Showing 45001 words to 48000 words out of 98004 words

Chapter 16 - SAUYIN KADDARA COMPLETE HAUSA NOVEL

06 Jan 2025

11607

gani.

A hankali ya warware ta yana runtse idon sa, babu abinda ya raba ta da takardar dake rike a hannun sa ta saman, da sauri ya rike kofar wardrobe d'in Jin Kamar zai fad'i

*Pregnancy test report. Shine a saman takardar farko sai sunan ta dake rubuce baro baro a saman da babban baki,

Sai kuma takardar sa hannu ta *abortion* a kasan ta.

"Innalillah wa inna ilaihi raji'un." Kawai yake maimaita wa dan ya rasa abinda zai ce,da sauri ta matso kusa dashi tana kokarin riko shi ganin kamar zai fad'i, hannu yasa ya bige hannun ta ya juya da sauri ya bar dakin. Kanta ne ya daure, da sauri ta hau tattare kayan daya zubar, ajiyar zuciya ta sauke ganin be riga ya xubo dana alluran ba, tana gama kwashe wa sai ta tsaya kuma ta kasa komai tana tunanin bin shi zatayi taji menene ko yaya? Har ta zauna sai kuma ta kasa nutsuwa, gashi ko kaya ta kasa sawa saboda tunanin abinda yake faruwa. Tashi tayi kawai ya yanke shawarar bin shi taji damuwar sa kar yaje ya aikata wani abin. Kama handle din kofar tayi ta jita a rufe ta ciki, komawa tayi ta zauna a falon tana kallon dakin zuciyar ta duk babu dadi.

Tun tana zaune tana tunanin zai bude har ta fara bacci a wajen. Sai chan cikin dare ya fito, yadda ya ganta tana bacci a zaune ne yasa ya tsaya akanta yana kallon ta,zafi ya saka ta finceke hijab din daga ita sai towel Wanda ta tattare gaba daya ya fito da ilahirin jikin ta. Zuciyar sa ce ta hau bugawa da sauri da sauri cikin wani yanayi yake kallon ta, idon sa ya daga sama yana jin wani irin tashin hankali idan har ya tuna abinda ya gani

"Allah karka sa abinda na gani ya zama gaskiya, Allah ka kawo min mafita ya Allah."

A hankali yasa hannu ya dauke ta cak yana kallon fuskar ta a bacci so innocent, tun dazu ya rasa in da zai saka kansa idan ya tuno gashi ya kasa daidai ta abin ya dora shi a mizani guda, ba wani sani na azo a gani yayi mata ba balle yace ya san abinda zata iya da wanda ba zatayi ba, babban tashin hankalin sa daya ga takardar a cikin kayan ta wanda ita kadai take da ikon ajiya a wajen.


***Rugumtsumi*** wayyo Mero😭😭😭😭
***
Sai daya bari yayi aikin sati ya dan samu wani abu sannan ya sanar musu da ya ajiye aikin, babu wanda beyi mamakin hakan ba haka ya tattaro ya dawo gida. Abin mamaki yana dawowa Asi na kiran sa akan su hadu, be fito ba sai daya huta sosai sannan ya kira shi, a chan wani waje suka hadu sukayi magana sannan ya dawo gida.

Daddare Inna ta kirashi akan maganar gidan da kuma dalilin dawowar sa,be sanar da ita ainihin maganar ba kawai ya barta ne a zuwan wani aikin ya samu anan sannan uban gidan nasa da ya dauke shi aiki shi ya taymaka ya basu gidan su zauna na dan wani lokaci, murna sosai Inna ta hau yi tana shi masa albarka, zuciyar sa ce tayi nauyi be kuma cewa komai ba ya bar dakin yana wasi-wasin abinda yake so ya aikata.

Wajen takwas na dare Asi yazo kofar gidan ya tsaya bayan ya kirashi a waya, be wani bata lokaci ba ya fito suka wuce bayan ya rufo gidan saboda be san lokacin dawowar sa ba. Tafiya sukayi me nisa da har ya wani abu ya darsu a ransa sai dai kuma ya zuba ido ya ga yadda komai zai tafi. Sanda suka karasa wajen Asi ne kawai ya fita ya bar shi a motar shi kadai bayan yace ya jirashi zai karbo sako ne. Be wani jima ba ya fito rike da leda babba sannan yaja suka bar wajen. Sai da suka daidai ta a titi kafin Asi ya mika masa takardar

"Ka duba bayanin komai yana ciki, ba wani aiki ne me wuya ba, dashi zaka fara kafin kuma kuyi magana da hajiya, zan dawo na dauke ka da safe."

Kallon sa Hafiz yayi ya kalli ledar, a kasan kafar sa ya ajiye ta yayi shiru kawai ba tare da yace komai ba.


Not edited...
Manage dearies🚴🚴🚴😔😔😔
Kunsan Idon nawa sai a slow wlhi

*25* S K
©*Hafsat Rano*

*_ZAFAFA BIYAR na kudi ne idan kana son kowanne daga ciki ka nemi Wannan numbers din_*

*08030811300*
*07067124863*

*_Daurin boye_*
_safiyya huguma_
*_Buri daya_*
_mamuhgee_
*_Wutsiyar rakumi_*
_billyn Abdul_
*_Kai min halacci_*
_Miss xoxo_
*_Sauyin kaddara_*
_Hafsat rano_

***
Kayan ya shiga fiddawa daya bayan daya yana kallon su, sai daya gama gaba daya sannan ya tattare su gefe daya, tsiren daya tsaya ya siya a hanya ya jawo ya hau ci yana korawa da fanta me sanyi. Har ya gama gaba daya ransa a jagule yake, ya rasa yadda zai bullowa al'amarin gashi babu wani kwakwaran dalilin ta na son ya aikata abinda take so ya aikata. Gefe ya ture komai ya kwanta bayan ya kuskure bakin sa. Bashi da wani zabi illa kawai yayi yadda take so É—in in yaso sai ya aiwatar da abinda shi ma yake ganin shine daidai.

°°°°
Yana ajiye ta tana buÉ—e idon ta, da sauri ta kalle shi tana kokarin tashi,hannu yasa ya mai da ita ta koma baya, bin ta yayi ya rufa akanta,da sauri ta runtse idon ta zuciyar ta ta shiga harbawa da sauri da sauri. Be yi magana ba haka nan be daga ta ba yayi shiru ne yana tunanin yadda zai yi, ilahirin jiki da zuciyarsa sun gama aminta da abinda yake ganin shine sai dai yana tararradin yadda zaiyi idan har zaton sa ya zama gaskiya. Sosai ta fara gajiya ta hau kokarin janye jikin ta, rinannun idanun sa ya zuba mata yana tamke fuskar sa kamar be taba dariya ba

"Idan kika kuskura kika kara motsi sai kinyi mamaki." Ya fada yana sake sakar mata dukkan nauyin sa. A take tayi tsit dan ba karamin tsorata tayi da yanayin sa ba, daga sama taji yace

"Takardar dake cikin kayan ki."

Dan kallon sa tayi ya sake hade rai sosai, shiru tayi hakan ya sake tunzura shi, cikin daga murya yace

"Am asking u,takardar cikin kayan ki, can U depend it?"

"Wace takarda?" Ta tambaya adan tsoro ce

"Are You asking me?"

Da sauri ta girgiza kai.

Buga hannun sa yayi a kusa da fuskar ta, da sauri ta rufe ido,

"Ya Allah, ya zanyi?? Menene matsalar, waye yake son ganin baya na ne wai, I have face alot yanzu kuma dis? No I cnt take it."

Zame wa yayi ya sauka kasan gadon ya dora kansa a saman ƙafafuwan sa, so yake ya fitar da abinda yake ji a ransa saboda yadda ya tokare masa makoshi ji yake kamar ransa zai fita. Ita dai Maryam gaba daya kanta ya daure ta rasa gane kan abinda yake faruwa, bata kawo tunanin komai akan ta ba har sai da yayi maganar takarda, iya sanin ta bata ajiye wata takarda a dakin ta ba, sai dai kuma ai ta ga lokacin daya dauki takardar a cikin kayan ta, toh takardar mece ce? Ita ta saka shi a halin da yake ciki ko kuma me? Ta rasa ganewa. Jin kamar yana jan numfashi sama-sama yasa tayi saurin saukowa ta manta da yadda take, da sauri ta rike hannun sa ganin yana kokawa da numfashi, kuka ta saka ta tashi da gudu ta shiga neman inhaler sa, babu a dakin haka ta sake fita tayi dayan dakin, a saman drawer ta hange ta tayi saurin daukowa ta fito, da sauri ta koma dakin jikin ta sai rawa yake dan bata taba ganin wani mutum a makamancin halin da yake ciki ba,wani irin zama tayi a gaban sa irin na yan bori ta mik'a masa inhaler, da kyar yasa hannu ya karba ya fara shak'a, zura masa ido tayi cike da tausaya wa, sai daya fara dawowa daidai sannan ta matso kusa dashi sosai tana kokarin rike hannun sa, kasa hanata yayi ya dai sauke kansa kasa yana sauki ajiyar zuciya da sauri da sauri kamar wanda yayi gudun tsere.

Sau uku tana yunkurin yin magana sai dai ta rasa yadda zata yi, da kyar tace

"Dan Allah kayi hakuri, idan ma wani abu ne ya faru, ka sani duk tsanani yana tare da sauki, mu cigaba da addu'a komai zai zama norma'."

Gyara zaman sa taga yayi, ya d'ago yana fuskantar ta

"Zaki fada min gaskia duk abinda na tambaye ki?"

Da sauri ta daga kanta

"In Sha Allah."

"Owk taso." Yace yana mik'ewa, da sauri ta kalli kanta, kasa tashi tayi, be ce komai ba yayi hanyar fita,sai daya kai kofa sannan yace

"Ina jiran ki."

Tashi tayi ta zura doguwar riga a gurguje ta fito, baya falon, kai tsaye dakin ta wuce tana wasi-wasin abinda zata tarar. Yana zaune yana tattara takardun waje daya ta turo kofar hade da sallama, kai tsaye ta karasa wajen kafarsa ta zauna a kasa tana kallon shi, mika mata yayi yana tashi tsaye

"Ki fada min gaskiyar abinda ke cikin takardun nan guda biyu, bana son ki boye min."

Cikin rawar hannu ta karba tana kallo, da farko bata gane abinda takardar ta kunsa ba sai da idon ta ya sauka akan sunan ta dake rubuce baro-baro a dukkannin su. Wata irin zabura tayi tayi jifa da takardun ta mike cikin tsananin tashin hankali,

"Innalillah wa inna ilaihi raji'un."

"Tell me the truth."

"Wallahi wallahi Allah ne sheda ta, bansan komai akai ba, wallahi Allah sharri..."

"Sharri?" Ya katse ta,

"Wallahi sharri akayi min, na shiga uku, innalillah wa inna ilaihi raji'un.

Yake yayi wanda yafi kuka ciwo

"Amma ya akayi na ga same report a kayanki?"

Wani irin matsanancin bari jikin ta ya hau yi, gaba daya ta rude ta rikice, ihu zatayi yayi saurin sa hannu ya rufe mata baki, wani irin kuka ta saki, bata da wata dabara da zata iya kare kanta, duk wanda yayi mata sharrin nan ba karamin mara imani bane. Yadda take kuka sosai ne ya bashi tausayi, gaba daya ta rikice ta rasa in da zata saka kanta, dana sanin sanar da ita yayi dan beyi tunanin kalar tashin hankalin da zata shiga ba kenan. Juyawa yayi da nufin barin dakin tayi saurin rike masa kafa

"Dan girman Allah ka yarda dani, wallahi tallahi ban aikata abinda aka ce na aikata ba, wayyo Allah na wayyo Umma na shiga uku."

Runtse idon sa yayi bayan ya tsaya chak, gaban sa ta dawo ta sake zubewa yana fama magiya da roƙo. Kafad'arta ya kama ya miƙar da ita tsaye yana girgiza mata kai

"Ya isa, don't hurt ur self, I believe u." Ya samu kansa da fada mata ba tare ya shirya ba.

Da sauri ta rungume shi tana rage karfin kukan da take yi, shiru yayi yana jin yadda zuciyar ta ke bugawa da karfi da karfi. Kallon agogon dake saman dakin yayi yaga biyu har ya ta gota, ajiyar zuciya ya zare ta daga jikin sa

"Zaki iya Sallah?."

Kasa magana tayi sai jan hancin ta kawai take, riko hannun ta yayi

"Muje kiyi alwala muyi sallah, ki daina kuka and please forgive me owk?"

Alwalar tayi kafin ta fito ya dauko mata hijabin ta, kasa kallon shi tayi yana mika mata hijabin, karba kawai tayi ta saka tana jin idon ta kamar zai fado saboda radadi.

Raka'a biyu sukayi kowa yayi addu'o in sa sannan yace su je su kwanta, tashi tayi ta ninke carpet din da sukayi sallah zata koma dakin ta ya hanata yace su kwana anan. Ba musu ta koma ta hau gadon ta kwanta dan bata so suyi wata doguwar magana ma dashi a yadda take ji, ta san kawai ya kyale maganar ne ba wai dan ya yarda ba sai dan ya tausaya mata, shi yasa ma tun data kwanta sai faamn juyi take ta kasa baccin a hankali take sa hannu ta goge hawayen dake faman zarya a kan fuskar ta.

"Kinyi bacci.?" Taji maganar sa dan bata yi zaton ma idon sa biyu ba

"Um um." Ta amsa mishi, daga gefen sa ya sa hannu ya bubbuga wajen yace

"Matso nan."
Ba musu ta matso, matsowa yayi sosai ta dan matsa kadan bayan ta juya masa baya, hannun sa taji ya sa a saman fuskar ta ya shafo hawaye

"Ohh Allah, kukan dai?" Ya tambaya yana mirgino ta ita tana fuskantar shi

Ji tayi wani sabon kukan ya sake taso mata me karfi ba kamar da data ke yin sa a zuci ba.

Dafe goshin sa yayi jin yadda take shasheka, irin kukan nan da kana ji kasan mutum na jin ciwo a kasan ransa.

Share mata ya hau yi yana share wa wani na bin wani, sosai kukan nata ke taba shi ya hanashi sukuni, ganin da gaske ba zata daina ba yasa shi yanke shawarar sata tayi shirun ko da kuwa batayi niyya ba.

Cikin wani irin salo me cike da karsashi taji ya had'e bakin su waje daya. Tuni taji kukan ya dauke dip, a hankali a hankali komai ya shiga sauya wa, sabon shafin rayuwar su ya bude a lokacin, abubuwa da yawa sun faru, masu tsawa wa bawa a kahon zuciya, masu wanzuwa a tsakanin kowanne ma'aurata, wani irin kundi ne me wuyar fassarawa, a ranar Maryam ta shiga jerin mata masu daraja, fagen manya kamar yanda hausawa ke cewa, komai da ya faru kamar wasan kwaikwayo haka Arkel yaji shi, abinda yake zato sam babu makamancin sa, hakan yasa ya rasa in da zai dauki tunanin sa ya kai, menene alakar sakon da aka aiko masa da zamantakewar sa da ita? Waye ne baya son ganin su tare. Da sauri zuciyar sa ta rayo masa Hafiz. Sai dai bashi da wata gamsasshiyar hujja akansa, toh amma idan ba shi bane toh waye? Ganin zai matsawa kansa da tunani yasa ya bar komai zuwa wayewar gari, sauƙin ta daya yayi dabarar rike mutumin, dole ya sanar dashi wanda ya aiko shi idan ba haka ba kuwa sai ya kulle kaf ahalinsa.

Gefen sa ya kalla, tana kwance tana kuka kadan-kadan, kukan da ya zama dole ga duk wata macen kwarai a irin wannan ranar, cikin tsananin tausayi ya matsa daf da ita sannan ya jawo ta jikin sa.

Shafa bayan ta yake yana jin tsananin haushin kansa akan tuhumar da yayi mata, sai dai fa hakan ya kara mata wani babban girma da matsuguni me girma a ransa, yana jin ta tana goge hawaye da majina a jikin rigar sa, dariya yayi ya janye ta yana kallon fuskar ta, da sauri ta rukumkume shi ta cusa kanta a kirjin sa cikin tsananin kunya. Shafa kanta yayi ya gyara mata kwanciyar.

Kafin safiya tayi jikin ta yayi mugun rikicewa da zazzafan zazzaɓi saboda uban kukan data sha ga wahalar ba kadan bace, daa k'yar ya tayamaka mata tayi alwala bayan ta gasa jikin ta, a zaune tayi sallah saboda jirin dake kokarin kayar da ita, sai a sannan ta tuno babu wanda yaci abincin dare a cikin su. Hijabin ya cire mata ya taymaka mata ta koma ta kwanta, duddubawa yayi babu ko paracetamol dole ya hakura zuwa gari ya kara wayewa.


****
Babu irin zagayen da batayi ba tana jiran taga Maryam ta sakko da kayanta zata koma gidan uban ta, shiru har ta hakura ta kwanta ba dan taso ba.

Shi yasa da safe tayi sammakon tashi sai dai abin mamaki babu ko alamun sun tashi ma a lokacin, haka ta hakura ta zauna a falon tana jiran ta ga ya abin zai kasance. Karar text message ce ta shigo wayar ta tayi saurin dubawa, da sauri ta ajiye wayar bayan ta gama karantawa jiki na rawa ta fito harabar gidan, buzu na hango ta yayi saurin tahowa


"Waye jiya yazo da daddare Arkel yace ko ajiye masa shi?"

Da sauri yace

"Wani bako ne, bayan sun gama magana yace kar mu barshi ya tafi."

"Yana ina? Me yasa yace a rufe shi?" Duk ta rude

"Gaskia bansan dalili ba , sai dai naga hankalin oga ya tashi sosai."

"Owk muje na gani."

Be kawo komai ba ya rakata har kofar dakin, zai bude kofar tayi saurin cewa

"Kyale shi ma, in yazo da kansa zai fi."

Juya wa tayi tana dan kallon gefe, sai kuma ta juyo

"Ka gyara mota kazo na aikeka."

Da sauri ya juya, tunanin in da zata aike shi da uwar safiyar nan take, chan tunanin yazo mata tayi murmushi.

Kudi ta shiga ta dauko ta mika masa

"A chan kofar famfo akwai wata me sai da masa, kaje ka siyo min."

Babu bata lokaci ya karba ya tada mota ya bar gidan, me gadi dake chan kofa be san abinda yake faruwa ba, dakin ta nufa ta bud'e, yana takure yana ganin ta ya tashi

"Hajiya na shiga uku."

"Shish." Ta dora hannun ta a saman bakin ta

"Ka shirya, idan kaga mun shige ciki kayi gaggawar barin gidan."

"Nagode Nagode Hajiya."

Juyawa tayi tana kwalawa me gadin kira, da gudu ya karaso,

"Muje ciki ka duba min kafar kujera, kamar rawa take."

Yana ganin sun shige ya bude kofar ya fice daga gidan a dari.

****
Yanayin fuskar sa take kallo har ya sauko kasan, a tunanin ta zata ji ko ta ga ya tattara Maryam ya watso ta watakila ma a kakkarye sai kuma daga akasin haka, yadda ya saba ya gaishe ta ya sa kai ya fice, saman ta kalla shiru bata ji ko motsi ba a ka'ida Maryam tana fitowa da wuri sai gashi yau har 10 ta gota bata fito ba alamun kenan babu matakin da ya dauka, kamar zata zare haka ta koma duk tabi ta shiga matsananciyar damuwa. Tana nan zaune ya dawo dauke da leda me dauke da tambarin wani drug store dake kusa dasu, da sauri ta tare shi cikin son nuna kulawa tace

"Waye ba lafiya?" Kai tsaye yace

"Ita ce." Hannu ta É—ora aka tace

"Subhanallah, me ya same ta? Bari naje na gani idan abin babba ne gwara a tafi asibiti gaskiya."

Da sauri ya dakatar da ita

" Ba wani abu bane Serious,am...amm dama bige wa tayi ne tazo fita."

Dadi ne ya kamata har ta kusa yin murmushi, saurin saita kanta tayi cikin tausaya wa tace

"Ayyo...Allah sarki, na zata abun Serious ne, ta dinga kula dan Allah, Allah ya sauwake."

"Amin." Ya amsa yana haye wa

Dariya ta yi ta shige daki tana fatan Allah yasa targade tayi ko ta karye ma baki daya.

A makure ya hange ta

27, January 2025
Rukayya

Good

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login