Showing 87001 words to 90000 words out of 98004 words

Chapter 30 - SAUYIN KADDARA COMPLETE HAUSA NOVEL

06 Jan 2025

11624

na gane kuskure na."

Dariya ta saka

"Wai me kyau, banda fasa kai."

"Allah kuwa. My wife."

"Uhum.. Wai dama kana magana haka sosai sosai."

"Kinyi mamaki, anything for you, feel free with me,share all your problem with me I promise zan tsaya miki."

"Nagode sosai."

"Kice kina so na toh."

Rufe fuska tayi da sauri tana dariya. Basu koma da wuri ba sai wajen goma Ummi har ta shiga daki ta kwanta.


***
Tana kwance bata ko iya buɗe idon ta sosai saboda azaba, kwana tayi tana zawo saboda warin bandakin, wasu manyan kuraje ne suka fito mata a gadon bayan ta duk sun ja ruwa babu kyaun gani, tsananin azaba ga yunwa ta haɗar mata, iya kar galabaita ta galabaita bata taba tunanin hakan a tattare da ita ba, a kullum burin ta ta kuntata wa kowa ta raina kowa tana ganin babu me iya takata sai yau ta tabbatar da ita ɗin ba komai bace a wannan sahun. Tana ji aka zo aka bude ta, abinci ya turo mata cikin harshen sa da baya fita sosai yace

"Ka tashi kaci abinci, dan iska kawai."

"Magana nake maka fa? Ka tashi ko sai naci ubanka?"

"Zan tashi wallahi, bani da lafiya ne." Tace cikin raunin murya

"Ka taimaka min zan mutu."

"Ka mutun, kai ka sani."

A tunanin ta zai tausaya mata sai ta ga aka cin haka, sai ji tayi ya kai mata gula a ciki ba shiri ta mike ya tura mata kwanon abincin da kafa

"Maza ka cinye shi."

Tana kallon abincin zuciyar ta ta tashi ta hau amai, dariya ya saka ya juya ya fita ya rufe ta yana jin dadi a ransa.

Satin ta guda tana cin uwar azaba, tayi kuka tayi magiya amma sam basa ko sauraran ta ma, babu alamar sassauci shiyasa ta hakura ta daina rokon su, ta riga ta saddakar ita shikenan ta kare mata, kila ma sai ta mutu zasu fitar da gawar ta.

Da daddare suka shigo mata su uku, saboda tsabar rudewa sai data saki fitsari a wando, toshe hancin su sukayi dukka saboda masifaffen warin da dakin yake, mik'ewa tayi saboda taga yadda suka tunkaro ta, hannun ta daya ya kama ya ingiza ta waje, wani dan corridor ya kai ta ya nuna mata tsintsiya. Da sauri ta dauka jikin ta na bari

"Je ki wanke toilet d'in chan kin cika mana gida da wari, har yanzu baki mutsu ba."

"Wallahi tallahi na nutsu, ka dubi girman Allah ka barni na tafi, wallahi na zan sake shiga rayuwar kowa ba, barin garin ma zan yi wallahi Allah."

"Kinsan da wannan kika yi ta iskanci kika cuci bayin Allah? Kin manta abin da kikayi ko?"

"Na tuna Wallahi ban manta ba."

Daka mata tsawa yayi

"Kin wuce ko sai na kakkaryaki na zubar? Da girman ki da komai shegiya baki kama kanki ba, mu nan wallahi bama tausayin kowa sai mun tabbatar kin ci ubanki sosai da sosai sannan zaki tafi."

"Wuce ki wanko bandakin nan kuma ke zaki dauko ruwa a waje kin cika mana duk kayan ruwan gidan nan."

"Na shiga uku."

Hannu ta ɗora aka zatayi ihu ya bige bakin ta.



***
Zainab na kwance sai jiran Arkel take amma baya dauka, ta rasa yadda zata yi gashi wani irin mahaukacin son sa ya kara sakata a gaba, Rauda sai habaici take mata, sam bata jin dadin zama a gidan Hajiya Maman saboda Rauda, Sultan ne ma suke dan zama suyi hira amma idan baya nan shikenan zata shiga kunci, gashi uwar gayyar gaba daya ta sake birkicewa, surutai kawai takeyi babu magana daya ta kamawa, a haka zaka ganta a nutse a zaune amma idan ta fara sako maka zance sai kaji kamar kayi kuka, shi kuwa Alhaji Faruku ya tattara su dukka ya zubawa sarautar Allah ido, ya san tabbas abinda suka shuka ne zasu girba, shiyasa ya daina takurawa kansa ya cigaba da sabgogin sa kuma be bari hakan ya shafi alakar sa da Baba ba, yadda suka saba tun da haka suka cigaba da zumunci su, shiyasa yayi niyyar duk ranar da za'a tafi Mali toh lallai dashi za'a je.

*** 
Sosai sauki ya samu a gun Hafiz, karo na uku ya sake aran wayar me kula dashi ya saka Number Inna ya sake kiran, cikin sa'a ya samu ta shiga, suna zaune da suwaiba sun dawo Gumel abun duniya yayi mata yawa, duk sanda sukayi waya da Arkel sai yace mata ai ana kan nema in Sha Allah zaa ganshi, Kiran na shigowa tayi hanzarin dauka.

"Assalamu alaikum."

Yace yana kara wayar a kunne

"Hafizu, Hafizu kai ne? Alhamdulillah ya Allah."

"Inna... Ni ne Inna."

"Kana ina? Ina ka shiga ka barmu da fargaba?"

"Ina asibiti inna, asibitin murtala."

"Na shiga uku, me ya faru? Hatsari kukayi?"

"Sai dai kunzo inna, idan kunzo ku kira lambar nan, amma ku bari da safe sai ku taho yanzu yamma tayi."

"Da yau zan tawo ai, hankali na ba zai kwanta ba."

"A ah, kiyi hakuri zuwa goben, ina samun kulawa daidai gwargwado."

A sanyaye tace

"Shikenan Allah ya baka lafiya, Suwaiba na gaishe ka."

"Amin Inna"

"Na bata wayar?"

"A ah Inna, Kinga Kar a cinye kudin ara nayi, tayi hakuri zuwa gobe, idan baku da kudi ki ranta zan biya."

"Shikenan, sai munzo."

Kashe wayar tayi duk sun rikice,

"Kinga kira mun yaron nan Arqe yake ko wa?"

"Kai inna Arkel."

"Yawwa shi, kira na sanar masa an ganshi, ko zai taymaka tun da kin ga bamu da kudi asibiti kuwa dole a charji kudi."

"Gaskiya ne, bari na kira shi."

Kiran shi tayi be daga ba, shine ta tura masa text.

Ya gama yadda zai ɓullo wa Salim dan sanin ainihin gaskiyar sa, jira suke su hadu kawai yayi masa yadda zai masa, gwara ya san a in da zai ajiye shi dan ba zai cigaba da zama dashi in dai ha'intar sa yake ba. Kiran sa yayi a waya yace su hadu bayan sallar magriba a gidan su. Yana ajiye wayar ya ga text ya shigo, har zai share sai ya duba dan ya tuno yayi wa Maryam text dazu batayi masa reply ba, yana budewa yaga Number Inna, karanta text din yayi sai kawai ya juya zuwa asibitin Murtalan maimakon gida da zai je.

***
Manage pls yau dai sai a hankali Please i need ur du'a🤲
[3/18, 22:28] Hafsat Rano: 52 SK

Yana isa asibitin be wani sha wahala ba ya gane bangaren, sosai Hafiz yaji dadin ganin sa ba zato, hira suka dan yi yayi masa maganar abinda ya faru, cike da tausaya wa Arkel din yake sauraron sa, be taba ganin mace kamar Hajiya Mero ba, zata iya komai akan abinda take nema, zuwa yayi ya karbi Bill din komai yaje ya biya ya chanja masa daki sannan ya tafi da nufin zai zo gobe.

Inna ma asubanci sukayi suka zo,  dan bata iya baccin kirki ba, shiyasa ana idar da Sallah gari ya ɗan yi haske suka taho.

***
Kafin ya isa gida har Salim ya riga shi zuwa, ya matsu yaji abinda yasa ka gaba daya Arkel ya sauya masa, babu fuska duk da yana kokarin nuna babu komai amma shi yasan akwai wata a kasa. Yana ganin ya shigo da mota yayi saurin tashi ya isa, shi ya bude masa kofar ya fito ya bashi hannu

"Sannu da zuwa."

"Yawwa, ka ƙaraso kenan."

"Eh tun dazu, na shiga na gaida Ummi shine na fito nan ina shan iska."

"Ok yayi, dan jirani ina zuwa."

Ciki ya shiga, motsin da ya ji a toilet yasa ya murd'a, tana gaban sink ta gama amai kenan, duk ta galabaita, riko ta yayi suka fito yana mata sannu

"Me ya faru kuma?"

"Zuciya ta ce naji tana tashi."

"Haka kawai? Me kika ci?"

"Dan-malele."

"Dan me?! Disgusting, aina kika samu?"

"Sadiya ce tayi min na taho dashi daga school."

"Kin ganki ko? Bana son kina cin irin abubuwan nan gaskiya."

"Huta bari na ga Salim, idan na dawo sai muje asibiti."

"Owk tam."

Har ya juya ta tsai dashi

"Please dear karka masa da zafi, don't be harsh kaji.?"

"Zan kokarta, for you."

"Thank you."

Murmushi yayi ya juya ya jawo mata dakin, ruwa ya dauka yasha sannan ya fito, a in da ya barshi anan ya same shi, zama yayi a gefe ya ciro waya ya kira Arab, yana cikin gidan yace ya fito compound. Tashi yayi ya zura rigar sa ya fito, ganin su tare da Salim yasa ya gane dalilin kiran. Kujerar dake gefen shima ya ja ya zauna suka gaisa kafin Arkel ya kalle su duka yace

"Salim, iya zaman da nayi da kai akwai wani abu dana taba maka da baka ji dadi ba.?"

Kai tsaye yace

"Idan nace akwai nayi karya, babu abun da ka taba yi min."

"Nagode."

"Menene matsalata? Wanne abu ne kake ganin ina yi be dace ba?"

"Babu gaskiya, abu daya na san kanayi yawan fada sosai, shima da ne kuma amma tun da komai ya daidai ta ka daina, amma ko alokacin bana damuwa ko jin haushi, saboda na san wayr kai, nasan matsalar dake sa ka hakan."

"Gaskiya ne wanna."

Arab yace yana bawa Lubna amsa ta chat, ba wani fuskantar zancen nasu yake ba, hankalin sa na chan suna soyewa.

"Akwai abin da na taba boye maka? Akwai abin daya dangance ni da baka san shi ba?"

"Babu shi."

"Amma me yasa na yarda da kai ka ha'ince ni?"

Zubura yayi

"Ha'inci Oga, Subhanallah, wannan wacce iriyar magana ce ?"

"Yadda kaji."

"Ban gane ba wallahi oga, ya za'a yi na ha'ince ka, ka taba duba kudin da ake samu kaga wani abu ya bata? Ko na taba kawo maka cikas a harkar? Wallahi tallahi tsakani na da Allah nake maka komai, duk da ba zance bana samu a karkashin ka ba, amma wallahi tallahi ban taba cutar ka ba, ban taba tunanin cutar ka ba, me yasa zaka ce haka? Ka manta waye ni? Ka manta hali na?"

Kallon sa Arkel yake, ya gaza cewa komai, maganganun sai yawo suke a kunnen sa, ya rasa a wanne bigire zai dauke su ya ajiye su? Me yake shirin faruwa? Waye me gaskiya.?

Maganar Arab ce ta dawo dashi daga tunanin daya tafi,

"Karka damu salim, ina ganin dai wani dan tangarda aka samu da rashin fahimta, kasan dai maganar Hajiya Mero, toh a gaskiya mun samu leakage ne na cewa duk wani sirri kai kake sanar mata dashi, kai ne partner din ta, shiyasa hankalin sa ya tashi, amma ba wai zargin ka yake ba, so yake dai ka fada mana gaskiya."

"Ya Salam. Abinda ya faru kenan? Ta nan ta bullo min? Hmm lallai ma."

"Bari kuji, wallahi tallahi ban taba daukar maganar da mukayi na fada wa wani mutum ba, abu daya na sani ta zo ta same ni akan lallai sai na hada hannu da ita wajen lalata dukiyar ka, da fari ma wasu kudade ta nema na hanata, a lokacin babu irin barazanar da batayi min ba wallahi, ban bata ba na hana ta, shine daga baya tazo akan waccan maganar, Allah ne shaida ta, ban bata goyon baya ba, a lokacin tayi min ikirarin sai ta bata ni a wajen ka, sai ta jawo ka kore ni. Ban dau hakan a matsayin komai ba sai barazana, dan tasan da aikin na dogara, ni kuwa da na yarda da ita gwara na rasa aiki na, wannan shine abinda ya faru a takaice wallahil azim karya take min, so take ta bata ni."

Shiru duk sukayi suna kallon sa

"Ku yarda da ni, wallahi sharri tayi min."

"Arkel, hanya daya ce kawai,bari na kira Abdul ka gani."

Daga mishi kai yayi dan baya jin zai iya magana kuma. Dubawa yayi babu Number a wayar sai a karamar wayar sa dake daki

"Bari na dauko wayata Please."

Zagaye kawai Arkel yake a wajen ya kai nan ya kawo yana fatan Allah yasa ya zama sharrin, zuciyar sa ba zata iya daukar akasin haka ba, shi kanshi Salim ɗin a rud'e yake, ya rasa me ma yake masa dadi a duniya, addu'a yake tayi kawai har Arab ya dawo daga dauko wayar ya kira shi. Handfree ya saka duk suka yi shiru suna sauraran sa

"Oga how far?"

"Oga Arab, komai fine fine kwana biyu?"

"Normal sir, ya ajiya ta? Tayi laushi dai ko?"

"Ah sosai."

"Good, haka nake so, tayi kamar two weeks nan gaba kafin ka sake ta, for now Ina so Kayi mata tambaya ne, amsa kuma muke so ta gaskiya, if she tried to hide the truth kaci ubanta sosai dan Allah."

"An gama, bari na kira Samuel ya fito da ita nan dakin da take babu network."

"Ok Ina jira."

Tana tsugune ta saka kafarta a cikin guiwar ta taji ana bude kofar, abinda ta tsana kenan taji ana budewa saboda tasan ba sauki sai sun ci zalinta, mik'ewa tsaye tayi har ya shigo ya damke ta ya fito da ido, raba ido da dinga yi kamar tsohuwar munafuka har ya kaita. Tana hada ido da oga kwata-kwata ta tsure, ta hau rawar jiki

"Ke...!!!"

Da sauri ta durkusa kaasa

"Kayi hakuri dan girman Allah."

Wata irin dariya ya kece kafin ya bata rai kamar ba shine yayi dariya ba, tana ganin haka ta sake shiga tashin hankali, jiki ta ta ko ina rawa yake kamar mazari

"Me yasa kika yi wa Salim sharri?"

"Eh... Na'am?"

"Eh? Me yayi miki?"

"Umm.. umm dama bashi da kirki..."

"Kee!!!"

Da sauri ta ce

"Wallahi sharrin shedan ne, na rantse da Allah babu ruwan sa."

"Ohh.. sai kika sa yarki tayi mishi sharri kenan ko?"

"Wallahi ba haka bane, ba ta gane kan maganar bane wallahi, ni bana ma sata a abubuwa na saboda bata tare dani, taji muna waya ne ina ga ranar ta zata da shi ne."

"Gaskiya zaki gaya min in ba haka ba yanzu na sa a kawo yar taki nan itama na haɗa ku."

"Toh.. Toh mmm mmm wallahi sharrin shaidan ne."

"Kece ai shaidan ɗin da kanta, kin yi hakan me kinsan zata fada, gaskia baki da kirki wallahi, aikuwa har yanzu baki gama horuwa ba, maida ita ka chanja mata dakin da muke ajiye robbers, batayi hankali ba."

"Wayyo na shiga uku, wallahi na tuba na daina, na shiga uku zan mutu wayyo Allah na."

Jan ta yayi shi kuma ya maida wayar kunnensa

"Kaji komai Oga, matar nan criminal ce ta gaske, ina ganin kuje ku dawo kafin nan ta sake hankali."

"Yadda kayi yayi ai babban Oga, Allah ya baka General na Nigeria Baki daya."

Dariya ya saka

"Amin toh, sak anjima."

Kallon Salim da Arkel yayi ya mike yana zura wayar sa a aljihu,

"Sai ku karasa tattaunawar ni na gama,."

Dariya suka saka a tare ya juya yana daga kafada, sai da yayi gaba sosai sannan ya waiwayo yace

"Baban soyayya, karka manta da auren yar ta daka yi Alk'awari."

Dariya suka saka gaba daya ya cire takalmin sa ya jefe shi dashi, gocewa yayi yana dariya ya shige, a hankali ya furta

"Dan iska."

"Oga zan wuce."

Kallon sa yayi duk babu dadi yace

"Zamuyi waya, I'm sorry."

"Babu damuwa."

***
*Bayan sati biyu*

Kwana biyar visar su ta fito, tafiyar awa biyu da yan mintuna ne zai kaisu kasar ta Mali a jirgi, abinda ya sa ma aka jinkirta tafiyar saboda Maryam ne da aka jira ta gama first trimester din ta, tafiya a jirgi tafi ga me ciki idan ta shiga second trimester, duk shirye shiryen da ya kamata yayi yayi musu har ticket ya siya. A ranar ne kuma yaje asibitin tare da Maryam aka sallami Hafiz in da zai karasa jinya a gida, dan madaidaicin gida aka samu na haya da zasu zauna a ciki bayan da Arkel ya shawo kan inna da kyar ta amince dan ma tana tsananin jin nauyin sa saboda alkhairin sa gare su.

***
Tafiya ce da zata hada bangarori da yawa, bangaren Maryam, Baba, Umma, Habubu, Walid sai Alhaji Faruku. Bangaren su Arkel kuwa Ummi, Arkel, Arab, Alhaji, Nabila, Kamal da yaran su biyu.

Tun safe aka hau shiryawa kowa sai zumud'i yake, snacks akayi a gidan Ummi na tafiya a daren jiya saboda dai yanayi karsu nemi wani abu, kafin sha biyu kowa ya gama shiryawa tsaf, Maryam da Arkel anko sukayi na shadda kalar cheese me matukar kyau da kyalli, mota biyu suka Ummi, Umma, Ya Nabila, Maryam  sai Habubu da Walid suna mota daya Arkel ne yake jan motar, in da motar Arab kuwa shi yake jan Alhaji na gaba sai Baba da Alhaji Faruku da kamal a baya rike da su Amna, suka nufi airport abun sha'awa, suna zuwa basu wani jima ba jirgin su ya daga zuwa kasar ta Mali babban birnin Kasar Bamako a in da nan ne filin hawa da saukar jiragen kasar yake, tafiyar awa biyu da yan mintuna suka isa, Maryam hannun ta yana damke dana mijin ta duk a tsorace take, ko da za'a fito ma sai daya taimaka mata ya rike ta suka fito, Nabila da Kamal sai dariya suka musu su kuwa basu san ma anayi ba wai kunu a wani gida.

***
Babban hotel din garin na Bamako suka sauka saboda su huta gobe su dau hanyar garin na Mande,da la'asar bayan kowa ya huta suka fita zaga gari suka bar manyan a hotel din, ba laifi garin yayi kyau sosai duk da suna da yawan sahara amma ba karamin kayatar dasu yayi ba, sai wajen isha suka dawo masauki. Da daddare bayan kowa ya kwanta Arkel ya kira Maryam a waya, kallon ya Nabila tayi ganin kamar bacci take yasa ta tashi a hankali ta fito, yana tsaye a wajen dakin yana ganin ta ya sauk ajiyar zuciya. Hannun ta ya rike suka sauka gaba daya daga saman, hawa na farko suka koma ya bude dakin suka shiga. Kallon tuhuma take masa ya kanne mata ido ɗaya yana dariya

"Wayo ko?"

"Emana, shikenan sai a wani hada ni da garada ace na kwana,haba ina ai ba zai yiwu ba wallahi."

Dariya tayi tana buɗe baki

"Su Ya Kamal ɗin ne garada, bari ya Nabila ta ji ka."

"Taji mana, ina zan iya, zo ki ji wata magana."

Make kafada tayi ta saka dariya

"Ahaap ai na sani, sai da safe kafin Ummi su tashi da safe su ga bana nan."

Hanyar waje tayi zata fita yayi saurin durowa ya riketa

"Ai wallahi baki isa ba, na riga nayi budget dake, babu in da zaki wallahi, chab mutuwa ma kenan."

Ita dai dariya kawai take masa ganin yadda ya hakikance, babu yadda ta iya da rigimar arkel,dole ta bada kai bayan jan aji da noke-noken da tayi ta gama.

*Asubah ta gari Mr and Mrs M.Arkel😍

Ke kuma Maryam  Kin dai ji me Anty Farida ta fada ranar babu ruwana wallahi nima🤣🤣🚴🚴🚴

[3/18, 22:28] Hafsat Rano: 53 *SAUYIN ƘADDARA*

*HAFSAT RANO*

****
Sanda suka isa Mande dukkan su

27, January 2025
Rukayya

Good

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login