tace “eh” saikuma chan asanyaye tace “wani laifi nayi”? Ahankali yace “kin manta alkawarin dana miki zan kaiki kiga Gwaggon ki shine zan cika” murmushi tayi taushi tace “Allah yasaka maka da alkhairi” murmusawa yayi shima yace “kinga kayanki cikin kayan danasa gateman yakawo miki?” Dasauri tace “naga slippers dina na dauka, naga wasu kaya duk sainakai store na ijiye” cikeda so yace “nakine akwai wani black abaya mai stones ahannunshi shinakeso kisaka gobe kinji” gyadamai kai tayi kaman yana gabanta tace “to nagode Alhaji” shiru yayi bai sake cewa komiba tagaji da shirun tace “hello” kaman daga sama yace “zaki aureni Ummi?.
Matan Abuja!
Matan Abuja!!
Matan Abuja!!!
Haaaaa, HADIZA has been making countless reference daku, the women of Abuja come close are you all the way Hadiza ke suffanta ku? Ance idan miya yayi yaji??? Ai dole yaji ne zai saka miyan yaji ko??
So kunada dogon explanation you guys need to come clean🤣
But then again all I see in Hadiza is so much soyayya for her man but this stupid mentality nata is leading her astray, why must you be the one to call shots agidan mijinki? To shi mijin is there for what? Name ko fame????
Hello Ladies both married and unmarried are you learning one or two lessons from this novel nawa???
But again kuma let’s not be sentimental, mu kalli Hadiza da kyau, all she ever wanted is power which is normal akwai dominating mata dama, itama tanason kawayenta susan tana juya mijinta but maganan yayanta is valid sabida kunje Italy saikice saikin maida mijinki Italian???
Share your 2cents ladies and gentlemen ❤️
See you asabar💃
💫MATAN?? Ko MAZAN??💫
✍🏻M SHAKUR
EPISODE 7️⃣
THIS PAGE IS FOR YOU ZEE, MY NUMBER 1 MOTIVATOR, I LOVE YOU❤️❤️
Saukan tambayanshi Ummi taji kaman daga sama saikuma takai hannunta ta taba kirjinta daya buga, to kodai sabida yanda taketa tunaninshi tun jiya yasa taji kaman yace mata zata aureshi? Ta tambayi kanta, me Alhaji zaiyi da itama in banda shirmen tunainta hakan yasa tace “na’am banji abinda kace ba Alhaji?” Ijiyan zuciya Nura ya sauke wlh yadade baiji murya mai dadi kaman na yarinyar nan ba komi nata sanyaya mai zuciya yake, the feelings he’s developing for her is growing a fastest rate, cikin taushashiyar murya dake kashewa mace zuciya yace “ina sonki da aure Ummi zaki aure ni?” Yanda gaban Ummi ke bugawa saida tacire wayan dasauri daga kunninta takifa shi kan cinyanta tadaura duka hannayen ta biyu kan wayan ta runtse idanunta tana breathing so fast this is unbelievable, yasan tana sonshi ne? Yasan tana tunaninshi ne? Ta tambayi kanta takai almost minti daya sannan tamaida wayan kunneta daidai Nura nacewa bakice komiba, itama wlh bala’in nauyi da kunya takeji tace ta yarda haba saikace jira take, kaman yana magana da little Amal yace “Ummimy” yanda yakira sunanta har cikin jinin jikinta taji itama anarke tace “Na’am” cikeda so da bege Nura yace “ataimaka abawa Alhaji amsa eh Hajiya Ummi na” rufe fuskanta tayi dasauri akuma kunyace, murmushi yadan subuce daga bakinta da yaji karan kadan hakan yasa yayi murmushi yace “Ina jinki” Abala’in kunyace tarufe fuskanta da hannu daya tarike waya da dayan hannun akunnenta tace “idan munje kauyen mu ka tambayi Gwaggo na” murmushi yamata shi babba ne this amsan kadai ya wadatar da curiosity dinshi yace “okay yanzu kije kiyi sallama da matan gidan kice mata zakije kauyenku gobe an kiraki daga gida, kada ki fada mata wani abu bayan haka kinji” gyadamai kai tayi tace “toh” dan ijiyan zuciya yasauke kaman kada yayi sallama da ita yace “tom saina dawo” akunyace still tace “mezan dafa maka”? Cikin kashe murya yace “nabarwa Hajiya Ummi zabi” dasauri ta cire wayan daga kunnenta takashe sai murmushi take, amsanshi melt zuciyanta, wai itadai Alhaji keso ya aura ikon Allah, takai awa daya awajen zancen zuci take ita kadai sannan ta tashi tawuce sama sallama da knocking tayi gaban dakin Hadiza akace shigo bude kofa tayi ta shiga Hadiza na kwance kan gado da babban IPad dinta na apple tana kallon cctv footage na shagonta yanda yau takasa zuwa shagon dan batada karfin zuwa dukawa Ummi tayi tace “sannu da hutawa Anty” kallo daya Hadiza tamata tadauke kai tace “lafiya?” Kan Ummi na kasa tace “Anty tafiya takamani kauyen mu gobe!” Dasauri Hadiza ta yunkuro ta kalleta hakan yasa Ummi tace “Gwaggo na batada lpy tace tanason ta gani maza maza” wani kalan harara Hadiza tamata tama kasa magana to idan ta tafi yaya zatayi da yaran nan gashi kafin su sami wata yar aiki dazasu saba da ita sai an wahala, cikeda asalin rashin son ta tafi tace “inhar kinsa kafa kinbar gidan nan da sunan tafiya to kisani na sallameki daga aikin nan kinajina”? Gyadamata kai Ummi tayi ahankali tace “toh” tsaki Hadiza taja danta dauka she will start begging her tace tafasa tafiyar, rai abace tace “sabida dan rashin lafiya ne yanzu harsai anwani kiraki kinbar aikin ki dake ciyar dasu kinje kauye? yanzu ma tukunna kwana nawa zakiyi idan kinje? Kan Ummi na kasa tace “sati daya ko biyu hala” Hadiza jitayi ranta yabaci datana da wani power da wlh saita hana tafiyan nan cus yaranta zasu shiga wani hali yazatayi dasu yanzu? Ga agency nan kokai requesting yan aiki unless akwai akasa shine zaka samu fast Inba hakaba sai an kawo, tsakin takaici takaraja tace “tashi kifita ki tabbatar dai goben kin shirya yaran nan sun tafi school kafin kibar gidan nan dan da sassafe zanje aiki yanda yau banje ba din nan” “to zanyi Anty, nagode” Ummi tafadi tana mikewa tafice daga dakin tawuce kasa yan karikechan ta tashiga hadawa bayan tagama taje tayi girki, yaran suka dawo ta shirya su bayan sunci abinci takaisu islamiyya dake nan cikin estate nasu itama takasa gayamusu zatai tafiya dan tasan kuka zasuyi sosai amman wlh zatayi kewansu sosai.
Wuraren 10 yashigo gidan zama yayi a dinning yaci abinci bura busko Ummi tamai da wani miyan veggies mai dadi abincin dayaci saida yabashi tsoro tass yagama yakalli dakinta yayi murmushi yawuce sama ga mamakinshi Hadiza yagani a falon sama kwance kan dogon kujera daga ita sai wani dan black short mai kaman pant yanada lace abakin wandon very sexy, tasaka half vest milk na silk material mai kyau shima, dan juyowa tayi suka hada ido itada Nuran sannan ta maida kanta kan throw pillow ta kwanta tana kallon tv, ita kanta bama tasan maisa tayi gayun nan tazo nan ta kwanta ba, deep down so kawai take ya kulata, dakin Aman Nura yashiga yadubashi yamai addu’a yafito ko kallon inda take baiyiba yashiga dakin Amal yamata addu’a yafito ta gefen ido Hadiza keta binshi da kallon ganin su Hajiya basu dawo tareda shi ba to ya komar dasu Kano ne? Ko yamaka musu hotel ne?.
Dakinshi yashiga bayi yafada direct yayi wanka fitowa yayi daure da towel a waist ga mamakinshi Hadiza yagani kan gadonshi ta kwanta tana kallonshi exactly irin kallon shima yamata yadauke kai yawuce gaban madubi ya shafa mai ya feffesa lafiyayyun turarenshi yaje gaban wardrobe yaciro pajamas nashi yakoma bayi yasaka yafito, ganin ya dumfaro gadon yasa Hadiza tasoma jin dadi aranta agaban gadon ya tsaya yasake kallonta ido cikin ido itama kallonshi take right in the eye amman bazata iya bude baki ta gaidashi kota cemai sannu ba taga shigowanshi gida tun dazu, dauke idanunshi yayi daga kanta, filon dake gefenta yasa hannu yadauka yayi wajen kofa yabude yafita yawuce dakin Aman kan gadon Aman yahau yana kashe wuta ya kwanta abinshi yana sauke ijiyan zuciya.
Bugo kofan Hadiza tayi tashigo ta kunna wuta dakin yayi haske takalli Nura tace “kanka akeji daman sabida Mama tamin fada ne nazo turakan ka amman jibi yanda ka wulakanta ni, ka shanyani agado kataho dakin danka zaka kwana anjima kahau cewa ban maka komi na aure, oya kajika gabanka aruwa kasha mana kasan ai ka iya biyo sahu idan jarabanka yataso maka ka lallabani nabaka, ina jiran ranan zakasha mamaki na nima wlh” tajuya fuuu tafice daga dakin ta bugomusu kofa saida Aman ya firgita cikin bacci dasauri yarike Aman yana patting head nashi, chan bayan yakoma bacci yatashi yakashe wuta yadawo ya kwanta yayi bacci abinshi.
**
Washegari normal aikinta Ummi tayi Hadiza tasauko tai breakfast around 8 tawuce tafita abinta ko biyar bata bawa Ummi ba dan ba son tafiyan takeba, saukowa Nura yayi yana sanye da wata farar shadda yayi kyau bana wasa ba har gaban dakin Ummi yaje yayi knocking bude kofa tayi chak numfashin shi ya tsaya ganin Ummi tana sanye da sabon black dogon rigan daya saya mata, ta tsife kanta jiya da daddare ta wanke da sabulun wankanta abinta ta taje tayi Parking batada cikan gashi at all dan kanta ma small head gareta amman wani kalan coily blonde-black hair gareta dan gashinta ba baki sidik bane irin jajajan nan ne orange orange baki baki, fari fari irin gashin agwai haka gashinta yake ta yana gyale akai daya dan ja baya tasa kwalli a idanunta, rigan yamata chass ajiki ganinshi dan tun jiya sai yanzu suka hadu yasa ta juya dasauri zata koma cikin daki karaf yakamo hannunta dasauri tajuyo suka hada ido ta zubamai fararen idanunta dasuka sha kwalli ta diga kwalli in between giranta guda biyu tayi wani kalan unexplainable kyau, ahankali yasaki hannunta dayaji yamai taushin gaske kaman yarike hannun Amal sai kawai yajuya dasauri yayi dinning dan rabon dayaji wani abu yatadamai da sha’awa harya manta, ganin Ummi da dan kama hannunta dayayi just awaken libido nashi zama yayi a dinning yayi crossing leg da sauri batare daya juyoba yace “kin gama hada komi ina gama breakfast zamu wuce” daga chan ta dakinta tace “eh nagama” itama komawa daki tayi dasauri yanda taji hannun Alhaji cikin nata sai taji tana fitar da numfashi kashi kashi.
Tass yayi lafiyayyan breakfast sannan yazo wajen kofan yace “kawo kayanki mutafi” bude kofa tayi rike da ghanamasgo dinta akunyace kallon Ghanamasgon yayi sai kawai yajuya yace “ina zuwa” sama yakoma yadauko babban suitcase nashi yakawo har gaban dakinta ya duka yabude ya karbi Ghanamasgon baiji kunya ko kyama ba da kanshi yabude yashiga jera mata komi a suitcase din, yarinyar nada tsafta dudda kayanta sun mutu but komi awanke alinke ga dan black leather dayakai hannunshi zai taba dasauri Ummi ta duka tarigashi dauka hakan yasa ya kalleta sai kawai yayi murmushi dan yasan menene turawa tayi akasan akwatin nan da nan yagama hadawa suka kulle yaja akwatin waje Ummi na biye dashi har mota gaba yau yabude mata yana kallonta shiga tayi ahankali ta zauna yakallulle yadawo gaba shima yatada mota har Gwarimpa bakaramin addu’a Hajiya tamusu ba sannan Meena da Baffan shi da ita suka tafi airport ga mamamkin Ummi abokanshi tagani a airport already suna jiransu da Musa da engineer sunci manyan kaya sai kallo Ummi suke munafukai saijin dadi suke, jirgi suke shiga kalan tsoron da Ummi taji a ko tadauka mutuwa zatayi haka sukakai Yola motoci taga suna jiransu guda daya daya security personnel sauran nasu nan aka dauki hanyar kauyensu though sun tsaya a hanya anyi sayyaya na ban mamaki kayan abinci shopping da sauransu.
Tunda Ummi taga sun dauki hanyar kauyensu gabanta ke faduwa hannunta suka fara rawa komi nadawo mata sabi fill
Hannunta Meena tarike tace “ga dukanmu, ga mopol yan sandan chan babu abinda wani katon dan daban kauye ya isa yamiki” tafiyan awa daya da rabi yakaisu kauyensu, kauye ne da yamayi developing ga government work akwai government school, burtsatsai, primary health care da sauransu sai kallon ko’ina take komi ya chanza ta dade rabonta da garin har gidansu wanda yake babban gida ginin kasa irin na da din nan.
Wata tsohuwa sosai haka na zaune a tsakar gida tana mulmula hura taji ihuuu hayaniya a waje tace “Allah yasa ba shaidanin yaron nan ne yazo dawani bala’in ba yau” da gudu wata yarinyar mai kama da Ummi yar karama da bazata wuce 13yrs ba tashigo tana hakki. “Gwaggo Gwaggooo Ummi, Umm…..” kafi takarasa magana Ummi tashigo gidan tareda Meena, mikewa tsaye Gwaggo tayi saikuma tasa zani ta murje idanunta tasake kallon Ummi data tsaya tana kallon Gwaggo, Gwaggo tace “Kodai mutuwa ce tazomini yasa nike ganin kaman Ummi achan tsaye dawata balarabiya” dawani kalan gudu Ummi tazo tafada jikin Gwaggo sai kuka ga kanwar Ummi ta biyun itama tashigo sai kawai dukansu sukahau kuka dagota Gwaggo tayi tace “Ummi kene binni ya karba haka kin ganki kuwa ya akayi kikazo? Banace kada kizo ba duk sati sai Mudi yazo gid…..” fuska Ummi ta share tace “Gwaggo akwai baki maza awaje dauko tabarma Aisha ki shimfida wajenki zukazo” dasauri Gwaggo tace “bakin yan uwan baturiya nan ne, yaki yarinya gaki fara kaman madara” murmushi Meeena tayi tazo ta gaida Gwaggo, Gwaggo ta aika Aisha ashigo dasu nan da nan aka shigo dasu wai bakin Gwaggo yaki rufuwa taga manyan dattijawa ansha shadda fura tashiga hada musu kowanne a kwarya mai kyau su Aisha harda Ummi dama Meena natayasu har Baffa saida yasha huran sun dade basu sami aslin ingantaccen fura irin wannan ba sukai salla.
Daukan nasu huran sukayi su Ummi duk suka tafi daki saida aka gama Baffa ya gabatar da zancen daya kawosu wai Gwaggo kasa boye farin cikinta tayi nan ta sanar dasu komi game da Ummi da aurenta ada tace zancen aurenta kuma maigari ne mai bada yaran aure Dan haka atafi wajenshi nan akanshigo da komi aka shiga mota aka tafi wajen mai gari shima yayi naaam babu wani wahala Dan Auren bazawara ba wahala and tanada right Ummi tafito da mijinta yanzu tunda nabiyu ne kuma itane takawoshi har kauyensubnan da nan su Musa suka ijiyema abokinsu sadaki dubu dari uku aka daura aure tsakanin Nura da Zainabu Ummi akan sadaki 300k mutane dayawa sun shaida aka kawo su goro cingam menene menene aka rarraba wai Nura sai murmushi yake he just can’t believe it duk suna wajen Aisha tazo da gudu tace “Gwaggo ga Mudi chan yazo amman yan sandan nan sunmai duka” tashi Nura yayi da sauransu Maugari yace “dan Allah kukai yaron nan gidan yaro ya addabi mutanen Hm kauyen nan” komawa sukayi akai arresting Mudi nan fa Gwaggo tayi throwing small party itadai Ummi taja makale adaki taki fitowa Meena ko tafito sai video take yanda matan kauye ke rawa Musa yakawo bakinshi saitin kunnen Nura yace “kai mutumina bura’uban chan haka kauye keda tsala tsalan mata bazanyi wuff dawata ba kuwa anan kai jibidai kirjin wanchan dake rawa” tureshi Nura yayi yace “dan iska” dariya Musa yayi yana kallon yammatan, Musa yataba engineer yace “kaga yara amman Allah yamusu kindirmo a kirji” Nura yayi kaman baijishi ba aranshi yace “na Matata Ummi tamafi kowa nan kindirmo” yadan lashe lips yana kallon agogo, Aisha ne tazo tace “Gwaggo tace kazo” binta yayi zuwa falon Gwaggo tana zaune ga Ummi agefe kanta akasa zama yayi ahankali Gwaggo tace “Nura na yaba da hankalinka ne saisa nabaka Auren jikata dan mutumin kwarai ne zaisa diyarka a mota da yan uwanshi azo har kauyenku a nemi aurenta dan haka nabaka ita amana kagansu nan su hudu ne dukansu marayun Allah ne ba uwa ba uba kaji tsoron Allah bamu da kowa a binni dazance je gidan Ummi dobamin ita, tana hannunka ka kulamin da ita na yarda da tarbiyan dana bama yaran nan sunada kunya natsuwa amana da girmama na gaba dasu Ummi bazata taba cutarda kai ba Ummi matace karike ta amana sai kuma inaso nadan roki alfarma ka barta tadanyi ko sati guda ne anan wajena a danyi mata gyaran amare” abu Nura yaji ya tsayamai awuya Gwaggo tace “kayarda”? Ahankali yace “ba matsala” Gwaggo tace “yauwa tunda an kama shegen yaron nan banda sauran tashin hankali na gode Nura bari nafita nabaku guri kuyi sallama” Gwaggo ta tashi tafice.
Juyoda kanshi yayi yakalli Ummi da kanta ke kasa tana jikin bango kaman ruwa ya hadiyeta mikewa tsaye yayi yana duba agogon dake daure da writs nashi sannan yakalleta yace “tashi ki rakani Amarya zan tafi” akunyace Ummi tadaura duka hannayenta kan fuskanta tarasa inda zatasaka kanta sabida kunya, he loves yanda takemai yarinta yarintar nan kunya kunyan nan, gently ya duka agabanta dab da ita yana kallon dogayen yatsunta masu fararen kumba
25, August 2025
Saadatu Ali
Yes