Showing 48001 words to 51000 words out of 98004 words

Chapter 17 - SAUYIN KADDARA COMPLETE HAUSA NOVEL

06 Jan 2025

11618

a chan karshen gado, gaba ɗaya idon ta ya koma ciki saboda azabar kuka, gadon ya hau ya jawo ta yana girgiza mata kai

"I'm sorry please,kukan ya isa haka nan kinji jikin ki har yayi zafi."

"Kin daina ko?" Yace yana mata murmushi

Ciki-ciki tayi magana be jiba sai daya sake matso wa sosai,

"Me kika ce?"

"Ummi, kaje ka duba ta Please."

Sakin ta yayi ya dora mata ledar akan kafarta yace

"Bari naje, Please ki sha maganin sai ki sha tea din kar yayi sanyi, paracetamol ne sai wani pain reliever shikenan."

Ya mutsa fuska tayi, murmushi yayi yana ayyano kalar rashin mutuncin da zai yiwa mutumin nan na jiya, sai a lokacin ya tuno dashi dan shaf ya manta.

Dakin ummin ya shiga, tana kwance idon ta biyu, kallon gadon yayi ya tuno da maganar da Maryam tayi masa, salim ya tuno yayi saurin kiran sa

"Sai oga."

"Kana ji, wheel chair nake so kaje ka siyo anjima kadan, sai ka kawo min gida."

"Owk an gama, yau ba zaka shigo bane?"

Har zai ce zai shigo sai ya tuno

"Ba zan shigo ba, Madam bata jin dadi."

"Madam...?" Salim ya maimaita, kafin yayi magana ya kashe kiran.

Dariya kawai yayi yana mamaki. Wai Madam. Ah lallai.

***
A firgice ya tashi saboda mummunan mafarkin da yayi, gaba daya ya jike da zufa da kyar ya ja ƙafafuwan sa ya fada bayi,haka ya fito jikin sa duk a mace, yanke shawarar fasa zuwa aiki yayi ya kwanta kawai bayan ya dan sha tea kad'an

Har wajen azahaar yana kwance sai ga mustapha ya shigo, daga wajen aiki yake ya zarto saboda ya kirkira shi a waya be daga ba. Ganin shi a kwance ne yasa ya tabbatar babu lafiya.

"Baka da lafiya ne?" Ya tambaya yana ajiye jalar hannun sa

"Bana jin dadi ne musty, yau mafarkin gida nayi."

"Shine yasa ka kwanta? Naga ba yau ka fara ba ai."

"Amma na yau is totally different, Arkel yana cikin matsala, i can feel it, ya zanyi?"

"Kaje kawai?"

"Kai! Ina? I can't face him, kasan kuwa laifi na? Ko kai kaji abinda na aikata sai ka guje ni, sai dai nasan ba yin kaina bane, bansan me ya hau kaina ba, bansan ya akayi ba. Duk da haka amma laifi nane, shiyasa ba zan iya yafe wa kaina ba, ba zan iya taba zuwa in da suke ba, na cuci kaina na cuci dan uwa na."

Mike wa Mustapha yayi ba tare da yayi magana ba ya dauki kayan sa

"Ka dade kana fada min hakan, ba tare da ka sanar dani ainihin matsalar ka ba, na sani baka daukeni yadda na dauke ka ba shiyasa har ka kasa sanar min, babu komai bari na wuce kawai, ina ganin ba sai na sake dawowa nan ba, ba amfani zuwan nawa."

Hanyar waje yayi da sauri Arab yace

"Dawo na faɗa maka, amma ka shirya rabuwa dani dan nasan kana ji zaka gujeni."

Abinda dama yake so kenan, dawowa yayi ya zauna yana bashi dukkan attension din sa.




***
*Assalamu alaikum jama'a
Ni dai bansan da bakin da zan kuma yin bayani ba, na sanar muku wlhi ciwon ido nake, abu har ya kai da glass, Amma wasu sun kasa yi min uzuri, suna ganin bana musu typing ko ina jan rai, abubuwan ne sun min yawa dole ba zan iya typing me yawa kamar yadda wasu a cikin mu sukeyi ba.*


*Karku manta yawancin ku ta wajena kuka siya books din mu, bafaa karamin aiki bane, na tura maka details, idan ka biya sai na je na duba account name ɗin ka, sannan nazo nayi saving dinka , nayi adding a kowanne group, kuma a haka bana mantawa ina kokarin saka kowa a in da ya dace tun da wasu ba dukka biyar din suka siya ba, sannan dana yi adding sai maganar turawa daga farko, plus am married, Ina da iyali ga typing banda aikin gida,ga lalular ido da ta sakani a gaba. Ya kuke tunanin xan iya zama nayi typing me readmore biyar shida ko bakwai bayan a kullum nakan amsa mutane sama da 200 a rana. So ni dai ina kara baku hakuri, sannu sannu bata hana zuwa, akwai yiyuwar ku dan jini shiru ma kwana biyu saboda lafiyar ido na kar na kashe ido na garin neman gira*😅
Nagode

*26-27* S K
©*Hafsat Rano*

*_ZAFAFA BIYAR na kudi ne idan kana son kowanne daga ciki ka nemi Wannan numbers din_*

*08030811300*
*07067124863*

*_Daurin boye_*
_safiyya huguma_
*_Buri daya_*
_mamuhgee_
*_Wutsiyar rakumi_*
_billyn Abdul_
*_Kai min halacci_*
_Miss xoxo_
*_Sauyin kaddara_*
_Hafsat rano_

°°°
"Da wani yammaci ina zaune a daki ni kad'ai bayan tafiyar Arkel ina kallon wani film sai Ummi ta kirawo ni ta aike ni wani store, a kafa na fita na tari abun hawa. bamu yi nisa ba wani holdup ya rik'e mu, ganin haka yasa na ciro wayata na shiga chatting saboda na rage wa kaina zaman. Ina cikin duba wayar ne naji wata mata na tambayar in da zamuyi, ina ji ta shigo napep ɗin da alama hanya daya mukayi kenan, daga sama naji muryar ta saboda haka ban iya tantance yanayin ta a lokacin ba, ban ko d'ago ba na cigaba da danna wayata. Tsawon mintuna biyar aka fara ja, ganin haka yasa na kashe wayata na maida aljihu saboda yanayi na tsaro.
Kallon gabana kawai nake kamar wasa sai naji alamun ana taka mun kafa, kallon kasa nayi sai naga ta janye kafarta da sauri, sai a lokacin na kalle ta, mace ce babba a ƙalla zatayi shekara 40 da sauri ta sakar min murmushi tace nayi hakuri bata sani ba, ban ce komai ba na gyara zama na kawai. Lokacin da muka isa in da zan sauka sai naga ita ma ta fito, muka sallami me napep na juya zan shiga store din , da sauri ta tsayar dani tana gyara mayafin dake makale a kafardar ta, kallon kurillah nayi mata fara ce tas daga gani ta sha bleaching sai uban jambaki data saka ja wanda ya kara sakata tayi bau kamar ba mutum ba.

"Sannu dai." Nace mata ina kallon ta,

"Sannu handsome, ya gida ya komai.?"

"Lafiya." Na amsa mata kai tsaye sannan na juya na shige ciki, ba wani abu na siyo da yawa ba shi ya sa nayi saurin fitowa, abun mamaki tana nan a tsaye tana dube-dube, dauke kai nayi na tare wani me napep din, tare muka shiga da ita kuma dai har aka zo unguwar mu, ina sauka naga ta sauko ita ma, daga nan sai naji zuciya ta bata yarda da ita ba sam, ja nayi na tsaya cikin hade rai nace

"Malama lafiya kike bina?"

Murmushi naga tayi kafin tace

"Kawai naji kayi min ne wallahi, so handsome Masha Allah, so nake muyi magana shiyasa ma nayi ta maka alamar da zaka ankara ka gane sai kuma naga kamar baka gane ba, yanzu dai idan zai yiwu muyi exchanging number a Kaduna nake zama nazo ganin gida ne so ba dadewa zan ba."

Kallon banza na watsa mata saboda yadda ta kular dani, sake kallon ta nayi sosai rai na ya kara baci, tsohuwa ce sosai amma banda iskanci tace nayi mata, yawo na zubar a gefe ta fito da ido waje tana kallo na

"Allah ya sauwake dai, wallahi kinyi asarar zuwa duniya, bari kiji ni ba sa"an ki bane mata a haife kin haife ni shine zaki kawon maganar banza."

"Ni ce na haife ka? haba dan samari, Kalle ni sosai mana, ni ba wani abu nake nufi ba kawai ina so mu zama friends ne."

"Chab, Allah ya kiyaye ni wallahi, kije ki nemi tsoho daidai dake ki aura kin tsaya bata wa kanki lokaci."

"Ni fa ba mijin aure nake nema ba, kawai dai na ganka na k'yasa ne idan zai yiwu, ka duba dan Allah."

"Allah ya kiyaye, ke kuma Allah ya shirye ki, dama ance akwai irin mata haka tsofaffi amma basa jin kunyar rashin mutunci, toh dai kinyi asara wallahi."

"Dakata dallah, dan kaga ina binka shine zaka nemi ka zage ni, ka kula da maganar ka karka
jawa kanka da ahlin ka abinda zai zame muku masifa."

"A lokacin kaina ya dau zafi dan ba karamin bata min rai tayi ba,haka na zage na zage ta tas na juya na shige link din mu, ashe bansani ba hakan danayi ba shine daidai ba, ban sani ba na daba wa kaina wuka a ciki na. Ashe bata bar ni ba, sai data bibiye ni tsawon kwana uku tasan komai akai na da gidan mu, a kwana uku ta kama mahaifina, ta saka mishi soyayyar ta me zafi, duk ban san wainar da ake toyawa ba."

Sati daya da faruwar al'amarin sai na dinga jin hayaniya daga ɓangaren su Ummi, abun yayi matukar dauren kai nayi saurin fitowa, cikin tsananin mamakin abinda ban taba gani ba naga Ummi da Alhaji suna hayaniya sosai cikin tsananin bacin rai, ina zuwa ya juya ya fita ita kuma Ummi ta saka kuka, zama tayi na hau tambayar ta abin da yake faruwa, bata boye min komai ba ta sanar dani wai Alhaji aure zai yi, saura sati daya ayi bikin ma, sannan binciken da tayi ta gano matar muguwar hatsabibiya ce babu Allah ya zuciyar ta, kwantar mata da hankali nayi tayi na yi mata alkawarin binciken abinda yake faruwa dan musan yadda zamuyi."

"Abin mamaki washegari sai na tashi a wani irin yanayi me wuyar fassarawa, naji bana sha'awar komai face kayan maye, wani irin tashin hankali na shiga na kasa sukuni a daren ranar sai dana nemo sigari na fara zuka, kamar wasa a cikin kwana uku sai gani na zama tataccen dan maye sai na fara neman in da zan samu giya, duk abin nan da nake babu wanda ya sani saboda ina daki kullum a rufe gashi Ummi da Alhaji kullum cikin tashin hankali zaman yaki dadi, a haka na cike kwana biyar cif ina wannan halin na maye, ana i gobe daurin auren Alhaji Ummi ta shigo daki na katsaham, abin da ta gani ne ya saka ta rawar jiki saboda tsabar k'aduwa, lokacin ina cikin yanayin maye saboda haka ban ji komai ba, duka ta rufe ni dashi ko ta ina ina jin sautin fitar kukan ta a saman kaina sai dai babu abinda zan iya yi, har da gaji da dukan ta juya da sauri ta fita daga dakin."

Hawayen daya zubo masa yasa hannu ya share ya juya wa Mustapha baya saboda abinda zai fada yana da matukar nauyi

"Na cuci kai na na cuci yan uwa na da dangi na." Ya fada yana jan Muryar sa cikin wani yanayi da kana ji zaka san ba karamin nauyi yake ji a zuciyar sa ba

"Kayi hakuri man, komai yayi zafi maganin sa Allah, ka daure ka karasa min labarin nan, in Sha Allah komai ya zo karshe."

Da kyar Muryar sa na rawa yace

"Washegarin ranar da Ummi ta kamani bansan me ya hau kaina ba, bansan wani irin mummunar ƙaddara ce take bi na ba, na sha giya sosai na bugu har bana jin komai saboda tsabar yadda na bugu, babu kowa a gidan me aikin ta ta tafi Ummi ce kawai tana zaune a dakin ta tayi tagumi tana tunanin abinda ta gani, damuwar ganin da tayi min ce ta danne damuwar auren shiyasa duk abin duniya yayi mata yawa,babu wanda ta sanar wa da auren tun da dama ba wasu mutane take harka dasu sosai ba, a yadda na shigo mata daki ne yasa ta tsorata, maganganu kawai nake bansan ko me nake cewa ba Mustapha, wallahi tallahi bansan me ya hau kai na ba, kawai sai naga ta rikid'e ta koma min kamar wata budurwa yar shekara sha takwas, wallahi Allah ba Ummi na gani ba Mustapha, wallahi ban san komai ba, bani da wani iko da kaina ko zuciya ta, komai ji nake ana ingizani, bansani ba? Na aikata abinda zuciya ta ta ingizani ko ban aikata ba? Shine abin da na kasa sani har yau iya kaci dai naji Muryar matar a kaina tana salati, wannan shine silar shiga halin da Ummi take ciki, wannan shine silar barin gida na, da wanne ido zan iya zama na kalli mahaifi na? Dan uwa na? Da sauran mutanen gari? Wanne irin mutum ne ni?  Bani da wani sauran amfani a duniya shiyasa nake yin komai da rayuwa ta saboda nasan ni tawa ta kare, tsawon wannan shekarun ina dauke da wannan masifar, gashi har na kawo yanzu ban mutu ba, bayan tun a lokacin na roki mutuwa ta akan rayuwa ta."

Da sauri Mustapha ya taso ya rike shi ganin yana neman sakin layi, kuka dukkan su suke dan yadda abin ya girgiza Mustapha be taba shiga tashin hankali irin wannan ba, lallai dole ne ya aikata abinda yake aikata wa yanzu ko ma fiye da haka, wannan wacce irin kaddara ce haka? Wacce irin rayuwa ce haka? Innalillah wa inna ilaihi raji'un." Kawai dukkan su suke nanatawa,wani irin tsoron Allah ne ya shigi Mustapha a lokaci daya yaji komai ya dauke masa.
yake sakawa a ransa, abu daya Mustapha ya sani ya kuma ɗaukar wa kansa alk'awari shine sai yayi kokarin yadda ya kawo wa abokin nasa sauyi a rayuwar sa.

***
A tare suka fito da safe zuwa wajen aiki, kallo ɗaya zakayi masa ka tabbatar da tsantsar damuwar da yake ciki. Sanda suka isa office Mustapha be zauna ba, signing kawai yayi ya fita bayan ya dauki excuse. Direct wajen siyan ticket din mota ya nufa ya yanki ticket biyu na zuwa Sokoto sannan ya dawo office.

Da daddare suna cin abinci duk da ba wani dadin abincin yake ji ba Mustapha ya zaro ticket din ya mika masa

"Gobe idan Allah ya kaimu zaka rakani sokoto, alfarma nake nema a wajen ka saboda haka karka ce min a'ah, idan har ina ko da muhimmanci a rayuwar ka."

Be jira amsar sa ba ya kwashi shirgin sa yayi gaba, hannun sa kawai yake kallo ya rasa yadda zai yi, ga dai ticket ya karba sannan yasan zuwan ba karamin aiki bane a wajen sa,sai dai ba zai iya musa masa ba bayan bashi da kowa sai shi, shi yayi masa dukkan gata tun da ya baro gida har kawo yanzu bai taba nuna gajiya wa da al'amuran sa ba, bashi da wata hujja ko dalilin kin amsa gayyatar tasa. Haka ya kwana sukuku  washegari suka dauki hanyar sokoto.

***
Wajen azahar tadan ji ƙarfin jikin ta, wanka ta sake ta shirya cikin atamfa riga da zani ta ɗora hijabi a saman ta sauko tana jin ta kamar iska zata kwashe ta ta watsar gefe, babu kowa kai tsaye ta buda dakin Ummi ta shiga, da sauri ta karasa wajen gadon ganin ta a gefe saura kadan ta fado, da k'yar ta gyara ta tana mamakin yadda akayi hakan ta faru. Cike da tausaya wa yake kallon ta kafin ta tashi ta duba magungunan dake zube a gefen gadon, ajiyar zuciya ta sauke ganin na gaskiyar ne, gefe ta zauna tana tunanin makaranta da zasu koma dan har an fara registration. Tana nan zaune ya shigo dauke da wheel chair din, da sauri ta tashi ya sakar mata murmushi dan beyi tunanin ganin ta ba, sunne kanta kasa tayi cikin kunya ta kama masa ya ajiye, gumi ya goge yana sauke ajiyar zuciya. "Sannu." Ta fada kasa-kasa. "Tun yaushe tayi bacci?" Ya fada yana kallon ta.

"Tun da nazo."

"Ok ya jikin?" Ya fada kasa-kasa yana daga kashe mata gira, shiru tayi taki magana yayi dariya kawai. Kallon wheelchair din yayi yace "na kira wani Dr ya fada min yadda zamuyi mata, yanzu anjima sai mu taimaka mu sakata akai a zagaya da ita, a hankali a hankali sai a maidashi twice a day." "Owk." Tace tana kallon ummin, "baki fada min magungunan sun kare ba." Da sauri ta kalle shi, kallon ta shima yayi, "I'm sorry." Kawai ta samu kanta da cewa dan bata san me zata ce ba, murmushi yayi mata ya matso kusa da ita yace "karki damu, Hajiya ma ta fada min dazu, gashi nan har na siyo." Bata san me zata ce ba sai kawai tayi shiru, shafa cikin sa yayi ya kalli kofa "yunwa muje ki bani abinci pls." Ba musu ta tashi suka fito, Hajiya na ganin su gaban ta ya fadi, fita tayi dawowar ta kenan bata yi tunanin hakan ba, ganin sun hada ido ne yasa Maryam ɗin gaishe ta, kamar babu komai ta amsa tana kallo Arkel ɗin "an siyo maganin kuwa?" "An siyo." Ya fada kai tsaye. Kallon Maryam tayi,

"Ki dinga kula dan Allah,kinga ke kika kori me zuwa tana kokarin ta gashi kuma an fara samun sakaci, ki kula sosai gaskia, bama wasa da komai nata." Mamaki sosai tayi har ta kasa magana sai da tace "Baki amsa ba, kar dai ko haushi kika ji Dan na fad'a miki gaskiya?" Da sauri tace "zan kiyaye in Sha Allah." Harara ta sakar mata ganin Arkel ya yi gaba sannan ta shige ciki, jiki a sanyaye ta ja kafarta tayi gaba tana mamakin matar, duk in da take tunani ta wuce nan, toh ta Allah ba tata ba wallahi,zata dage da addu'a kawai. Yana cin abinci yana tunanin maganar Hajiya Mero, baya so ya ga laifin Maryam amma dai ba zai yadda da sakaci ba kuma, a haka dai ya gama ya dan mike yana duba kasuwar tasu ta Forex. Kiran da ya shigo wayar sa yabi da kallo, salim ne, yana dagawa yace "ka samu in da mutumin yake?" Daga dayan bangaren salim yace "Na saka dai a kara bincika mana, in Sha Allah xaa samo shi." "Shikenan, thank you so much." Dariya salim yayi kawai ya kashe wayar.

Shiru yayi yana tunanin abin, dole ne ya sake tuntubar su buzu yaji garin ya hakan ta faru har suka bari ya gudu. Da daddare suna zaune a falo bayan ta baro dakin UMMI, sallah ta shiga dakin tayi ta sake wanka bayan ta karanta text d'in Anty Maryam akan lallai bayan kula da mahaifiyar sa ta dage wajen kula da kanta da gayu da wanka kar ta zama kamar wata yar kauye, haka ta haɗa ruwan tayi wanka ta fito ta shirya tsaf cikin shigar ta me kyau da sauki, kamshi ne kawai ke tashi daga jikin ta kamar anyi barin turare, tana gama daurin dankwali

27, January 2025
Rukayya

Good

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login