Showing 90001 words to 93000 words out of 98004 words
kowa dauki da murna yake, tuni dama an san da zuwan su, an shirya abubuwa kala kala dan tarbar su, Ummi da ke ta faman goge hawaye kadan kadan saboda yadda take ji a ranta abinda bata taɓa tunani ko kowa wa a ranta ba, sanda suka karasa masarautar ta kowa sai daya buɗe baki saboda mamaki da Al'ajabi, ba zaka taba tunanin akwai halittar dake rayuwa a wajen ba kafin ka karasa.
Firfitowa sukayi aka hau bushe bushe da kad'e-kad'e, Sarkin da kansa ya fito ya tsaye a daidai kofar yana me tsananin farin ciki, karasawa sukayi cike da farin ciki aka hau gaisuwa duk da yaren da sukeyi ya banbanta amma da yawansu suna jin hausa, sai kuma france da ya zama shine official language na kasar sai kuma yaren Bambara da ya zama kamar Hausa a Nigeria bayan fulatanci da ya zama yaren garin nasu.
Hannu Baba Sarki Àraàbú ya kama suka shiga ciki, a fada aka yadda zango aka shiga sabuwar gaisuwa sannan Arkel ya gabatar da Ummi da Baba,da kowa da kowa, daga nan kuma ne aka sa matan da yaran suka tafi cikin gida dan su huta su ci abinci suyi sallah, babban masaukin da aka tanada domin su aka kai su, ba karamin kawata wajen akayi ba duk saboda zuwan su, Ummi da take jin ta kamar an sata a aljanna don murna sai taji bata da wani sauran damuwa a rayuwar ta, duk da Allah be sa taga iyayen ta ba, amma tana tunanin hakan wani tsari daga Allah cikin hikimar Sa ya hukunta mata hakan, ta gode Allah ta kuma sawa ranta wannan shine jarabawar ta.
***
Tana zaune ana gyara mata gashi ta cigaba da jin bushe bushen da akeyi tun safe, duk da ita mutum ce ba me son kwaramniya ba amma hakan ya saka ta son sanin abinda yake faruwa a masarautar tasu, ta san dai koma menene yana da matukar muhimmanci ga ahalin gidan. Janye kanta tayi ta tashi tana daukar rigar ta zata dora a sama, da sauri baiwar ta ta mike ta taimaka mata, takalmi ta zura ta sake gyarawa sannan ta kalle ta
"Me akeyi a gidan nan?"
"Ranki ya dade, bakon nan ne na kwanaki ya dawo, sai dai wannnan zuwan da yawan su suka zo har da mata da yara."
"Suna ina?"
"Mazan na tare da maimartaba, matan na chan karshen babban gida anan aka sauke su."
Bata yi magana ba ta juya ta fito, tsayawa tayi a kofar bangaren ta tana kallon fadar daga nesa, zuciyar ta na ingizata taje ta ganshi, ta rasa dalilin da yasa ya tsaya mata arai tun ranar data fara ganin shi, sai dai a yadda take jin kanta da mulki ba zai a iya ba, tsaki tayi ta juya wani shashen tana tafe tana kallon in da aka ce an sauki bakin a chan.
***
Da daddare duk kowa ya hallara a fadar, har da Bongel da sarki ya aikata tazo ita da dan uwan ta yôùsòfà, sai sauran dangin da abin ya shafa, bayan dogon jawabi daga bakin sarki da abinda ya tara su sai ya bawa Baba dama yayi magana ya sake gabatar da kansa da yar uwar sa Ummi, sannan aka bawa sauran kowa dama shima ya fadi nasa bayanin, Bongel na daga ɓangaren dake fuskantar Arkel, shi kuwa hankalin sa na kan Maryam, duk motsin ta a idon sa yana lura da ita, ya san ta gaji so take ta huta shiyasa kawai ya ga gwara ya nema mata alfarma tun da tana da uzuri, fita sukayi duk kunya ta kamata bayan ya nemi alfarmar zai rakata ta kwanta, suna barin wajen mutane yayi saurin jawo ta jikin sa.
"Sannu my wife."
"Uhum sannu, kawai sai ka bani kunya a cikin mutane."
"Kunyar me? Dan nace zaki huta kina da uzuri?."
"Baka ga yadda kowa ke kallo na ba, wanda be gane ba da yanzu kasa duk sun gane, sai wani sannu ake jera min."
"Haha, toh me kike so suyi, ni ai tausaya miki nayi ashe ban yi gwaninta ba."
"Kayi... Kadan amma, kuma wallahi idan munje baccin zanyi karma kace..."
Rike ta yayi ya tsaya yana mata kallon mamaki
"Wai me kika mai dani ne yarinyar nan?"
Zame wa tayi tana dariya tace
"Bance komai ba ni."
"Zakiyi bayani ne."
"Daga fadan gaskiya."
"Zaki sani ne, wanka zanyi kinji zafin garin nan kuwa? Ai sai ka dafe dan ma akwai wuta."
"Kasan sahara, dole za'a yi zafi dama."
"Aikuwa akwai, kwana uku zamuyi mu tattara mu koma gaskiya, sai dai in Ummi zata zauna da Baba bamu sani ba."
"Suyi kamar sati ba, nima in zasu zauna zaman zan gaskia."
"Sannu toh."
"Please...."
"Kafata kafarki Madam."
Tura baki tayi gaba ta hau kunkuni, be bi ta kanta ba ya shige toilet d'in ya tara ruwa sannan ya fito, towel ya dauko a cikin kayan su ya daura sannan ya matso kusa da ita, rigar jikin ta ya kama zai cire ta rike hannun sa da sauri, hannun ya janye ya cigaba da abinda yake, sai daya gama ya mika mata dayan towel din yace
"Manzon Allah (S.A.W) ma yana wanka tare da iyalin sa, sunna ce me kyau so don't ever deny me again ba zanji dadi ba."
A sanyaye tace
"In Sha Allah."
***
Washe gari aka gabatar da wasanni a kofar fadar, mutanen gari duk sun zo har da wanda suke makwaftaka dasu, wasan ya kayatar sosai sun ga banbancin al'adah, bayan an gama kowa ya watse, gari aka zagaya dasu aka nuna musu ko ina sannan suka dawo da yamma likis.
Kwanan su biyu Bongel ta gama fuskantar alakar Maryam da Arkel, duk da sau tari bata iya banbance su sai dai idan an kira sunan, sai kawai ta hakura ta watsar da komai ta cigaba da addu'ar Allah ya zaba mata mafi Alkhairi. Shi kuwa Arab ko lura da ita be ba, abu daya ya riga ya sawa zuciyar sa zai bawa Lubna dama, yana komawa zai sanya aje a tambaya masa auren ta. Washegari suka fara shirye shiryen tafiya in da za'a bar Ummi da Alhaji, sai Baba, Maryam da Ya Nabila sun so su kara zama amma sam ogannin nasu sun rufe idon su sun ce no, haka suka tattara suka bi su ba dan sun so ba, ita kanta Ummin taso a bar mata wata tun da sati biyu kamar yau ne, sai dai tun da ta lura da yanayin yaran nata ta share batayi zancen ba, musamman Arkel daya fi kowa rawar kafa babu yar kunyar nan duk mantawa yake da kowa na wajen idan aka ce abu ne daya danganci Maryam.
***
Sati biyu aka sallami Hajiya Mero, saboda tsabar yadda ta koma da kyar zaka gane ta, har kofar gida suka kawo ta suka tafi, bata bari ta kwana a garin ba ta saka Zainab a gaba suka koma Kaduna, bata fatan ko da wasa ta sake dawowa Kano, Hajiya Mama kuwa bata gane komai gata nan dai hakkin mutane ke bibiyar ta. Shi kanshi Alhaji Farukun ya daina damuwa da lalular ta ta bikin Rauda ne a gaban sa yanzu, ya matsa so yake kawai yayi mata aure dan rashin jin nata kara yawa yake shiyasa kawai ya yanke shawarar aurar da ita ko ya huta.
***
Bayan dawowar su abubuwan duk suka hade wa Maryam, ga project ga ciki yayi nauyi ga hidimar gida haka dai take daurewa tana kokartawa dan bata son samun matsala, shi kanshi uban gayyar ya sake zama busy saboda ginin da yake yi ga shagunan da yake shirin budewa, haka dai yake yakicewa yana kula da Madam din tasa, har aka samu aka kammala karatun dai da kyar lokacin cikin ya tsufa haihuwa ko yau ko gobe.
***
Shagon Baba na kasuwa aka sake buda masa aka zuba masa kaya, sabon gida Arkel ya haɗa mishi ya bashi a matsayin sa na wan mahaifiyar sa kuma uban matar sa, sosai Baba ya zama Babban mutum harka ta bude masa ba laifi yana samu a shagon nasa tun da yanzu ya zama saro kayan yake yana siyar wa ba pieces ba.
***
Bayan kwana biyu Arab ya nemi aje a tambaya masa auren Lubna, Alhaji ne ya wakilta Baba da Alhaji Faruku suka je suka tambayar masa aka ce an bashi, murna ba'a magana tsakanin masoyan biyu, ba a wani ja da yawa ba aka kai kayan aka saka rana wata hudu. Tun daga lokacin aka shiga shiri bangarorin biyu kowa yana so ya burge danuwan sa.
***
A gajiye ya dawo tun daya fita be zauna ba, shirye shirye kawai yake na shagunan da zai bude, Maryam na gaban akwati tana jera kayan da za'a tafi dasu asibiti ya shigo, tashi tayi da kyar ta yi masa sannu da zuwa, ruwa ta doro akan tray ta kawo masa ya sha sannan ya kalli kayan
"Komai ya zama ready ko?"
"Eh, Zaitun da Spirit ne kawai babu."
"Owk hadda su ko? Mantawa nayi wallahi."
"Ai dole, kana kokari ma Allah ya saka maka da Alkhairi."
"Amin."
"Allah ya raba lafiya."
Kasa ta sauka ta jawo kayan abincin data ajiye mishi ta zuba masa, zama yayi kusa da ita ya karba yace
"Thanks."
Murmushi tayi ta sake mike ƙafarta da take jin tayi mata nauyi sosai.
Da magriba suna sallah sun kai raka'ar karshe taji kamar an buga mata ciki, suna sallama ya juyo yana fuskantar ta, ganin da yayi tana ya mutse fuska yasa yace
"Ya dai?"
Cikin ta ta nuna masa tace
"Ji nayi kamar an buga ni ta cikin."
"Toh, sannu Bby ke exercise."
"Uhum."
Tun daga lokacin ta cigaba da jin babu dadi, wajen goman dare ciwo ya fara tsananta, tun tana dauriya har ta zama ta kasa, dole ya sauka ya kira Ummi, tana zuwa tace su fito a tafi asibiti haihuwa ce, kayan kawai ya dauka ya saka mata Hijab ya rikota suka sauko da kyar. A motar abun ya cigaba da karuwa, sosai take kokarin ganin tayi dauriya sai dai ciwon ma neman fin karfin ta, bata san lokacin data fara kuka ba tana kiran sunan Allah. Arkel duk ya rikice ya rasa me yake masa dadi, sauƙin ta ma Arab ke tukin da kuwa an samu matsala.
[3/18, 22:28] Hafsat Rano: SAUYIN KADDARA
54
***
Zagaye kawai yake a wajen ya rasa abinda yake masa dadi, tsawon awa biyu babu wani labari, kana kallon fuskokin su zaka san suna cikin tashin hankali, jiran me haihu bashi da dadi akwai tashin hankali da zulumi, kallon Arab Ummi tayi tace ya kira mata Ya Nabila, gefe ya koma ya kirata ya kashe ya dawo yana kallon yadda Arkel yake zagaye baya ma gane komai, har Nabila ta karaso bata haihuwa ba, duk sun yi jigum jigum dasu babu me wa wani magana ana addu'a.
A chan gida gaba daya sai Umma taji jikin ta babu dadi, tun daren ranar ta kasa sukuni, jikin ta ne ya bata Maryam ba lafiya, addu'a tayi ta yi mata tana fatan idan haihuwa ce Allah ya raba su lafiya.
Gaf da asubah ta haifo yar ta bayan bakar wuyar data sha, da sauri nurse din ta fito ta sanar dasu, ta koma, Arkel na Masallaci yana addu'a be san anyi haihuwar ba har aka fito dasu daga labour room aka mai da su dakin hutu, kiran wayar sa Arab ke tayi be daga ba dan basuyi tunanin yana masallacin ba, duk sun shiga wajen ta sai sannu suke mata, da ido kawai take bin su,ta riga ta dandano bakar wuyar da kowacce uwa take sha yayin haihuwa, lallai ba karamin kokari iyayen mu suke sha ba da zaka ga sun haifi goma sha sannan suzo suyi tarbiyyar dukka. Allah ya kara wa iyayen mu daraja.
Fitowa yayi daga Masallacin yana kallon sararin sama, jikin sa babu kuzari ko kadan, tsoron sa daya kar ya rasata, zuciyar sa ba zata iya dauka ba, wayar sa dake haske a aljihun sa ya lalubo ya duba, kiran Arab ne ya sake shigowa yayi saurin d'agawa
"Kana ina ne? An fito dasu fa."
Da sauri yace
"Ta haihu?"
"Emana, kayi sauri."
Be jira komai ba yayi saurin komawa ciki, yana tafiya iska na kada shi saboda tsananin farin ciki, yana zuwa nurses din wajen suka hau yar rige-rigen tare shi, murmushi kawai yake yana kokarin yin gaba yana sauraron su
"Bari na fito zan ganku."
Cike da karsashi ya isa ya tura kofar, da sauri Maryam ta rufe idon ta ya Nabila ta hau gud'a, dariya kawai Ummi take tana kallon Arkel, sai ya tsaya chak ya kasa karasawa kunya na kamashi, dariya Arab ya saka yana kallon shi
"Su kunya manya."
"Ƙaraso mana angon karni."
Kallon Ummi yayi yaga shi take kallo, sai ya sauke kansa yana dariya
"So yake mu fita naga alama."
Ajiye baby tayi a gefen Maryam ta kalli Arab da Nabila
"Muje waje."
"Gaskiya ni ban ga gama ganin my princess ba." Arab yace yana sake zama
"Amma ai ka bashi waje ya ga lafiyar matar sa ko?"
Nabila tace tana dariya, lokacin Ummi ta fita ganin haka yasa ya cije yatsa yace
"Allah muma ya aurar damu a daina mana gori."
"Da dai yafi,muje ni."
Fita sukayi Arkel ya maida kofar ya rufe har da saka key, da sauri ya dawo gefen ta ya zauna yana kallon fuskar ta yadda tayi fayau, d'an yatsan yasa ya zagaye a saman girar ta, bude idon ta tayi kadan tana kallon sa, dariya yayi ya manna mata peck a kuncin ta yasa hannu ya dauko babyn sa ya zuba mata ido, babu in da ta barshi, hannun ta ya rike a cikin nashi yana kallon kankantar hannun, murmushi ne kwance a fuskar sa ya rasa ya zai fasalta ranar,
"Sannu Wife." Yace yana shafa fuskar ta,
"Haka ake shan wahala dama?"
Tace tana girgiza kanta, fuskar tausayi yayi ya rike hannun ta da dayan hannun sa
"Kinsha wahala ko? Sannu Allah yayi miki albarka."
"Amin."
"Kinga carbon copy d'ina ko? She looks exactly like me."
"Uhumm.. Son kai ko?"
"Kalle ta mana, ba wani son kai."
"Uhum."
"Ya kike ji?"
"I'm weak."
"Sannu Allah ya Kara lafiya."
"Amin."
Wasa ya cigaba da yi da babyn, idon ta ta soma budewa kadan-kadan har ta samu nasarar bude shi dukka, kallon ta kawai yake in admiration, Wai shine yau da baby, Allah kenan, kuka ta fara tana taɓe baki yayi sauran kallan Maryam
"Ya zamuyi? Kuka."
"Nima na sani." Baya ta juya ya kwantar da ita ya fita waje, be ga su Ummi a reception ba sai wajen nurses yaje yace musu tana kuka. Kallon juna sukayi suka sa dariya a tare
"Baban baby, madam ta dan daure ta gwada mata maman."
"Ok." Yace yana juyawa dan yaji haushin dariya da sukayi masa, komawa dakin yayi yace
"Sun ce ki dan bata ta sha."
"Wa! Hum um."
"Haka suka ce ai."
Kin tashi tayi babyn ta sake bude murya sosai, jijjigata ya hau yi daga kwancen da take yana kallon Maryam yana mata magana ta tashi, banza tayi taki tashi har sai da Ya Nabila ta shigo, daukar babyn tayi ta jijjigata.
"Kanina dan bamu waje mana."
"Ok toh."
Yana fita ta kalli Maryam
"Daure ki tashi kiga."
Kamar ta fasa ihu ta tashi da k'yar saboda ɗinkin da akayi mata ya soma daddaure mata jiki shiyasa bata son ko motsawa
"Sai fa kin daure, shi dinki dole sai kana motsawa, idan kaso jikin ka ya kwabe ma."
"Akwai zafi ne Ya Nabila."
"Sannu... Daurewa ake."
*Uhum."
Mika mata ita tayi ta taimaka mata da yadda zatayi, duk kunya ta mamaye ta haka ta daure tana ciccije baki kamar zatayi kuka, tsabar azaba da rashin sabo.
Gari na fara haske Ummi ta kira umma da kanta da sanar mata, Barka sukayi wa juna Umma na ajiye waya ta shiga dakin Baba da murna, zama tayi a gefen gadon bakin ta yaki rufuwa, kallon ta baban yayi ya gane akwai magana
"Ya akayi ne?"
"An samu karuwa."
"Ah Alhamdulillah, Masha Allah, lafiya dai ko?
"Lafiya lou yanzu Ummi ta kira ni."
"Toh Alhamdulillah, me aka samu?"
"Kayi amarya."
"Lallai, kice na fara hada lefe, Allah ya raya yayi mata albarka."
"Amin ya ALLAH."
"Sai ki aika a sanar da mutanen gidan chan ko, ko kiyi musu waya?"
"Eh idan garin ya sake wayewa zan aika."
"Ok Allah ya Raya, sai Hankali ya kwanta yar ki ta sauka lafiya."
"Baban Maryam!"
"Karya nayi? Kwata-kwata baki da sukuni tun da watan nan ya kama ina sane dake."
Dariya ta saka kawai ta tashi ta fita, wayar ta ta dauka ta kira Anty Maryam ta fada mata, murna ta hau yi tace zata taho anjima kadan.
***
Likita ne yazo ya duba ta ya tabbatar lafiya sannan ya sallame su, Alhaji na gida suka dawo, yar aka kai masa shashen sa ita kuma me jego Ummi ta sa aka gyara mata daki a kasa ta saka ta, Arkel be gane kan hakan ba, zuba ido yake yaga sun hawo sama tun da suka dawo amma yaji shiru, yana saukowa ya tarar da aika-aikar da Ummi tayi masa, kamar ya dora hannu a sama yayi taa zunduma ihu yaji, tuni gidan ya fara cika da yan uwa da abokan arziki na bangaren Alhaji da Umman su Maryam din, ganin haka yasa ya bar gidan ba dan yayi niyya ba.
Da daddare bayan kafa ta dauke ya faki idon Ummi ya fada dakin, Ido ta zuba masa har ya karaso ya zauna a gefen ta yana kallon babyn, saman dakin ya kalla ya ga fan din a kashe, tashi yayi da sauri zai kunna tace
"Ba'a kunna wa jarirai fan, it's to early."
"A haka zamu kwana?"
"Zaku kwana?" Ummi dake cikin toilet d'in d'akin ta fito tana hararar sa
"Aina zaka kwanan?"
"Umm... na'am um dama."
"Minti biyu na baka kayi musu sai da safe ka kama gaban ka, bari naje wajen Alhaji."
Marairaice wa yayi yace
"Ummiiiiii!!!"
Sa kanta tayi ta fita ya bata fuska yana kunkuni
"Kina jin Ummi fa, ganin ku ma sai an bani time?"
"Emana."
"Tab lallai, ashe mun kusa parking daga gidan nan kenan."
"Babu in da zamu"
Dariya take masa ya dauki babyn ya kalle ta
"Wanne suna zamu sa mata?"
"Uhmm.. wanne kake so?"
"Zabin ki ne, ke kika sha wahala so ki zaba kinji."
"Sunan Ummi?"
"Yayi miki?"
"Sosai, sai muce mata Hudah."
"An gama ranki ya dade."
"Thanks dear, nagode Allah ya saka da Alkhairi."
"Shishshi, karki wani yi godiya,next haihuwa sunan Umma zan sa idan baby girl ce."
Zaro ido tayi
"Zan kara haihuwa kenan?"
Dariya ta bashi sosai, kwantar da Baby Aysha yayi ya kamota ya sakata a jikin shi yana dariya
"Menene na tsorata haka daga maganar haihuwa."
"Hmm ba zaka gane ba, a bar zancen kawai."
"Na barshi toh, yanzu me zaki bani tukwaicin sa sunan Ummi da nayi."
Ture shi tayi tana dariya tace
"Babu wayon da zaka
27, January 2025
Rukayya
Good