Showing 66001 words to 69000 words out of 98004 words
dai dole ne ya karasa abinda ya faro, abinda ya katse shi ya dakile shi tsawon wasu shekaru ya hana masa jin dadi da kwanciyar hankali, komai yazo karshe da izinin Allah sai kuma shirin ginin kyakkyawar rayuwa dashi da yan'uwansa baki daya.
Ko da ya isa gida dukkan su suna zaune a falon, Baba Ladingo ma data tafi cikin gari ta dawo ta tarar da abinda ya faru murna tayi tayi harda kwallar ta, Ummi kuwa an samu ta koma bacci bayan Nabila ta goge mata jiki ta gyara ta tsaf, kamal da ya san komai be yi yunkurin zuwa ma daukar ta ba saboda yasan tana bukatar lokaci da yan uwanta, sai kawai ya gyara su Amna ya shirya su ya saka su bacci sannan ya samu sukunin sawa cikin sa wani abu.
Bayan ya duba Ummi ya tabbatar komai kalou dan dama yasan hakan shi yasa ma ya bar su da ita su samu lokaci, saman ya haura agajiye yake tikis dan ma wajen Maryam daya tsaya ya dan huta kadan, yana shiga ya jefar da kayan hannun sa, ya cire komai na jikin sa yayi saura daga shi sai singlet sai karamin boxer ya fad'a toilet, kasalar yin wankan ma yake ji dan dai kawai ya saba ne yasan in be yi ba, ba zai ji dadin barcin bane shiyasa, aikuwa ya dade a ciki yana zubawa kansa ruwa sai daya ji bashi da wani sauran gajiya sannan ya fito.'
Kayan sa marasa nauyi ya zura ya fito falon, da mamaki yake kallon sa a zaune yana duban hanyar, sai da ya kalle shi sannan ya dauke kai zai wuce Kitchen.
"Arkel..."
Yaji muryar Ya Nabila, juyowa yayi ya ganta a tsaye ga dukkan alamu shigowar ta kenan, da baya da baya ya dawo ya tsaye daidai gaban ta
"Kanina magana zamuyi dan Allah."
"Maganar me? Ko mu bari da safe?"
Dan kallon bangaren da Arab yake zaune tayi ganin su yake kallo yasa tace
"Yanzu zamuyi tun dazu muke jiran ka."
Daga kafadarsa yayi ya samu waje ya zauna. Zama tayi a gefen sa ta nuna Arab kusa da ita
"Dawo nan.".
Tashi yayi ya dawo kusa da ita shima, hannun su ta kama ta saka a nata sannan ta shiga magana a hankali. Kusan raba dare sukayi suna hira da labarin bayan rabuwa, tun Arkel na basarwa Arab har ya sake dashi bayan yayi masa bayanin komai, shi dai yayi shiru da komai da yake shiryawa har zuwa ranar daya tsara , ranar ne zasuji komai da ya faru.
****
***
Bangaren Hajiya Mama kuwa ganin Alhaji Faruku shiru yasa ta zari mayafin ta ta shiga gidan su maryam, tsawon lokaci kenan rabon data shiga ko da zauren gidan ne yau sai gata a ciki, da sauri umma ta tarbe ta ta shinfida mata tabarma, bata zauna ba daga tsaye take tambayar baba, lokacin yana ciki yana Sallah ya dan makara be samu jam'i ba, tsaya wa tayi ya idar ya fito, yana ganin ta ya rude yana tambayar ta ko lafiya, ita kanta a rud'e take ta sanar masa abinda yake faruwa, takalmin sa kawai ya saka suka fita yana bata baki, suna fita sai ga Alhaji Faruku, gida suka sata ta koma suka fita tare, tun a hanya suke tunanin in da aka kaita, gashi Arkel ɗin duk wayoyinsa a kashe suke, haka suka k'araci yawon su Baba yace suje gidan Alhaji Faruku yace sam ba za'a yi haka ba, shi da yake ya san komai ya san halin ta shiyasa ya kafe akan su koma gida kawai idan gari ya waye sai su tuntubi Alhajin su Arkel ɗin suji.
Haka suka hakura suka dawo gida,Hajiya Mama sai kuka take tana tsine-tsine, Zainab da Rauda ma kukan suke sai dai zainab naji a ranta tabbas wani gagarumin abun tayi dan tasan halin uwarta, ta dade tana abinda take so.
***
Tashin hankalin da ba'a sa maka rana shi ake kiran wannan, cikin tsananin mamaki Hajiya mero ke kallon Sambo da Asase a cikin wajen, duk sun yi wujiga wujiga alamun sun sha wahala, babban dalilin da ya saka kenan ta kasa samun daya daga cikin su, bata sake tsorata ba sai lokacin da ta ga mutumin da ta saka kawo takarda, anan ne ta sake tabbatar wa kanta tata ta kare, ihu da kuka ta hau yi a wajen sai da suka tsawatar mata da barazana sannan aka samu tayi shiru duk ta tuje daurin kanta sai kanta ya bayyana kamar hammatar dan iska, irin gashin nan ne da ita kamar na yara marasa gashi ga taurin masifa ya sha wani abun kitso babu kyan gani, tana nan tana kallon hanya a tunanin ta zasu zazzo har dare ya fara yi shiru babu kowa haka aka tattara ta aka zuba a bayan cell, k'aramin daki ne me yar karamar window daga chan sama ga banɗaki irin pit din nan a ciki da yake buso uban wari da doyi, kamar zatayi amai haka ta dinga ji haka ta takure kanta tana kallon mata biyun dake ta fada a ciki an kawo su sun cinye wa wata mata kudi.
Yadda taga rana haka taga dare ga uban sauro kamar ruwan su ake, bata taɓa ganin masifa irin wannan ba, gaba daya jikin ta yayi tsami ga wani irin hamami da yake tashi abin ba'a cewa komai.
Sanda gari ya waye ne aka fito dasu ana jiran dpo yazo, Asase da Sambo sunki yarda ma su hada ido da ita gashi babu abin tayi musu magana tana tsoro, duk da haka tana nan akan bakanta dole ta dau fansa ba zata taba kyale Arkel ba dan ba karamin shammatar ta yayi ba har ya iya bata mata aiki, bayan ta samu tabbacin babu abinda zai iya karya abinda ta kulla, haka dai take ta sake saken ta har aka zo aka kwashe su sukayi ciki.
***
Dukkan su babu wanda yayi ishashen bacci gashi basu kwanta da wuri ba suka tashi saboda yadda Ummi take wani irin abu kamar zata mutu, nishi ne me cike da firgitarwa, magungunan ta tasha sannan aka kira nurse Latifat tazo tayi mata allurar bacci, ko data tashi jikin da sauki tana kallon kowa tana jin su, asibitin suka shirya maida ita kafin zuwan malam saboda jin ta in da zasu fara dan kuwa har tafiya sai an fara koya mata daga farko dan babu abinda zata iya yi duk da komai nata ya dawo yana aiki yadda ya kamata amma shekara biyar ba kwana biyar bane.
Arkel be bisu ba ya zauna a gida bayan ya amsa kiran Alhaji Faruku da suka ce zasu zo gida su same shi, ya riga ya san kwanan zancen sai ya zauna yana jiran su, fatan sa daya kar azo da baban Maryam ya nemi wata alfarmar ba zai iya ki ba.
Tare kuwa suka zo, da sauri ya fita ya shigo dasu suna zama sai ga motar Baba ta shigo, curtains din falon ya buda ya hango shi sanda driver din sa ke gyara parking din motar, ajiyar zuciya ya sauke ya ajiye musu ruwa da leme. Alhaji na ganin su ya karbe su hannu bibbiyu aka gaisa a mutunce dan dama ba haduwa suka taba yi ba sai ranar, Arkel dai na gefe kansa a kasa yana jiran yaji ta in da za'a fara, Baba ne ya sako maganar da sauri Alhaji ya kalli Arkel dan be san komai akai ba, fada ya hau shi dashi ta in da yake shiga ba tanan yake fita ba, sai da Alhaji Faruku yasa baki sannan yayi shiru yana kokarin danne abinda yake taso masa tun yana chan, daurewa kawai yake amma bashi da wani kuzari kamar zai yi zazzaɓi haka yake ji sai dauriya kawai irin ta maza dan ita mace ce take jin abinda yake ji dole ta kwanta. Tashi sukayi gaba daya suka nufi station din har lokacin Baba na jin sa kamar ba a duniyar ma yake ba baki daya.
Lokacin da suka je an gama shigar da case ɗin komai an dau report ɗin su Hajiya meron dasu Asase da suka ƙaryata duk abinda ake bin su, ganin haka ya saka DPO ya tattara case din gaba daya ya aika su kotu sannan ya bada belin Hajiya meron a zuwan sai ranar da za'a zauna amma da sharadin idan suka barta ta gudu toh fa dole a cikin su ukun nan dole daya za'a kama a cikin su, su Asase kuwa cigaba akayi da tsare su har zuwan ranar.
Godiya su Baba sukayi sannan suka tafi, Hajiya mero saboda tsabar bacin rai ta kasa ko magana dan bata taɓa ganin wulakanci irin wannan ba, har suka zo gida babu wanda yace komai shi kansa Alhaji ya kasa mata magana gashi abinda yake ji a jikin sa na kara tasiri sosai haka dai ya daure ya shige dakin sa ya kwanta, kafin wani lokaci zazzaɓi me karfi ya rufe shi, karkarwa kawai yake ya rasa in da zai tsoma ransa yaji dadi, Ya Nabila ce ta shigo dakin jin ance ya dawo ta tarar dashi a haka, da gudu ta fita ta kirawo su aka yi saurin kiran Dr dake dubasa sai gashi yazo, duk abin nan Hajiya mero ta kulle kanta a daki bata san me yake faruwa ba, Arkel kuwa yana sauke su ya juya dan ba zai iya zama a gidan a lokacin ba, tsaro sosai ya saka dan ba zai taba yarda Hajiya mero ta kubuce musu ba sai ta fuskanci hukunci ne tsanani sannan ne ya san ya cika dan halak ne kishin iyayen sa.
Magunguna da allurai aka bashi hadda allurar bacci da haka aka samu yayi bacci, Arab dake kansa tsaye yana kallon sa cike da tausaya wa, hannun sa ya Nabila ta kama suka fita tana kokarin kwantar masa da hankali.
***
Shirya shiryen dauke Ummi suke daga gidan su mai da ita gidan ya Nabila saboda zuwan malamin dan ya samu damar aiwatar da abinda zai aiwatar, duk da yace gidan ma dole ne ayi aiki akansa amma yafi so su dauke ta daga gidan baki daya hakan zai saukaka musu aikin, hakan kuwa akayi a daren ranar suka dauke ta ba tare da sanin kowa ba suka tafi da ita.
Bayan tafiyar su Alhaji ya farka a firgice yana kwala kiran Ummi, Hajiya mero da take tunanin yana bayan ta tana jin abinda yake ta sake tsurewa gashi lambar malamin ta sam bata tafiya not reachable gashi arkel ya saka tsaro wasu manyan maza ne masu siffar samudawa ke gadin gidan gaba daya.😂😂😂
***
Dakakkiyar shadda light brown ya saka ya kafa hula damanga sai sheki da kyalli take, agogon hannun sa na kamfanin apple yayi kyau ainun, so yake yaje ya dauko Maryam dan ya ji fa ba zai iya hakura ba har zuwa yadda aka ce gwara kawai ta dawo daga kusa dashi kafin ranar da za'a zauna, duk wasu shedu da hujjoji ya gama hada su waje daya ya damka wa Barr. Nasir yana jiran ranar, a jikin motar sa ya tarar da Arab yana jiran sa, yana bude motar shima ya bude ya shiga.
"Yau dai dole na ga matar mu, nasan dai wallahi can zaka."
"Haka nace maka? Wajen aboki na zani."
"Aboki? Haba malam nafa sanka, wanne abokin kake dashi?"
"Toh zama zan tayi a yadda ka sanni kenan."
"Eh toh kusan haka ne ai."
"Toh ba haka bane, na chanja sosai fiye da yadda kake zato."
"Tabbas na gani kuwa, ga babban chanji nan na gani, shiyasa nake so naga wadda ta sace ma kanina ciyazu, har tasa ya zama haka."
Da Sauri Arkel ya kalle shi
"Nifa ba kanin ka bane, girman mintinan awa ga bani ne wai? Haba mr man gyara maganar ka."
"Ko sakan nawa ne dai na girme ka yaro kake waje na."
"Sai kayi ai."
Dariya Arab ya saka har da buga kujera, da haka suka karasa kofar gidan anty Maryam, da sauri Arab ya ɓalle murfin motar ya fito yana gyara jikin sa
"Bari na ga ko zata gane ka, ko zata rungume ni a matsayin kai lover biyu."
Dariya ya saka Arkel yayi saurin fitowa yana hararar sa
"Wallahi karma ka fara kaji na rantse, mata ta mata ta ce."
"Matar mu dai point of correction."
"Kaji da..."
Bude gare ɗin akayi hakan ya saka Arkel yin shiru yana kallon ta, kokarin daidai ta kanta take ganin su su biyu babu abu daya da ya banbanta su, sai ta kasa karasawa ta tsaya tana kallon su, ta kalli wannan ta kalli wannan ta rasa me zatayi kuma.
"Taho mana matar..." Arab yace yana cin Serious Kamar gaske
Harara Arkel ya sakar masa hakan yayi saurin bata satar amsa dan tasan babu yadda za'a yi Arkel yace mata matar. Bude mata hannu yayi alamun ta taho gare shi, da sauri Arab ma ya bude yana sake kanne idon sa. Ganin haka yasa Arkel karasawa ya rungume kayar sa tsam a jikinsa. Baki bude Arab ya saki yana kallon ikon Allah, lallai ma gayen nan ya bala'in raina masa hankali, wato dan yaji haushi ya aikata hakan kenan, aikuwa ya shak'a su kuwa suka hau nasa dariya Maryam harda kwallar ta ganin yadda Arab ɗin keta yarfe hannun daya bude alamun kamar abu yake nema.
Karasowa yayi suka gaisa yana dariyar kansa shima, farin ciki ne yake shigar sa ganin yadda rayuwar dan uwansa ta ji gaba, harɗe hannu kawai yayi yana imagining kansa a condition din, lalli dole yayi aure da komai ya lafa dan ba zai juri kallon su suna soyewa yana gefe ba😅
**
Niko nace yazo ya zaba ga su nan ko hudu yake so zan bashi
#teema gabas
#meema
#pinky
#Sai wama dayar? Ba ruwana Anty Farida ki fara shirin biki kawai 😂🤾
#Not edited 🙈
_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A HALIN YANZU😁._
*ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma
*SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano)
*KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo)
*BURI ƊAYA!* (Mamu gee)
*WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull)
👇🏻karku bari ayi babuku
*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*
*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*
Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank
Saika tura shaidar biya ga wannan number ta WhatsApp
08030811300
Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN ta wannan number din
07067124863
Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.
*Karki bari ayi babu ke, Abari ya huce shike kawo rabon
Rano🚴🚴🚴
***
*39-40*
©*Hafsat Rano*
*_ZAFAFA BIYAR na kudi ne idan kana son kowanne daga ciki ka nemi Wannan numbers din_*
*08030811300*
*07067124863*
***
A hankali ya rada mata
"Tafiya zamuyi fa."
Da sauri ta d'ago, daga kansa yayi sai tayi dariya
"Malama don't pretend kema so kike ki tafi na gane ai."
"Ni nace haka?"
"Ko baki fada ba, na sani."
"Allah ni bance haka ba."
"Kin fada mana, ta zuciyar ki, U know I can read tru ur mind.".
Dariya tayi kawai,
"Toh ku shiga kuyi ma Anty Maryam sallama, dan bata san ma tafiya zan ba."
"Toh shikenan, fara shiga sai ki faɗa mata, sai mu shigo."
"Owk."
Komawa yayi wajen Arab daya harɗe yana waya da Mutsapha, taɓe baki yayi ganin ya nufo shi yayi wa Mustapha sallama sannan ya kalle shi.
"Ka gama soyayyar ne? Mr Lover Boy?"
"Ina ai ba'a gama wa, saboda tuxurai irin ka, dole mu rike wuta ko zakuyi zuciya dai kuma."
"Kan bala'ee, amma wallahi ka cini wasa."
"Sai ka tsaya ai, saura kiris ka ganni da baby ma, kaji ana dada, dada daga nan zaka gane ai."
Duka ya kai masa ya goge yana dariya, a haka Maryam ta fito ta tarar dasu suna tsokanar juna, sai suka bata sha'awa.
Shiga ciki sukayi suka gaida Anty Maryam, a sace take kallon su, ba karamin birgeta sukayi ba, sai ta dinga hango Areef ɗin da sun girma suma haka zasuyi, dama suma gasu identical, har sun fara rarrafe ma kamar ka sace su very cute Masha Allah. Fita sukayi kowanne su dauke da yaran dan suma sun shiga ransu yan kubul-kubul dasu kamar yayan turawa, daki Anty Maryam ta jata ta kwaso shirge shirgen kayan gyara ta cika mata wata babba leda bayan ta gama mata bayanin kowanne su, aikuwa ta hau kunya tana wani murmushi dan wasu bayanan sun fi karfin kai na nima🤭.
Kayan ta ta kai mota sannan ta karbo yaran ta dawo dasu ciki, suka tafi. Gidan Ya Nabila suka nufa Arab dai sai tsokanar su yake Maryam nata aikin dariya Arkel kuwa ji yake kamar ya mazge shi ya huta, haka dai ya daure suka karasa. Maryam bata san Ummi na gidan ba sai da suka shiga ciki ta ganta, idon ta biyu a zaune akan wheelchair din, da gudu gudu ta karasa ta zube a gaban ta farin ciki kwance a fuskar ta, kuka ne ya taso mata cike da tausayin baiwar Allah, sai ta durkusa a wajen ta saki kuka a hankali. Kukan Ummi ta saka itama ta mika mata hannu alamun tazo gareta, hannun ta ta kama ta rike a hankali ta furta
"Daina kuka yar albarka, alhamdulillah na samu sauki ai.".
"Ummi..."
"Alhamdulillah."
Kallon kowa tayi na falon idon ta ya sauka akan Arkel, ido ɗaya ya kanne ya girgiza mata kai, alamun tayi shiru, sai tayi kasa da kanta tana murmushi. Ya Nabila ce ta daga ta sannan suka shige ciki, dakin ta kaita sannan ta dawo ta tura Ummi ta kaita, fitowa tayi ta kwashi sauran kayan da sauri Arkel ya tsaida ta
"Tafiya zamuyi fa."
"Toh ku tafi man, wana rike?
"My wife mana, naga kin shige da ita."
"Anan ai zata kwana, kuje kawai sai da safe."
"Inaaa."
"Toh muje ko?" Arab yace yana kunshe dariyar sa. Key ya wurga masa yana kallon ya Nabila
"Kaje kai ni gaskia ba tafiya zan ba."
"Toh shikenan, ga BQ nan sai kaje ka kwana, Kanina ka gaida gida."
"Gida ya ji, sai da safe."
Marairaice fuska Arkel yayi, duk suka saka dariya, haushi ne ya kamashi yayi kicin kicin da fuska
"Please kice mata ta fito mu tafi dare."
"Allah ka zama mara kunya, saboda tsabar rashin kunya ni ba cewa nayi zan rike ta ba, magana kawai na shiga zamuyi sai ka zauna ka jira mu gama."
Sosa kansa yayi kunya duk ta kamashi amma sai ya basar yana zama, gaban Arab ta taka tana kallon sa
"Har yanzu ka kasa fuskantar ta? Ya kamata kayi magana da ita."
Take annurin fuskar sa ya dauke
"Tsoro nake walalhi, karki manta laifi
27, January 2025
Rukayya
Good