Showing 54001 words to 57000 words out of 98004 words

Chapter 19 - SAUYIN KADDARA COMPLETE HAUSA NOVEL

06 Jan 2025

11619

hayyacin sa, wannan shi ake kira tsaka me wuya, sai yanzu ya tabbatar da Hajiya Mero ba mutuniyar arziki bace, niyyar ta tayi amfani dashi ta cimma wata manufa tata kenan. Ransa ne ya kara baci ganin kira yaki karewa ya daga ya makala ta a kunnen sa

"Kana ina ne wai? Kar fa ka raina mana hankali malam."

A cunkushe yace

"Gani nan zuwa ai ko? Kar ka damen mana."

A tunanin Asi ya zata ya l
Kashe wayar sai kawai ya jefa ta aljihu, Sambo ya kalla ya kwashe da dariya yace

"Shegen yaron nan ba dai izza ba, shiyasa naji dadi zai yi daidai da aikin da muke so, gashi be san rufta shi muke so muyi ba, da zarar ya aikata zamu maida laifin kansa, kai baka san wani rainin wayo ma da mukayi masa ba fa, gidan da suke haya Hajiya ta siye shi sannan ta barmin nasa tsohuwa ta a ciki, shi kuma ta kaishi wani tsohon gidan ta in da take kai mutanen ta da."

"Shegen kai, ashe kana nan kana dukan kan hajjaju,wato har gida ta baka mutumina, yanzu ka maida tsohuwa ciki kenan."

Dariya ya shek'e da ita suka tafa

"Wacce tsohuwa kuma ana zaune kalaou, gyara shi nake so nayi na samu na shek'e aya ta wallahi."

"Shegen sama, ina yin ka wallahi, muje daga can mu jira shi."

Kamar wanda aka dasa haka Hafiz ya tsaya kawai yana jin su, Allah ya taymaka yayi saurin danna recording tun fara maganar tasu, gumi ya sharce yana jin wani zafi na taso masa, wato Allah ne ya soshi dan ba karamin tarko sukayi niyyar dana masa ba kenan. Tashi yayi a gurguje ya shirya ya fito bayan ya kulle gidan ya dau hanyar in da zasu hadu yana ayyana yadda komai zai kasance.

***
A tare suka kalli juna bayan sun zauna a motar, shigar da yayi ba karamin kyau tayi masa ba haka take ayyana wa a ranta, ashe shima hakan ce dan sosai yaga ta sake yi masa kyau ainun gashi a yadda ya lura da ita mace ce me son classy abubuwa tun daga shigar ta idan tayi zaka ga komai yayi matching tun ba yanzu ba ya lura da hakan tun tana gida balle yanzu da ta samu uban kaya masu kyau da tsari, wani irin farin ciki ne yake bin kowacce kofa ta jikin sa ga sanyin Ac da ya hadu da sanyayyen freshner da hadaddun turaren jiki dana kaya da ta hade jikin ta dashi sai ya chakude ya bada wani kalar kamshi na daban da be taba shaƙar irin sa ba, ita ma mutuniyar taku hakan ce ta faru da ita shiyasa ta koma tayi luf a jikin kujerar motar tana sake bude kofofin hancin ta tana shaƙar ni'imattaccen kamshin da zai iya saka ka bacci ba tare da ka sani ba.

* (Jama'a turare Rahma ne, yana cikin main main Abu da yake saka annashuwa da farin ciki by the way ma ai kamshi is part of sunna in ban manta ba, tsafta Rahman ce, tsafta wajibi ce, kamshi yayi, try as much as possible a dinga turara kaya da gida dan ba karamin weapon bane to bring ur man close to u ba tare da ya shirya ba🚴🚴🚴🚴😂 Ghen ghen......na fece, Ohh wait na tuna ma, me son haddadden turare dan ubansu ya nemi *Miss Xoxo* *CEO YERWA* kenan gidan kamshi🤓 amma bata taba ban alakoro ba😂😂🤫🤭🤪)*

A hankali yake driving d'in kamar baya son zuwa saboda yadda yake jin wata iri yar kasala be ki ba su kwana a haka, ganin da gaske abun na neman tabashi yasa ya lalubo hannun ta ya damke a cikin nasa, kashe mata ido ɗaya yayi ganin ya kalle shi. Har suka isa gidan be sakin hannun nata ba yana murzawa a hankali.

Jin tsayuwar mota yasa Yaya Nabila fitowa da sauri, kamal dauke da Amna ya riko hannun Afnan, suna turo gate din suka gansu a tsaye, da sauri Ya Nabila ta karasa tayi hugging din  Maryam tana mata sannu da zuwa, duk kunya ta kama ta ta rasa ina zata saka kanta, haka dai ta daure tana ta yake baki suka shiga ciki. Kamal ne ya bigi kafad'ar Arkel ya kwashe da dariya.

"Ango ango." Yace yana mika mishi Amna dake ta miko hannu ya dauke ta, Maimakon ya gimtse fuska kamar yadda ya saba sai kawai yayi dariya dan sunan angon ba karamin dadi yake masa ba yanzu, ya rasa dalili kuma amma yana jin dadi idan aka kira shi da sunan. Ohh su malam Arqe 😂🤭

"Ashe kana gida." Yace bayan ya zauna

"Ina nan ango,ina zan motsa bayan kace zaka kawo maana amaryar, Madam ma tun dazu take kallon hanya saboda zumud'i."

"Ah lallai, toh gamu dai, me aka shirya mana?"

"Ba zaka ji a baki na ba,amarya ya gida ya komai da komai."

Kanta a kasa ta amsa

"Alhamdulillah."

"Masha Allah, ya hakuri da kanin nawa kuma? Kinsan auta nasan yana nan yana taba miki halin nasa."

Da sauri Arkel ya tabo shi

"Auw wai so kake nayi shiru, kinga wai nayi shiru, Allah idan bakayi wasa ba sai na bata labarin nan."

Jin haka yasa Arkel yayi saurin cewa

"Allah ya baka hakuri Uncle, na tuba wlhi." Gaba daya suka kwashe da dariya har ya Nabila dake jera musu uban kayan kwalam da makulashe,

"Allah Dear ka takura kanina."

"Auw yar haka ce? Toh nima ai ga kanwata nan Maryam sai mu hade kai."

"Ita ma tawa ce ai."

Dariya aka sa gaba daya, sosai gidan ya birgeta dan kamal mutum ne me barkwanci ga fara-faran.

Haka suka sha hira a gidan har wajen goma suna nan kamar ma basu da niyyar tafiya, tun Maryam na kunya har ta sake da yaya Nabila sosai dan daki suka shiga, da suka tashi tafiya ta haɗa mata kaya masu yawa har da yan kayayyakin gyara tayi ta jin kunya da tana mata bayanin yadda ake amfani dasu, haka suka fito sukayi musu sallama suka tafi, hankalin su dukka a kwance yake shiyasa suka shantake saboda Iya talatu yar uwar Alhaji tazo gidan zata kwana biyu kuma a dakin Ummi ta sauka dama chan ita din mutuniyar ta ce sun saba sosai. Tun zuwan Hajiya Mero gidan ne duk kowa ya ja baya da zuwa saboda bata son kowa ya rabi gidan da suka gano haka sai duk suka dauke kafa saboda gudun wulakanci.

***
A yan kwana biyun da yayi yana shan magungunan sa ba karamin sauki yake samu ba, a hankali nauyi da yake ji a zuciyar sa yake raguwa kadan kadan tunanin gida ya fara zuwa masa kadan kadan shima dan ya kasa tasiri ne amma ga dukkan alamu koma menene yana gab da barin kansa,  Mustapha dai yana lura da duk wani chanji kuma yana sanarwa malam shiyasa komai yake tafiya a daidai cikin tsari da ka'ida, ko da yayi shaunin shan maganin da Mustapha ya tuna masa zai dauka yasha dan baya son yayi masa musu ko ya bata masa shiyasa yake bin komai yace.

***
Daga nesa Hafiz ya hango motar, sauka yayi ya taka a kafa fuskar sa cikin wani irin yanayi da ba zaka iya tantance wane iri bane, hannu ya mika musu suka bashi a d'arare ganin yadda ya gimtse fuska kamar be taba dariya ba gashi dama irin giant din nan ne kallo ɗaya zakayi masa kaji ya maka kwarjini musamman idan ransa ya baci.

"Kun tabbata dai sun fito ko?"

Ya tambaya yana fadawa bayan motar

"Hajiya da kanta ta tabbatar mana, kawai zaman jiran dawowar su zamuyi tun da baka zo ba har suka wuce."

Bece komai ba ya kunna yar wayar sa ya makala earpiece yayi kamar baya jin me suke cewa. Gani dare ya soma yi yasa duk suka karaya suka fara tunanin ko ba zasu dawo bane, kiran Hajiya Mero Asi yayi ta sake tabbatar musu da su kara jira sunanan dawowa komai dare dan tasan ba zasu kwana a waje ba. Haka kuwa akayi suna nan a labe sai ga su nan sun shigo layin, face mask Sambo ya ciro ya wurgawa Hafiz, sai da ya fara bin ta da kallo sannan yayi ajiyar zuciya ya dauka ya saka.

Duk a tare suka fito kowa rike da yar karamar bindiga mara harsashi a ciki, wani irin birki Arkel ya taka da ya sa Maryam dagowa da sauri

"Innalillah wa inna ilaihi raji'un." Suka hau furtawa a tare, tsantsar tashin hankali ya rasa ya zai yi, kallon gefe da gefe yayi babu hanyar juyawa gashi baya sun tare, layin tsit baka jin komai sai karar injina dake wasu gidajen dake chan nesa dasu, knocking din glass din sambo yayi Asi kuma ya zagaya ta bangaren Maryam.

"Buɗe malam." Sambo ya fada yana saita bindigar, da sauri ya sauke glass din kasa ya bude motar,

"Fito." Yace masa a dan tsawace, kallon Maryam yayi da ta kankame hannun shi dan har ta fara kuka, ji yayi ya kasa fita,

"Ba zaka fito ba sai na yi maganin ka ne?" Asi ya murde murya yayi maganar yana saita wa sosai akan maryam

"Idan kana so ka ceceta ka fito daga motar nan, idan kuma kayi taurin kai zan saki kunamar bindigar na fasa mata kai."

Da sauri Arkel yace

"Me kuke so? Su waye ku waya turo ko?"

"Tambayar mu kake kenan? Toh uban ka ne ya turo mu, ka fito ko ka tsaya bata mana rai?"

Zai sake magana Sambo yasa hannu ya finciko shi da karfi, ihu maryam ta saka Hafiz yayi saurin sa hannu ya rufe mata baki, jan ya yayi har wajen motar sannan ya buɗe ya sakata ciki, hannun Asi na saman bakin sa dan karma yayi ihu, wajen zaman sa Hafiz ya shiga, ya tada motar bayan ya rufo kofar yadda Maryam ba zata iya budewa ba, ihu take tana bige bige tana rokan sa, wani irin karfi ne ya wa Arkel ya fincike, kan mtar yayi da gudu kafin ya k'arasa Hafiz ya juya da mugun gudu ya fita daga layin, motar dake tsare a bayan ta Arkel ɗin da suka tare kar yayi reverse sambo da Asi suka shiga suka taka ta da gudu suka bi bayan Hafiz saboda ba haka suka tsara ba sam..

Gudu yake baya ko jin kuka da nacin da take yi masa, shi kansa be san in da zai je ba, hanyar ya dauke musu ganin suna bin bayan sa, sai da ya ga ya bace musu sosai kafin ya zare abinda ke fuskar sa. A razane ta ce

"HAFIZ!!!!"


****
NOT EDITED, IGNORE ALL ERRORS.


*29-30* S K
©*Hafsat Rano*

*_ZAFAFA BIYAR na kudi ne idan kana son kowanne daga ciki ka nemi Wannan numbers din_*

*08030811300*
*07067124863*

*_Daurin boye_*
_safiyya huguma_
*_Buri daya_*
_mamuhgee_
*_Wutsiyar rakumi_*
_billyn Abdul_
*_Kai min halacci_*
_Miss xoxo_
*_Sauyin kaddara_*
_Hafsat rano_
31 *ARADDAK NIYUAS*

©ONAR TASFAH

®RAYIB AFAFAZ

🤫🤭😂

***

Gudu yake sosai babu alamun zai tsaya, shi kansa be san in da yake kokarin zuwa ba sai dai abu daya ya sani dole ne ya taimake ta, dole ya nuna wa Hajiya Mero kuskuren da tayi na shiga gonar sa, kukan da take yi ne yake kara taba shi gashi Asi kiran sa yake ba kakkautawa ya rasa yadda zai yi. Ganin bata da niyyar daina kukan ne yasa shi daka mata tsawa da ta saka ta yin shiru da sauri

"Kar na sake jin bakin ki, dame zanji? Mtsw." Yaja dogon tsaki yana gangara wa gefen hanya, karfe 12 ta gota garin yayi shiru sosai babu kowa sai yan tsirarin mutane da suka baro a baya, a saman sitiyarin motar ya dora kansa da yake ji kamar zai rabe masa biyu saboda tunanin mafita, kiran dake jerin gwanon shigowa wayar sa ya kalla ya yanke shawarar d'agawa kawai, a handsfree ya saka ta bayan ya daga,

"Karamin kwaro, me kake tunanin ka aikata? Kana nufin ka lalata komai da muka shirya ko me?"

"Abinda kake zato shine, na riga na gano komai da kuke shirya wa, ya kake tunanin zan goyi bayan ku bayan ni kaina amfani kuka so kuyi dani ku cimma manufar ku."

Dariya sosai Asi yayi har sai da ya dau lokaci me tsawo kafin yace

"Lallai kayi dabara, ashe kasan duk plan din amma ka biye mana, babban kuskure kenan na farko daka aikata, lallai ka taro match ɗin da babu ranar karewar sa, ko ka manta da tsohuwar ka da kanwarka suna karkashin ikon mu ne? Wai har ka manta fa ko? Dadi SOYAYYA hahahaha."

Da sauri HAFIZ ta matso da wayar kunnen sa

"Karka saka kowa nawa a cikin wannan abin, be shafe su ba ya tsaya iya ni da ku, kar ka kuskura kayi musu wani abu wallahi tallahi."

A yadda yayi maganar Asi ya gane a rikice yake sosai, kuma ya tsorata, dariya ya sake kecewa da ita ya kalli Sambo dake gefe yace

"Mu fasa kawai na tuna akwai yar chamas ɗin kanwar sa zatayi daidai da kai mutumi na."

Dariyar shakiyanci suka kwashe da, roko da magiya Hafiz ya hau yi musu amma suka ki sauraran sa karshe ma suka kashe wayar baki daya.

Cikin tsananin tashin hankali ya juya kan motar ya hau titin da zai mai dashi cikin gari, gudu yake yana innalillah wa inna ilaihi raji'un, Maryam kam gaba daya kanta ne ya kulle ta kasa gane in da suka sa gaba, me Hafiz yake nufi? Me kuma suna suke nufi? Idan har abinda taji daidai ne kenan Hafiz taymakan ta yayi kenan, toh amma ya akayi suka fara aiki tare? Bata da amsar, kadan kadan take goge hawayen dake faman sintiri a saman fuskar ta da gaba daya ta sauya saboda tsabar kuka, tausayin kanta da yadda in dan su Umma suka ji labari yadda za su ji kawai takeyi, bata san me yasa ba amma a kasan ranta tana jin kamar da sa hannu Hajiya mero, idan haka ne kuwa to tabbas Hajiya Mero bata cikin jerin mutanen duniya basu hankali, bata ki ba, zata iya sakata a jerin mugayen mutanen bara gurbi masu fuska biyu. Sake takure jikin ta tayi ganin yadda yake gudu da su ko tsoron rayuwar su baya yi, babu wanda yake yi sai kiran layin Suwaiba dake nuna alamun waya take gashi ba bata yi activating call waiting ba balle idan ta gama ta ga misscals ɗin, haka ya cigaba da gwadawa har suka shigo cikin gari sosai still amsar daya ce, ya rasa yadda zai yi, yana son taimakon Maryam sai dai kuma wani sashi na zuciyar sa na tuna masa su waye inna da suwaiba a wajen sa, kallon ta yayi tausayin ta na sake shigar sa, abu daya yake ganin shine kawai mafita shine ya kira mijin ta ya ajiye a wani wajen yazo ya dauke ta shi kuma ya wuce wajen su Inna, baya so sanadiyar sa wani mummunan abin da zai tarwatsa farin cikin Kanwar sa ya faru, ya san ba zasu taba yafe masa ba kuwa idan har gaskiya tayi halin ta.

"Bani number Mijin ki."

Daga sama taji maganar sai bata gane ba, sake kallon ta yayi ganin bata da alamar bashi yace

"Number mijin ki nake so, ya kamata a dan zaman nan ki fuskanci ba cutar dake zan ba, mafita zan neman miki."

"Babu waya a hannu na ai."

"Baki haddace ba?"

Daga mishi kai tayi tana janye kukan dake taso mata, dukan sitiyarin motar yayi da dan karfi ya danna kiran Asi, ringing d'aya ya daga yana kara wayar a kunnen inna

"Tsohuwa yi magana da mara kunyar danki."

"Hafizu, Hafizu, dan girman Allah kayi sauri kazo, kar suyi wa Suwaiba illa dan Allah Hafizu, innalillah wa inna ilaihi raji'un...."

"Inna... "

Warche wayar Asi yayi yasa dariya

"Ka tsaya wajen mace ka bar su anan, toh ai shikenan tun da haka ka zaba, Sambo muje da ita in yaso sai mu bar masa tsohuwar."

"Zan ƙaraso yanzu, ku jirani dan girman Allah."

"Minti nawa?"

"Goma, ko sha biyar."

"Na baka ishirin, Ina jiran ka." Ya kashe wayar yana kallon inna da suwaiba dake takure a gefe.

"Kiyi hakuri bani da ishashen lokacin da zan iya kai ki gida na kuma taimaki mahaifiya ta da kanwata, na miki alkawarin taymaka miki amma kiyi min wannan alfarmar."

Toshe bakin ta tayi jin wani kuka ya taso mata, tayi saurin yin kasa da kanta dan kar ya gani.

Cikin mintunan da basu ga za goma sha shida ba ya karasa unguwar tasu, motar su ya hango  a gefen gidan yayi saurin yin parking,

"Ki zauna a ciki ina zuwa."

Kwantar mata da kujerar yayi baya ya fita bayan ya rage mata glass din yadda iska zata shiga.

***
Kamar zai yi hauka haka yaji, gudu yake yana bin su har suka tsare masa saboda mota da kafa ba abu daya bane, haki yake sosai numfashin sa na neman dauke wa, yanzu ta ina zai fara neman ta? Ya zai yi? Yana kallo aka tafi da ita ya kasa aikata komai. Wanne irin miji zai kira kanshi kenan? Haka ya juyo ya dawo in da ya bar motar sa, wayar ta ya gani a yashe a kasa yayi saurin dauka yana kankamewa, wa zai kira ma? Ya shiga tunani, da sauri ya danna kiran Kamal dan shine kawai mafitar sa, yana zaune yana duba wayar sa yana ganin kiran Arkel yayi saurin d'agawa

"Lafiya?" Yana d'agawa abinda yace kenan, dan duk wanda ya ga kira a irin wannan lokacin ya san babu lafiya, muryar sa a shake chan ciki kamar alamar kuka-kuka yace

"Sun tafi da ita."

Da sauri kamal ya mike,

"Ban gane ba, su waye? Kuma wa?"

Kasa magana yayi saboda yadda numfashin sa ke hawa da sauka, sosai Kamal ya rude ya shiga tambayar sa yana ina, da kyar ya iya bashi amsa ya koma jikin motar yana jingina da kansa. Kuka yake so yayi amma ya kasa, yana nan tsaye ya hango hasken motar kamal, da sauri ya karaso wajen ko kashe motar beyi ba ya fito da sauri yana riko shi

"Ya akayi Arkel? Ina Maryam ɗin me ya faru?"

Tun daga farko ya fada mishi abinda ya faru, kafin ya riko hannun kamal ɗin hawayen da yake makale wa a idon sa ya samu damar fitowa.

"Yanzu ya zamuyi? Ta ina zamu fara neman ta? Abu har cikin unguwa, kuma kace basu taba lafiyar ka ko tata ba?"

"Basu yi mana komai ba, ita ɗin kawai suka dauka, idan kudi suke so ko motar da sai su dauka ai amma why ita? Me yasa?"

"Innalillah wa inna ilaihi raji'un,

27, January 2025
Rukayya

Good

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login