Showing 15001 words to 18000 words out of 98004 words
san ma a fili yayi maganar ba, wanke hannun sa yayi ya mike ya hau kwashe kayan, saurin dakatar dashi tayi ta karba taje ta ajiye ta dawo.
Saman kujerar ya zauna yana maida hankalin sa kan tv, remote ya dauka ya chanja tashar zuwa channels, hoton da ya bayyana a akan screen din ne yasa daga shi har ita suka yi wata irin zabura, labarai yake karantawa cike da kwarewa, fuskar sa ta cika sosai da sai dai yasha gyara saboda aikin sa, babu abu daya daya banbanta da shi a da sai cikar fuskar sa da gashi, daidai lokacin yake kokarin tattare shirin, duk sunyi tsaye a gaban talabijin din suna jira suga karshe, cikin harshen nasara ya yi godiya a karshe ya fadi sunan sa. MUHAMMAD ARAB ALMUSTAPHA.
Screen din na dauke wa ya Nabila ta shiga lalubar wayar ta da sauri, Arkel kamar gunki haka ya kame a wajen ya rasa yadda zai fassara al'amarin, dan uwan sa rabin jikin sa da suka jima suna nema shine ya cigaba da rayuwa a wani waje daban ba tare da su ba? Duk shakuwar su da kaunar junan su ya tashi kenan? Wanne irin babban laifi ne haka da har zai bar gida? Ya bar dangin sa da kowa nasa? Wa zai amsa masa tambayoyin nan?
Manage dan Allah ciwon ido ya sani gaba. 😭
Bana so kuyi ta jira ne shiyasa nayi wannan
[3/18, 22:23] Hafsat Rano: *SAUYIN K'ADDARA*
*8*
*HAFSAT RANO*
*ZAFAFA BIYAR MASU ZAFI*😅😂
*Littafin nan na kudi ne me so ya karanta ya nemi wannan number 08030811300
***
A hannu ya riko wayar ya shigo gidan ba tare da ya daga ba,
"Ya akayi? Naga kin kira."
Ya fada yana shiga falon, kallon yanayin da Arkel yake ciki ya yi kafin ya maida kallon sa kanta
"akwai matsala ne?" Ya sake tambaya
"Please wa ka sani a channel tv?"
"Mutane da yawa, me ya faru ne wai?"
Ido jajir Arkel ya dawo tsakiyar falon ya zauna, yaya Nabila a tsaye ta tsaya ta kasa zaman, cikin dashewar murya yace
"Yanzu muka ga an nuna shi, ashe yana raye?" Yayi maganar yana jinjina da jikin kujerar yana jin wani irin yanayi
"Are you serious? Arab yana nan da rai kake nufi??"
"Yes... Yanzu ma aka gama program din sa a channel Tv, he's still alive."
"Toh how comes? Bari kiga dai,bari nayi mana confirming."
Daukar wayar sa yayi ya kira wani abokin aikin sa da ya san sun yi aiki tare a gidan Tv na NTA daga baya ya koma channel Tv, har ta k'araci ringing d'in ta be dauka ba, haka yayi ta fama kiran mutane baya samun su.
A yadda yake jin kirjin sa yayi nauyi yasa kawai yayi musu sallama ya fito, ko ta ina gefe kafar sa yake har ya isa titi ga dare ya soma yi dama, yana tsayewa ya samu abun hawa ya nufi gida zuciyar sa kamar zata tarwatse ta fito, kansa cike yake da tunanin abinda ya faru, Hajiya Mero na zaune a falon ita da Alhajin su ya shigo bakin sa dauke da sallama duk kuwa da ba wai da karfi yayi ba amma dai sun ji shi, niyyar sa ya wuce daki amma ganin idon su akansa yasa ya dawo da baya ya zauna daga dan gefe ya yi irin zaman rakumi kansa a kasa yana kokarin danne komai. Maganar Rauda sukeyi ya shigo hakan ya k'ara yi wa Hajiya Mero dadi
"Ya ake ciki kai da Rauda?"
Muryar Alhaji ta daki dodon kunnen sa.
"Mun gama ai."
Ya amsa dan har ga Allah baya son ko sunan ta yaji balle wani abu da ya dangance ta, idan sun ga dama su dauko ta su auro masa ita a gobe ma ba sai jibi ba shi bashi da wata damuwa balle yanzu da wannan abin ya kunno kai,
"Magana fa nake ma"
Dagowa yayi da sauri dan be ji me aka ce masa ba ya tafi tunani
"Cewa nayi kun game me? Ko kana nufin kun sasanta kanku?"
"Eh." Ya amsa kai tsaye.
"Masha Allah, wannan labari yayi min dad'i, kinji yaran naki Hajiya ashe sun hade kansu har muna tunanin kar suki."
"Wallahi fa, dama ita Rauda tuni na gama gano ta, ta riga ta amince dari bisa dari kunya ce kawai irin ta ta."
"Kunya?" Ya fad'a a zuciyar sa, gaskia an cuci kunya wallahi.
Dariyar farin ciki Alhaji yayi ya sake kishingid'a yana mike ƙafafuwan sa, matsa masa kafar ta shiga yi cike da kissa,
"Zan iya tafiya?" Arkel da ya kagu ya bar wajen yayi maganar.
"Sarkin daki, ina Sarkin falo kuma?"
Da Sauri ya kalli Alhaji, shi din ma kallon sa yayi dan be yi tunanin maganar zata fito mishi ba, hankali tashe Hajiya Mero ta dago ita ma jin abinda Alhajin yace,
"Kana tuna shi dama?" Idon sa ya cicciko yayi maganar, kauda kai Alhaji yayi kawai ba tare da ya ce komai ba, ya zai ya manta da shi? Akwai mutumin da zai ce ya manta da d'an sa kuwa duk duniya? Kawai dai ya rasa dalilin da ko zancen sa baya so ayi masa.
Girgiza kai Arkel yayi ya mik'e kawai, har zai tafi sai ya dawo a hankali yace
"Na gano in da yake."
Wata irin zabura Hajiya Mero tayi kofin da Alhaji ya gama shan Lipton ta bige da hannun ta ragowar ya zube akan carpet, kallon ta sukayi dukkan su suna mamakin abinda ya sata wannan firgicin, saurin waskewa tayi tace
"Me kace? Kaga kasa na kasa zama sosai saboda zumud'i."
Kin magana yayi ya bar wajen kawai, kallon Alhaji tayi taga yana kallon wani wajen daban, cikin tararradin amsar da zata tarar tace
"Kaji kuwa me yace? Ko kunne na ke min gizo?"
"Bana son maganar nan dan Allah."
Ajiyar zuciya ta sauke da karfi har sai da ya sake dubanta, mikewa tayi tana kwala kiran Sadiya ta shiga daki a zuwan abu zata dauko.
Tana shigewa ya tashi ya fara zagaye a tsakiyar falon, duk yadda yaso yayi tunanin maganar sai yaji ya kasa, sai yaji kamar ana hanashi tunanin su, dakin ya kura wa ido yana tuno dad'ewar da yayi be shiga ba, kamar ana fizgoshi baya ya dau hanyar dakin yana wasi-wasi, murd'a handle din yayi yaji kamar an turo shi baya, daidai lokacin Hajiya Mero ta fito hannun ta dauke da kwalbar turaren wuta, ganin shi a kofar dakin ba karamin kadawa cikin ta yayi ba, da wani irin sauri da bata san tana dashi ba ta isa kofar tasa hannu sai ji yayi an riko rigar sa, kallon ta yayi kawai ya saki handle din,
"Kana so ka ganta ne?" Tayi masa tambayar tana kallon cikin idon sa, girgiza mata kai yayi ya juya kawai ba tare da ya shiga ba..
Wata wawuyar ajiyar zuciya ta sake sauke wa a karo na uku, dire kwalbar tayi a jikin wajen ta juya da sauri tabi bayan sa, kafin taje har ya rufe kofar dakin, hannu biyu tasa ta rik'e kanta, idan komai ya bayyana fa?" Ta shiga tambayar kanta, babu abinda zai faru, dayar zuciyar ta ta ta sanar da ita
***
Wajen karfe biyu ya rasa abinda yake damun sa, wayar sa dake gefen sa tana ta haske alamun akwai sako a kan wayar, bashi da zarafin dubawa dan baki daya kuzarin sa ya tafi wajen matsanancin tunanin da ya sawa kansa, duk yadda yaso ya gano dalilin da yasa ya tafi ya barsu ya kasa samun ko da kwakkwara guda daya, tunanin rayuwar su ta baya da yadda suka gina komai yasa yake jin lallai akwai wani babban al'amari da yasa shi yin haka.
Da safe a makare ya tashi saboda ya raba dare yana tunanin mafita, babu wani abu da yasan ya cimma na nasara a tunanin nasa shi yasa ma ya hakuri ya kwanta dan ya ga alamun zai iya kai asubah be samo bakin zaren ba, abu daya ya sani shine dole zai yi bincike ya gano garin da yake zaune, idan ya samu wannan komai me sauki ne, hakan kuma ba zai yi wuya ba tun da har ya iya bayyana fuskar sa a gidan Tv.
Sharce kansa yake a gaban mudubi ya kurawa fuskar sa ido, gani yayi yayi zuru zuri da shi kamar wanda ya kwanta jinya, dan sakin ransa yayi yana cigaba da kallon kan nasa, so yake ya hango abin tsoron da yar rainin hankalin chan tace, shi yasan daidai yake abubuwan sa amma ya rasa dalilin da yasa yake yawan tunawa da maganar ta mafi akasarin lokuta, share wa yayi ya bude wardrobe d'in sa ya ciro shud'iyar riga long sleeve da baƙin jeans, yana balle botir ɗin karshe wayar sa ta hau vibration, da sauri ya dauka ganin number Kamal mijin Ya Nabila,
"Owk gani nan."Abinda yace kenan ya zura takalmin sa ya fito, Zee na zaune a falon ta sauko tayi saurin sakin murmushi, mai da mata yayi da murmushin duk da ba wai yana da walwala bane sai dan tausayin data ke bashi, har waje ta rakashi ba maganar breakfast ya fice da sauri.
A office din sa suka hadu nan branch na NTA dake kano, yana zuwa suka shiga mota suka nufi unguwar danladi na sidi, a hanya yake fada masa jiya ya kira abokin nasa da sukayi aiki tare ya koma channel kuma ya bashi tabbacin cewa shine kuma yana Cross river yanzu ma address din sa zasu je su karba a wajen wani abokin aikin sa zai kuma iya barin Kano a yau shi yasa ma suke sauri.
Rufe gidan yayi kenan yana mai da dan mukullin cikin yar karamar jakar sa ta matafiya suka riske shi. Ido ya zura wa Arkel cike da mamakin ganin sa nan bayan ya baro shi a Chan, duk da dama ya taba fada mishi dan asalin Kano ne shi amma beyi tunanin ganin sa ba, be bar mamaki ba sai da suka ƙaraso wajen sa.
Rike ha'ba yayi yace:
"Man yaushe kazo Kano bayan na baro ka CR?
Dariyar yak'e Arkel yayi dan ya gane in da zancen ya dosa, kamal ne ya fara miƙa masa hannu suka yi musabah sannan Arkel ma ya bashi. Jikin motar su suka matsa Kamal yace
"Kar dai tafiya zakayi muka tsaidaka?"
"No ba komai, zamu iya magana ai akwai sauran lokaci."
"Owk mun gode, Please alfarma muke so wajen ka, wannan da ka gani twin brother d'in wanda ka sani ne, be shi d'in bane."
"Are You Serious?" Ya fad'a yana xaro ido dan idan ba yaga girman Kamal ba zai iya cewa karya yake.
Dariya Kamal yayi yace
"Gaskiyar kenan, twins ne wannan Muhammad Arkel sunan sa, wanda ka sani kuma Muhammad Arab."
"Ikon Allah."
"Abun da ya kawo mu shine number Arab, ka taimaka ka bamu number sa muna so mu kai masa ziyara gashi mun yi loosing contact din sa, tsohuwar number sa kuma ta daina shiga, kaga tafiya ba zata yiwu babu number ba, gashi irin suprise visit muke so muyi masa, ba ma so ya sani sai yafi murna."
"Haka ne, tare muke dashi ai a wajen aiki, yana da kirki sosai gaskia, dan idan ba dan nasan ba zaku min karya ba ma sai nace shine wannan, bari muga."
Number ya lalubo a wayar ya karanto musu, godia sukayi masa suka tafi, a hanya Arkel ya kasa nutsuwa sai da yayi dialing number, tana ta ringing ba'a daga ba, cigaba da kira yayi ba kakkautawa, Kamal ne ya rik'e wayar yana kokarin sake kira,
"Ka sani ko yana da number ka? He won't answer idan yasan kai ne."
"Me nayi masa?" Ya faɗa cikin Muryar rauni
"Baka yi masa komai ba, mu bi komai a sannu, kar kayi stressing kanka da yawa zamu samu komai a hankali."
Ajiye wayar yayi ya cigaba da tukin sa kawai, a wajen aikin ya ajiye kamal ya wuce.
****
Shara take kunnen ta sakale da waya, magana suke da Hafiz kasa kasa take dariya, shigowar Baba gidan bayan ya tafi yasa ta yi shiru da wayar da take, kiran umma yake ta fito da sauri, daga tsayen ba tare da ya shiga dakin ba yace
"Umaru ne ya tsaidani akan maganar yaran nan, yace min ya riga ya gama shirya komai rana ma zai saka, tare yake so ayi dana Raudatu, toh ni dai nace masa duk yanda ya yanke, sai ki fito da tsohuwar ajiyar ki dan nan kusa za'ayi komai."
Ya kasashe cikin zolaya, shiru umma tayi bata ce komai ba, ya riga ya san ba zata ce d'in ba kuma, juyawa yayi ya fice daga gidan.
Gaba daya sai sharar ta fita akan ta, kasa k'arasa wa tayi ta ajiye tsintsiyar ta shige daki da sauri, umma bata kulata ba ita ma tana bukatar tunani, dama tasan haka za'ayi kuma ita shine kwanciyar hankalin ta, karatun daidai gwargwado ai an same shi, auren shine mutuncin mace. Daki ta koma ta kira Anty Maryam ta sanar da ita abinda yake faruwa.
***
Kallon shi Hajiya Mama take har ya kai aya, wata uwar harara take watsa masa tana girgiza kafa
"Ka gama?" Tace tana kallon sa
"Na gama Hajiya." Ya fada cike da ladabi
"A wanne dalili zaka hada mana biki da wadanchan mutanen?".
"Yaya Garba ne fa Hajiya."
"Yaya Garban! Kanin uban ka ne ko na uwar ka?"
"Allah ya baki hakuri Hajiya,Allah ya huci zuciyar ki, nayi ne dan karfafa zumunci kawai, bansan zai bata miki rai ba."
"Toh naji."
"Allah ya huci zuciyar ki."
"Amin." Ta amsa tana kauda kai gefe
Tashi yayi ya gyara babbar rigar sa, Rauda ya kwala wa kira ta fito da sauri, daga gefe ta tsugunna tace
"Gani Abba."
"Na riga nayi magana da mahaifin yaron, sati hudu na saka tun da kun riga kun gama daidai ta kanku, sai dai babu lefe, babu laifi idan yayi miki ya ajiye idan kika je gidan sa ya baki, amma ban yarda a kawo min nan ba."
Baki sake Hajiya Mama take kallon sa, wani salon wulakanci ne wannan ko me? Dan wadanchan matsiyatan zasu auri matsiyaci kamar su sai a hana jikar ta wataya wa, ta san halin shi sarai yayi hakan ne saboda su, kar a kawo lefen aga nata kamar na kaza, dan a yadda taji labari yaron bashi da komai sai garari kawai yake a gari da sunan bige bige.
"Hajiya mun fita ayi mana addu'a."
"Allah ya bada sa'a."
Yana jin yadda ta amsa ɗin yasan bata ji dadin abinda yace ba, sai dai dole ba zai yadda su wulakanta ba, da Rauda da Maryam duk daya suke a wajen sa babu bambanci, kuma yasan abinda yake yi akan daidai yake.
Yana fita tace wa Rauda
"Kira min H Mero da gaggawa."
***
Hafiz abin dunya ya ishe shi tun bayan da Kawu ya kira ya sanar masa sakon Alhaji Faruku yasa biki wata daya kachal, duk da ya dauke masa babban aikin wato lefe amma ko muhallin da zasu zauna babu, gidan nasu daki daya ne felle sai nasa dake zauren gidan, ga Inna ga Suwaiba da babu alamar tashin ta nan kusa.
Yana kwance inna ta budo labulen dakin nasa, cire kansa yayi da k'yar ya kalle ta cikin mugun ciwon kai da yake ji kamar zai rabe biyu,
"Maganar da Kawun ku ya fada ce ta kwantar da kai wai?"
"Ita ce inna, bansan ya zanyi ba wallahi, gashi ina son ta, wata daya yayi min kadan Inna, son samu asa kamar shekara daya, zuwa lokacin na nemi kudi na karbo result d'ina a Sa'adatu Rimi, kinga ko teaching sai na nema."
"Toh sannu, da yake jiran ka zasu tsaya yi ko?"
"Amma inna ai yayi wuri, shi in ya shirya ni ai ban shirya ba, sai a duba ni fisabilillah"
"Kasan baka shirya ba ka tura kawun ku? Ko shawara bakayi dani ba sai ganin sa nayi, shiyasa babu ruwana in kana son Yar su toh, ga dakin nan naka ai zaku iya zama a ciki."
"Nan dakin kuma Inna?"
"Toh ba aure kake so ba?"
Shiru yayi dan ya gano Inna so take ta nuna masa kuskuren sa nakin shawara da ita, shi dai yanzu ba wannan yake bukata ba, yadda zai gama komai cikin wata daya kachal shine kawai.
Sakin labulen tayi ta shige ciki ta barshi da karantun wasikar jaki, rashin mafita yasa ya tashi ya fice daga gidan
***
Allah sarki Malam Hafizu, rashin kuɗi be ba wallahi, Allah ya bamu me albarka, talauci ba dadi😔.
Duk wanda ya karanta page din Nan Allah ya sa yana daga filon barcin sa yaga kudi dumus😂😂🤣
Akwai runguntsumi a gaba, har yanzu bamu shiga ainihin labarin ba, masu magana sun ce slow and steady win da race, a hankali zamu zo in da muke son zuwa.
****
_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A HALIN YANZU😁._
*ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma
*SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano)
*KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo)
*BURI ƊAYA!* (Mamu gee)
*WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull)
👇🏻karku bari ayi babuku
*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*
*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*
Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank
Saika tura shaidar biya ga wannan number ta WhatsApp
08030811300
Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN ta wannan number din
07067124863
Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.
*Karki bari ayi babu ke, Abari ya huce shike kawo rabon
Rano🚴🚴🚴
*SAUYIN K'ADDARA*
*9-10*
©*Hafsat Rano*
*_ZAFAFA BIYAR na kudi ne idan kana son kowanne daga ciki ka nemi Wannan numbers din_*
*08030811300*
*07067124863*
*_Daurin boye_*
_safiyya huguma_
*_Buri daya_*
_mamuhgee_
*_Wutsiyar rakumi_*
_billyn Abdul_
*_Kai min halacci_*
_Miss xoxo_
*_Sauyin kaddara_*
_hafsat rano_
***
A in da suka saba haduwa da Hafiz suka hadu, kallon sa take duk yayi baki ya rame kamar ba shi ba, yanayin fuskar sa kadai zaka kalla ka gane yana cikin matsala gagaruma, cike da tausaya wa take kallon sa, kallon ta yake shima sai yaga ta kara fresh hadda yar kiba, be sake cewa komai ba bayan gaisuwa suka shiga takawa a hankali, yau ce rana ta karshe da za tayi sallama da Arkel Poultry farm, a kofar wajen ya tsaya ganin motar sa a fake a wajen, gefen bencin me gadi ya zauna yana kallon ta
"Ya ka tsaya kuma?" Ta tambaya da mamaki
"Shiga ki fito kawai ina jira."
"Haka mukayi?"
"A ah, hakan dai naga ya dace."
"Shikenan."
Shigewa tayi da sauri cikin nuna jin haushin ta, a tunanin ta zai biyo ta sai taga yayi zaman sa ya
27, January 2025
Rukayya
Good