Showing 81001 words to 84000 words out of 98004 words
taymaka, tun da a halin da ake ciki ma Baba ya gama shirin sa na komai kara kawai zai shigar.
***
Tana idar da Sallah sai ga kiran Arkel, lokacin ya fito kenan yana zagaye masarautar, da Bongel suka hadu yau ma kamar kullum ta kalle shi, ganin yana waya yasa ta fasa wuce tayi wajen sa, cigaba yayi da tafiya salim na gefen sa ita kuma ta cigaba da tunkarar su
"Oga kai fa take kallo." Salim yace yana kunshe dariyar sa, sai gaban Maryam ya fadi jin abinda Salim yce, banza Arkel yayi masa ya cigaba da wayar sa har ta karaso,
"Sannun ku." Tace
"Bby, zan kiraki bari na karasa masauki."
Kafin tayi magana ya kashe wayar, wani tukukin bakin ciki ne da kishi suka taso mata, radau taji maganar mace, kuma ga abinda salim yace, ai gaba daya sai taji komai yayi mata zafi, duk sai ta kasa cigaba da aiwatar da abinda take har Arab yazo suka tafi bata da wata walwala.
***
Satin su daya sannan suka dauko hanya, wannan karon su biyu suka taho babu malam wanda yace ya zo gida, aikawa kawai iyalin sa da sauran jikokin sa suzo su ga dangin su.
Arkel yana cikin tsananin farin ciki har Allah Allah yake ya isa gida, babu wanda ya fadawa zuwan sa, maigadi na zaune yana jin yar Radio sa yaji ana buga gata ɗin,, tashi yayi ya leka, da sauri ya zare sakatar ganin ashe oga ne da kansa, da sauri ya karbi kayan hannun sa suka wuce ciki.
Lokacin Maryam na zaune a falon tare dasu ummi da Arab suna ta hira, magana ce a bakin Maryam ɗin amma ta kasa furta ta, sai sakawa da warware wa take ta rasa ta in da zata fara, ita kadai take ta hasashen ta har zuwa lokacin da ya turo kofar bakin sa dauke da sallama, ita ce a saitin kujerar da ke kallon kofa, saboda haka yana shigo wa da ita yaci karo, idon sa a kanta ya zuba mata su, Ummi da ta saki baki tana mamakin ganin sa dan bata yi zata ba, murmushi ne kwance a fuskar sa ya karasa gaban Ummin yana sauke dukkannin jikin sa a kasa,
"Ummi..."
"Ikon Allah... tafiya ba shiri dawowa ma ba sanar wa."
"Wallahi Ummi."
"Sannu da hanya toh."
Kallon Arab yayi yaga ya dauke kai yana danna waya, ya san haushi yaji da be sanar dashi ya sauka ba, sai ya maida kallon sa wajen Maryam data sauke kanta kasa tana wasa da gefen mayafin ta.
"Wasu basu iya sannu da zuwa bane Ummi?"
Sanar ta gane da ita yake, dariya kawai Ummi tayi, ta tashi tana cewa
"Kaga ban san maka ba, bari na shiga ciki."
Tashi tayi ta shige ciki a nutse tana dan taka kafar, bin ta sukayi da kallo cike da tausaya wa, tana shigewa Arkel yayi saurin dawowa gefen ta, kallon sa tayi ya bata fuska
"Baki ganni bane wai madam."
"Sannu da zuwa." Ta fada a kasa kasa kar Arab yaji,
"Tashi tashi, muje ciki kawai akwai yan sa ido anan, muje sama."
Sai a lokacin Arab ya kalle shi, dariya kawai yayi yace
"Idan ka dawo normal munyi magana."
Da sauri Arkel yace
"Yanzu hauka kaga ina yi kenan?"
"Kusan hakan ne."
Yace yana dariya gami da mik'ewa yayi waje gaba daya. Sai ya maida kallon sa wajen Maryam dake dariya k'asa-k'asa, hannun ta ya kama ya murd'a, da sauri ta daina dariyar.
"Tashi muje."
Yace yana rike ta, har sunyi hanyar saman sai ya tsaya
"Samo mana abinci a Kitchen din Ummi idan mun hau mun hau kenan sai da safe."
Zame hannun ta tayi ta juya Kitchen din, hancin ta tasa hannu ta rufe hancin ta sannan ta shiga, kamshin da Kitchen din yake ne bata so, abincin ta hado akan tray da duk abin da zata bukata ta wuce saman. Tana ajiye kayan yayi saurin rungume ta jikin sa yana saka hancin sa a saman wuyan ta
"Ya naga kin rame, rashin lafiyar da kikayi ne haka?"
Daga mishi kai tayi, kashin wuyanta ya taba
"Gobe dole mu koma asibiti, ba zai yiwu ba, ba zan yarda kashi yana cizo na ba."
"K'ashi kuma? Ina k'ashin?" Ta fada tana hade fuska ka
Gefen kugunta ya taba
"Gashi nan kashin wajen ya fito ba meat, kin ga ai sai ki dinga buga min shi cikin dare."
"Kai ko?" Ta fada tana dariya
Dariyar shima yayi
"Ko nayi karya ne?"
"Uhum."
"Bari na watsa ruwa nazo, ko zaki taymaka min ne?" Ya fada yana kanne mata ido ɗaya, girgiza kai tayi
"A fito lafiya."
Zama tayi tana dora hannun ta a saman cikin ta, mamakin abinda ya mai dashi so happy haka take, murmushi tayi ta cigaba da jiran shi har ya fito.
***
Da daddare suna kwance ta rasa ta ina zata fara fada masa, kunya da nauyi take ji,gashi gogan naka sai budurin sa yake yi be san dawar garin ba. Hakura tayi kawai har zuwa gobe idan taji yadda Baban sukayi da Umma sai ta sanar dashi komai, tana fata da hasashen hakan ya zama gaskiya.
Da safe kuwa kusan makara sukayi, a gurguje ta shirya tayi kicin saboda yadda cikin ta yake kiran ciroma, Allah ya taymake ta babu abinda bata ci sannan babu amai sai yar kasala kawai da kuma tsanar Kitchen, wari yake mata sosai shiyasa idan zata shiga sai ta toshe hancin ta dukka da abu, tea ta hado ta zo tasha da cake ta koma dakin, baccin safen nan kamar farilla ya zame mata, lokacin Arkel ya fita ma hakan yasa tayi kwanciyar ta bayan ta karo karfin Ac.
A harabar gidan suka hadu da Arab, hannu ya bashi kafin yace
"Baka yi min murna ba.".
Dan kallon sa Arkel yAyi
"Ka samo matar aure halan."
Dariya Arab yayi
"Wanne matar aure ana maka maganar na kusa zama DAD!."
"Kai fa matsala ta da kai kenan, yaushe kayi auren har ka zama DAD?"
"Wallahi da gaske nake, yaron ka ai nawa ne, idan Maryam ta haihu ai ni ta haifa ma."
Dariya yayi
"Auw auw. Toh sai ka jira ta samu cikin ai ko? Sarkin azarbabi."
"Auw wai baka sani ba? Wallahi jiya Ya Nabila ke fadan ashe na kusa zama DAD, anan naji ai ashe Madam ce ke da juna biyu."
Wani gingirin Arkel yaji maganar, da sauri ya kalle shi
"Are You Serious?"
"Allah kuwa, na zata ka sani ai."
Da sauri Arkel ya juya
"Mu hadu anjima a falo akwai babban al'amari, for now bari na ganta, Thanks bro for this beautiful news."
Dariya Arab yayi
"Sai ka fito, ina jiran gift d'ina."
"Baka da matsala."
Yace yana shigewa da sauri. Tana kwance taji an daga ta sama, a firgice ta bude ido saboda baccin ya fara hawa kanta, zagaye ya fara yi da ita a tsakiyar dakin kafin ya ajiye ta yana dariya.
"Shine baki fada min ba? Kika barni na wahalar dake jiya."
"Me?"
"Ban sani ba, zauna." Yace yana nuna mata kan kafarsa, zama tayi ya zagayo da hannun sa ta bayan ta, rigar ta ya daga ya shafa cikin nata sannan yayi mata peck a gefen kunnen ta.
"I so much love... Children Maryam, Allah na gode maka."
Ta zata cewa sai he so much love her, har da dan rufe idon ta sai taji yace children, shiru tayi masa ya gama lalube laluben sa ya maida ta saman gadon yana gyara mata kwanciyar.
"Kin daina komai daga yanzu, kiyi ta hutawa abinki kinji my lady."
Haushi take ji shiyasa tayi masa kus ya gama maganganun sa ya fita.
Tashi tayi ta dauke waya ta kira umma, tana d'agawa tace
"Ya jikin naki?"
"Da sauki, ina wuni? Yasu Habubu?"
"Lafiya lou, ina ganin ki sanar wa me gidan baki abinda yake faruwa idan yaso sai kiga yadda zai dau al'amarin, kafin nan sai nasan me ya kamata muyi."
"Shikenan, zan kira."
***
Dakin Ummi suka shiga a tare , daki ne hade da falo bayan main falo a in da kowa ke zama, suna zaune da Alhaji yana shan kunu a dan madaidaicin kofi, gefen Alhaji Arab ya zauna shi kuma Arkel ya zauna a bangaren Ummi, kallon su Ummi tayi ta bata rai
"Ban ga 'yata ba, ina kuka barta?"
"Yanzu zata zo ummi."
"Yawwa, ga Nabila shiru, ko wani ya sake kiranta."
"Bama sai an kira ba Ummi, gani ma."
Duk sai suka kalli kofar, da sauri Arkel ya bude wa Amna hannun sa, da gudu ta yi wajen sa tana dariya. Gaisawa sukayi a cikin farin ciki da son juna sannan Maryam ta shigo, kanta a kasa yake kamar ko yaushe, hakan ba karamin kara mata daraja da kima yake a wajen iyalan gidan ba, a rayuwa kunya abune me matukar amfani, karka zama ka fitsare kafa duk tsiya akwai nauyi tsakanin ka da surukan ka, ka mutunta su ka girmama su.
"Malam Arkel, dukkan mu nan kai muke jira da sauraro, dalilin tara mu anan da kayi, me ya faru?"
A cewar Alhaji yana ajiye kofin kunun da yasha, magani Ummi ta mika masa ya karasa sannan ya gyara zama.
°°°
"Ummi, Alhaji. Akwai wata rana da ina duba wasu takardu na zo kan akwatin Ummi, hotunan da na gani da bayanin dake jikin takardar dake nuna tarihin Ummi da asalin ta, duk da rubutu ne akayi shi da wani yare daban, sai na dauke takardar nayi ta bincike akanta, a karshe sai da nayi nasarar gano fassarar yaren. Tun daga lokacin na dauki aniyar gano wa Ummi dangin ta, na sha wahala matuka, an cuce ni sosai akan hakan, nasha yawo gari gari, kafin Allah ya haɗa ni da Malam, ladanin wani masallaci da ke nan kasa da unguwar gano, bansani ba, ashe sunana ne babban alamar da zata bayyana dangin Ummi, rashin lafiyar Ummi ita ta dakatar dani, ta tsayar dani da aikata komai, toh cikin ikon Allah sai gashi yanzu Allah ya taimake ni, ya cika buri na a sanda ban zata ba, a yau na tabbata ko na mutu, ba zan tafi da bakin cikin rashin cikar buri na ba, a yau ina me farin cikin sanar muku da cewa Na gano dangin Ummi, asali tushe me karfi, ingantaccen ahali wanda kowa ne mutum zai yi alfahari da kasancewar sa a ciki."
A tare suka yi kabbara, hawayen tsantsar farin ciki ne ya shiga jeran gwano a fuskar Ummi, Nabila da Maryam, Arab da Alhaji kuwa rasa ta cewa sukayi, tsam Arab ya mike ya rungume Arkel
"Ban taba ganin mutum kamar ka ba, U r the best broda."
Satar kallon sa Maryam take ya shiga basu labarin komai da ya faru a Mali, gaba daya Ummi ta kama shiga tsananin mamakin dan nata, albarka kawai take shi masa ta kasa magana sai share hawaye take. Takardar ya fiddo musu, a kasan ta an fassara komai, karba kowa yayi ya kalla, kura wa sunayen dake jere ido Maryam tayi, ABUBUKAR HAMZA ne ya tsaya mata a rai, sunan Baba ne baro-baro, ajiyar zuciya tayi ta cigaba tayi da karantawa har tazo wajen sunan wadda tasa aka dauke ta, numfashin ta ne ya dauke chak ganin sunan Hajiya Mama baro baro, *Azeema Audu* sai ta cigaba da nanata sunan cikin tsantsar mamaki.
Not edited
Ignore typos
[3/18, 22:28] Hafsat Rano: 48-49 *SK*
***
Mika takardar tayi ta tashi tsam, duk suka bita da kallo, sama ta haye ta dauki wayar ta ta kira Umma, ta sanar da ita abin da yake faruwa, tsabar rudewa yasa Umma tayi dakin Baba da sauri, jin tafiyar sa a bayan ta yasa ta jiyo kunnen ta rike da wayar, kafin ya karaso tayi kansa da gudu, ganin haka yasa ya bude mata hannun gaba daya ta fada, sannan ya sa ya rufe.
Wajen mintuna biyu suka dauka a haka kafin ta janye tana riko hannun sa.
"Muyi magana."
Sai ya bita kamar raƙumi da akala har gefen kujerar dake ajiye a wani bangare na dakin. Sai data ja fasali kafin ta soma magana cikin wani irin yanayi me nuna tsantsar farin ciki.
Tun da ta fara maganar yake kallon ta, bakin sa a bude ya rasa me zai ce, baya so ya katse ta ya fiso yaji komai, sai ya sake gyara zama sosai a jikin ta yana sauraron duk wani abu dake fitowa daga bakin ta daki-daki.
Sai data kai karshe sannan ne yayi magana cikin tsananin murna.
"Maryam..." Ya ja sunan ta cikin wata iriyar murya da be san yana da ita ba, sai ta rausayar da kanta cikin wani irin yanayi ba tare da ta san tayi ba.
"You Are the real example of mace ta gari, barakallahu fikh, muje wajen su Ummi, wannan maganar abar dubawa ce, idan hakan ya kasance gaskia bansan wanne irin tukwaici zan miki ba."
"Amin ya ALLAH."
"I..." Sai ta bude idon ta sosai tana sauraron sa.
"Muje dai."
Yak'e tayi kawai tabi bayan shi kasan Zuciyar ta na jin haushin rashin furtawar sa.
***
Kowanne bangare ya rikice da farin ciki, duk da akwai sauran manya manyan dalilin da zasu sake tabbatar da komai, sai dai ko a hakan kawai zaka tabbatar da gaskiyar maganar. Tare suka shiga dakin Ummi yana rike da hannun ta, tana tsaya tana kokarin saka hijabin ta, fuskar ta kamar gonar auduga tayi saurin taro Maryam da ke shirin zubewa a kasa
"Ina alfahari dake 'yata, tun ranar da na fara ganin ki naji ina kaunar ki, ashe ke din jini na ce."
"Allah yayi muku albarka."
Murmushi sukayi a tare suka hada baki
"Amin Ummi."
Wayar Maryam ce tayi kara, Baba ne ke kira da kansa, tana d'agawa yace
"Kun taho ne ku muzo?"
Kallon Arkel tayi sukayi dariya kfin tace
"Gamu nan Baba, mun fito ma."
"Ina MUHAMMAD?" Ta kallli Arkel, kallon waje yayi
"Ai tuni yana mota shida Alhaji, Nabila ma ta karaso, tana waje."
"Muje toh, na shirya ai."
Jakar ta Maryam ta karba suka sata a tsakiya, a haka suka jera har waje kafin su shiga mota su dauki hanyar gidan na su Maryam.
***
A gyara gidan yake tsaf, komai an ajiye shi a wajen daya dace, kejin Habubu ma an sake matsar dashi dan ya bada fili, babbar tabarma aka aro a gidan bayan su aka shinfida, ana jiran zuwan su, kiran Alhaji Faruku Baba yayi kafin su ƙaraso yace idan zai yiwu yana bukatar sa a gida yanzu yanzu. Be wani bata lokaci ba sai gashi har ya riga su Maryam ɗin ma zuwa, Baba be sanar masa da abinda yake faruwa ba yace dai akwai bakin da zasuyi shiyasa yake so yana wajen, sai ya shiga gidan sa a gurguje ya fito.
Sun dan samu holdup a kabuga da kofar famfo shiyasa ka suka dan kara bata lokaci, Ummi duk ta kagu aje bata sauraran hirar da suke tayi, ana isa kofar gidan taji kwalla ta zo mata, kwallar tausayin kanta da dan uwan ta, jiki a mace ta fito daga motar tana kallon su Baba dake tunkaro su, sai ta tsaya tsak a maimakon ta karasa kamar kowa, ido ta zuba musu kwallar da take ta kokarin boye wa ta sake zubowa, Maryam da Ya Nabila ne suka taimaka mata suka shiga gidan, da fara'a Umma ta tarbe su tana musu lalle marhabin, suka zazzauna Ummi dai sai kalle kalle take, shi kanshi Baban kallon ta yake babu ko dauke wa, babu tantama balle shakku, tsantsar kama da mahaifiyar su, babu ko digo na babbanci kamanni, duk da shi be yo bangaren Mahaifiyar tasu ba, bangaren mahaifin su daya kasance bahaushen Kano sukayo, a yan ganin da yayi wa Arkel na duk da ba wai kallon sa yayi sosai ba, ya raya wani abu a ransa, sanin babu abu makancin haka yasa ya watsar ya bar hakan a matsayin kamace kawai, dadin dadawa be taba sanin Arkel ne sunan nashi ba, da Muhammadu ya sanshi, shine sunan da Alhaji Faruku ya fada masa lokacin da ya haɗa auren, shine kuma sunan da Ummi take fada masa a duk sanda zata sanar dashi wani abu daya danganci ita Maryam ɗin, sau tari ma sai dai tace mijin wance a dabiaa da kara irin ta malam ba haushe.
Duk shaidun da ya kamata dukka bangaren biyu su gabatar sun gabatar, tsananin mamaki Baba ya shiga in da sau daya be taba raya ya nemi dangin mahaifiyar tasu ba duk da ta sanar dashi wani bangare na labarin su, duk sai yaji kunya ta kamashi da jin ai Arkel yayi komai ya gama, Alhaji Faruku kuwa ya kusan fin kowa farin ciki, yana da yakinin Hajiya Mama zata samu saukin wani abu, duk ba be san kuma ya makomar maganar tatan take ba, sai dai yana fatan ta samu afuwa duk da baya goyon bayan abinda ta aikata ɗin, gashi yanzu komai nata ya lalace tun a duniyar, shiyasa a kullum ake so mutum yayi abu me kyau, hakan shine zai tabbatar da mutum akan tafarkin daidai har zuwa ranar sa zai koma ga mahaliccin sa.
Yinin ranar baki dayan ta cikin farin ciki aka yi ta, da labarin Rayuwar data wuce, Ummi ji take kamar sallah gashi sun dinki da umma kamar dama sun san juna, aikuwa da aka zo tafiya sai tace su tafi ita anan zata kwana, kallon Arkel Maryam tayi alamun ita ma zata zauna aikuwa yayi kicin kicin da fuska, tana ji tana gani ta bishi suka tafi, sai da suka fara sauke Ya Nabila a gidan ta sannan suka wuce nasu.
Bayan magriba Umma ta raka Ummi gidan Hajiya Mama bisa umarnin Ummin da tace lallai sai taje, tana zaune kamar kullum dai babu wani ci-gaba ta bangaren yanayin nata, tana ganin su ta hau surutai da suka-suka. Babu ɗaya daga cikin bayanan da Ummin tayi mata da ta gane sai data ambaci sunan Ummin da sunan Baba Yelwa sannan ta ne ta zabura kamar zata fita da gudu, rirrike ta suka yi cike da tausaya wa, babu wani abu da mutum zai aikata na sharri face Allah ya nuna maka iyakar ka. Ummi sarkin tausayi tuni har ta fara sharar kwalla da kyar Umma ta janye ta suka koma gida. Da daddare Baba ya zauna suka sake sabuwar hira, hira tsakanin Ya da kanwa da basu taba sani ko hasashen irin wannan lokacin ba, basu farga ba saboda tsabar hira har sai da Umma ta ankarar dasu da dare sannan suka hakura akan gobe zasu dora. Duk wasu tambayoyi da Ummi take buƙatar sani ta sansu yau, hatta da yarintar Maryam sai da aka bata labari, ji take kamar bata da wani sauran bacin rai a duniya, abu daya yanzu ya rage musu shine
27, January 2025
Rukayya
Good