Showing 96001 words to 98004 words out of 98004 words
likis ta shiga kitchen ta dauko tarkacen kayan da Maman Walid ta bata, ganyen idon zakara, mazarkwaila, ya'yan zogale, minannas, kanumfari, zogale an dake su waje daya ta hada madara a kofi da yawa ta zuba su kayan sannan tasa zuma me yawa ita ma ta juya ta hade su ta shanye, sosai abin yayi mata dadi, wanka tayi ta goya Hudah tayi sallah, kafin ta idar tayi bacci, kwantar da ita tayi ta ciro sababbin English wears din ta, ta saka bata wani bata lokaci a wajen kwalliya ba saboda ita na gwanar kwalliya bace, sanyayyen kamshin khumra da haaddadun turarukan jiki dana kaya ke tashi, burner ta kunna daga corridor din falon kamshi ya shiga tashi ta kowanne lungu da sako na gida.
Sai da ya tsaya ya sai abin da zasu bukata da safe sannan ya nufo gidan yana jin wani karfi, yana bude gate din gidan kamshi ya daki kofofin hancin sa, ja yayi da baya ya lunshe idon sa yana jin wani sanyi na ratsa shi, bayan ya shigo da mota ya kwaso kayan ya turo kofar, bata falon sai karar Tv dake ta faman yi, ajiye kayan yayi a saman Centre table ya nufi dakin ta, tana zaune kan gado tana bawa Hudah abinci ya shigo, sam bata ji shigowar sa ba saboda kukan da hudan keyi, kafe ta yayi da ido yana noticing din ta, sannu da zuwa tayi masa sannan ta ajiye Hudan a hankali saboda ta samu ta koma barci, sake kallon sa tayi ganin
Ranar wata Laraba aka gabatar da bude shagunan guda biyu dake manne da juna, babban shine na Ummi in da aka zuba mata kayan provision da su kayan abinci, da sauran abubuwan bukata, dayan kuma dake gefen shine na Maryam, babu ce kawai babu a shagon dangin su handbags kayan ado dai na mata sai saloon da wajen spa d'aga gefe, babu wanda be yi farin ciki ba a ranar
***
Bangaren Hafiz kuwa ya warke sosai har ma ya dawo aikin sa, shine ya zama me taimaka wa Salim sabida aikin sun fara masa yawa, tare suke komai, a haka ne suka hadu da wata yarinya Zaituna yar secondary ce a shekarar zatayi candy, be wani sha wahala ba iyayen ta suka amince aka saka rana da komai, Suwaiba ma lokacin wanda zai aure ta har ya kawo lefe, sai aka saka rana daya kawai ayi komai a lokaci daya, Inna ba k'aramin farin ciki tayi ba da Allah ya dube su ya kawo masu sauki a rayuwar su ba, gashi Hafiz din ya koma makaranta yana karatun sa yana kuma aikin sa babu laifi yana samu shima, Arkel bashi da mugunta wa ma'aikatan sa, ya buda wa kowa a cikin su, tuni ya sake habaka arzikin sa har yfi na da.
***
A kwance take gaba daya ta sauya kamanni tun bayan dawowar ta take ta fama da rashin lafiya, ciwon siga ne ashe da ita yayi mugun karfi, bata iya komai sai kwanciya ga kafarta har ta fara kumbura tana fitar da wani irin ruwa me wari, duk yan kudin da take dashi ta karar dashi wajen magani amma babu wani sauki abu sai gaba yake, so take ta koma asibiti babu kudi gashi tana jin jiki sosai, ko waya bata iya dauka, tana nan k'wance a falo da yake dauke da kujerar zama one seater sai ledar tsakar d'aki duk ta yayyage, babu komai duk ta tattara ta sai da saboda neman magani, Zainab ce ta fito daga dakin zata fita waje tana ta yatsine fuska, da kyar ta daga kanta ta kalle ta cikin ciwo tace
"Yanzu Zainab kina gani na a halin nan kike ficewarki ki barni, baki da tausayi ko?"
Dan tsaya wa tayi daga fitar tace
"Haba Mummy ya kike so nayi? Zan zauna ne ba zanje makaranta ba? Me zanyi tun da ba auren ai gwara nayi karatu."
"Amma Zainab da kudin makarantar ba gwara ki kawo na sai magani ba."
"Kai karatun? A ah gaskia mummy, ki barni kawai kika ma san da ya na koma makarantar? A ah gaskia."
"Ba zaki taimaka min ba Zainab? Eh? Me nayi miki haka kika tsaneni?"
"Kai Mummy ki jiki da wani zance, sai kin min wani abu zan fadi gaskia? Ni babu abinda kikayi min kawai ina da bukatar kudin ne nima."
"Ai shikenan, ki zo ki kira min Yaya Alhaji toh."
"Kai innalillah, na fa makara walalhi, idan kika fara waya sai kin fi rabin awa kina masa koke koke, ki bari na dawo kawai ba yace ma zai aiko da kudin bane wai? Zai aiko ai."
Tana kai wa nan ta sa kanta ta fice tana kunkuni, kuka ne ya taso mata ta hau yin sa babu kakkautawa, wato a duniya ana so ka zama na gari, kada ka cuci mutane, idan ba haka ba tun a duniya zaka ga sakamako, gashi dai yanzu rayuwa ta juya wa Hajiya Mero, a lokacin da take tunanin tana cikin jin dadin rayuwar.
Haka ta cigaba da jinya kafar na sake rubube, da k'yar Alhaji Faruku ya zo data matsa masa da kira, sosai ya girgiza da yadda ya ganta, be yi tunanin abin nata ya kai haka ba, a take ya dauke ta ya kaita asibiti sai dai suna zuwa likita ya duba kafar ta yace lallai sai dai a yanke, dukka biyun sun lalace ba zata sake taka su ba har a bada, kuka ta dinga yi tana kiran sunan Ummi akan ta yafe mata, duk wanda yazo wucewa sai ta bashi tausayi yadda take kuka kamar ranta zai bar jikin ta. Rayuwa kenan
*SAUYIN KADDARA*
*56*
©Hafsat Rano
****
*Bayan Wasu shekaru*
Abubuwa dayawa sun faru ciki har da mutuwar Hajiya Mero bayan tasha jinya, a lokacin ne Ummi ta dauko Zainab tace zata rike ta ai d'a na kowa ne, Arab yaso ya hana amma sai ya kyale ganin shi ne kaɗai baya goyon baya.
Wani zuwan Mustapha Kano abokin Arab bayan ya koma Sokoto da aiki suka hadu da Zainab ɗin a gidan taje kai wa Lubna sakon Ummi, tun daga lokacin yace ya ga mata, duk da Arab be so ba amma haka ya hakura, akayi auren Zainab da Mustapha, aka kai ta Sokoto.
Rayuwa ta cigaba da tafiya yadda ya kamata, kowa ya samu abinda yake so. Salim ma yayi aure da dadewa suna nan yadda suke da Arkel babu abinda ya chanja na daga amintar su. A chan Mali ma Bongel ta hakura da komai ta samu mijin ta daidai da ita da tsarin rayuwar su, gaba daya suka je bikin aka sha shagali da irin al'adar yan garin.
***
Tana zaune a falo tana duba kayan da sukayi order a shagon su Habubu ya turo kofa ya shigo dauke da Aman a kafadarshi, kallon su tayi ta cigaba da abin da takeyi, shi din ma be yi mata magana ba yasan idan tana aiki bata son hayaniya, yana zama suka ta jiyo ihun su a compound din gidan, da sauri ta daga curtains din falon ta hango su suna sauke kayan su daga mota, kallon shi tayi yayi saurin kama kunnen sa yana dariya
"Wallahi Umma ce tace a dawo dasu, sun ishe ta kuma, wai a kaiwa Ummi su."
"Amma dan Allah ba kaga aiki nake ba, sai kawai ka kawo su ai da ka kai su gidan Ummin."
"Ita ma tace bata so."
Dafe kanta tayi ta cire glass din idon ta ta hau tattare kayan aikin mata tana cewa
"Sai ka zauna dasu anan bari na hau sama, kace musu ina bacci kar wanda ya tashe ni wallahi."
Dariyar sa ya kunshe har tayi gaba ta tsaya tace
"Kajin naku nawa ne ma umma tace sun mutu?"
"Guda hamsin ne saboda ruwan da akayi."
"Owk sai a zuba wasu, a madadin su, so nake umma wannan karon ta fitar da kamar guda 500 haka.'
"Allah yasa babbar yaya."
A guje suka shigo su uku duk maza sai Inas da Iman dake take musu baya, dafe kanta tayi ta harari Habubu dake dariya ta fasa shiga dakin ta dawo tsakiyar falon
"Maaamaa mun dawo." Suka hada baki a tare,
"Na ganku, sannun ku, a wuce daki a cire kaya sannan bana son gagara kuje compound kuyi wasa."
Ihu sukayi mazan suka shige dakin su matan ma, Hudah na zaune tana karatu suka fado dakin a guje, hararar su tayi ta tashi ta bar musu dakin dan tasan yanzu zasu hargitsa gidan, ita kuma a rayuwar ta bata son hayaniya ko kadan.
Mazan biyu twins din Lubna da Arab ne amma kusan rabi da kwatar rayuwar su a gidan Arkel sukeyin ta, ko yaushe suna tare da Taufiq sai suka tashi kamar yan uku duk da sun dan girme shi da kadan. Bayan Taufiq Maryam ta haifi Iman da Inas sannan Aman, yanzu haka Lubna cike ne da ita tsoho haihuwa ko yau ko gobe, tun bayan twins bata sake ba sai yanzu da ake sa ran ta haifo musu Bby girl.
***
Ruwan sama ake zugawa kamar da bakin kwarya, kwance take akan chest ɗin sa a hankali suke hira kasa kasa wadda duk yawanci akan rayuwar su ce, yanayin yayi musu dadi dukka su biyu, hakan ya haifar musu da wani yanayi na shaukin juna, iska ce take busawa kadan kadan hade da kamshin kasa, lumshe idon ta tayi ta sake bude so a hankali ta lalubo hannun sa ta saka a cikin nata ta damƙe shi kam tana sake shigewa jikinshi, be hanata ba sai ma kara matsowa da yayi, a kunne ya rada mata
"You Are the best wife in the whole world."
"And you are the best husband to."
"Allah ya barmu tare."
"Amin my wife, my everything."
Bacci me cike da ni'ima wanda suka dade basu taba yin irin sa ba ne ya dauke su kowanne su da tsananin so da kaunar abokin rayuwar sa a ransa.
Alhamdulillah ana na kawo karshen wannan littafin nawa, Nagode kwarai da kaunar da kuka nuna min, Allah ya saka wa kowa da Alkhairi ya haskaka wa kowa rayuwar sa, Allah ya sa mu gama da duniya lafiya. Wanda na bata wa da sani na ko bisa rashin sani yayi hakuri ya yafe min dan Allah. Nagode Nagode kwarai da gaske, domin dai ku ɗin masoya ne na kwarai. ZAFAFA BIYAR na godia bisa halaccin ku karemu.
Anan ne kuma nake so nayi amfani da damar nan wajen tallata muku bussiness din mu na Longrich, bussiness ne da ya kamata ace duk wata mace ta yi, zama haka kawai bashi da amfani, yadda muke amfani da wayoyin hannun mu ko da yaushe ya kamata ace mun koyi sana'a da su muna samun wani abu ba wai karatun Novel kawai ko chatting da kallon status ba.
Duk wadda ta san ta shirya tana son ta shigo a dama da ita tayi min magana da number ta 08030811300. Sauran bayanin mu hadu ta pc.
Nagode Nagode Nagode
Rano🚴🚴🚴🚴
***
_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A HALIN YANZU😁._
*ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma
*SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano)
*KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo)
*BURI ƊAYA!* (Mamu gee)
*WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull)
👇🏻karku bari ayi babuku
*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*
*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*
Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank
Saika tura shaidar biya ga wannan number ta WhatsApp
08030811300
Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN ta wannan number din
07067124863
Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.
*Karki bari ayi babu ke, Abari ya huce shike kawo rabon
Rano🚴🚴🚴
***
********************** ⬇ **************************
************* Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.
Visit > https://www.aihausanovels.com.ng
Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.
Email > aihausabooks@gmail.com
******* FOLLOW US ******
Facebook: Ai Hausa Novels
Twitter: Ai Hausa Novels
Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels
Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.
********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************
27, January 2025
Rukayya
Good