Showing 9001 words to 12000 words out of 98004 words

Chapter 4 - SAUYIN KADDARA COMPLETE HAUSA NOVEL

06 Jan 2025

11601

ya amsa yayi gaba, har ya juya ya sake tsaidashi

"Koma ka sanar da Hajiya zaka je in yaso sai ta kira ta sanar musu chan d'in."

A ba yadda zai yi ya amsa da toh,  yana jin kamar ya fasa ihu.

Sai da ya gama uzurin da ya fitar da shi sannan ya shiga contact d'in sa ya lalubo number Zee, tana kwance taga kiran sa ta mike da sauri, tana d'agawa taji yace

"Wacce unguwa ce ma gidan su Hajiya?"

"Salanta?."

"Tambaya kike?"


"A..."

Kit ya kashe wayar sa yana tsaki, juya motar yayi ya koma baya don ya baro hanyar, ya manta ne ma yana wani tunani chan daban, duhun magriba ne yasa ya d'an saki ransa saboda yasan kafa ta dauke, a masallaci kan layin ya tsaya yayi Sallah, sosai yaji dadin karatun limamin dan k'in fita yayi har sai da ya jira aka watse sannan ya k'arasa wajen sa ya gaishe shi.

A wajen masallacin ya ajiye motar sa ya taka a kafa hannayen zube a cikin wandon sa. Kofar gate d'in ya zubawa ido yana kallo, juya kansa yake yana tunanin ta ina zai fara shiga gidan, Sultan ne ya fito da sauri yana gyara hannun rigar sa alamun alwala yayi yana sauri kar ya rasa sallah, yana ganin sa yayi saurin tsaidashi

"Sannu." Ya mik'a masa hannu yana kallon gidan,

"Wajen ta nazo ko zaka yi magana."

"Wa fa?" Sultan Ya tambaya dan be gane kan zancen ba.

Susa kansa yayi yana son tuno sunan, kallon sa Sultan ya sake yi sosai

"Ikon Allah, wallahi ban gane ku ba, ashe Arkel ne."

"Ni ne." Ya fad'a yana yak'i

"Shiga toh mana, ka tsaya anan, rabon ka da gidan nan fa ka dade, ashe zaka gane."

"Uhum."

Kawai yace don be san wacce maganar zai amsa masa a ciki ba, bin bayan sa kawai yayi ciki yana jin kamar ya fasa ihu.

Idar da sallar Hajiya Mama kenan taji maganar Sultan yana ce masa ya shigo, farin ciki ne ya lullube ta mik'e da dukkan saurin ta ta shiga dakin Rauda, tana zaune a gaban mirror tana shafe-shafe

"Tashi tashi maza, gashi nan yazo."

"Haba?" Ta fada da sauri tana mik'ewa

"Me?" Hajiyan ta fad'a tana kallon ta

"Naga kamar ya zo da wuri, ina laifin kamar 8."

"Kin tashi ko sai na make ki?"

Turo baki tayi ta sake gyara kanta ta, Hajiyan ce ta fara fita suka gaisa, sannan ta koma ta turo ta. Gefen kujerar da yake kai ta zauna tana murmushi, saurin dagowa yayi ya watsa mata kallo, far tayi da idon ta hakan ya sake kular dashi.

Surutu ta hau yi masa cike da wayewa, jin ta kawai yake ya ma rasa me zai ce mata, batan ta gaji ba tayi shiru tana kallon sa

"Are You done?"

Ya tambaya yana kallon gefe, mamaki ne ya kamata,

"Are You done?" Ya sake tambaya a karo na biyu,

"Eh." Ta daga kai kawai dan ba karamin haushi maganar ta bata ba, mik'ewa yayi kawai yace

"Kice mata na tafi."

"Wa?" Ta tambaya ranta na sake ɓaci, da hannu ya nuna mata dakin Hajiyar, bin hannun sa tayi da kallo ta gane me yake nufi, kafin tayi magana har yayi gaba, komawa tayi kawai ta zauna a cikin kujerar tana cire dankwalin kanta.

Tsaki yaja bayan ya fito daga gidan, be taba ma ganin mara class ba irin ta, wayar sa ce tayi k'ara ya tsaya cirowa yana sake sakin tsaki sau ba adadi, daidai lokacin Maryam ta fito daga gida zata shiga gidan Hajiyar Umma ta aiko ta ta gaya mata haihuwar Anty Maryam, tun ranar haihuwar bata dawo gida ba sai yau tayi tunanin ma sun fadawa Hajiyar, sai da ta tambaya sannan Habubu yace mata basu fada ba, fad'a ta hau maryam tace lallai sai ta je ta fad'a mata a lokacin kafin washegari ta shiga.

Jin an fito ne yasa ya d'an haska da hasken dake kan wayar sa, a tunanin ta Sultan ne, dariya tayi ta ce

"Ya Sultan ana nan ana yaudarar ne?"

Jin beyi magana ba yasa ta matsowa sosai, cire wayar yayi daga kunnen sa ya haska ta.

Da mamaki yake kallon ta, me take anan kuma? Ya ayyana a ransa, daidai lokacin wutar kofar gidan ta kawo, da sauri ta matsa baya tana xaro ido.



_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A HALIN YANZU😁._

*ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma
*SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano)
*KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo)
*BURI ƊAYA!* (Mamu gee)
*WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull)

👇🏻karku bari ayi babuku

*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi  daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*

*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*

Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank

Saika tura shaidar biya ga wannan number ta WhatsApp

08030811300

Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN  ta wannan number din

07067124863

Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.

*Karki bari ayi babu ke, Abari ya huce shike kawo rabon wani*🤝🏽🤝🏽🤝🏽
[3/18, 22:22] Hafsat Rano: *SAUYIN K'ADDARA*
*5*

*©HAFSAT RANO*

*®Haske Writers Association 💡*
(Home of expect and perfect writers)

****

"Laaa..."

Kallon da yayi mata ne yasa tayi saurin cewa

"Ina wuni."

"Hello... Ina jinka..."

Gaba yayi kawai tabi shi da harara tana tabe baki

"Bakin ran tsiya."

Gidan ta shiga, bangaren su Sultan ta wuce da shiga ta tarar da umman su tana cin tuwo, zama tayi ta gaishe ta kafin ta sanar mata da sakon umman su, murna tayi sosai tace zata shigo da safe in Sha Allah.

Hajiya Mama na jin tafiyar sa ta fito da sauri taji kanun labari, yanayin data ga Raudan ne yasa ta sha jinin jikin ta, gefe ta zauna tana kallon ta

"Ya kukayi?"

"Gaskiya Hajiya da sake, bashi da mutunci wallahi Allah."

"Toh... Me yace miki ni nake so naji, kar dai korar sa kikayi fa?"

"Allah ni ba zan iya ba, me yake ji da kansa?"

"Ba zaki fada min bane sai na makeki?"

"Saboda wulakanci fa cewa yayi na gama?"

"Sai me?

"Babu fa abinda yace min, sai kace kanya ya barni ina ta zuba, kai da sake wallahi."

"Ke fa ba'a abin arziki dake, shegiyar zuciyar ki ce zata kaiki ta baro ki, ba a hankali ake bin komai ba, a hankali zai saki jikin in kin iya yin ki."

"Ayi masa magana gaskia, ba zan dauka ba ni dai."

Kamar karta shiga wajen Hajiyar sai dai kuma tasan kadan da aikin Umma ta sake dawo da ita, bude kofar tayi suka juya gaba daya, saurin katse maganar ta tayi ta dan bata fuska,

"Ba sallama sai ki fado haka."

"Nayi baku ji bane, ina wuni.?

"Lafiya."

"Umma ce dama tace na fad'a miki Anty Maryam ta haihu, zata shigo gobe."

"Yaushe ta haihun?"

" Ranar juma'a."

"Sai yau za'a fada min, saboda bani da muhimmanci?"

"Ni tace na fad'a miki mantawa nayi ba laifin ta bane."

"Saboda kin raina ni?"

"Ayi hakuri."

Da k'yar ta bud'e baki tace

"Allah ya raya."

***
Wanki ta tashi dashi ranar, bata yi niyyar zuwa aikin ba yau, mamakin yadda Hafiz ya dau fushi da ita take gashi har kwana  kusan uku kenan be sake neman ta ba, sosai abin ya dame ta saboda ba kad'an tayi kewar sa ba. Karatun suratul bakra da ta kunna a wayar ta ne ta tsaya alamun kira, da sauri ta goge hannun ta a jikin gefen zanin ta tana daukar wayar, ganin Hafiz ne ke kiran yasa tayi saurin d'agawa kar ta katse.

"Zaki fita yau kuwa, naga shiru ina ta tsaye fa."

"Kana wajen? Bari na fito toh."

Ba maganar wanka tayi saurin daurayi wanda ta wanke ta shanya, a gurguje ta shirya tayi wa umma karyar supervisor d'in su ne ya kira ta fito, a chan ta hange shi ya jingina da jikin wani shago yana danna waya, ajiyar zuciya ta sauke ta k'arasa wajen sa, daga idon sa yayi yana kallon ta, murmushi yayi mata ta mayar masa.

"Na zata ba zaki fito ba, wai fushi kike dani?"

"Kai dai kake fushi dani."

"Haka dai kika ce, sai ina? Naga kamar kinyi rana da zuqa."

"Ban niyyar zuwa bane ma yau, kai ka fito dani, mu shiga school kawai ko?"

"Muje toh, naga samarin ki na chan."

"Kishi?" Ta fada tana dariya

"Koma mene dai."

***
*MUHAMMAD ARAB*

Kida ne yake tashi sosai a wajen har baka jin maganar dan uwan ka, mata da maza ne cike da wajen kowa da abinda yake, yanayin wajen da shigar su kadai ta isa ta sanar da kai ina ne, babban club ne dake babban birnin na Cross river

Yan mata biyu ne suka nufe shi suna taka rawa kadan kadan, tun da suka taho ya hango su sai dai bashi da niyyar motsawa daga in da yake, hannu daya daga ta mika masa ya kalli hannun ya kauda kansa, bangaren kan nasa ta sake komawa tana sake bashi hannun, a fusace ya tashi, tangal tangal yayi kamar zai fad'i dayar tayi saurin taro shi.

Mustapha dake chan nesa dasu ya hango abinda yake faruwa, da sauri ya taso yazo wajen yana hararar su

"Me haka?"

Ya tambaya yana dank'ara musu harara, hararar suka maida masa a tare ta ja ta suka bar wajen, kama hannun sa yayi kawai ya riko shi jikin sa ganin yadda ya bugu sosai yana kokarin faduwa, matsa musu hanya sukayi ya fita dashi daga wajen gaba daya.

A mota ya saka shi ya koma dayan bangaren yaja suka bar wajen. Gida ya ajiye shi ya wuce yana mamakin abokin nasa

***Bacci ya ke sosai har be san sanda gari ya waye ba, mik'a yayi ya mike ransa a jagule, toilet ya fara shiga ya watsa ruwa cike da k'yamar kansa, zuciyar sa babu dadi ya shirya ya tafi office.

Aiki yake sosai baya ko gajiya, duk abinda zai yi don ya mantar dashi komai kawai yake ba tare da la'akari da halin zai shiga ba, a gajiya ya koma gida likis ya wurgar da komai a tsakiyar falon, sassauta zaman necktie din wuyan sa yayi ya fad'a saman kujera yana dafe da kansa, runtse idon sa yayi yana hango komai kamar alokacin yake faruwa. Saurin dauko wayar sa yayi ya saka #31 a farkon number da zai kira,

Arkel na zaune gaban Ummi yana aiki da system d'in sa, duk motsi kad'an sai ya juya ya kalle ta, kiran da ya shigo wayar sa ya ne yasa shi kura wa wayar ido, private number da ya gani yake sake kallo, ya rasa wanda yake kiran sa da number tsawon wannan lokacin, duk lokacin da ya d'aga baya jin komai sai shashek'ar kuka k'asa-k'asa, ba karamin daure kai abin yake masa ba, yau ma hakan ce ta kasance ya d'aga kawai ya barta a handfree ya cigaba da aikin sa, sai bayan lokaci me tsawo sannan yaji an kashe.

Kasa cigaba da abinda yake yayi kawai ya sauke komai ya kashe computer ya kwantar da kanshi a jikin gadon.

Jin kiran sallah yasa ya fad'a toilet d'in dake manne dakin ya dauro alwala, fitowa yayi yana nad'e hannun rigar sa suka yi kicibis da Zee

"Kana ciki dama?"

"Kinje chan ne?"

"Naje ai baka nan."

"Owk. Sallah."

"Owk."

***
Zuciyar ta fes ta dawo gida dan ba k'aramin hira suka sha da Hafiz ba, kallon da umma ta aika mata ne yasa ta sha jinin jikin ta, bin bango ta fara yi dan tasan akwai magana, umman bata ce mata komai ba ta cigaba da aikin gyaran zogalen da take, sai data ajiye komai ta fito tana so tayi wa umman hira ta kasa samun fuska, har dare umman bata sakar mata fuska ba balle tasan laifin da tayi, gaba daya ta sha jinin jikin ta ta kasa sakewa, sai da umman ta bari su Habubu sun yi bacci sannan ta kira ta dakin ta, zama tayi tana leken fuskar umman, cikin in da in da tace

"Umma ina wuni?"

Dariya umma ta kunshe  ta sake tsare gida sosai kafin tace

"Waye yake bin ki a unguwa kuna yawo.?"

Zaro ido tayi ta dafe kirji

"Umma waya gaya miki?"

"Karya akayi miki? Amsa nake so kin dai san halin mahaifin ku sarai wallahi, bashi da zafi amma akan wannan ranki zai mugun ɓaci."

"Hafiz ne." Ta fad'a tana sunkuyar da kai

Fad'a sosai umma ta hau ta dashi a karshe tace sai ta fad'a wa Baban,tashin hankali sosai ta shiga dan tasan zafin umman ba daga mata zai ba, hakuri sosai ta hau bata da k'yar ta yarda akan ta fad'a masa lallai in har da gaske yake ya turo bata son hauka.

Tana komawa d'aki taga misscals d'in Hafiz d'in, bin kiran tayi ya kashe ya kirata, hira yake mata amma ita sam hankalin ta baya wajen sa, daure wa tayi ta cije da k'yar tace

"Am... Amm.. an ce wai ka turo."

"Na'am."

Ya fad'a cikin tashin hankali dan beyi tunanin hakan kusa ba. Sake maimaita wa tayi yayi shiru yana tunanin rayuwar, yanzu ma shi da mahaifiyar sa da Kanwar sa wani lokacin sai an sha wuya suke ci sau uku a rana, gashi buga bugar da yake ba wani samu ake sosai ba da har zai iya daukar nauyin mace, jin shirun yayi yawa ne yasa tace

"Kayi hakuri kaga hakan shine ya dace."

Da k'yar ya tattara nutsuwar sa waje daya yace

"Shikenan zanyi magana da Inna gobe."

"Karka damu please, kasan tambaya ba wai aure bane, kuzo d'in Baba ya san da kai shine."

"Shikenan Allah ya taymaka mana."

"Amin ."

Kasa k'arasa hirar yayi ya mata sallama. Shiru tayi tana tunanin mafita, tasan dai Hafiz basu dashi, gashi ba wani zurfin ilimi yayi ba saboda halin yau da kullum, kamar tayi kuka haka take ji saboda halin da taji muryar sa kawai tasan akwai matsala, daren ranar haka ta raba shi tana tunanin makomar su.

**
Mustapha ne ya kura masa ido yana kallon sa, kamar k'aramin yaro haka yake kuka sosai, sai da yayi me isar sa sannan ya tashi, cilla masa mukullin mota yayi yace

"Lets go clubbing."

"Amma Man baka ganin rashin dacewar hakan?"

"Kai kaga haka, rayuwa ta bata da amfani kwata-kwata, barni kawai."

"Amma..."

"Bana son ji please, muje kawai am bored."

"Shikenan lets go."

***
Dan Dan, waye wannan kuma? Menene asalin labarin ne wai?

Ga Ummi kuma a gefe, wace Hajiya Mama? Wace Hajiya Mero? Me yake Shirin faruwa da zai zama wata kaddara a rayuwar su? Sauyin ƙaddara!!!

Akwai sarkakiya sosai ko? Muje zuwa komai zai warware. 🚴🚴🚴🚴🚴🚴🚴

#Muhammad Arkel
#Hafiz
#Muhammad Arab
#Maryam
#Rauda
#zainab.

_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A HALIN YANZU😁._

*ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma
*SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano)
*KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo)
*BURI ƊAYA!* (Mamu gee)
*WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull)

👇🏻karku bari ayi babuku

*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi  daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*

*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*

Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank

Saika tura shaidar biya ga wannan number ta WhatsApp

08030811300

Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN  ta wannan number din

07067124863

Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.

*Karki bari ayi babu ke, Abari ya huce shike kawo rabon

Rano🚴🚴🚴
[3/18, 22:23] Hafsat Rano: *S K*
    *6*

*Littafin nan na kudi ne me so ya karanta ya nemi wannan number 08030811300*

***
Tun bayan ajiyar wayar sai ya rasa in da xai saka ransa, wannan shi ake kira ga koshi ga kwanan yunwa, a tsarin sa beyi niyyar aure ba nan kusa,saboda bukatu na yau da kullum haka ya kusan kwana be runtsa ba yana tunanin mafita, da safe ya makara sosai dan har sai da Inna ta leko shi data ji shiru, sai a lokacin ya mike da k'yar idanuwan sa sun kad'a sunyi jajawur kamar gauta, kallo Inna ta bishi tana son gasgata abinda idon ta ya gani, basarwa yayi ya zari buta ya zagaya bayi, yana idar da sallar suwaiba ta shigo kiran sa, ya san sauran maganar, aljihun sa ya laluba ya ciro Naira dari biyu ya mik'a mita, hijab din ta ta zura ta tafi gidan koko, kokon hamsin sigan hamsin ta siyo musu ta hado da kosan d'ari, yana dauraye fuska da hannun sa ta shigo, kallon ta yayi cike da tausaya wa ya cigaba da abinda ya keyi, kayan jikin sa ya bari ya shafa mai ya fito, Inna tana lura dashi bashi da walwala kwata-kwata, gaishe ta yayi yana daga kofa kansa ya kasa yace

'"Bari na fita Inna, naga ma ba ruwa a gidan, in na dawo sai a siya."

"Abinci fa?"

Kallon kwanon shan yayi ya kalli kosan, bashi da yawa su kansu ma ba dole ya ishe su ba

"Kuci kawai Inna, zanci wani abu."

"Kana da kudin ne?"

"Za'a samu in Sha Allah."

D'an jim tayi kafin tace

"Allah ya kiyaye Allah ya tsare."

"Amin." Ya amsa yana mik'ewa, a dawo lafiya Suwaiba tayi masa yayi mata murmushi kawai ya sa kai ya fice yana tunanin in da zai kama.

Kofar famfo gidan kawun su ya sa'be ba tare da ya shirya ba, yaci sa'a kawun na gida yau be fita kasuwa ba yana hutawa, gaisawa sukayi da matar gidan kafin ta sanar ma kawun da zuwan sa. Da fara'a ya karbe shi suka gaisa da tambayar su Inna. Kadan kadan suke d'an taba hira yana ta ayyana ta ina zai fara masa maganar? Ya motsa bakin sa yafi sau hudu yana kasawa har sai da kawun yace

"Akwai magana ne Hafizu?"

Sosa kansa yayi cikin kunya yace

"Dama... dama yarinyar da muke tare ne iyayen ta suka ce na tura magabata na."

"Toh."

"Eh wai daama a san dani ne dai kawai ba auren za'a yi ba."

"Yar ina ce yarinyar?"

"Anan unguwar tamu ne ba nisa."

"Toh..., Shikenan dai, zan zo gida muyi maganar da mahaifiyar taka zuwa gobe in Sha Allah."

"Nagode Allah ya k'ara girma."

"Amin."

"A huta lafiya."

Karka cewa yayi ya ciro gudar dubu a aljihun sa yace

"Ungo a sai wani abun, a gaishe su kafin na shigo."

Hannu biyu yasa ya karba yayi masa godiya ya tafi.

Kayan miya ya tsaya ya siya a gaban layin su da indomie ya kira me ruwa suka tafi gidan tare.

Indomien ya bawa Suwaiba ta dafa mishi ya shige daki dan ranar baya jin sake fita, kwanciyar sa yayi yana tunanin yadda inna zata dauki maganar gobe idan Allah ya kaimu.

Washe gari da wuri Kawu ya duro gidan, tabarma aka baje masa Hafiz naji kamar ya shige kasan gado, haka dai ya daure ya fito ya gaishe shi, har ya mik'e ya dawo da shi yana nuna masa wajen zama

"Zauna ayi a gaban ka."

A gefe ya zauna yana jin wani iri, kora wa Inna bayani yadda sukayi Kawu yayi karshe

27, January 2025
Rukayya

Good

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login