Showing 63001 words to 66000 words out of 98004 words
ce, hannu ya mika musu suka gaisa.
"Tana ina?"
"Muje sir."
Har dakin Zainab ya kaisu ya sa hannu ya kwankwasa kofa, gaban Hajiya mero ne ya fadi da sauri ta rike Zainab
"Karki bude dan Allah."
"Amma mummy me yasa? Me wai yake faruwa ne? Waye dayan that look exactly like him."
"Dalla karki isheni da tsinannan tambaya, mafita kawai nake nema ba zancen banza ba."
Sake buga kofar akayi, tashi Zainab tayi kawai ta bude aikuwa sai ga yan sandan nan sun dira a cikin dakin, wani irin zawo ne ya tasowa Hajiya mero tayi toilet da gudu, riko ta macen tayi tana cewa
"Ita ce sir?"
Daga mata kai Arkel yayi yace
"Yes."
"Za muje dake Station muna so Zaki amsa mana wasu tambayoyi."
"Na shiga uku? Me nayi wai? Menene haka arkel? Ya zakayi min haka? Ka manta wacece ni?"
Kin magana yayi, magiya ta hau yi tana turje-turje. Tsaye yayi kawai yana kallon ta, ihu da haukan ta ya cika gidan gefe daya zainab na tayata da kuka dan bata san mene ke faruwa ba,
"Dan Allah kayi magana, karka bari su tafi dani, shirin nan naka yana kashe ni kayi magana dan Allah, wayyo Alhaji menayj musu zasu kashe ni?"
"Dan sake ta Madam." Ya fada
A hankali ya furta
"Where is my wife?"
"Ban gane ba, matar ka kuma? Aina?"
Dan murmushi yayi yace
"Sambo da Asase, Malam lado, nurse Latifat, Hajiya Turai?"
Zamam yan bori tayi jin waɗanda ta ambato, be sake magana ba ya juya ya bar dakin yana kokarin kin kallon Zainab, haka suka fito da Hajiya Mero suka tisa k'yeyarta, tana ihu tana kunji suka tura ta amota suka tafi da ita.
*So sad🤪*
***
D'akin Ummi ya koma, a gefen ta ya zauna ya sadda kansa kasa, tana kallon sa, hawaye ne kawai ke bin fuskar ta, komai na jikin ta na aiki, hannu, kafa, ido har ma maganar ta ta dawo sai dai ba zata iya wani kwakkkwaran yunkuri ba saboda shekarun da yawa, Arkel ne ya budo kofar ya tsaya yana duba abu daga nesa, ganin bashi da niyyar yi masa magana yasa ya taso
"Bro."
Da Sauri yace
"What?"
"Baka ganni bane? Are you not happy to see me or what?"
"Eh toh kusan hakan ne, amma right now ba zan iya baka amsa eh ko a'ah ba, I'm very busy as u can see."
Kallon sa yayi, da confidence yake masa maganar alamar da gaske dai be yi wani mamakin ganin sa ba, juya masa baya yayi ya gama abinda zai yi a dakin ya fice.
Wayar sa ya dauko ya kira Mustapha, yana dauka yace
"Man ka sauka? Ina ta kiran ka baka daga ba, ya gida ya kowa."
"Alhamdulillah wallahi, Komai lafiya, Number malamin nan zaka turo min, ina so muyi magana naji yadda za'ai."
"Karka damu, na sanar dashi komai, ya gama shirya wa ma jiran lokaci kawai yake, yanzu in sha Allah zan bari weekend zan je sai mu taho kanon tare dashi, duk da dai ya girma ga shekaru, amma a hakan zamu zo in Sha Allah."
"Alhamdulillah, U r indeed a true friend, bansan me zan ce maka ba, all I know shine in Sha Allah I ll repay this kindness."
"Haba haba, karka wani damu, ka nutsu kawai in Sha Allah komai yazo daidai, dnt stress ur self."
Jinjina kansa yayi,
"Shikenan, Thanks."
"Welcome."
Ajiye wayar yayi ya duba Ummi, kasa ya sauka ya durkusa
"Ummi...."
Dan jim yayi kansa a kasa yace
"Bansan da wane baki zan fara magana ba, bansan me zance ba, dan girman Allah kiyi hakuri, ki yafe min, hakika ban chanchanci yafiyar ki ba, ban cancanci ki kalle ni ba ma, dan Allah Ummi nah, ki yafe min."
Kuka ne yaci karfin sa ya shiga yin sa wiwi, daga hannun ta take tana magana a hankali, be ji ba saboda yadda yake kuka sannan Muryar tata bata fita sam, haka yayi tayi tsawon lokaci kafin ya tashi yana jin kansa na juya masa.
Ya dade a zaune yana duban ko ina na dakin, haushi kansa yake ji gashi sam ya kasa sukuni, so yake suyi magana da Arkel ko yaji saukin abinda yake ji.
Turo kofar akayi, da gudu ta karasa shigowa ciki, tsayawa tayi tana kallon sa, shi din ma ita yake kallo, babu wani dalili ko abu da zai sa ta kasa banbance su, tare suka taso komai nasu daya ne, mik'ewa yayi da dukkanin karfin sa, sai kuma ya tsaya yana kallon ta, a dah babu wani shamaki zai rungume ta sai yau yaji kamar bashi da karsashin ta zai iya fuskantar su, ba shi da fuskar da zai iya kallon ta, baki sake take sake kallon sa
"Ya bilaaaa.."
Ya ja sunan yadda ya saba faɗa mata, sai data ji abin akanta, wani irin yanayi ya zo mata abubuwan da suka faru a baya suka fara gudu a zuciyar ta, ta rasa a wanne irin yanayi zata ajiye abinda take ji, farin ciki ne ko me? Yadda ta tsaya still tana kallon sa yasa shi karasa wa, rungume shi tayi ta saki kuka me cin rai. Har cikin ransa yake jin kukan, babu abinda ke masa yawo akansa sai tunanin halin daya jefa kowa akai, sakin sa tayi tana ja da baya
"Moha..."
"Kaine? Ashe zan sake ganin ka? Why? Why?"
"Am so sorry, am sorry."
"Alhamdulillah ya Allah, Alhamdulillah."
"Ya Bilaaaa... Ya bayan rabuwa, kin ga yadda abubuwan suka zama ko? Haka na tarwatsa komai? Haka nayi da rayuwar mu?"
Da sauri tace;
"Baka yi komai ba, haka Allah ya tsara nice dai me laifi, ban kula da Ummi yadda ya kamata ba, Arkel shi kadai ne yake komai, babu wanda ya damu da halin da yake ciki, me yake yi? Ina yaje? Me Ummi take bukata? Wacce irin rayuwa mukayi haka!"
"Allah ya gani bansan in da zan yi da rayuwata ba, bansan menene ya hau kaina ba, bana jin komai a raina, Ya Allah... Me muka aikata ne wai?"
Girgiza kai kawai yake Ummi dake jin su babu abinda take sai tsiyayyar hawaye, duk abinda ya faru itace sila, ita ce musambabin komai, gashi abun da hakan ya jawo mata.
***
Zainab na fita tayi gidan Hajiya Mama, tana tafe tana kuka har ta karasa, Hajiya na ganin ta ta mike da sauri.
"Menene ya faru.?"
Kuka take taki magana, hakan yayi mugun kular da Hajiya ta buga tsaki tace
"Ke dan ubanki kinzo kin sani a gaba kina kuka, uwar me akayi miki?"
Kwafa tayi ta juya fuska ganin taki magana, sake jan tsaki tayi yadda kukan ke hawa mata kai ta kai mata bugu tana cewa
"Kin tashi kin bani waje ko sai na kakkarya miki kafa, kinzo kin sani a gaba da shegen kuka ke murya ba dadi ba, Haba!"
Cikin muryar kuka tace
"Mummy ce aka tafi da ita Station."
"Ina ne kuma Station, dalla kiyi min bayani."
"Police station fa, yan sanda ne suka tafi da ita."
A zabure ta mike har tana kusan yadda zani
"Yan me? Yan sanda kuma? Na shiga uku ne indo."
"Me ya faru haka? Na shiga uku."
"Nima ban sani ba."
Sultan ya hau kwala wa kira, daga nan ta koma Rauda, sai Maman su, a tare Rauda da Maman tasu suka shigo a tunanin su wani abu ne ya sake ta.
"Ina Abban su, ayi maza a kira shi ba lafiya."
Basu tsaya tambayar me ya faru ba Rauda ta ruga ta dauko wayar ta a daki ta kirashi, a gaggauce ya ajiye abinda yake ya taho gida yana fatan kome ne ya zama da sauki.
***
Hafiz ganin inna sun nutsu sai ya sudade ya dawo, yana zuwa Number Arkel ya nema, be wani sha wahala ba ya samu, kiran sa yayi yace yana so su hadu.
Wajen magriba suka yi zasu hadu, ranar duk abu daya kawai arkel ke tayi har wajen magribar be nutsu ba yana so ya tabbatar da abinda ya saka a gaba komai ya tafi daidai, haɗuwar su da Barr.Nasir ce ta sake rike shi sosai gashi Asase da Sambo na tsare har ma da shi kansa Malam Lado wanda shine ya taimaka aka samu su Sambon, kansa ya dau zafi sosai sai dai hankalin sa na kwance saboda yasan Ya Nabila da Arab suna tare da Ummi, duk wani abu da ya kamata suyi mata ya san zasuyi, mutum daya yake jira yaga yadda zai yi shine Alhaji da ake saka ran dawowar sa gobe.
A in da sukayi zasu hadu suka hadun sai dai zaman jiran da Hafiz din yasha kafin yazo, bayan sun gaisa ya zayyano masa komai daga farko har karshe, jin sa kawai Arkel yake har ya gama sannan ya sauke ajiyar zuciya, hannun sa ya lankwasa ya dan jingina yana murmushi da shi kadai yasan manufar sa, Hafiz na kallon sa har ya gama sannan yayi masa godiya sosai, sannan yace zai neme shi lokaci kadan, maganar su Asase kuma ya barta a hannun sa, idan zai iya ya dawo da Innar sa daga Gumel babu abinda zai faru. Akan haka suka rabu a daren ya juya ya koma kafin inna ta tada hankalin ta idan ta lura baya nan.
A yadda ya gaji gida ya kamata ya wuce, sai dai a yadda yake ji ba zai iya ba sai yaje ya ganta. Gidan ya nufa ya kunna kira'ar Ghamid'i lokaci lokaci yana bi a hankali.
A hadaddun flask na Alhaji Rabi'u aka zuba masa tuwon semo miyar zogale, gefe kuma coconut milk shake ne yana ta kamshin flavours masu dadi ga kankara da akayi crushing aka watsa, a babban tray aka jera komai aka jiya. Wanka Anty Maryam ta sata ta fara yi kafin ya zo ya shirya tsaf, doguwar rigar abaya ta saka me masifar kyau anyi mata ado da wasu duwatsu farare kal masu matukar kyau da kyalli, kanshi kuwa da yake tashi ba'a cewa komai. Kamar anyi barin turare haka ko ina ya dau kanshi, Anty Maryam sai farin ciki take ganin yadda ta zage ta gyara kanta gashi nan ta fito kamar ka sace ta ka gudu, tana nan zaune suna dan hira da Anty Maryam duk rabin hankalin ta na chan ganin shiru be zo ba, wayar ta datayi kara ne yasa tayi saurin jawowa a tunanin ta shine, ganin kawar ta Asma'u ce ke kiran ta yasa ta ɗan bata fuska kadan sannan ta daga, maganar school da zasuyi resuming tayi mata suna cikin wayar kiran sa ya shigo, bata san sanda ta jefa Asma'u a hold ba ta d'aga da sauri. Tana daga wa yana kashewa, saboda yaji busy, samun kanta tayi da katse kiran asma'un ta sake kiran shi, yana d'agawa yace
"I'm out."
"Owk ka shigo tom."
"Um um... Ki zo dai ki shigo dani."
"Please ka shigo falon dazu."
"Nima please ki Zo ki shigo dani ko na koma."
"A'ah wait... I'm coming."
Da sauri ta tashi, takalmin ta flat ta zura ta rik'e wayar a hannu ta fito, a cikin motar ta hange shi, tsayawa tayi tana maamki, nufin sa kenan ta karasa, sai ta tuno ranar da yazo ya sata dole taje, tasan yau din ma hakan ce sai kawai ta karasa ta bude motar ta bangaren sa. Yana hakimce ya manna kansa da jikin kujerar alamun gajiya, idon sa a rufe yake daya ƙaraso sannan ya bude ya dora su akanta, kallon tsaf yayi mata kamshin nan ya bigi hancin sa, take yaji ya nemi kaso tamanin cikin dari na gajiyar daya kwaso ta ragu, hannu ya mika mata ta kama ta taimaka masa ya fito, gefe ya matsa ta rufe kofar sannan tace
"Ina wuni?"
"Gaisuwar ki kenan, ina wuni?"
"Toh me zance?"
"Hmm." Kawai yace yana girgiza kai
"Me zance dan Allah."
"Baki sani ba?"
Daga kanta tayi
"Owk bari kiga what i prefer."
Kafin tayi aune sai ji tayi yayi hugging nata tight, lamo tayi zuciyoyin su na karbar sakon kowacce zuciya, sai daya dade sannan ya sake ta
"Nafi son irin wannan gaisuwar, ina wuni kamar wata yar kauye."
Dariya ta saka kawai
"I'm serious fa, na soke ina wuni."
"Toh." Kawai tace tayi gaba dan taga alamar jan magana yake son yi, bin ta yayi suka shiga ciki, suna zama Anty Maryam tasa me aikinta Rabi ta kawo kayan abincin, tana ajiye wa ya zamo ya zauna yana tankwashe kafa, babu ko kara ya hau bubbud'e kwanukan, murmushin jin dadi yayi ya nuna mata gefen sa
"Sauko kiyi saving dina, ga yunwa ga gajiya, idan naci sai kiyi min massage kin ga idan dadin yayi min yawa sai kawai na karasa lada na na kwana nan."
"Anan!?" Ta zaro ido
"Kina mamaki ne?"
"Uhum."
"Ke dai bani abincin tukunna, sauran bayanin zaizo daga baya."
Da mamakin sa ta zuba abincin dan bata taba tunanin shi haka ba, ya sake sosai da ita a dan wanakin nan freely yake watso maganar sa babu wani kunya ko nauyi. Tana daga gefe tana kallon sa yake cin abincin yana lumshe ido, ba karamin dadi tuwon yayi masa ba, dadin dadawa kamshin dake tashi ta kowanne lungu da sako na gidan, gata ita kanta uwar gayyar tana ta feso masa nata, dukkan wata damuwar sa ajiye ta yake a gefe a duk sanda yake tare da ita, a hankali a hankali take shiga jikin sa, gashi har tana so tayi masa shigar bazata, wani abu me kama da mayen karfe ne yake fusgar shi zuwa gareta, babu tantama ko shakku, ya san ta samu tarbiyya wadda tayi wuya da karanci a wannan zamani.
Sosai yaci yasha milk shake din ya masa dadi ainun, cikin sa ya cika kamar zai fashe, tsalle ya tashi ya hau yi aikuwa Maryam ta samu abin dariya, dariya sosai ya bata ganin yadda ta daddage yana tsalle, ganin da gaske dariyar take sosai sai ya kara kaimi wajen tsallen dan ba karamin birgeshi dariyar ta ta take ba.
***
Hi dearies, I'm very very very sorry for the inconveniences. Ido ne sai godiyar Allah. I'm just managing saboda am not seeing clearly wallahi. But alhamdulillah sha. A kara hakuri dai dan Allah.,🤝🤲
Ba editing just manage a haka
_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A HALIN YANZU😁._
*ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma
*SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano)
*KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo)
*BURI ƊAYA!* (Mamu gee)
*WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull)
👇🏻karku bari ayi babuku
*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*
*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*
Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank
Saika tura shaidar biya ga wannan number ta WhatsApp
08030811300
Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN ta wannan number din
07067124863
Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.
*Karki bari ayi babu ke, Abari ya huce shike kawo rabon
Rano🚴🚴🚴
***
*SAUYIN KADDARA*
*37-38*
©*Hafsat Rano*
*_ZAFAFA BIYAR na kudi ne idan kana son kowanne daga ciki ka nemi Wannan numbers din_*
*08030811300*
*07067124863*
*_Daurin boye_*
_safiyya huguma_
*_Buri daya_*
_mamuhgee_
*_Wutsiyar rakumi_*
_billyn Abdul_
*_Kai min halacci_*
_Miss xoxo_
*_Sauyin kaddara_*
_Hafsat rano_
***
Zama yayi yana fuskantar ta, sai ta katse dariyar ganin ya zama serious alamun magana yake so suyi, hankalin ta dukka ta tattaro ta ajiye waje daya tana dan gyara zama, a kan kafarta ya jingina tasa ya sa hannu ya dora kafad'arta a saman tasa, shiru sukayi na wani lokaci kowa da abinda yake tunani, shine ya fara karya shirun ta hanyar riko hannun ta yasa a nashi, kadan kadan yake murzawa yana kallon hanya kamar wani ne zai shigo, ajiyar zuciya ya sauke ya dan ja baya kadan.
"Kinsan me?"
Girgiza kai tayi jin yana yawo da hannun sa cikin kanta dake tufke waje daya cikin ribbon
"I'm so happy yau, and it's because of you."
Dan cire kanta tayi ta kalle shi
"Yes, kece silar komai, ko kin dauka bansan me yake faruwa ba.?".
"Ka sani dama? Kasan komai?"
"Na sani, da taimakon ki na sani, kece fitila me haske data saka na gane komai, i owe you alot."
"Ummm... Alhamdulillah."
"Maryam..."
Sai taji wani yarr saboda shine farko a irin wannan yanayin daya kira ta da wannan sunan, yadda sound din ya fita sai taji kamar ba'a taba yi mata magana me sanyi da dadi irin ta ba, samun kanta tayi da sake narke masa har bata jin shi sosai saboda tunanin data tafi, tabo ta yayi ganin yayi magana sai murmushi take, da sauri ta yawance tana sunne kanta a jikin sa, sai ta bashi dariya yayi murmushi sannan ya d'ago ta yana mana duban tsanaki
"Yau na cika wani bangare na buri na, bangare mafi girma a rayuwata, a yau na tabbatar da cewa mace ta gari itace silar komai, alhamdulillah ya ALLAH, na gode miki."
"Me ya faru ne? Dan Allah ka fada min."
"Sai kin kawo cin hanci."
"Na me?"
"Umm bari na ga."
"Me?"
"Tashi kiga."
Tashi tayi yace
"Koma chan jikin kofar."
Komawa tayi tana facing d'insa, kallon ta yayi daga sama har k'asa yana danne dariyar sa, sai daya dan bata rai sannan yace
"Toh taho da gudu mu gani ko kin iya gudu."
"Gudu kuma?"
"Eh ni ba tsalle nayi miki ba, toh in ba zakiyi gudu ba yimin rawa toh."
"Na shiga uku, wallahi ba zan iya ba."
"Aiko kin fasa jin albishir ɗin da zanyi miki dah."
"Dan Allah,Dan Allah... kajiiiiii."
"Na'am?"
"Dan Allah, I'm eager fa."
"Toh shikenan, Ummi tayi magana yau...."
"Wayyo Allah..."
Ai bata san sanda tazo gabansa sai kawai gani yayi ta fada kansa tana dariya, dadi ne ya kamashi ganin yadda take farin ciki, be san wai har haka ta dauke su ba, sai kawai ya tsaya yana kallon ta cike da sha'awa, ita kuwa sai murnar ta take ta rasa in da zata saka kanta, sai daya bari ta nutsu sannan ya sanar mata da abinda ya faru a takaice, sosai tayi farin cikin dawowar Arab ɗan ji tayi ma kamar tace ita binshi zatayi kawai dan hankalin ta gaba daya ya koma chan, shi din ma haka ne sai dai dole zata zauna anan din kafin abinda suka shirya ya tabbata, daga nan sai komai ya daidaita, school ma da sukayi resuming sai dai ta yi hakuri zuwa lokacin da komai zai tabbata, ya riga ya tsara ya shirya musu daddadar rayuwa me cike da soyayya da shiga rai, babu wata tantama ko shakku ya riga ya san ya gama fadawa kogin son ta, lokaci kawai yake jira da zai tabbatar mata da hakan, anan ne zai sanar da ita abinda bata taba sani ba, da duk wani abu da ya shafi zaman ta tun daga ranar farko a gidan su, ko ma ace tun ranar daya fara dora idon sa akanta. Da kyar ya yakice ya tafi yana ji kamar su dawwama a hakan, sai
27, January 2025
Rukayya
Good