Showing 51001 words to 54000 words out of 98004 words
taji ya turo kofar, sai da wata masifaffiyar kunya ta taso mata amma sai ta dake har ya karaso yana kallon ta irin kallon up and down din Nan, ba kadan ba tayi masa kyau dan tayi shar da ita so cute Masha Allah. Nan fa mutumin ku ya kara shiga ciki ya dora kansa saman bayan ta suka kurawa juna ido ta cikin tafkeken mudubi da ya kusa cinye jikin su taf, ita ta fara dauke kanta saboda yadda ta ga yana wani lumshe ido tana budewa kadan kadan.
"U look gorgeous." Ya rad'a mata a kunne ta, wani irin yar taji tayi da saurin damƙe idon ta, hannu yasa ya juyo da ita tana fuskantar sa, gefe yaja yana screening din ta tayi kanta da kasa, dariya yayi kawai ya riko hannun ta, "muje nima a hada min ruwan." Make kafardar ta tayi tana dariya, dariyar yayi shima ya hau cire kayan sa. Da sauri ta fita daga dakin tana sauri kamar zata tashi sama. Shi kadai yake ta murmushi har yayi wankan ya shirya ya fito, tana zaune bata ji fitowar sa ba sai ji tayi yayi hugging din ta ta baya, da sauri ta juya suka yi gware, hannu tasa a wajen shima ya saka kamar tayi kuka saboda zafi. Yadda ta yi da fuskar ta ne ya bashi dariya ya dungure mata kai "raguwa kawai." "Allah baka ji zafi ba." Ta fada tana taba wajen, "Kawo na danna miki toh." Matsowa tayi ya zauna yana dan danna mata wajen a hankali yana kallon fuskar ta. "Bakya so ki ga umma?". Taji yace, da sauri tace "Ina so wallahi." Shiru yayi yana tunani kafin yace "ki shirya gobe muje kiyi registration sai ki je ki gansu."
Manage pls
*28* S K
©*Hafsat Rano*
*_ZAFAFA BIYAR na kudi ne idan kana son kowanne daga ciki ka nemi Wannan numbers din_*
*08030811300*
*07067124863*
*_Daurin boye_*
_safiyya huguma_
*_Buri daya_*
_mamuhgee_
*_Wutsiyar rakumi_*
_billyn Abdul_
*_Kai min halacci_*
_Miss xoxo_
*_Sauyin kaddara_*
_Hafsat rano_
*Assalamu alaikum, jiya nayi mistake ɗin sa Number instead of 26 nasa 27 afwan. A tafi a hakan kawai kar mu zama confuse. So yanzu Number 27 shine 26. Nagode*
°°°
Da sassafe ta tashi ta shirya tsaf saboda zumud'i, bata kira umman ba so take kawai sai dai ta ganta, dan in taji zata zo zata iya hanata shiyasa tayi shiru, har gidan anty Maryam take son zuwa zata tambaye shi idan sun je ya taymaka ya barta.
Tana gyaran gado ya shigo tun fitar sa sallar asubah be shigo ba, yana can suna magana da Alhaji da yake yana gari, maganar ritayar sa yake masa dan gaf yake da yin ritayar, kallon mamaki ya ke mata ganin ta a shirye daga gani shirin fita tayi. Be ce komai ba dai ya amsa gaiswar da take mishi ya haye gadon dan wani bacci bacci yake ji, dan fitar ma da yake da wuri wani lokacin yanzu ya daina sai dai yayi ta bacci, tsaye tayi tana kallon sa ita a tunanin ta wanka ma zai shiga dan har ta gama hada masa ruwa da komai, yana kallon ta ta kasan idon sa tayi kicin-kicin da fuska kamar zatayi kuka, ganin da gaske bashi da niyyar tashi yasa ta fita daga dakin, dariya yayi kawai ya maida kansa yana mamakin zumudin ta.
***
Hajiya Mero na ganin fitowar Arkel daga dakin tayi saurin fadawa tana addu'ar samun abinda taje nema,Ummi na kwance idon ta biyu taji an budo kofar, da sauri ta rufe idon ta ta dan bar shi kadan yadda zata ga komai, Hajiya Mero ce ta shigo tana kalle kalle, a gaban gadon ta tsaya tana yatsine fuska, kanta ta rankwafa wajen saitin kanta tace
"Kin ga karshen abinda kika jawo ko? Yanzu rayuwar da kike kina ganin dadi ce? Ke kika jawa kanki amma dai, ban yi niyyar akai haka ba, kika tursasa ni, ki sani rayuwar dayan dan naki ma gab take ta tarwatsewa, da shi da tsinanniyar yarinyar da kike ganin kamar itace jigon ku, yadda na juya tunanin kowa naki daga kanki, har yar cikin ki, haka zan juya tasu yanzu, zaki kare rayuwar ki ne a haka in dai ina numfashi."
Numfashin Maryam ne ya dauke saboda tsabar tsoro, ta kama kofar kenan zata shiga taji wannan maganar, da sauri ta ja da baya da baya ta haye saman da mugun gudu, a falon ta tsaya tana matukar haki, ta rasa me zatayi, kawai sai ta fara zagaye tana kai wa da komowa, dakin da yake ta shiga tana neman bugewa da kofa, bude idon sa yayi ganin ta a kansa tana haki, kallon da taga yana yi mata ne yasa tayi saurin saita kanta.
"Menene.?" Ya tambaya yana nazarin ta
"Um.. um dama so nake ka taymaka min na daga Ummi, so nake na sata a wheelC din na zagaya da ita kafin ka tashi."
Be musa ba ya sauko, hannun ta ya riko ganin kamar rawa yake, da sauri ta kalle shi, hannun ya kalla tayi saurin kallo itama.
"Are You ok?" Ya tambaya yana matse hannun nata, bata iya magana ba sai kawai ta daga masa kai, be kuma magana ba har suka sauko kasan, tsoron ta ne ya karu tana tunanin abin da zasu tarar.
Tana tsaye a kanta suka shigo, yadda tayi firgigit da ta gansu ya kamata ace gogan ya dauki wani haske, amma sai kawai Maryam taga ya matsa jikin gadon yana kokarin d'ago Ummin
"Ina kwana?" Yace yana yin abinda ya kawo shi
Cikin in ina ta amsa tana ficewa daga dakin bayan ta aika wa Maryam da wani irin kallo me cike da ma'anoni da yawa.
Ajiyar zuciya Maryam ta sauke ta rasa ta ina zata fara sanar masa, haka dai ta taymaka masa suka dora ta a kujerar, shi kadai ya fita da ita ya zazza gaya sannan ya maida ita. Wanka ya fara sannan yayi breakfast suka fito, manyan kaya ne a jikin sa ta zarce masu ruwan bula, a hannu ya riƙe hular hakan ya zama kamar wata dabi'a tashi, ita kuwa Maryam hadadden lace na cikin kayan lefan ta ta saka pink and ash ɗinkin bubu, tayi kyau sosai kana ganin ta ka ga amarya tayi fresh da ita abun ta. Zainab na fitowa suna fita, sosai suka birge ta ba karya ta san ko ta ina sun yi matching, kallon kanta ta sakeyi ta zauna tana jin haushin kanta.
School suka fara zuwa tayi abinda zatayi yana zaune yana jiran ta a mota, kawayen ta su Asma'u sai tsokanarta suke yi ita dai kawai murmushi take yi, sun jero zasu rakata wajen mota sai ga Saddi da jama'ar sa, wani kallon kasa kasa ya ke mata tayi saurin had'e ranta dan ma kar yayi mata magana, da sauri ta karasa wajen ta bude motar ta shiga tana daga musu hannu. Duk abinda ya faru ashe yana gani har sanda Saddi yake kallon ta, gani tayi yayi kicin kicin da fuska ya figi motar da gudu, shiru tayi tana tunanin abinda ya chanja masa mood, gashi ya tsare gida babu halin tambaya.
Yana ajiye ta a kofar gidan ya dauke kansa gefe, kin fita tayi tana kallon sa, jikin ta ne yayi sanyi
"Ki gaida umma idan na dawo zan shigo." Taji yace
Kin fita tayi, juyowa yayi da nufin magana idon su suka sark'e da juna, marairaice fuska tayi kamar zata yi kuka, kauda kansa ya kuma yi kawai ta saka hannu ta riko shi
"Kayi hakuri." Tace muryarta na dan rawa, Bata san me tayi masa ba amma tasan tabbas fushi yake da ita tun da yaki kallonta
"Kaji dan Allah,." Ta sake maimaita jin yaki cewa komai.
Hannu sa ya zare ya danna lock din motar, dama tint ce ba'a ganin na ciki ta waje, ta zata cire hannun nasa da yayi fushin ne sai ji tayi kawai ya jawo ta jikin sa
"Baki yi min komai ba fa, kawai ji nayi ina jin fushi."
"Haka kawai?" Ta tambaya
Daga mata kai yayi
"Ka faɗa min pls."
"Kinsan me? I'm just jealous dana ga kazamin yaron nan yana kallonki, saurayin ki ne ko?"
Ya dan danne mata hannu da karfi yana bata fuska, da sauri tace
"Allah ba saurayi na bane, ni bama magana nake dashi ba."
"Fadi gaskia dai, nasan halin samarin jami'a, in sun ga me kyau."
Dariya ta saka ta boye kanta a jikin sa.
"Allah ba haka bane."
"Toh shikenan na yarda, Amma one condition sai dai aka fara lectures kina saka nikab gaskia."
"Mika?" Ta zaro ido
"Yes of course, ko ba Zaki saka ba?"
"Hmm, bari na shiga sai ka dawo." Tace tana zare jikin ta dan bata ma san maganar taja da yawa Allah ya gani bata son nikab. Hana ta fita yayi yace
"Kin fasa shiga ma gidan komawa zamuyi kawai tun da ba zaki sa nikab ba."
Da sauri tace
"Zan saka wallahi."
Dariya yayi, kiss yayi mata a saman hannun ta sannan ya bude mata kofar.
"Da wuri zan dawo mu tafi."
Kallon sa tayi yayi saurin cewa
"Kin ga saboda Ummi ko?"
"Haka ne, sai ka dawo tom."
Tana fita ya shafi kansa yana murmushi, a hankali ya furta
"Saboda Ummi da kaina zan dawo da wuri, i just want u close."
Hannu ta daga masa ta shige ya k
Ja motar ya bar kofar gidan.
Da gudu gudu ta karasa shiga gidan, Habubu ne ya fara ganin yana wajen kajin sa da ya zuba yana chanja musu ruwa, ihu ya hau yi ga yaya Maryam su Walid suka fito da sauri. Murnar ganin ta suka hau yi kowa so yake ta kula shi. Umma na daki taji ana ga yaya Maryam, da sauri ta fito fuskar ta dauke da tsantsar farin ciki ta hau yi mata lale marhabin.
Kamar wata bakuwa haka aka mai da ita, komai aka debo aka zube mata a gaba, farin ciki bakin ta yaki rufuwa gata ga yan uwan ta.
Zuwan ba karamin dadi yayi mata ba, bayan yaran sun gama murna suka kulle a daki da umma ta fara bata labarin abinda yake faruwa, sosai al'amarn ya bawa Umma tsoro sai dai bata nuna mata ta karaya ba, shawarwari sosai ta bata ta kuma jaddada kar tayi sakaci da addu'a dan ita ce makamin mumini.
Be tashi dawo wa ba sai bayan magriba hakan kuwa yayi mata dadi kamar kar ta tafi gida dadi, shigowa yayi suka gaisa da Umma lokacin Baba ya dawo shima suka gaisa, da zasu tafi umma ta saka suka shiga gidan Hajiya Mama suka gaishe ta sannan suka je suka gaida Alhaji Faruku yaji dadin ganin su kuwa sosai dan har kudi ya bawa Maryam ɗin ko zata bukata. Da haka suka yi musu sallama suka tafi.
***
Arab da Mustapha Basu isa Sokoto ba sai wajen magriba, hakan ya saka babu wani abu da suka iya aiwatarwa, washegari tun kafin ya tashi Mustapha ya fita, bashi ya dawo gidan ba sai bayan azahar, lokacin Arab ya gaji da kiran shi a waya ya hakura, da harara ya bishi ganin ya shigo yana wani wash Allah alamun ya gashi, a hotel dama suka sauka abincin da yayi musu order ya nuna masa da hannu, kai ya hau ci ba kakkautawa saboda ba karamar yunwa ya dauko ba, gidan wani babban malami abokin babanshi yaje wajen sa ya sanar masa da matsalar abokin nasa, be rufa ba kaf labarin ya kwashe ya fada masa, ya jinjina lamarin kuma ya gane sihiri ne akayi masa aka raba shi da yan uwan sa, sai dai dole sai ya dage da addu'a dan ba karamin kulli akayi musu ba. Magunguna ya bashi na su ganyen magarya, habbatussaudah sai ayatusshifa sai wani rubutu sannan yace lallai suzo tare gobe akwai tambayoyin da zai yi masa. Babban matsalar shine ta yadda zai fara sanar masa da abinda yake shirin yi, ya san kafiya irin ta shi ba lallai ya yadda ya sha maganin ba.
Har suka tashi da safe suka shirya ya kasa sanar masa, sai da suka dau hanya ne idea ta fado masa, da sauri yace
"Man, kasan wani abu?"
"Sai ka fada."
"Wani babban malami ne abokin me gidan mu, tun wani zuwa na kebbi aka sa nazo na karbi wani dan rubutu haka dai kasan Rayuwar yanzu sai kana tsare kanka da yan addu'o i gamu mu da muke cikin kabilu mabanbanta ina ganin why not mu k'arasa kawai mu karba sai ka rakani family house din mu kaga dangi na."
"Owk hakan yayi, kace main family ɗin ku anan suke kenan?"
"Eh gaskia kusan haka ne, aiki ne kawai ya kai me gidan namu Kebbi."
"Owk."
Da haka ya samu ya hada mishi duk magungunan Malam yayi mishi bayanin yadda zai yi amfani dasu, daga nan suka je chan arkilla main house din su Mustapha, anan ne jikin Arab yayi sanyi yaji dama shine sai dai hakan ba me yiwuwa bace. Kwanan su uku suka koma Mustapha ya tattaro ya dawo gidan Arab saboda dai magungunan dan idan babu me sashi yasha toh ba zai sha ba.
***
Ran Hajiya Mero ya baci sosai, gidan Hajiya Mama taje ta wuni a hanya ta kira Asi suka hadu, maganar Hafiz tayi mishi taki shiru babu wani abu da yace gashi lokaci yana ta tafiya, kiran Hafiz din yayi kawai yazo ya same su. Sai da ya dan bata lokaci sannan yazo, yadda Hajiya Mero ta hau shi da masifa da bala'i ransa yayi mugun baci, shi fa dama baya daukar raini kuma ba'a nuna masa yatsa, a ransa ya ayyana abinda zaiyi ko dan ya fanshe cin mutuncin da tayi masa. A take ya karbi aikin su ya tabbatar mata a daren yau komai zai wakana, ta zama cikin shiri ita ma sannan ta tanadi kudi. Da haka sukayi sallama ya koma gida yana tunanin babban dalilin da yasa Hajiya Mero ta nace sai lallai shi zai yi mata aiki, bayan gashi tana da yara irin su Asi amma me yasa sai dai shi? Bashi da amsar haka ya hakura ya jira zuwa dare kamar yadda suka tsara.
***
Girki tayi ta gama wajen magriba, wanka ta shiga tayi sannan tayi alwala, sai data fara sallah sannan ta hau shirya wa, gidan Yaya Nabila zasu je tun rana ya fada mata, tasan yana kusa tun da ce mata yayi ta zama cikin shiri da anyi magriba zai dawo. Aikuwa ana idar da Sallah taji shigowar sa, be shigo dakin ta ba nasa ya wuce baya jin zai iya cin komai haka ya ajiye kayan da ya shigo dasu ya fito, tun dazu yaya Nabila ke kira shiyasa kawai ya haqura da abincin idan yaje chan yaci.
Lokacin da suka fito zasu tafi Hajiya Mero na falo, farin ciki sosai tayi ganin sun fito da alama fitar zasuyi, hakan yayi mata dadi sosai komai zai tafi yadda ta shirya, suna fita ya kira Asi ta sanar masa sun fito,Hafiz ya kira yace su hadu a in da sukayi zasu hadu.
Yau ma manage😝 Affan ya hanani typing kememe wlhi, hannu na yake rikewa yana ihu😔
Mun dai kusa zuwa in da muke so. Zuwa in Sha Allah.
Thanks for ur soyayya 😍😍😍😍
SAUYIN KADDARA
29-30
***
Ciki ya shiga wajen Inna, suna zaune da suwaiba tana waya k'asa-k'asa, tana ganin shi tayi saurin shigewa daki, dariya inna tayi ganin ya bita da kallo tace
"Dama ina jira shigowar ka, yaron da yake neman Suwaiba ne yace mata wai zai turo, shine nace bari na sanar maka dan kai yanzu ba zama kake ba."
"Aure ya zo kenan, Allah ya sanya alkhairi." Yace yana daukar kwanon abincin sa, budewa yayi a wajen ya fara ci sama sama inna ke yi masa hira sai ta ga kamar bashi da walwala da nutsuwa ba baki daya, tunanin abinda ta aikata masa ne ya fado mata, tun jiya take fama da abin tun bayan saurayin Suwaiba yace zai turo, sai a lokacin tayi tunanin irin bacin ran da iyayen Maryam suka ji lokacin da ta aika aka ce musu sun fasa, bata taɓa auno abin a ranta ba sai yanzu da maganar Suwaiba ta tashi sai taji idan ita akayi wa haka dole abin da ciwo, shiyasa gaba daya ta rasa sukuni jiya sai yau ne ma da yake ta dan fita taji dama-dama. Tana ta tunanin taji ya ajiye kwanon ya na kokarin fita tayi saurin dakatar dashi
"Zo ka zauna, magana zamuyi."
Sai da ya fara kallon agogon wayar sa kafin ya dawo ya zauna ɗin yana fuskantar ta
"Kayi hakuri da abinda zan fada maka, a matsayi na na mahaifiyar ka dole ne idan naga abinda zai saka a matsala nayi iya kar iyawa ta naga na tsare ka da abun, bansan ashe ba haka ya kamata nayi ba, ban kyauta maka ba Hafizu, kuma ban kyautawa yarinyar da iyayen ta ba, na manta Allah shine yake azurta bawa a duk sanda ya so, ni a ganina hakan shine maslaha ga dukkanin mu, ashe ba haka bane."
"Wai me ya faru ne inna? Irin wannan wa'azi haka?"
Murmushi tayi tace
"A lokacin da naje Gumel sai nake bawa Baba Ladingo labarin halin da muke ciki, toh a gaskia ita ta bani shawarar cewa na tura ka chan Gumel din idan yaso sai na tura gidan iyayen yarinyar nace musu ka janye suyi wa yarinyar su aure..."
Wata irin zabura yayi da jin abinda tace ba zato,
"Na san halin ka sarai idan nace ka hakura ba zaka hakura ta sauki ba, shiyasa nayi hakan ni a tunani na shine daidai."
"Innalillah wa inna ilaihi raji'un, yanzu inna dama aikawa kikayi kika ce na fasa? Haba Inna, haba Inna ya zakiyi hska? Idan suwai akayi wa haka inna ya zakiji? Wallahi inna ban taba ko da da rana daya tunanin matsalar daga mu ne ba, hakan tasa na kullece su kulla ta me ksrfi,kinsan halin da nake shirin sa kai na kuwa Inna? Innalillah wa inna ilaihi raji'un."
"Tabbas nayi maka laifi, amma na riga ya wuce yanzu, kuma tabbas ban kyauta ba ko kadan, na biye wa shedan tun da shine dama baya so ayi sunnar ma'aiki, in Sha Allah zan je kafa da kafa har gida na bawa iyayen ta hakuri na wanke ka kuma,ayi hakuri."
Bashi da abinda zai ce kuma, uwa tafi gaban wasa, dan haka sai kawai ya tashi ya bar dakin yana jin kamar ya dora hannu aka yayi ta kurma ihu. Uban kiran da Asi ke tayi masa ne ya dawo dashi daga
27, January 2025
Rukayya
Good