Showing 27001 words to 30000 words out of 98004 words
da goro dai akansu kake neman fada min magana ko? Toh a ajiye ko almajirai na raba wa, tashi ka koma Allah ya bamu Alkhairi."
Kauda kanta tayi gefe tana yatsine, jiki a sanyaye yace
"Allah ya huci zuciyar ki Hajiya, sai da safe."
"Amin."
Fitowa yayi ya jawo mata kofa, part din sa ya nufa yana ayyana kalar rikicin da Hajiya zatayi idan taji yadda al'amarin ya juye.
***
Tun da ya fita babu wanda yayi magana a cikin su, maganar sa da yayi ce lokacin da suke gaisawa da Alhaji Faruku ke mata yawo akai, idan ba har kuskuren ji tayi ba toh tabbas shine, maganar sa ce toh amma shi kuma? Me hakan ke nufi? Ta cikin mayafin ta ta d'an kalle shi kadan, kansa na k'asa yana danne danne a wayar sa, yawun bakin ta ta hadiye da k'yar ta zaro ido, dukkan hannu tasa ta rik'e saitin zuciyar ta da ke wani irin bugawa da sauri da sauri.
Gyara zaman sa yayi ya kashe wayar ya d'an kalli gefen ta, a takure take ta sadda kanta ƙasa kamar tsohuwar munafuka, samun kansa yayi da sakin murmushi kad'an kafin yace
"Baki iya gaisuwa bane wai?"
Hadiye yawon bakin ta ta sake yi da karfi ta saka hannun ta ta damƙe saman mayafin ta,
"Haka ake karbar ango ne a kauyanku?"
Da sauri ta d'ago idanun su suka sark'e da juna, a saman labbanta ta furta "ango?" Ciki ciki tayi maganar, kallon bakin ta yayi ya gane me take nufi, daga kansa yayi sama yana kallo kafin ya maida kallon sa gareta, d'an bata fuskar sa yayi yace
"Ba zaki gaishe nin ba dai a takaice ko?"
"Ina wuni.?'" ta fada murya a cunkushe, ya k'yale ta ma da abinda yake damun ta zai zo ya k'ara mata da wani, a tunanin ta ma tare aka daura auren da nasu dana Rauda, amma menene dalilin da yasa aka hada su waje daya? Kila Abban yaje kirawo Rauda ne, zuciyar ta ta bata amsa.
Kurawa Tv ido kawai yayi yana ayyana yadda zasu kwashe, suna nan zaune shiru Abba be dawo ba, kallon ta yayi zai yi magana yaga kyankyaso d'an karami ya hau kan mayafin ta, tsam ya mike ya isa wajen ta, kallon shi tayi shima ita yake kallo, ganin kyankyason na neman shigewa jikin ta yasa shi saurin saka hannun sa ya fisge mayafin.
Yarfe shi ya hau yi zatayi magana kyankyason ya fado, da sauri tayi tsalle ta haye saman kujera saboda bala'in tsoron kyankyaso take, dariya ta bashi yadda tayi tsallen kamar wata mage,
"Look at u,matsoratsiya kawai."
Kasa tayi da kanta duk kunya ta kamata, kamshin turaren dake jikin mayafi ya shak'a a hankali ya lumshe idon sa, damƙe mayafin ya sake yi yaki bata ganin yadda ta takure kanta, komawa yayi ya harɗe kafa a saman kujerar sannan ya mika mata
"Zo ki karba Malama."
"Ka kawo min toh, ba zan iya tashi ba." Ta fad'a tana mika hannun ta daga nesa itama, banza yayi mata ya cigaba da kallon tv mayafin na rik'e a hannun sa, so yake ta taso ta karba da kanta.
Gyaran murya Alhaji Faruku yayi hade da sallama, da sauri ya jefa mata mayafin yana sauka k'asa, tana kici-kicin yafawa ya shigo, dauke kai yayi kamar be ga komai ba ya zauna sannan yace su matso, kusa dashi, matsowa sukayi suka sashi a tsakiya, jikin maryam ne ya k'ara sanyi sosai, nasiha ya shiga yi musu me ratsa jiki da zukata, har ya gama babu wanda yayi ko da kwakkwara motsi a cikin su, kuka maryam kawai keyi k'asa-k'asa saboda ta gama fuskantar komai.
Kallon Arkel yayi kafin yace
"Kayi mana alfarma ayi biki zuwa karshen sati sai ta tare, kafin nan kai ma ka gama shirin ka."
"Babu damuwa Abba, duk yadda akayi yayi."
"Toh madallah, Allah yayi muku albarka."
"Amin ya Allah, Allah ya k'ara girma."
Juyawa yayi ya dora hannun sa a saman kanta yace
"Maryama...
"Na' .. am.." Tayi maganar Muryar ta na rawa
"Raka shi wajen yaya."
"Toh Abba."
"Kuje Muhammad."
"Ok tam, nagode Allah ya k'ara girma."
Tashi tayi jikin ta yayi sanyi, tana gaba yana bin ta a baya har suka fita daga gidan, zasu shiga zauren gidan yayi saurin rikota ganin zata shige, kallon ta yayi ya bata fuska
"Muje mana." Tace
"Ki shiga ki ce zan shigo tukunna sai kizo ki tafi dani, ba kai tsaye zan shiga ba ai ko?"
Bata ce komai ba ta shige ciki, wayar sa ya ciro zai kira salim saboda yana so ya kawo masa mota, yana danna wayar ta fito
"Ka shiga wai..." Ta fad'a a ciki ciki. Juyawa tayi yabi bayanta bakin sa dauke da sallama, Umm da Anty Maryam ne a tsakar gidan, hasken nepa ya haske ko ina na tsakar gidan, Walid da Habubu na gefe sai Ahmad dake tsaye a jikin kofar Kitchen.
Kallo ɗaya Anty Maryam tayi masa taji wani irin farin ciki, Allah Allah take su gama gaisawa ya fita, ya dan jima a wajen Baba kafin ya fito yayi musu sallama, hannun Walid ya riko suka fito zauren, walet ɗin sa ya zaro ya ciro dubu biyar ya damka masa.
"Ku sai sweet kaji?"
"An gode." Ya karba yayi ciki.
Yana fita Anty Maryam ta fad'a daki ta sauri, taso ta tayi tace taje ta rakashi, yana tsaye a zauren yana magana da Salim yaji tafiyar ta, dan juyowa yayi ya kalle ta ya cigaba da waya. Tana tsaye tana ta cika tana batsewa har ya gama ya maida wayar aljihun sa.
"Are you not happy?" Ya tanbaya ganin yadda take bata rai, shiru tayi tana jin duk babu dadi, tunanin abinda Hafiz yayi mata take da yadda auren ya kasance, samun kanta tayi da sakin kuka a hankali.
"Gosh... Me nayi miki? Daga tambaya?"
Shiru tayi yace
"Am sorry, kije ciki zan wuce yanzu nima, ina jiran salim ne."
Juyawa tayi ya bita da kallo har ta shige, dan fitowa yayi ganin hasken mota. Mika masa key salim yayi bayan sun gaisa, shiga yayi shima salim ɗin ya shiga ya rage masa hanya, suna zuwa titi yace
"Dan cire min password ɗin wayar ka."
Ba musu Salim ya cire ya mika masa, contact ya shiga yayi searching Maryam, Maryam Siwes yaga yayi saving number, kallon ta yayi ya haddace sannan ya danna delete ya mika masa. Godiya yayi masa ya bude motar ya fita.
***
Hajiya Mero na zaune a daki tana gyara zaman sarkokin ta, so take ta sake musu ma'ajiya me kyau, jin wayar ta na k'ara yasa ta d'an sa hannu ta dauko, ganin sunan Alhaji ne yasa ta daga cike da zumud'i
"Please ki turo Buzu Airport nan da 1hour zan sauka."
"An gama ranka ya dade."
Da sauri ta maida sarkokin waje daya ta fita dan sanar wa buzu, bata zata yau zai dawo ba a tunanin ta ma sai irin jibin nan. Cije bakin ta tayi tana tuno sharadi nan, yanzu da ace kwatsam ya dawo da ya kenan? Ta mutu ta gama yawo
Daki ta koma ta shiga wanka da sauri bayan ta zuba garin maganin, doguwar riga ta zura kawai ta nufi kitchen tana kwalawa Sadiya kira, daga dakin Ummi ta fito ta kalle ta da mamaki
"Uban me kike a ciki?" Ta tsare ta da tambaya dan ta hanasu shiga dakin,
"Kiyi hakuri Hajiya, naga yau duk babu kowa shiyasa na duba na gani."
"Zaki ci ubanki kuwa wallahi zaki bar gidan nan in dai zan sa doka kina karya min."
"Kiyi hakuri wallahi ba zan k'ara ba."
"Wuce muje Kitchen munafuka, yanzu ina da abin yi zan dawo kanki."
Kitchen suka shiga ta saka ta ɗora abinci, tana tsaye har ta gama ta kwashe a food flask, karba tayi ta fita daga kitchen din, a saman dinning ta ɗora masa ta fito da wani kullin ta sake barbadawa, tana rufewa Arkel ya turo kofar ya shigo, da sauri ta maida hannun ta baya, ko kallon in da take be ba ya shige ciki kawai, dakin Ummi ya bude ya shiga yana kallon gadon cike da tausaya wa.
Yana zaune yaji tsayuwar mota a harabar gidan, bude labulen dakin yayi ya hango Alhaji yana fitowa, tashi yayi ya fito falon yayi daidai da shigowar Alhaji, Hajiya Mero ya kalla sannan ya maida kallon sa wajen Alhaji yace
"Sannu da zuwa."
"Yawwa, kaga ka taso ni ban gama abinda nake ba ko?"
Sosa kansa yayi yayi murmushi kad'an, Hajiya Mero data shak'a kadan ta danne zuciyar ta ta karasa wajen sa tana yi masa sannu da zuwa, amsawa yayi ba yabo ba fallasa sannan yace
"Fushi fa nake dake da d'an naki."
"Da mukayi me kuma ya Haj."
"Had'a baki mana, sai ji nayi za'a daura, ko nace an daura, na rasa saurin me akeyi kuma."
"An daura me kuma Alhaji?"
"Karki ce min baki sani ba mana, gashi nan da kike ganin sa ai ango ne, dazu Alhaji karami ya kirani yake fada min, Alhaji Faruku ne ma ya jagoranci daurin auren, shine fa dalilin dawowa ta ba shiri."
Kamar zaurance haka taji maganar, bata fuskanci komai ba hakan yasa tace
"Allah ni fa Alhaji ban fuskanci komai ba fa."
Dariyar kasa kasa Arkel yayi ya harɗe hannun sa kawai yana jin su
"Toh aure dai an daura shi, in ma dai su chan basu sanar miki ba ko kuma dai ya akayi ni ban sani ba wallahi, amma tabbas an daura aure dan ga alawa nan da goro ma Karami ya zuba mana a booth da yake ta wajen sa na fara biyawa kafin na zo gida."
Wucewa yayi ciki tayi saurin kallon Arkel,
"Me Alhaji ke cewa ne wai? An daura auren ku da Rauda kenan ko me?"
"An daura Hajiya..."
Da sauri tace
"Kai Alhamdulillah... "
"Amma fa ba da Rauda ba, da Maryam ne."
Da sauri ta kalle shi, daga kansa yayi cikin son sake gamsar da ita yace
"Sati daya ma yace za'a yi biki sai ta tare, kafin nan zan fara gyaran gida."
Tashi yayi ya haye saman be jira amsar ta ba,
Daurin dankwalin kanta ta cire tayi jifa dashi ta shiga neman wayar ta a cikin kujeru tana ji kamar zata yi hauka.
Nace Kadan kika gani Madam🤪🤣 sai ma mun shigo gidan
***
Daga shi sai singlet da boxer ya kwanta rigingine yana busa sigari, Mustapha dake gefen sa yana rike da remote yana kallon wasan sport, lokaci zuwa lokaci yana juyawa ya kalli shi, hankalin sa sam baya wajen kallon wasan, tunanin gida yake da yan uwan sa, tun ranar da suka zo abubuwan suka sake tabarbare masa, da ya ja baya sosai da shan sigari amma yanzu ya dawo dashi fiye ma da dah din, duk yadda yaso yaji sauki a ran sa abin ya faskara, bashi da sukuni ko kwanciyar hankali sam, rayuwar baki dayan ta yin ta kawai yake babu wani alamun farin ciki a ciki.
Tashi yayi ya wuce toilet, amai ya shiga yi sosai kamar zai fidda komai na cikin sa, cike da tausaya wa Mustapha ke kallon kofar yana mamakin irin matsalar sa, tsawon lokacin da suka dauka tare a garin na Calabar be taba ganin wani abu na jin dadi a tattare dashi ba, a yadda yake abubuwan sa ma baki daya zaka san ya fitar da rai da rayuwar da komai da yake ciki, gani yake bashi da wani sauran amfani a duniyar.
Shi kuwa wane irin abu ya aikata haka?
***
Yar karamar jakar sa ta makaranta ya zuba kayan sa kala biyu, sai zumud'i yake zai zo gida, yan kuɗaɗen sa ya kalla daya tara, wajen matsa mai suke samu suyi rara ko wasu su bar musu chanji, tattare kansu yayi ya tura a cikin jakar sannan ya saba ta ya fito.
Yana sauka daga mota ya wuce farm center, yar karamar waya ya siyo sannan ya nufo gida yana Allah Allah ya isa ya saka sim ya kira Maryam.
_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A HALIN YANZU😁._
*ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma
*SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano)
*KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo)
*BURI ƊAYA!* (Mamu gee)
*WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull)
👇🏻karku bari ayi babuku
*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*
*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*
Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank
Saika tura shaidar biya ga wannan number ta WhatsApp
08030811300
Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN ta wannan number din
07067124863
Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.
*Karki bari ayi babu ke, Abari ya huce shike kawo rabon
Rano🚴🚴🚴
[3/18, 22:24] Hafsat Rano: *SAUYIN K'ADDARA*
*16*
©*Hafsat Rano*
*_ZAFAFA BIYAR na kudi ne idan kana son kowanne daga ciki ka nemi Wannan numbers din_*
*08030811300*
*07067124863*
*_Daurin boye_*
_safiyya huguma_
*_Buri daya_*
_mamuhgee_
*_Wutsiyar rakumi_*
_billyn Abdul_
*_Kai min halacci_*
_Miss xoxo_
*_Sauyin kaddara_*
_hafsat rano_
**
***
A gigice ta d'ago wayar data kusa shigewa cikin kujera, number Hajiya Mama ta kira tana ta Allah Allah a daga, har ta k'araci ringing d'in ta bata d'aga ba, cigaba da kira tayi tana zagaye a tsakiyar falon kamar wata zararriya, sai datayi wajen kira sau goma babu alamun xa'a daga, Rauda ta kira da Sultan dukkan su kamar hadin baki basu daga ba basu kuma biyo kiran ba,
"Wayyo na shiga uku."
Da sauri ta tuno da Zainab,
"Yawwa..." Tace tana danna mata kira, ringing d'aya kuwa ta dauka, da sauri tace
"Ina Hajiya Mama?"
"Suna falo."
"Maza jeki kai mata wayar."
"Mummy ina dan abu ne ki kirata a wayar ta mana."
"Dan ubanki kinje kin kai ko sai na zo na kakkaryaki?"
Ta fad'a a harzuk'e, da sauri ta mike tana kunkuni
"Kullum sai masifa haba dan Allah."
Lank'anji ta tsaya yi tana neman hular ta, sai data gama jan aji da shan kanshi sannan ta fito falon ta mikawa Hajiya Mama wayar
"Mummy ce."
"A daren nan, toh Allah sa lafiya."
"Mero ya akayi?" Ta kara wayar a kunnen ta tana nuna wa Sultan hannu alamar ya rage volume d'in TV
"Na shiga uku Hajiya, abinda na ji gaskia ne ko kuwa?"
"Me kika ji? Me yake faruwa?"
"An daura auren Maryam ne ko kuwa?" Ta tambaya cike da tashin hankali
"An daura mana..."
"Innalillah wa inna ilaihi raji'un., Hajiya garin yaya haka ta faru?"
"Me ya faru? Wai dan sun mata aure ko me? Aini dadi naji an raba auren, baki ji farin cikin da nai ba."
"Amma gaskia yaya Alhaji ya cuce ni, ko nace ya cuce mu Hajiya, kinsan da Arkel aka daura auren? Muna can mun saki baki ashe ya san shirin mu?"
Zumbur Hajiya Mama ta mike ta manta da wani ciwon kafar da ta wuni tanayi,
"Ban fahimce ki ba dai, me kike so kice!?"
"Hajiya yanzu dare yayi, zan shigo gidan da sassafe, zakiji komai, zanzo na sami yaya Alhajin sai ya faɗa min dalilin da yasa yake son yaga bayana, kwata kwata baya kauna ta Hajiya, yafi son wadanchan mutanen akai na, me nayi masa??."
"Kwantar da hankalin ki, Allah ya kaimu goben, idan har da gaske ya kulla auren nan toh kuwa dole ya warware shi, ba zan masa da sauki ba sam sakarcin nasa ya fara isata."
Kallon ta Sultan yayi da sauri,
"Dena kallo na malam."
Dariya yayi kawai a ransa yace
"Hajiya masifa, gobe Abba zai sha ta."
Huci kawai take ta rasa me yake mata dadi, sai data zagaye falon yafi sau nawa, shirun da Alhaji yaji yayi yawa ne yasa ya leko, tana ganin shi tayi saurin daidai ta kanta ta nufi dining da sauri ta kwaso kayan abincin sa ta shirya masa a tsakiyar falon.
***
Daren ranar baccin mutane da yawa ƙalilan ne, Hajiya Mero kuwa bata ko runtsa ba tana Allah Allah gari ya waye. Bangaren Maryam da Arkel ma hakan ce ta kasance, kowanne a cikin su da tunanin yadda al'amarin ya kasance ya kwana.
Shida da yan mintuna ta dira a gidan, a zaune ta samu Hajiya Mama tun da tayi sallar asuba bata tashi daga wajen ba, tana ganin ta ta saki ajiyar zuciya, alawa da goron da ke zube a falon Hajiya Mero ta kalla, hakan ya sake tabbata mata da komai.
Ka'ida sa ce duk asubah duniyar idan yaje sallah ya dawo yana fara zuwa ya gaida mahaifiyar sa, yau ma kamar kullum hakan ce ta kasance, tura kofar yayi a nutse hade da sallama, da mamaki yake kallon Hajiya Mero, babu wanda ya amsa masa sallamar a cikin su, murmushi yayi kawai ya zauna yana gaida Hajiya
"Da wa ka daura auren Maryam?" Maimakon ta amsa gaiswar sai ta jeho masa tambayar
Kai tsaye yace
"Da Muhammad Hajiya."
"Wanne Muhammad?"
"Yaron dai da zai auri Rauda dah, Ashe Maryam ce rabon sa,kinji al'amarin Allah."
"Dakata... Me kake so kace min??"
"Dan Allah Hajiya wannan ba abun tashin hankali bane, da Maryam da Rauda duk daya suke a wajena, ni nayi masa sha'awar Maryaman da yake kuma Allah ya ƙaddara sai kawai hakan ta kasance, mu dauki hakan a matsayin tsarin Allah."
"Hmm..." Kawai tace ta rasa me zatace, cikin bacin rai Hajiya Mero tace
"Amma Yaya ai baka kyauta ba sam, ga wadda ya gani yace yana so sai kuma..."
Daga mata hannu yayi yace
"Ke kika haifi Rauda?"
Hadiye yawon bakin ta tayi ta zaro ido dan bata zata ba, dauke kansa yayi ya bar kallon ta yace
"Karki kara shiga hurumin da ba naki ba, ki tsaya matsayin ki."
"Hajiya nayi laifi kuma na roki alfarma da ki yafe min tun jiya, ki bar komai ki daina sawa kanki damuwa, kin ga dai yanayin da kike ciki, ki daina bari wata chan tana zuwa tana dora miki matsalar ta kina hawa kai."
Da sauri ta kalle shi, idon ta ne ya cicciko tace
"Nice wata chan Yaya? Uwa daya kuwa ai tafi gaban wasa, dama nasan ka tsane ni, saboda ba mahaifin mu daya ba ko? Gani kake ni bare ce."
Kuka ta saka sosai, danne zuciyar sa yayi yace
"Ni ban tsane ki ba, halin ki nake gyamata, ki daina zuwa kina assasa matsala tsakani na ni da mahaifiya ta, shine kawai zamu shirya ni dake."
"Ya Isa..." Hajiya Mama ta katse shi,
"Tun da har kayi abin da kake ganin shine daidai, kaji kawai Allah ya bada sa'a."
Sosai jikin sa yayi sanyi, a haka ya mike kawai ya fita. Ba ya son yadda Mero take zuwa tana juyawa Hajiyar tunani, ko tsofan da Hajiyar tayi bata gani kullum sai ta bullo da abinda zai zama fitina.
"Kika barshi ya tafi Hajiya? Yanzu shikenan aure ya dauro,maimakon ki tilasta masa ya warware."
"Ya zanyi toh ni? Kina jin yadda yake magana, sai mu zuba musu ido kawai."
"Ba zai sabu ba, dole na cimma buri na, dama na sani tun
27, January 2025
Rukayya
Good