Showing 42001 words to 45000 words out of 98004 words

Chapter 15 - SAUYIN KADDARA COMPLETE HAUSA NOVEL

06 Jan 2025

11611

shine komai na gidan nan, duk wani abu shine akai, banbanci na dashi kenan, he's my only friend Amma shi yana da abokai da yawa, haka muka taso kowa yayi choosing part din sa a University, bayan mun gama karatu dama ni bussiness nake so and anything kiwo, daga nan ne na fara tunanin yadda zan fara, a lokacin shi kuma yana zaune a gida yana jiran aiki tun da shi dama bangaren mass communication yayi."

"Bakar rana ita ce ranar da na tafi anambra, tare muka tafi da Kamal wanda yake auren ta jikin hoton nan (yaya Nabila) har tasha ya rako mu sannan ya dawo gida. Sati biyu mukayi a garin muka dawo gida in da nazo na tarar da Ummi a wani irin hali, babu kowa a gidan, abun da ya kara tayar min da hankali shine ban san in da ya nufa ba, bansan ina zan ganshi ba, ko na kirashi bana samun sa, gashi kwata-kwata Ummi ko magana bata iya yi, daga nan muka hau yawon asibitoci bama nan bama chan, lokaci me tsawo muka dauka ana abu daya babu wani sauki, abubuwan suka taru sukayi min yawa gashi Alhaji ya janye hannun sa baya komai, tun daga nan komai nawa ya chanja, na sake jajircewa a komai, bansan komai ba sai nema, tun lokacin zuwa yanzu take a haka, ban kuma sami amsar da nake nema ba har tsawon wannan lokacin."

Da wayo tasa hannu ta goge hawayen da taji yana neman zubo mata, wani irin tausayi ne ya kamata, lallai idan ban da shi namiji ne da mace ne da ba zai kawo haka ba ma, sake goge kwallar tayi, gani tayi ya taso ya dawo kusa ta ita, hannu yasa ya jawo ta jikin sa ya rungume ta. Wajen minti biyar babu wanda yayi magana sai ajiyar zuciya da yake saukewa Lokaci zuwa lokaci, kamar me rada tace cikin tararradin amsa da zai bata

"Hajiya fa? Tana ina abin ya faru?"

Dora kansa yayi a saman bayanta yana kallon kofa yace

"A sati biyun da bana nan Alhaji ya aure ta, amma bata tare ba sai bayan wata daya da auren."

Shiru tayi bata kuma magana ba, sakin ta yayi ya kwantar da kanshi a jikin kujerar ya jawo ta kusa dashi

"Me yasa nake sanar dake komai? Ban taba maganar nan da wani stranger ba."

Kallon sa tayi bayan ta janye jikinta daga nashi tace

"Nima stranger ce?"

Daga mata kai yayi alamar eh, tashi tayi ta koma dayar kujerar ta kauda kanta gefe, bude ido yayi yana kallon ta da mamaki, haushi taji kome? Jin yaki magana tasa ta mike zata bar dakin yayi saurin tashi ya tsai da ita ta hanyar rikota

"Ina zaki?"

"Zanje daki ne." Ta amsa kai tsaye

"Nan fa? Shima ai daki ne."

"Uhum." Tace kawai ta sake juya da kanta.

"Please ki zauna har a kira sallah, i just need a company."

Shiru tayi kawai tana mamaki be masan me yayi mata ba, wai ita ce stranger hadda ce mata eh, aikuwa wallahi sai ta saka shi maimaita kalmar nan wataran. Share wa tayi ta dawo ta zauna tun da be ma lura da fushin da tayi ba kenan, kansa taji ya dora a saman ƙafafuwan ta ya rufe idon sa. Murmushi kawai tayi dan har yanzu mamaki yake bata, tunawa tayi tace

"Zan iya samun zam-zam Please.?"

"Owk muje mu siyo in anyi sallah."

Wayar ta ce tayi kara, Anty Maryam ta gani da sauri ta daga, a shagwabe tace

"Anty Maryam...."

Daga dayan bangaren Anty Maryam ta saka dariya

"Ke fa kina da shiririta, kuka zaki kome?"

Dariya tayi kawai

"Anty Maryam ina wuni yasu Areef."

"Lafiya lou amarya, ya bakun ta?" Da sauri ta kalle shi, ya bude idon sa ya zuba su akanta, turo baki tayi ta kauda kanta gefe.

"Shine Babu wanda yazo Anty Maryam."

"Shiririta, sai kuma mu debo kafa muzo ko? To sannun ki, kira nayi naji ba matsala dai ko? Kinsan yanayin dai."

"Na'am?"

"Babu wata matsala dai ko? Kiyi amfani da ruwan dumi dai kinji?"

Kasa magana tayi ta hau in-i nah har Anty Maryam ɗin ta d'ago ta, da sauri tace

"Ki gaishe shi toh, zamuyi waya dai." Kafin ma ta kashe ita ta kashe da sauri, dariya yayi sosai dan ya kusa gano in da maganar ta nufa tun da yana jiyo maganar Anty Maryam ɗin sama sama. Yunkurawa tayi zata tashi ya sake matseta yana dariya.

Haka suka zauna har aka kira sallar magriba sannan ya tafi masallaci ita kuma ta koma dakin ta dan shirya wa tun da yace zasu je siyo zam-zam idan anyi sallah.

Yana dawowa bayan an kunna gen ya shigo ya chanja kayansa, kofa ya bude mata ta baya suka fita dan bata ma san da kofar ba sai lokacin.


***
Satin ta daya a gidan tuni ta fara bawa Ummi ruwan zam-zam da take karanta fatiha kafa bakwai a ciki, (zaku iya gwadawa domin ita suratul fatiha waraka ce ga dukkanin wata cuta, a karanta kafa Bakwai a cikin ruwa amma ba wai tofi za'a yi a ciki ba,abinda ake so karatun ya shiga cikin ruwan)

Ba karamin kona ran Hajiya Mero haka ke yi ba, bata so dai tayi saurin fito da komai shi yasa take bin komai a sannu. Tun ranar data kwashe maganin nan da alluran ta kafa ta tsare duk sanda nurse din tazo bata barin ta ita kadai a dakin, bata sanar wa da Arkel komai ba dan ta lura kamar ma be san komai ba shiyasa kawai take komai kai tsaye tana dagewa sosai wajen azkar din safiya da maraice dan shine babban makari ga duk wani abin ki.

Tana zaune a dakin ta kunna karatun Alkur'ani a wayarta yanayi a hankali, nurse ɗin ta shigo, gaisawa sukayi sama-sama ta tsaya kawai ba tare da tayi komai ba, saboda dama a ka'ida goge wa ummin jiki take sai da bata magunguna da allurai shine aikinta, yanzu kuwa kafin tazo ma Maryam tayi komai shi yasa idan tazo sai taga babu abinda zatayi.

Ta dade a tsaye Maryam na kallon ta ta gefe, sannan ta juya ta fita, da sauri ta rufe alkur-anin ta bi bayan ta, dakin Hajiya Mero ta shiga tayi saurin zuwa ta tsaya a kofar.

"Yau ma wai?" Taji ta tambaya

"Eh wallahi, tana dakin karatu ma take, duk ta kankane komai."

"Gaskiya zanci uban yarinyar nan wallahi Allah, shegiya zata bata min aiki."

"Ni wallahi tsoro ma take bani, kamar tasan komai da mukeyi, kinga fa ita ta tattare duk alluran nan babu ko daya yanzu.".

"Kan bala'in chan,alluaran da na sa kudi masu yawa na siyo su, tun yaushe ba'a yi mata ba kenan?" Ta fada a rude

"Wajen sati kenan walalhi, na kasa fada miki ni kiyi hakuri "

Da sauri ta mike

"Har sati?" Amma wallahi kin cuce ni, baki gaya min ba amma, kai amma wallahi ban taba ganin tsinanniya irin ki ba, Allah ya isa ban yafe ba wallahi, kuma sai kin bar gidan nan."

Magiya ta hau yi ta hambare ta tayo waje, turus tayi ganin Maryam a tsaye, kallon kallo sukayi wa juna tayi saurin daidai ta kanta

"Ke kuma fa?" Ta fada a fusace

Kin magana tayi ta juya zata bar wajen tayi saurin riko ta

"Uban me kike a nan? Kinji wani abu ne?"

Girgiza kanta tayi tace

"Banji komai ba, dama so nake na tambaya me za'a dafa da daddare?"

Tsaki taja ta juya ta koma dakin.

Da kyar ta daga kafarta ta bar wajen saboda yadda ta sake tsorata da lamarin hajiya Meron.

Kasa barin dakin Ummin tayi har zuwa lokacin da Arkel ya dawo, rike hannun sa tayi a karo na farko ta jashi har dakin

"Ka zauna zanje na dawo dan Allah."

Zama yayi cikin mamakin dalilin hakan, sharewa yayi ya dauki alkur-anin dake gefen gadon ya fara karantawa.

Sama ta koma bayan ta kawo masa abincin sa dakin,wanka ta shiga a gurguje kafin a kira sallah saboda ta sami tsarki, bata wani tsaya k'alk'ale k'alk'ale ba ta saka gown kawai ta shinfida sallaya tayi sallar la'asar, tana idarwa ta sauko. Da kallo ya bita har ta dauko ruwan zam-zam din ta dan karkata ta zuba mata a baki. Be yi magana ba yana ta kallon ta har ta gama komai ta tofa mata addu'o i.

Tashi yayi ya shiga toilel ɗin dakin yayi alwala, yana fitowa yaga zata bar dakin yayi saurin cewa

"Ina zaki?"

"Sallah zanyi." Ta bashi amsa kai tsaye ba tare da tunanin komai ba.

Wata irin shu'umar dariya yayi irin ta gfen bakin nan ya shafi saman kansa.

Woow ango Arqe😂


***
Yau duk bamu ji ina Malam Hafizu ya shiga ba, gobe gobe zai duro wasan ya fara in Sha Allah.
Nagode sosai da jimirin jira,ido Alhamdulillah ina samun sauki Nagode da adduoin ku. Allah ya saka da Alkhairi.














_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A HALIN YANZU😁._

*ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma
*SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano)
*KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo)
*BURI ƊAYA!* (Mamu gee)
*WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull)

👇🏻karku bari ayi babuku

*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi  daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*

*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*

Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank

Saika tura shaidar biya ga wannan number ta WhatsApp

08030811300

Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN  ta wannan number din

07067124863

Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.

*Karki bari ayi babu ke, Abari ya huce shike kawo rabon

Rano🚴🚴🚴
*24* S K
©*Hafsat Rano*

*_ZAFAFA BIYAR na kudi ne idan kana son kowanne daga ciki ka nemi Wannan numbers din_*

*08030811300*
*07067124863*

*_Daurin boye_*
_safiyya huguma_
*_Buri daya_*
_mamuhgee_
*_Wutsiyar rakumi_*
_billyn Abdul_
*_Kai min halacci_*
_Miss xoxo_
*_Sauyin kaddara_*
_Hafsat rano_

***
Kasa zama tayi saboda yadda abin ya dake ta, bata taɓa tunanin Maryam ɗin ta kai haka ba, kenan magungunan data ɗebe ta san komai akan su shiyasa ma ta dauke din, lallai ta debo ruwan dafa kanta, haukan datayi daya ne ga dukkan alama bata sanar wa uban gayyar ba, hakan ya saka mata nutsuwa har ta fara ƙoƙarin lalubo wayar ta. Ta riga ta shirya komai sanin cewa babu wani abu daya shiga tsakanin su, tana lura da duk wani takunsu shiyasa ma hankalin ta ya kwanta.


Kira tayi ana d'agawa tace

"Ka shirya komai yadda ya dace? Shigar sauri zamuyi mata kafin ta shige mu."

Daga chan dayan bangaren yace

"Na hada komai jira nake gobe tayi, babu yadda za'ai ya ƙaryata report ɗin dan na gasken ne."

"Yawwa hakan nake so, sai dai fa a daren nan nake so a aiwatar da komai, ka sami mutumin ka bashi dubu ashirin sai yazo kawai, ba zan iya jira har gobe ba kar tayi min illah."

"Shikenan Hajjaju. An gama sai kinji bayani."

Ajiye wayar tayi ta cije Lebanta kafin ta bushe da dariya

"Yanzu wasan zai fara, 1,2,3 bom."

Kofar aka buga ta kalla a fusace kafin tace

"Waye."

Zainab ce ta shigo hannun ta rataye da handbag

"Ke kuma? Kin dawo kenan."

Dauke kanta tayi,

"Mummy baki so na dawo bane?"

"Da ni na aike ki?"

Girgiza kai tayi

"Atoh, kinga ba ci ai kin dawo ko? Sai ki wuce dakin ki."

Tashi tayi ta fita tana kallon saman zuciyar ta duk babu dadi.


***
Har wajen goma suna zaune a dakin dan har sallar Isha'i a dakin sukayi ta, jefi jefi suke hada ido duk da aikin da yake a cikin na'ura me k'wak'walwa, a hankali yaga ta soma gyangyadi har tana dan yin baya kamar zata fadi, murmushi yayi ya kalli gefen sa, dan karamin fillo ya dauka ya wurga mata, firgigit tayi tana zaro ido

"Bacci?" Ya tambaya yana lankwasa hannun sa suka bada sauti me dan karfi

"Ba bacci nake ba."

A yadda ta amsa muryar ta kadai ta nuna baccin take amma saboda musu na me bacci sai tace ba bacci take ba, dariya yayi ya hau tattare kayan nasa, gyara Ummi ta hau yi sannan ta tofa mata addu'a yana tsaye ya makala computer a tsakankanin hannun sa yana kallon ta. Sai da ta gama ta gyara mata komai sannan ta dauki wayar ta.

A jere suka fito ya zura mata ido kawai yana aikin kallon ta, dauke kai tayi da suka zo zasu hau step sai ya ja ya tsaya yana kallon ta, tsaya wa tayi ita ma dan bata son tayi gaba yana bayan ta duk sai taji ta kasa tafiyar har wani harhaddewa kafarta keyi.

"Muje ko?" Yace yana gyara tsaiwar sa,

"Dan Allah ka fara tafiya."

Make kafardar sa yayi yana kunce dariyar sa, kamar ta fasa ihu haka ta hau takawa a hankali kamar me koyon tafiya, a baya yake binta yana kallon duk wani takunta har suka dangana da dakin kwanan su, maimakon ya shiga sai ya zarce dayan dakin ya ajiye kayan. Tsaye yayi rike da kugu yana kallon kayan sa da ya ware yake sawa a irin wannan lokacin na zafi, be fiya zama da kaya ba ma yafi zama daga shi sai boxer saboda yadda yake da jin zafi kamar maciji, sai daya dade yana kallon kayan kafin ya zaro wasu fararen riga da wando rigar armless wando kuwa babba ne ya bude sosai ta wajen kafar, kaya ne masu matukar kyau gasu unique dan shi a rayuwar sa yana son komai nasa ya zama ya fita daban shi yasa a komai sai ya tsaya ya dubo abinda yasan zai yi masa. Wanka ya fara yi yana yi yana ayyana komai a ransa, ya sani ba wai auren soyayya sukayi ba sai dai akwai wani al'amari game da ita da yake fusgarshi zuwa gare ta,har ya watsa ruwan ya fito tana cigaba da tunanin, a kasalance ya shirya tsaf ya saka haɗaɗɗun turarukan sa masu sanyin kamshi sannan ya rufo dakin ya fito.

Tana tsaye bayan ta gama karanta text d'in Anty Maryam taji ya shigo, da sauri ta kashe wayar ta juyo tana kallon sa, kallon ta yake shima har ya tako ya iso gaban ta. Zagaye ta yayi ya wuce toilet ba tare da yayi magana ba, da kallo ta bishi har ya shige yana mamakin kayan jikin sa, wandon ne ya bata dariya har taso yi sai kuma taga ya fito.

"Kinyi sallah?" Taji ya wurgo mata tambayar, daga masa kai tayi ya dan yi murmushi sannan yace

"Owk yi alwala sai muyi nafila."

"Owk tam."

Har ta juya sai kuma yace

"Madam..."

Dan juyo wa tayi,

"In zai yiwu ki fara watsa ruwa akwai dan zafi a garin."

Fita yayi ya rufo mata kofar dan dauko wayar sa, yana zuwa yaga an masa misscals da wata bakuwa number, sharewa yayi zai kashe wayar kenan kiran ya sake shigowa, kallon lokaci yayi ya sake kallon kiran, d'agawa yayi ya makala a kunnen sa.

Doguwar riga ya saka a saman kayan nasa ya fito harabar gidan, daga chan kofar gate ya hango su tsaye su uku, buzu ne sai me gadi da mutumin dake tsaye, har ya karasa wajen su be daina mamakin dalilin kiran nasa ba. Ganin shi yasa buzu saurin cewa

"Gashi nan oga, tun dazu muke yi dashi ya nace lallai sai ya ganka, nace ma ya bari zuwa safiya yaki sam, gashi nan bamu san meke tafe dashi ba."

'Dan kallon mutumin yayi kafin ya juya yana cewa

"Dan ƙaraso ciki."

Daga nesa suka tsaya ya harɗe hannun sa yana kallon shi,

"Malam lafiya kuwa? A wannan daren haka."

Dan kallon gefe yayi zuciyar sa na dukan uku uku yace

"Abu ne muhimmi ya kawo ni, ba zan iya bari a kwana ba dan bani ne rike da raina ba."

"Ina jinka." Ya fada yana kallon sa

"Game da matar ka ne, uhum Maryama, toh dama-dama..."

"Dama me?" Ya katse shi yana tattara dukkan hankalin sa.

Ajiya zuciya mutumin yayi kamar zaiyi kuka yace

"Dana likita ne, a halin yanzu Allah yayi masa rasuwa jiya, kafin ya mutu ya sanar dani wani babban al'amari da yake ganin ba zai iya mutuwa ba tare da ya sanar maka ba, yayi kokarin ya neme ka sai kuma ciwo daya kwantar dashi yayi masa kwaf daya toh..."

"Malam!" Ya fada à zafafe

"Ka faɗa min abinda ya kawo ka karka batan lokaci."

Share kwallar data taru a idon sa mutumin yayi ya ciro takarda a aljihun sa ya mika masa

"Ka karanta wannan duk bayanin komai yana ciki, amma dan Allah kayi hakuri da abinda zaka gani."

Da sauri ya warce takardar ya hau budewa,

"Dakata! Dan girman Allah karka bude anan ka shiga ciki saboda abinda zaka gani ba abu ne me sauki ba."

Banza Arkel yayi masa ya bude, ganin haka yasa mutumin juyawa zai bar gidan da sauri ya riko shi

"Tsaye nace!" Ya fada yana karanta abinda yake rubuce a jikin takadar, hannun sa ne ya fara karkarwa idon sa suka fito waje, a take yaji jiri na neman diban sa, kokarin sake karanta saman yake yana son tabbatarwa kansa ba gaskiya bane. Tuni idon sa ya rine zuwa tsananin ja, hankalin mutumin ne yayi mugun tashi ganin yadda lokaci daya ya koma, a matukar bacin rai ya hau kwalawa su buzu kira.
Da gudu suka ƙaraso ya nuna musu mutumin da hannun sa

"Ku saka shi a dakin chan zuwa gobe zan dawo kansa."

Nan fa ake yin ta, kamar zai tashi sama ya shige ciki ko ishasshen ganin hanya baya yi, Hajiya mero dake makale ta kalli shi lokacin da yake hayewa sama, murmushi tayi ta shige dakin ta tana tafa hannu, magana ta hau yi tana dariya.

"Yarinya in kin san wata baki san wata ba wallahi, ba dai ki zauna a gidan nan ba, tsawon shekarun dana dauka ina gina komai baki isa ki rushe ba. Shegiya dangin Mayu, Allah yasa ma ya lakada mata duka ya karya shegiya."

**
A yadda ya budo kofar ne yasa ta tsorata, tsaye take a gaban mirror tana taje kanta, dogon hijabi ne a jikin ta ta sauke shi a gafadar ta, towel ne kawai a ciki dan bata jima da fitowa daga wankan ba.


Kallon rinannun idon sa take da yayi dishi-dishi ga shi yayi wani irin ja ya taru da jini a ciki, tsoro ne ya kamata ta fara ja da baya da baya har ya karaso daf da ita, takardar ya kalla sannan ya nufi wardrobe d'in ta, daya bayan daya ya hau watsi da kayan ciki zuciyar sa na matuƙar harbawa yana tunanin abinda zai gani.

A hankali idon sa ya sauka akan takardar dake ninke a kasan jakar ta, da kyar ya mike hannun sa ya dauko yana jin tashin hankalin sa na daduwa da tunanin abinda zai

27, January 2025
Rukayya

Good

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login