Showing 21001 words to 24000 words out of 98004 words

Chapter 8 - SAUYIN KADDARA COMPLETE HAUSA NOVEL

06 Jan 2025

11602

a gajiye suke saboda haka basu iya yin komai ba a ranar, kwanciya sukayi suka huta sukayi ordering abinci daga reception din hotel din.

Da safe Arkel ya riga Kamal tashi saboda zumud'i, sai daya shirya tsaf sannan yaje yayi masa knocking, lokacin tashin sa kenan suna waya da Nabila yana kokarin shiga toilet, jallabiyar sa ya zura ya bude masa, kallon sa yayi daga kasa har sama ganin har takalmi da socks ya riga ya saka,

Daga mishi hannu yayi sannan yace

"Bari na shirya baby naga kanin namu har ya shirya a kular min da kids."

"Owk bye." Ya zare wayar, kallon Arkel yayi ya nuna hannun sa

"Bari na shirya Malam S... Auw..." Yayi dariya yana juyawa, dariyar shima yayi kawai ya koma dakin sa.

Address d'in dake kan wayar sa ya kurawa ido yana kallo,  searching location din yayi ya ga komai, Uber ya sake kira musu sukayi amfani da Navigation system suka isa unguwar, kallon kofar gidan Arkel yake jikin sa a sanyaye, dan dukan kafad'ar sa Kamal yayi

"Be brave to face him."

Ajiyar zuciya ya sauke Kamal ya danna Door bell, daidai lokacin yana zaune yana shiryawa, gefen sa wayar sa ce ke fitar da karatun Alkur'ani me girma cikin kira'ar ghamid'i, lokaci zuwa lokaci yana dan duba agogon wayar saboda kar ya makara sosai. Yana jin karar Door bell ya mike yana saka links a hannun rigar sa, a tunanin sa Mustapha ne ya zo dan babu wanda yake zuwa din sai shi, kai tsaye ya isa kofar ya bude da dukkan karfin sa, idon sa ne ya sauka akan shi, yayi saurin ja da baya yana kallon su dukka, kallon shi suke suma musamman Arkel da a take idon sa ya ciko da ruwa.

Da baya da baya ya dinga ja har ya isa tsakiyar falon yana juya bayan sa, kallon Arkel Kamal yayi yayi masa alamar da su shiga, jiki babu k'wari ya saka kafarsa cikin gidan yana jin zuciyar sa na wani irin bugawa da sauri da sauri.

Arab da yayi suman wucin gadi ne ya dawo hayyacin sa, maganganun da kamal keyi ne suka fara shiga kansa a hankali a hankali ya soma fuskantar su, kenan da gaske ne ba wai gizo idon sa keyi masa ba, dan uwan sa, rabin jikin sa ne yau a gaban sa? Wanda kullum da tunanin sa yake kwana yake tashi. Da sauri ya jiyo da niyyar yi masa magana, wani abu me karfi kamar iska ya bigi fuskar sa, a take ya ji ba zai taba iya yi masa magana ba,
Juyawa yayi da sauri ya shige daki, cikin zafin nama Arkel ya bishi Amma kafin ya isa har ya rufe ya murza mukulli.

Dunkule hannu Arkel yayi ya daki bangon dakin, me yake faruwa? Wanne irin abu yayi wa dan uwan sa haka da har zai guje shi, yazo kuma yaki sauraren shi, ji yayi gaba daya duniyar ta tsaya masa chak,

"Me nayi maka ne!!!"ya fada da karfi, shiru Arab yayi yana jin komai amma yaki magana

"Ka manta komai? Shakuwar mu? Komai tare mukeyi, bacci cin abinci sallah karatu? Duk ka ma ta? Kayan mu daya,maganar mu daya,kama daya komai daya,hali ne kawai ya banbanta,duk ka manta?"

"Ban manta ko daya ba." Ya amsa a raunane.

"Then why? Laifin me nayi maka har haka da zaka tsaneni, ka guje mu ni da Ummi, kasan halin da take ciki? Kasan yadda muke rayuwa? Ka tafi ba sallama, bamu ji daga gareka ba, yanzu na zo baka son kayi magana dani, tell me wanne irin laifi ne wannan?"

Shiru babu amsa, dan ja baya yayi daga jikin kofar yace

"Baka da abinda zaka ce ko, na san baka da shi dama, U r so selfish and cruel, kanka kawai ka sani, shikenan, tun da hakan ka zaba, yayi kyau am leaving, karka yi tunanin i ll come back for you, kowa yayi rayuwar sa yadda yake so, ka sani da kai ko babu kai zamu rayu har zuwa lokacin da Allah ya diba mana."

Danne bakin sa Arab yayi kar kukan da yake taso masa ya fito, girgiza kai kawai yake yana sauraron sa, bashi da baki ko fuskar da zai iya fuskantar sa ya fada masa abinda yake son ji, duk abinda yake so ya fad'a ya fada amma ba zai taba yadda su sake haduwa ba balle har ya tuhume shi akan boyayyen al'amari.
Juyawa Arkel yayi idon sa yayi ja sosai be ko kalli kamal ba yace

"Muje kawai."

Kin binsa kamal yayi ya isa kofar yana kiran sunan sa ko zai bude, biris yayi masa sai chan yace

"Idan kun fita ku ja min kofa."

Jiki a sanyaye suka koma masauki, babu wanda yake da karfin gwuiwar yiwa dan uwan sa maganar, haka suka kwana dukkannin su zuciyoyin su babu dad'i, da sassafe Arkel ya shirya yayi wa kamal knocking, janye yake da trolley din sa alamar tafiya zaiyi, da k'yar kamal ya shawo kansa suka kara kwana biyu, a kwana biyun nan kamal yaje gidan Arab yafi sau nawa amma baya samun sa kwata kwata. Haka suka gama zaman su na tsawon kwana uku babu wani abu da ya sauya suka tattaro suka dawo gida.

***
Zama yayi cikin bacin rai, gefe ta samu ta rakube cike da fargaba, a zafafe ya d'ago bayan ya gama kallon ta

"Ashe baki da hankali?!"

"Dan Allah Abba kayi hakuri." Ta fada tana sauke kai kasa, shiru yayi yama rasa me zai ce mata, ya sani sarai ba wai laifin nata ne baki daya ba, Hajiyar su ce babbar me laifi wajen bata ta, ya rasa yadda zaiyi da ita kuma dan an bar kari tun ran zane.

"Tashi ki bani waje mutuniyar banza."

Da sauri ta mike, gyara zaman sa yayi sannan yace

"Kuma Ki tabbata kin tattaro kayan ki kin dawo nan kafin anjima."

Tun da ta fita ya shiga tunani, ya rasa ta ina zai ɓullo wa Hajiyar su akan maganar auren Rauda da yaron, ya riga ya san babu wani abu da Raudan zata aikata sai abinda Hajiya Mero ta ɗora ta akai, a matsayin sa na uba na gari ba zai taba so ayi amfani da yar sa wajen cutar wani ba, tun ranar da yaji maganganun su ya zama bashi da wani sukuni, gani yake idan har ya yarda akayi auren a haka ya cutar da bayin Allah, gashi kuma Hajiya Mama mahaifiyar sa ce, ba zai so su bata ba akan yar da ya Haifa, da shi da yar tashi dukkannin su ikon ta ne, tana da damar da zata saka su ko ta hanasu, tashi yayi yana zagaye a tsakiyar falon ya rasa mafita.

***
Hafiz na kwance a saman yagalgalalliyar katifar sa Inna ta dawo daga Gumel, daga labulen dakin tayi ta tsaya tana kallon sa, sai data dade a tsaye sannan ya san da zuwan ta, mik'ewa yayi da k'yar yace

"Inna... Ashe kin dawo."

"Uhum... Ka sameni a ciki." Gaba tayi ya mike da k'yar ya kuskure bakin sa, vest ce a jikin sa da gajeren wando ya shiga gidan yana bin bango saboda yadda yunwa ke nukurkusar sa, kujerar tsuguno ya jawo ya zauna yana kallon Innar tana kwance kayan data zo dasu, sai data gama gyara komai waje daya sannan ta saka Suwaiba ta kwashe ta kai ciki, daurin gyara me gishiri ta mika masa yayi saurin karba yana washe baki.

"Gyada muka samu Inna."

"Wai ka manta yadda ake sannu da zuwa ne Hafizu?"

Dafe kansa yayi

"Wallahi shaf na manta, Ya hanya?"

"Lafiya lou, duk suna gaishe ka."

"Ina amsawa kuwa."

"Toh dai Hafizu Allah ya yanke ma wahala, na samo maka aiki a gidan mai, aikin matsa mai."

Gyadar da yake kokarin zubawa a bakin sa ya saki yana kallon Innar cikin tsantsar farin ciki

"Da gaske Inna!!?"

"Ina maka wasa ne?" Ta fada tana bata fuska

"Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Allah na gode maka mafita tazo min."

A kaikaice inna ta kalle shi, girgiza kai tayi a ranta tace

"Yaro man kaza."

"Aina ne aikin inna? Yanzu zan tafi ko sai gobe? Na rasa in da zan saka raina ne ma wlhi."

"A Gumel ne."

"Gumel inna?"

"Eh Gumel dai, gobe da safe zaka tafi idan Allah ya kaimu, chan Gumel din ne wani sabon gidan mai da Hajiya Khadija Rano🤪 ta bud'e, kasan yanzu gidajen man ta sun fi na kowa yawa a Kano, toh yanzu ta sake yin sababbi shine har da Gumel din, gidan Hajiya talatu na shiga muke hirar rashin aiki, shine ta hadani da mai gidan ta ashe shine me daukar ma'aikatan a take kuwa ya saka sunan ka, kaji yadda akayi"

"Toh yanzu Inna... Idan na tafi Gumel sai yaushe zan dawo, gashi fa bikin nan ya sake matsowa."

"Kana tunanin zasu baka yar su ne baka da ko sadaki? Toh bikin nan dai ba zai yiwu a yadda suka saka ba, nayi magana ma da kawun ku badamasi zai zo yaje har gida ya sami iyayen nata, a daga bikin idan yaso sai kaje la dan tara wani abu, idan ka dawo sai ayi cikin karfin gwuiwa."

"Zasu yadda kuwa Inna?" Ya fad'a jiki a sanyaye,

"Me zai hana? Yarinyar ma naga karatu kace tanayi ai ko? Toh ba sai ta karasa ba itama cikin kwanciyar hankali."

"Haka ne kuma."

"A'ah... Hakan dole zamuyi, in Kuma ba haka ba da me za'a yi auren? Shekaru da naka zamu hada ko me?"

"Aikuwa."

"Ka je yanzu ka watsa ruwa ga rogo nan na taho dashi, Suwaiba zata dafa sai kaci kaje wajen yarinyar, idan kaje amma karka fada mata komai kai dai kace mata ka samu aiki zaka tafi gobe, idan yaso shi Badamasi yayi musu bayani dan sai sun fi gane wa akan ace ita ta sanar musu."


Ciki da gamsuwa ya aiwatar da abinda Inna ta dora shi, a tsaitsaye ya ci rogon ya nufi gidan su Maryama.

Tana zaune tana tsefe kanta Walid ya shigo gidan da gudu

"Uncle Hafiz yazo."

Da sauri ta dago dan batayi zato ba,kallon Walid tayi da alamun tambaya

"Allah da gaske nake yana waje."

Gefen da umma take tana gyara zogale ta kalla, jiki a sanyaye ta mike ta shiga daki, Hijab ta zura bayan ta tufke gashin nata waje daya ta fito

"Umma zanje wajen Hafiz."

"A dawo lafiya." Kawai tace ta cigaba da aikin ta

A zauren gidan ta same shi ya jingina da bango yana kallon kofar fitowar ta, fuskar sa a sake take dan ya ma manta fushin da yake yi, ajiyar zuciya ta sauke ta k'arasa, yadda yake kallon ta ne yasa ta ɗan ji kunya ta tsaya da nesa dashi tana wasa da gefen hijabin ta

"Ina wuni?"

"Lafiya lou, ya kika tsaya nan wai? Ki ƙaraso mana ko ba'a maraba dani ne?"

Dan matsowa tayi kadan ta tsaya ba tare da tace komai ba, ya gane sarai fushi take dashi

"Na samu aiki." Ya faɗa kai tsaye dan yasan shine kadai abinda zai wanke shi a wajen ta.

Da sauri tace

"Dan Allah!?"

"Da gaske."

"Kai masha Allah, Alhamdulillah amma wlhi nayi maka murna sosai, alhamdulillah."

"Kamar ya kinyi mun murna?auw ban da ke?" Yayi saurin fassara ta, da sauri tace

"Wallahi ba wani abu nake nufi ba, toh nayi mana murna Alhamdulillah."

Dariya yasa kawai ta kalle shi tana mamakin hali irin nasa, daga abu kadan sai ya fassara mutum bayan ba haka take nufi ba.

Hira suka cigaba da yi hakan ya mantar da su fushin da suke yi, ko da magriba tayi ma sallah kawai yaje yayi ya sake dawowa suka cigaba da wata hirar sai wajen takwas sannan ya tafi shima saboda Alhaji Faruku baya gida ranar amma da in ya gansu sai yayi fad'a.

washe gari Hafiz ya shirya ya nufi Gumel cike da daukin sabon aikin sa, yana tafiya Kawu Badamasi ya duro gidan, inna ce ta kimtsa masa abinda zai je ya sanar, abokin sa guda daya ya kirawo yayi masa rakiya har wajen Alhaji Faruku.

Da mutunci ya karbe su musamman lokacin da suka zo tambayar auren Hafiz ya gane Badamasin, ruwa da lemo yasa aka kawo musu suka sha kafin yaji abinda yake tafe dasu.

****
Bayan sati daya

Abun duniya ya taro yayi wa Maryam yawa, gaba daya Hafiz ya rufe ta, idan ta kirashi baya dagawa, duk sanda taso tayi wa Umma maganar sai ta kasa, ranar dai data gaji ta shirya ta tafi gidan anty Maryam saboda dai dole ta sanar ko dan asan halin da suke ciki, ga biki ya matso ana ta shirye shirye,

Hankalin Anty Maryam ya tashi ta sako ta a gaba suka dawo gidan, Umma suka sanar wa abinda yake faruwa, sosai hankalin ta ya tashi ita ma ta shige neman layin Baba, abinda yake faruwa ta fada masa yace suyi hakuri ya dawo gidan.

Da wuri kuwa ranar ya baro shago ya dawo gida, yan tambayoyi yayi wa Maryam ɗin kafin ya kira Alhaji Faruku ya sanar dashi komai, be ce komai ba shima yace zai ƙaraso gidan yana hanya.

Ko da ya dawo sai yaki shigowa kamar yadda yace, zama yayi yasa matar sa ta kira masa Rauda, kallon ta yayi kawai yana tunanin abinda yake shirin aikatawa

"Rauda!" Ya kira sunan ta

"Na'am Abba."

"Ki fada min tsakanin ki da Allah, kina son yaron nan ko ba kya son shi, tsakanin ki da Allah."

"Bana son shi Abba, kuma ban tsane shi ba." Ta amsa masa kai tsaye

"Me yasa zaki aure shi?"

"Hajiya Mama ce da Mummy suka ce na aure shi, idan na aure shi wai dukkan mu mun huta,shine kawai ya yarda."

Ajiyar zuciya ya sauke yace

"Kinsan aure Rauda?"

Girgiza ai tayi

"A'ah."

"Zaki aure shi ki cutar dashi da mahaifiyar sa ko? Haka ne ko ba haka bane?"

"Mahaifiyar sa kuma Abba?"

"Eh abinda suke so kiyi kenan, aikin da Mero take so kiyi mata kenan da har taki saka yar cikin ta sai ke da ake ganin ki shashasha."

Shiru tayi bata ce komai ba tana tunanin maganar sa

"Kiyi hakuri Rauda, kiyi min biyayya wannan karon,batun yaron nan a barshi."

Da sauri tace

"Nayi Abba."

"Allah yayi miki albarka."

"Amin." Ta amsa,

"Kina da babbar kyauta, bani number sa zanyi magana dashi."

Number Arkel ta karanto masa ya saka a wayar sa

Tashi tayi ta shige daki hakan yayi wa mahaifiyar ta dadi ta tashi tabi bayan ta da sauri.

Arkel na kwance be dade da farfaɗo wa daga zazzabin da ya kwanta ba bayan dawowar su daga CR yaji wayar sa na ringing, Kamar ba zai daga ba sai kuma ya daga ɗin, jin Muryar babban mutum ne yasa ya mike da sauri yana sake kara wayar

"Ok Tam in sha Allah zanzo yanzu."
Shine abinda kawai yace ya ajiye wayar

Tsam ya mike ya hau shirya wa,samun kansa yayi da ciro wata sabuwar shaddar sa fara kal anyi mata aiki da bakin zare tayi masifar kyau, bakar hula ya dora mata ya fito sosai sai yar ramar da yayi.


Yana driving yana tunanin kiran da Alhaji Faruku yake masa har ya karasa, kallon kofar gidan su Maryam yayi kamar me nazarin abu kafin ya fito ya nufi cikin gidan Hajiya Maman, a harabar wajen ya tarar da Alhaji Faruku yana ganin sa ya fadada fuskar sa, har kasa ya tsuguna ya gaishe shi sannan suka nufi falon sa da yake ajiye bakin sa masu muhimmanci.

A d'arare ya zauna yana karewa falon ido, kafin ya maida hankalin da wajen Alhaji Faruku da yake ta tattauna maganar da yake son fad'a masa.

Da k'yar ya aro jarumta cikin dakiya yace

"Zaka iya auren 'yata (yar wana) Maryam???????

Da sauri Arkel ya d'ago yana kallon shi, wani irin kwarijini yaji yayi masa cikin rawar murya yace.......

"

_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A HALIN YANZU😁._

*ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma
*SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano)
*KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo)
*BURI ƊAYA!* (Mamu gee)
*WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull)

👇🏻karku bari ayi babuku

*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi  daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*

*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*

Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank

Saika tura shaidar biya ga wannan number ta WhatsApp

08030811300

Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN  ta wannan number din

07067124863

Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.

*Karki bari ayi babu ke, Abari ya huce shike kawo rabon

Rano🚴🚴🚴

[3/18, 22:24] Hafsat Rano: *SAUYIN K'ADDARA*

*13-14*
©*Hafsat Rano*

*_ZAFAFA BIYAR na kudi ne idan kana son kowanne daga ciki ka nemi Wannan numbers din_*

*08030811300*
*07067124863*

*_Daurin boye_*
_safiyya huguma_
*_Buri daya_*
_mamuhgee_
*_Wutsiyar rakumi_*
_billyn Abdul_
*_Kai min halacci_*
_Miss xoxo_
*_Sauyin kaddara_*
_hafsat rano_

***
Da sauri Arkel ya d'ago yana kallon shi, wani irin kwarijini yaji yayi masa cikin rawar murya yace.......

"Abba..."

"Karka zurfafa tunani, Maryam da Rauda duk daya ne a wajena, Rauda yar ciki na ce Maryam kuwa yar dan uwana ce, nasan maganar Rauda ce a wajen ka, sai dai ina so ka dau hakan a matsayin wata qaddara me karfin gaske, ka san dai duk bawa na kwarai ba ya iya gujewa qaddarar sa, in Sha Allah zakayi alfahari da ita."

"Haka ne."

"Kaje kayi shawara, kayi tunani me tsawo akai, duk da ni ubane kuma kowanne uba yana so ya aurar da yar sa, sai dai ba zan zama daga cikin mutane masu son kansu ba, hakan da nayi sai ka ga Allah ya fito min da wata hanyar da banyi zato ba."

"Bana bukatar shawara ko tunani akan hakan Abba, na yarda na amince da duk abinda ka yanke."

"A'ah, ba za'ai haka ba, kana da na gaba da kai, dole ka sanar musu su baka shawara."

"A musulunci namiji yana da ikon ya karbar wa kansa aure, bayan haka Abba kai ma a matsayin uba kake a wajena, idan babu damuwa ka bani mintuna goma ina zuwa."

Tashi yayi ya fita yana jin wani karfi da kwarin quiwar aikata abinda zuciyar sa ta tsara masa.
Waya ya ciro a aljihun sa ya kira Kamal, sun dade suna magana sannan ya kashe, Salim ya kira ya sanar dashi abinda yake so yayi masa kafin ya kashe kuma ya kira kanin Alhajin su, shima sun jima suna magana dashi kafin ya ajiye wayar yana sauke ajiyar zuciya, agogon hannun sa ya kalla ya daga kansa sama yana kallon sararin samaniya.

"Ya Allah." Ya furta a hankali sannan ya koma cikin falon, zama yayi yana fuskantar Alhaji Faruku da tun dazu yake jiran shigowar shi.

"Abba... Idan babu damuwa xan auri Maryama a yanzu."

Da sauri Alhaji Faruku ya d'ago ya kalle shi, dan gyara zama yayi yana sake kasa da kanshi dan ba karamin nauyi da kwarijini Alhaji Faruku yake masa ba,

"Ayi

27, January 2025
Rukayya

Good

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login