Showing 30001 words to 33000 words out of 98004 words

Chapter 11 - SAUYIN KADDARA COMPLETE HAUSA NOVEL

06 Jan 2025

11629

farko Zainab ɗin na bashi, tun da ita ce tawa, da babu wanda zai nemi ya gaya min magana, amma babu komai, zan dau mataki da kaina."

"Da dai kin bar sun kawai, sai kiyi tunanin yadda zaki ɓullo musu ta bayan gida, tada hankali ba shine zai warware komai ba."

"Haka ne kuma, nasan me zanyi kawai."

"Shikenan,kibi komai a sannu."

Mik'ewa tayi ta goge fuskar ta,

"Toh Hajiya, bari na koma na kwantar da kai naji komai wajen Alhaji, in sun san wata basu san wata ba."

Hmmm...🙄🙄🤔

***
Tatar koko Suwaiba keyi sana'ar da Inna ta fara tun bayan dawowar ta daga Gumel, sallamar da taji ne yasa ta d'ago da sauri, sakin abin tatar tayi ta hau dariya

"Yaya sannu da zuwa."

"Sannu suwai suwai, tata ake yi ne?"

"Eh, Inna! Inna!! Ga yaya ya dawo."

Ta hau kwala wa inna kira, kamar a mafarki inna taji kiran, da sauri ta bantari goron dake hannun ta ta fito tana gyara zani, kallon mamaki ta bishi dashi dan bata tsammaci zuwan sa nan kusa ba, gefen tabarmar dake shinfide a tsakar gidan ya yi wa kansa masauki yana sakin yar k'ara

"Wash... Inna barka da gida."

"Barka, wai har kayi me kenan? Na ganka haka katsaham."

"Wallahi inna hankali na ne ya kasa kwanciya sam, gashi kwata kwata ba yar waya ma balle na rage shiyasa kawai na taho naji yadda ake ciki sai na koma lahadi in Sha Allah."

"Toh sannun ka ya ka baro su chan?"

"Duk lafiya inna, kai duk wanda ya bar gida..."

"Gida ya barshi inji malam bahaushe." Ta karashe masa tana mik'ewa

"Sai kaje huta ka zo muyi magana."

Da sauri yace

"Ai bar hutun nan inna, gwara naji halin da ake ciki kafin komai."

Kallon Suwaiba inna tayi tace

"Kawo masa ragowar farau-farau ɗin nan bari na zagaya."

"Toh Inna."

Buta ta zara tayi bayan gida tana tunanin yadda zata fara sanar mishi.

Kallon kwanon da Suwai ta dire masa yayi kawai ya mike ya nufi dakin sa, duk yayi kura haka ya cire kayan sa ya d'an tattare abinda zai iya tattarewa ya dan haye saman katifar sa yana kokarin bude wayar da ya siyo, sim din sa ya dauko ya saka ya kura wa wayar ido yana jira ta gama kunnu wa, a zahiri kallon wayar yake sai dai baki daya hankalin sa yana chan wajen maganar da Inna tace zatayi masa, a yadda yaga tana dojewa maganar ya riga gama shan jinin jikin sa.

Account balance ɗin sa ya duba yaga Mtn na binshi bashin dari uku, tsaki yayi ya ajiye wayar ya rufe idon sa kawai yana hasaso yadda yake so komai ya kasance idan har Allah yasa iyayen Maryam sun ƙara masa lokacin.

Suwaiba ce tayi sallama a kofar dakin, yana daga kwance ya tashi ya fito,

"Ya akai suwai?

"Inna ce take kiran ka."

"Ok muje."

Cikin gidan suka shiga inna na zaune, zama yayi ya tattara hankalin sa kachokam a kanta, sai data ja fasali kafin tace

"Maganar yarinyar nan..."

Sake nutsuwa yayi, tausayi taji ya bata har taji maganar tayi mata nauyi a harshen ta, Kallon ta yayi ta marairaice yace

"Inna dan Allah..."

"Iyayen ta dai basu amince da jiran ka ba, a takaice dai ma sun ce ka rabu da yar su Allah ya haɗa kowa da rabon sa."

Yana zaune ya mike da sauri, kauda kai inna tayi tana jin kamar bata kyauta ba, be yi magana ba kawai ya bar tsakar gidan da sauri,kiran sa inna ta hau yi be ko juyo ba ya shige dakin sa, rigar sa dake rataye ya saka ya fito ya bar gidan.

Kai tsaye gidan su maryam ya nufa yana tafe yana hada hanya.

Maryam na zaune tayi shiru tana tunani, haka kullum take bata da aiki sai tunani, jin kamar ana buga zauren gidan ne yasa ta kalli Umma,

"Kamar bugu nake ji umma."

"Gashi su Walid basa nan, ko yan Nepa ne?"

"Anya? Nepa da yamma haka?"

"Shi na gani kuma."

Bugawar aka cigaba, umma tace

"Sa hijabin ki ki duba waye."

Hijabin ta ta saka ta fito, yana tsaye ya zubawa kofar gidan ido, da sauri ya shigo zauren yana ganin ta

"Hafiz..." Ta furta a hankali tana kallon cikin gidan

"Maryam dan Allah kuyi hakuri, wallahi wallahi bansan cewa idan aka nemi alfarmar a kara mini lokaci su baba zasuyi fushi ba, na rantse da Allah Maryam ba zan iya rayuwa babu ke ba, kuyi hakuri dan Allah a yi bikin yadda aka tsara."

Sakin baki tayi tana kallon sa, surutai kawai yake data kasa gane kansu, yanayi yana sake matsowa cikin zauren sosai, hawaye ne suka taru a idon ta, kenan Hafiz yana nufin ba da sanin sa komai daya faru ya faru ba kome?

Amma ai kuma daina kiranta yayi gaba daya, shine yanzu zaizo ya raina mata hankali kenan, tunani yayi zata jirashi ko me?

Daure wa tayi ganin kamar baya cikin hayyacin sa tace

"Ni sam ban gane in da maganar ka ta dosa ba, me kake nufi ne wai? Bayan kace ba zaka aure ni ba ka daina kirana yanzu shine zaka lallabo ka dawo?"

"Ni, ni nace bazan aure ki ba Maryam? Ni ko me yasa zanyi haka? Billahillazi ban ce ba zam aure ki ba, cewa kawai nayi a kara min lokaci wallahi Allah."

Dariya tayi wadda tafi kuka ciwo, ta riga ta gano rainin wayo ne kawai zai yi mata, juyawa tayi zata shige ciki yayi saurin riko hannun ta, da sauri ta jiyo tana kallon shi cike da mamaki,

"Cika ni malam."

"Ba zan cika ki ba, idan har ba zaki tsaya ki saurareni ba, toh wallahi sai dai mu kwana anan."

Kici-kicin kwace hannun ta take ya rike kam, cikin takun sa na kasaita ya zuro kafar sa cikin zauren, kamshin turaren sa ne ya fara yi musu sallama hakan yasa Maryam kallon kofa, zaro ido tayi gaban ta yayi mugun faduwa, hade rai Hafiz yayi yana tuno fuskar mutumin da ya tsana. Kallon hannun nata tayi ta kalli Hafiz

"Ka cika ni dan Aallah."

Banza yayi mata ya sake rike hannun nata sosai, gashi yayi mata riko na sosai wanda ba zata iya kwace wa ba

Idanun sa rufe suke ruf cikin bakin glass baka ko ganin fuskar sa, cikin dakakkiyar muryar sa yace

"Sake ta malam."

"In naki fa? Uban waye kai da zaka sani nayi ko kar nayi? Ko shine sabon saurayin da kikayi bayan kin yaudare ni?"

Ya fada cikin kishi, dariya Arkel yayi kadan ya tako har gaban su, kallon cikin ido yake mata hakan yasa baki daya ta duburburce, hannu yasa ya fisge ta ta hade ta da jikin shi, wani irin rawa jikin ta ya dauka kamar mazari, a hankali ya furta

"Da izinin wa kika fito wajen wannan wawan?"

D'ago kanta tayi ta kalle shi, ya kafe ta da ido tana hango haske ƙwayar idon sa a cikin glass din,

"Wai me kake haka? Kai muharramin ta ne da zaka hada kazamin jikin ka da ita? Wato abin da kike yi kenan tun da Maryam da kuke kebewa a office din sa ko?"

Wani mugun kallo Arkel yayi masa,

"Kana so kaga kalar abinda mukeyi a office din?" Ya d'aga masa gira

"Lemme show u."

Jikin sa ya sakata sosai ya saka hannun sa ya zagaye ta.

Cikin bacin rai Hafiz ya bud'e baki zaiyi magana kawai sai gani yayi Arkel ya hade bakin su waje daya.

Gaba d'aya daina gani yayi, tashin hankali da ba'a sa maka rana kenan🤣🤣

Kansu yayi kamar zai yi hauka, ganin kamar ma basu san dashi a wajen ba yasa ya juya daga sauri ya fita, dutse ya dauka kato zai koma ciki, hango Baba yayi ya taho yayi saurin ajiye dutsen ya tsaya yana jira ya karaso.

Ko uban wa zai buga wa dutsen oho😂😂 kai gaskia Hafizu ya shak'a. Arkel fa ba sauki 😳🤔🤣😅

Hafiz na fita ya janye jikin sa yana hade rai, kamar kazar da aka tsamo daga ruwa haka Maryam ta ji ta, gaba daya wata irin muguwar kunya ce ta rufe ta.

"Malama bude idon ki, ki bude kunnen ki kiji, na rantse da Allah na sake ganin ki da wawan chan a tsaye kuna magana har ya yi gigin taba ki sai na kusa sumar dashi."

"Sannan kema sai nayi miki hukunci me zafi, kuma zan sanar wa su Abba."

Da sauri ta kalle shi, harara ya dalla mata ya kauda kansa

"Zuwa nayi muyi magana amma kin batan rai, ki shige gida zan dawo da daddare."

"Kayi hakuri."

Ta samu kanta ta furtawa, daga kafadar sa yayi ya nuna mata hanya

"Koma gida."

Juyawa tayi ta shige, murmushi yayi kawai ya fito, lokacin Baba ya karaso, Hafiz ne ya karbi kayan hannun sa yana gaishe shi, karasawa Arkel yayi shima ya tsuguna a kasa. Harara kawai Hafiz ke aika masa, yana kallo ya shiga motar sa ya tafi, kallon Baba yayi yana sosa kai yace

"Baba dama maganar Maryam ne..."

"Kaga mijin ta nan yanzu ya tafi, muyi hakuri da abinda Allah ya tsara kawai."

Yana kaiwa nan ya karbi kayan sa ya shige gida.

Allah sarki Hafizu 😭


***
Masu kwamplain na short page kuyi HAKURI, am trying my best wlhi Allah, answering messages kawai aka barka dashi an barka da aiki ga masu kira, masu siyan littafi, masu so a turo musu page kaza, ga typing banda al'amuran gida da iyali. A kullum nakan amsa messages ta private fiye da 200

Ina kokari sosai ku kara hakuri Please. Abubuwan sun min yawa ga ido ya sako ni a gaba. Sannu sannu bata hana zuwa sai dai a dade......




_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A HALIN YANZU😁._

*ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma
*SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano)
*KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo)
*BURI ƊAYA!* (Mamu gee)
*WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull)

👇🏻karku bari ayi babuku

*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi  daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*

*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*

Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank

Saika tura shaidar biya ga wannan number ta WhatsApp

08030811300

Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN  ta wannan number din

07067124863

Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.

*Karki bari ayi babu ke, Abari ya huce shike kawo rabon

Rano🚴🚴🚴
[3/18, 22:25] Hafsat Rano: *SAUYIN K'ADDARA*

*17-18*
©*Hafsat Rano*

*_ZAFAFA BIYAR na kudi ne idan kana son kowanne daga ciki ka nemi Wannan numbers din_*

*08030811300*
*07067124863*

*_Daurin boye_*
_safiyya huguma_
*_Buri daya_*
_mamuhgee_
*_Wutsiyar rakumi_*
_billyn Abdul_
*_Kai min halacci_*
_Miss xoxo_
*_Sauyin kaddara_*
_hafsat rano_

***
Da k'yar yaja kafafunsa ya bar kofar gidan zuciyar sa na matuƙar suya, be taba tunanin Maryam zata yaudare shi haka ba, duk yadda yake ta fafutukar ganin ya samo abinda zai taimaka musu amma tayi masa haka? Ba zai taba yafe mata ba kuwa, dole ya dau fansar abinda ta aikatawa zuciyar sa.

Ko da ya shifeega gida be nemi kowa ba ya bude dakin sa kawai ya shige, kwanciya yayi lamo baya jin zai iya runtsawa a daren yau ga wata uwar yunwa dake nukurkusar sa, duk sanda ya rufe ido abinda ya faru yake hangowa, hakan ya saka masa zazzafan zazzaɓi da ciwon kai me tsanani.

***
Gidan Ya Nabila ya zarce kai tsaye yana tafe yana tsaki har ya isa, knocking yayi yaji shiru hakan yasa ya kira wayar ta, bata gida ta dan fita ashe amma ba nisa tayi ba, komawa mota yayi ya jira ta.

Kujerar ya kwantar sosai ya jingina kansa a jiki, lumshe idon sa yayi ya fada kogin tunani, wayar sa ce tayi kara ya dan bude idon sa kadan, private number da ya gani ne yasa shi saurin tashi, d'agawa yayi ya kara a kunne sa, shiru babu wanda yayi magana, cire wayar yayi daga kunnen sa ya saka ta a handfree yace

"Stop calling me idan baka shirya magana ba, Ina da abubuwa da yawa da zan yi so stop wasting my time. Am hanging...."

"Wait..." Yayi saurin tsayar da shi

"Da gaske kayi aure bro? kayi aure ka barni? Dnt You care about me anymore?"

Wata bazawarar dariya Arkel yayi ya bigi sitiyarin motar

"Look who's talking! Yanzu har kana da bakin tambaya ta wanann? after all abinda muka shiga akan ka?"

"Baka tunanin komai nayi akwai dalili me karfi?" Shima ya katse shi

Share zancen yayi yace

"Me ka kira kace min? Na zata mun gama da wannan maganar ai."

"Arkel har yanzu kana nan da zafin ranka, baka chanja ba, man u need to grow up."

"Zan kashe please, bana son jin komai."

"Arkel ka..."

Kafin ya k'arasa magana ya kashe wayar,ransa ne ya ɓaci sosai, fasa jiran Ya Nabilan yayi ya tafi kawai.

A harabar gidan ya tarar da Hajiya Mero tana tsaye ita da wani mutum, kallon su yake har ya dangana da ma'adanar ajiye motoci, ganin ya bude kofar ne yasa tayi saurin cewa

"Gashi nan ya dawo, kaje kawai zamuyi waya."

Dan kallon shi mutumin yayi ya daga kai

"An gama hajjaju."

Da sauri ta juya zata koma ciki ta tsaida ita ta hanyar cewa

"Hajiya."

Dagata wa tayi har ya karaso,

"Ya akayi Arkel? Tun dazu nake jiran dawowar ka ina so muyi magana akan shirye shiryen bikin nan, kai ma naga ka zama busy."

"Maganar da zanyi kenan." Ya amsa mata

"Muje ciki toh."

Gaba tayi ya bita a baya yana kallon harabar gida.

Kallon falon yake yana ayyana yadda komai zai kasance

"Anjima masu kawo furnitures zasu kawo, falon saman chan za'a zuba su zuwa gobe zasu dawo su gyara, na bedroom d'ina ma za'a fito dasu..."

"Baka bukatar su ne kuma? Naga basu wani jima ba."

"Eh gaskia, da nace musu su hada su tafi dasu amma idan kina so sai ki dauka."

Yayi maganar yana basarwa dan ya gano in da maganar ta ta nufa.
Da sauri tace

"Nagode kuwa, amarya ai dama komai yar sabo ce, gwara a ake mata sabo, amma Arkel sai naga kamar be kamata ace baka hada dana Yaya ba."

"Sama zata koma." Yayi maganar yana hade rai. Da sauri ta kalle shi

"Sama kuma? A wannan yanayin nata?"

"Eh!"

Ranta ne ya baci har ta kasa boyewa

"Amma mesa ba zaka barta a kasan ba? Baka yadda da ni bane ko me? Ko ita maryam zata iya d'awainiya da ita ne ita kadai?"

Kallon ta yayi cike da mamaki, yadda taga yana kallon ta ne yasa ta tuna abinda take neman yi, da sauri tace

"Naga ace daga zuwan ta kaga aikin zai mata yawa, gwara ka barta a kasan kawai a hankali idan ta saba da gidan sai a mai da ita saman."

Shiru yayi be ce komai ba,

"Shikenan dama shawara ce, kayi yadda kaga yafi maka kwanciya hankali, ni dama ita yayan na duba saboda kasan zai fi mata."

"Shikenan, hakan yayi."

Murmushi tayi cikin jin dadi tace

"Ko kaifa, Allah dai ya bata lafiya."

Mik'ewa yayi ya wuce saman ta bishi da harara sannan tace

"Shegen taurin kai."

Number ta kira ta kara a kunnen ta, dariya tayi sosai kafin tace

"A nemo min shi."

Ajiye wayar tayi cike da farin ciki

***
Toilet ya d'aura a kugun sa ya tsaya a gaban mirror yana kallon kansa, hannu yasa ya shafi bakin sa sannan yayi murmushi

"So soft." Ya furta a hankali

wanka ya fad'a ya jima yana gurzar jikin sa kafin ya sakar wa kansa ruwa saboda zafin da ake yi yau ba sauki.

Karamar riga ya saka da wando wanda ya tsaya masa iya guiwar sa ya sauko kasan don duba Ummi, tana nan kamar kullum a kwance babu wani abu da ya sauya, a kasan gadon ya dire guiwowin sa ya riko hannun ta

"Sannu Ummi, kwana biyu nayi laifi na barki ke kadai ko?"

"Ayi min afuwa Ummi, na aikata wani babban al'amari a rayuwata ba tare da sanin ki ba, nayi aure Ummi."

Shiru ya dan yi yana jin kamar zai yi kuka, gyara zaman sa yayi,

"Ummi yau ya kirani, ya kira har munyi magana Ummi, bansan me zanyi ba Ummi, yace komai ya aikata yana da dalili, na rasa me zanyi? Na yadda dashi Ummi ko na share shi? Dan uwana ne Ummi, idan yana cikin matsala ni ya kamata ya fara sanar wa amma me? Ya zanyi ne Ummi?"

Hannu yasa ya share kwallar da ta gangaro masa, ya mike

"Kiyi min addu'a Ummi, ki kuma yafe min idan abin da nake shirin aikatawa ba daidai bane."

Juyawa yayi ya rufo mata kofa, kuka ta saka cike da tausayin rayuwar ya'yan nata. Ta dogara da Allah tasan akwai ranar da gaskiya zatayi halin ta, duk ni san jifa...

Turus yayi yana kallon uban akwatu nan dake zube a tsakiyar falon, ya Nabila ce ta shigo kunne ta rike da waya alamar magana ta keyi, harɗe hannun sa yayi ya zuba wa kayan ido yana kallon ikon Allah, bata kula shi ba ta wuce dakin Ummi tana cigaba da wayar da take, sai data fito sannan ta harare shi

"Wannan uban kayan fa?"

"Ban sani ba, ka saka nayi ta sauri ban gama abin da nake ba nazo naga ka tafi."

Shafa kansa yayi yace

"laaa... Sorry mantawa nayi."

"Mantawa?" Ta harare shi

"Eh wallahi, wani abu ne ne ya taso na tafi ba shiri."

"Kaji dashi."

"Toh wannan kayan fa?" Ya tambaya yana nuna mata da hannu

"Karka damen malam, tana ciki ne?" Ta nuna dakin Hajiya Mero

Dage kafada yayi

"Nima ban sani ba."

Dariya kawai tayi ta murd'a kofar, da sauri Hajiya Mero ta boye ledar tana kallon kofar

"Mummy... Ashe kina ciki, sannu da gida."

"Ina ciki Nabila, zuwan kenan?"

"Eh wlhi, wanchan yaron ne ya taso ni, ga kayan chan a falo nasa an shigo dasu."

"Auw wai har kin gama haɗawa, lallai kinyi kokari, muje na gani."

"Toh ai naga lissafin ya chanja ne shiyasa kawai na gama komai."

"Kin kyauta kuwa."

Kallon kayan Hajiya Mero tayi, haushi ne ya turnik'e ta ganin uban kayan, take ranta yayi mugun ɓaci, kokari tayi ta danne ta hau bud'e kayan, da tasan abin zai juya daga kan Rauda da bata sa ta hado wannan uban kayan ba, ranta be gama baci ba sai data bude kit din da aka zuba sarkoki, d'ago wata dank'areriyar sarkar gold tayi, kadan ya rage ta suɓuce a hannun ta tayi saurin taro ta, kallon Nabila tayi tace

"Amma wannan sarkar batayi girma ba kuwa?"

"Ah haba batayi ba, komai yadda kikayi list haka aka zuba, sauran jewelries din ma duk Dazz ne duba ki gani."

Yawun bakin ciki ta hadeyi da k'yar tana zare ido kamar akuya a dakin gari, rufe kit din tayi kawai dan in ta ci-gaba da kalla zuciyar ta zata iya bugawa.

Akwatin night wear ta bud'e Arkel ya sake gyara tsaiwar sa sosai yadda zai hango komai, daya bayan daya ta dinga daga su hakan ya saka shi xare ido, sai a lokacin ya

27, January 2025
Rukayya

Good

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login