Showing 33001 words to 36000 words out of 98004 words
Nabila ta tuna dashi
"'Laaa wai dama kana nan."
da sauri ya juya zai bar falon aiko ta kwashe da dariya
"Daka tsaya ka gama gani ai." Ta fada tana sake tuntsurewa da dariya, be kulata ba yayi ficewar sa yana danne tashi dariyar dan ba karamin kunya kayan suka bashi ba.
Shaf ya manta da shigar jikin sa kawai ya fada mota ya bar gidan, sai da ya hau titi sosai sannan ya tuna, babu damar komawa haka ya dau hanyar gidan yana addu'ar Allah yasa kar suyi kicibis da Abba ko Baba. Ba dan ma ya sanar mata zai dawo ba da bari zai yi ya je gobe, toh ya ga lokaci na tafiya gwara yaje suyi magana idan akwai abinda zata bukata.
***
Zaman sa yayi a cikin mota lokacin da ya isa kofar gidan dan be san ta inda zai fara fitowa ba a shigar jikin sa, tunowa yayi da sauri ya ciro wayar sa daga jikin chargy ya lalubo number ta daya dauka a wayar Salim.
Kira yayi lokacin tana zaune gaban anty Maryam ta tsare ta da wasu magunguna a gaba, da kyar take sha tana yatsine dalilin da yasa ka ma ta taho gidan anty Maryam ɗin kenan dan ita xata saka ta dole ta sha, kallon wayar ta da take ringing tayi ta ajiye kofin da sauri ta daga dan dama neman abinda zai sa ta ajiye ɗin take
"Hello." Tace cikin muryar ta very cool kamar ta miss Xoxo 🙄🤪
"Ina waje." Kawai taji yace,da sauri ta kalli Anty Maryam wadda tayi kamar bata san me take ba. Wayar tabi da kallo har ya kashe, tsaki tayi a hankali kar Anty Maryam taji
"Mijinki kika wa tsaki Maryam?"
"Bafa tsaki nayi ba."
"Kinsan bani da kunne ai."
"shine Allah sai yayi ta abu wani iri, wai kawai cewa yayi yana waje fa, toh ni ya zan masa?"
"Yayi ɗin, kina da shiri ta wlhi Allah, kamar ba yar jami'a ba, kira shi maza ki bashi address din nan din."
Turo baki tayi irin an takura matan nan tayi dialing number tasa,
"Ban ganki ba?" Shine abinda yace yana daga wa, harara tayi kamar yana ganin ta kafin tace
"Ina gidan Anty Maryam."
"Da izinin wa?"
"Na'am?"
"Nace kin tambaye ni ne? Ko bakiji dazu nace karki sake fita ba."
Shiru tayi kawai tana jin ikon Allah, sai da ya gama sababin sa tana jin sa sannan yace
"Bani address din."
Zatayi magana yayi saurin cewa
"Yimin sharing live gps din kawai."
"Me fa?"
"Yar kauye, shiga whatspp kiyi min sharing location din da kike, zanyi navigating nazo."
"Ohhh."
"Baki sani ba ko?"
"Na sani mana, kawai dai."
"Malama don't' lie, just do it na fara gajiya da jira."
Turo baki tayi tace
"Toh." sannan ta kashe, shiga tayi ta tura masa tana ta mamakin dama amfanin abin kenan, suna nan zaune suna hira da Anty Maryam kawai ya kirata yace gashi a waje, dama ta sauya kayan jikin ta shima saboda Anty Maryam ta matsa ne, mayafi ta dauko mata a cikin kayan ta ganin zata junbula hijabi ta mika mata
"Kai Anty Maryam kamar zanje wani biki?"
"Baki da hankali wlhi,dalla wuce kin bar mutum a mota."
"Ni yanzu kin daina sona."
"Na daina ɗin, kije in yaso sai ki shigo dashi falon chan, saura kiki jin magana ta."
Kumbure kumbure ta hau yi da haka ta fita, hasken motar sa ne ya haske ta tayi saurin sa hannu ya kare, sai da ya gama kallon ta sannan ya kashe, ja tayi ta tsaya a wajen taki karasa wa ganin shima yaki fitowa, gyara zaman sa yayi kawai yana so yaga iya gudun ruwan ta.
Ganin bata da niyyar karasowa yasa shi balle murfin motar ya fito, gaban ta ne ya hau faduwa ganin ya tunkaro ta har ya iso sannan a hankali ta sauke ajiyar zuciya.
"Wuce muje."
"Ina?" Ta d'ago da sauri ta kalle shi
"Sai da ke zanyi."
"Mu shiga ciki inji anty Maryam."
Kallon kansa yayi,
"Kalli shiga ta fa, a haka zan shiga?"
Kallon sa tayi daga sama har kasa, tayi saurin dauke kanta a ranta ta furta
"Ji wani iskanci."
Jin tayi shiru ne yasa shi riko hannun ta,
"Kina batan lokaci."
Bangaren me zaman banza ya bude mata ta shiga sannan ya koma side din sa ya shigo, sanyi Ac hade da daddadan turaren jikin su ya hadu ya bada wani irin scent me masifar kamshi da dadi, lumshe ido tayi a hankali taji wani irin yanayi na shigar ta, shi din ma hakan ce ta kasance masa yayi ta maza ya daure yace
"Me kuke bukata na biki, amma kamu kawai ya isa,bana son wani tarkacen biki."
Kasa buɗe baki tayi kawai tayi shiru, dan bata san me zatace ba
"Ba zakiyi magana ba?"
"Duk abinda Allah ya hore maka yayi, ni in tani ne ma a kyale komai."
Kallon ta yayi lokaci na farko data fara birgeshi kenan, ajiyar zuciya ya sauke cikin jin dadin amsar ta ya matso sosai sai jin maganar sa tayi a cikin kunnen sa
"A kyale komai kawai a kaiki ko? Are dat desperate to be with me?"
"Haka nace maka?"
"Toh menene? Nayi karya ne? I can see it a idon ki ai."
Da Saurii tasa hannu ta rufe idon nata, sake matsowa yayi sosai, shi kanshi be san me yake damun sa ba kwana biyun nan.
Hannu tasa ta dan ture shi yayi baya, gyara zaman sa yayi yana basarwa yace
"Zan san me zanyi akai, amma bana son wannan make up din da kuke komawa kamar wasu aljanu, kayan da zaki sa kuma su zama ba transparent ba, su zama masu kauri so samu ki hada da babban mayafi, please karki yi abinda zai hurting dina, Ina da kishi akan duk abinda ya zama mallakina, and komai nawa ina maida shi so important, akwai abubuwa da yawa da zan sanar dake nan gaba, for now wannan ne kawai."
"Owk tam." Ta amsa a sanyaye
***
Ranar Friday aka yi kamu me kyau a amneef, komai shi ya shirya ya dau nauyi, sosai amarya tayi kyau ta gayyato kawayen ta na buk su Asma'u su Sadiya zango da sauran su, babu wani hauka ko bidia komai anyi shi cikin tsarin addini Islama, ango ne halatta ba sai su Hajiya Mero (da ta zama uwar biki karfi da yaji) da Ya Nabila sai yan uwan Alhajin su. Su Ma'u an so aga ango har gulmar sa tayi wa Sadiya zango ko ta sanshi ta kwatanta mata shi, bata samu ba haka ta hakura da niyyar idan an kai amarya gobe zata tsaya ayi sayan baki dasu.🤪
***
Hafiz na xaune ya hada kai da gwuiwa yana tunanin yadda abubuwan suka zama, babu irin rarrashin da ban baki da inna batayi masa ba sam yaki sauraran ta, har ta fara danasanin aikata abinda ta aikata.
Tun dazu ake ta faman kiran sa da wani layi yaki d'agawa, text d'in da ya shigo ya bude
"Kazo wajen Sabuwar Kofa zamuyi magana, magana ce akan maryam, ko ka fasa daukar fansar???."
Zumbur ya mike ya zura rigar sa, takalmi ya zura ya fice da sauri yana kiran layin
_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A HALIN YANZU😁._
*ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma
*SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano)
*KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo)
*BURI ƊAYA!* (Mamu gee)
*WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull)
👇🏻karku bari ayi babuku
*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*
*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*
Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank
Saika tura shaidar biya ga wannan number ta WhatsApp
08030811300
Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN ta wannan number din
07067124863
Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.
*Karki bari ayi babu ke, Abari ya huce shike kawo rabon
Rano🚴🚴🚴
[3/18, 22:25] Hafsat Rano: *SAUYIN K'ADDARA*
*19-20*
©*Hafsat Rano*
*_ZAFAFA BIYAR na kudi ne idan kana son kowanne daga ciki ka nemi Wannan numbers din_*
*08030811300*
*07067124863*
*_Daurin boye_*
_safiyya huguma_
*_Buri daya_*
_mamuhgee_
*_Wutsiyar rakumi_*
_billyn Abdul_
*_Kai min halacci_*
_Miss xoxo_
*_Sauyin kaddara_*
_hafsat rano_
***
Daga chan nesa ya hango shi a tsaye ya rufe fuskar sa ruf da glass, k'arasawa yayi wajen, kallon sa asase yayi daga sama har k'asa, sai a lokacin ya lura da ashe rigar ma a baibai ya sakata,
"Kaga garin sauri shaf na manta a juye na saka rigar." Ya fad'a cikin borin kunya
"Ba case ai, shiga mota muje ko?"
Kallon motar Hafiz yayi ya dan yi jim kafin yace
"Na zata anan zamuyi maganar ai."
"Ba anan bane, Hajiya ce take son ganin ka."
"Toh..."
"Muje ko?"
"muje toh!" Ya fad'a a sanyaye dan sai yaji jikin sa yayi sanyi kuma.
Motar suka shiga wadda take rufe ruf baka hango ko na ciki irin dark tint ɗin nan, sanyin ac ne ya bige shi ya lumshe ido yana budewa kafin ya gyara zama sosai yana ayyana wa a ransa dama shine me wannan jibgegiyar mota haka.?
Be sake shiga rudani ba sai da aka wangale musu babban gate din gidan a jerin sababbin gidajen dake jere a hadaddiyar unguwar ta jan bulu 3rd gate, sai da Asi ya daidai ta kan motar a harabar gidan dake cike da motoci da mutane kungu-kungu yan biki, kallon Hafiz yayi yace
"Ka jirani a nan zan kira Hajiya."
"Toh."
Fita yayi bayan ya cire kwalbar fuskar sa ya koma gefe yana danna mata kira, tana zaune cikin jama'ar ta yan biki ana shirye shiryen tarbar Amarya duk da ba wani taro akayi ba saboda lafiyar Ummi amma ba laifi gidan ya dan cika saboda dangi musamman yan uwan Alhaji da ke cikin birnin na Kano da kewaye.
Kallon wayar tayi ba tare da ta daga ba ta mike tsam sannan ta kalli aziza tace
"Duk wanda yazo nema na ina zuwa."
Fita tayi cikin shigar alfarma tana tafe tana kallon ko ina na gidan, dakin dake chan gefe ta sake kallo kafin ta karasa wajen motar, kallon Asi tayi tayi masa alama daya bude mata motar, baya ta shiga ya rufo hakan yasa Hafiz saurin juyowa.
"Kai ne Hafiz?"
Ta fada tana kallon yanayin sa, kunya ce ta kamashi ganin yadda ta tsurawa rigar sa ido, dauke kanta tayi ta amsa gaiswar da yake mata
"Basu kyauta maka ba gaskia, naji labarin komai da ya faru da kai, sannan na tausaya maka matuka, dalilin haka ne yasa nake so muyi aiki tare, dan dukkannin mu a bigire daya muke."
"Aikin menene?"
"Biyan ka zanyi ai, abu na farko zaka fara dawowa gidan nan da zama."
"Nan gidan kuma, amma me yasa?"
Dan dafa kanta tayi, daga ganin sa talaka ne me uban girman kai, in ba haka ba menene na tsare ta da tambayoyi haka, tunani tayi kafin tace
"Aiki zamuyi tare, dole sai kana kusa dani, idan har kana so ka rama abinda Maryam da Arkel sukayi maka, dole sai mun hada karfi."
"Idan nace na yafe mata kuma fa?"
Da sauri ta kalle shi
"Yes... idan nace bana son daukar fansar ba
"Zan dinga baka albashi duk wata, zan sa a chanja wa mahaifiyar ka gida.".
Kallon ta yayi da sauri, cikin gamsarwa tace
"Zaman ka a nan din na dan lokaci ne, idan komai ya kammala zaka koma chan."
"Wacece ke?"
"Wannan ba matsalar ka bace, anan gidan Maryam zata zauna, anjima za'a kawo ta, idan ka amince da bukata ta ka kira wayar Asi, ina da baki sai na jika."
Balle murfin motar tayi ta fita tana hararar motar
"Shegen taurin kai, mtsw."
"Ka maidashi zai kiraka."
Har ya juya tace
"Ka kira me gidan da suke haya kace kwana uku ya basu su fitar masa daga gidan sa, ni zan siya in yaso sai ka maida mahaifiyar ka ciki."
"Godiya nake Hajjaju."
Motar ya shiga ya tada ya bar gidan, tun da suka dau hanya Hafiz yake cikin tunani, har kofar gida ya mai dashi ya ciro dubu biyar ya mika masa, kin karba yayi ya shige gidan yana mamakin yadda akayi ma yasan har gidan nasu.
Dariya Asi yayi ya maida kudin sa yaja motar ya bar unguwar yana hasaso abinda yake shirin aikatawa.
***
Gaba daya jikin ta ya gama sanyi musamman nasihar da Baba yayi mata sosai akan muhimmanci zaman aure, komai yin sa kawai take ba tare da tana gane wa ba, duk yadda Anty Maryam ke mata nacin ta tashi ta fara shirya wa ganin har anyi magriba tana zaune gashi takwas yayi mata text zai zo ya dauke ta.
Da kyar ta tashi ta shiga wanka zuciyar ta na tsananin harbawa kamar zata fado saboda tashi hankalin rabuwa da gida, ko da ta fito daga wankan sai da Anty Maryam ta sata ta sake komawa ta daureye jikin ta da wasu hadin turaren ruwa da ta siya a wajen wata kanwar mijin ta da yake barebari ne su, sosai ruwan yayi mata kamshi da dadi hakan yasa ta ɗan jima a ciki har sai da aka buga mata kofa, tana fitowa ta hau shiryawa a cikin haddadden lace ɗin ta dark Ash da touches na gold dinkin riga da zani, lafiyayyiyar laffaya Anty Maryam ta nada mata tayi kyau kamar ka sace ta ka runtuma da gudu😝
Hannun ta ta riko har dakin umma dake zaune cikin yan uwan ta suna ta shan shafta, ana ganin amarya a ka hau guda hakan ya sake saka zuciyar ta tayi rauni, kuka ta saka wiwi jin wata tsohuwa tana ta tsokanar ta tana Allah sarki zata bar gida.
Kowa kuma sai ya hau magana akayi mata cha masu fada nayi masu surutu dai ana tayi, tuni kanta ya fara daukar zafi babu abinda take fuskanta a maganganun nasu, ganin haka ne yasa Anty Maryam ta saka kawarta Asma'u ta fita da ita suka koma chan d'akin suka zauna ana jira ango duk da yace da shi kadai zai zo sai data saka masa kuka sannan ne yace zai duba, ko da aka fadawa Baba yace shi zai zo murna ya hau yi dan dama shi ba wani son bidi'ar yake ba, suna nan zaune Walid ya shigo da gudu yana ihun ga motoci nan sun fara zuwa, wani irin tashin hankali taji ta shiga wanda bata taba tunanin akwai irin sa ba, lamo ta sake yi a saman katifar tana jin kamar zata fita a dari saboda wani irin yanayi na tsoro tsoro daya ziyarce ta a take.
Sama sama take jiyo gaishe gaishe a tsakar gidan nasu, tana nan zaune tana jiran tsmammani text ya shigo wayarta
"Are You ready?"
Kallon sakon tayi, bata san me zata ce masa kuma ba, jin batayi reply bane yasa ya ajiye wayar ya fito harabar gidan yana kallon ko'ina.
A hankali ya daga kansa sama yana duba taurarin da suka yi wa saman ado, zuciyar sa ce ta lula chan wasu lokuta shudaddu, runtse idon sa yayi yana hango lokacin da suke wata hira shi da Arab, shekara kwana, yau gashi har sun cika shekara talatin da doriya a duniya, shekaru biyar kenan cif da barin sa gida, be taba tunanin rayuwa tana gudu haka ba, sauke kansa kasa yayi yana jin rauni sosai a kasan ransa, so yake ya tabbatar wa kansa auren da yayi hakan ba zai zama abin magana ba duba da yanayin da mahaifiyar sa ke ciki, yasan za'a yi magana tun da dai mutane ba'a raba su da magana, amma yana ji a ransa hakan shine daidai, shine cikar mutum da darajar sa.
Dafa shi yaji anyi ya jiyo da sauri, sakin hannun sa yayi ya koma baya yana jingina da mota
"Sun tafi ne?"
Ya tambaya yana ciro wayar sa daga wandon rigar sa,
"Munyi waya da Anty Nabila tace sun je, amma suna bukatar a karo motocin saboda mutanen da yawa."
"Amma nace fa bana son gayya,na fada mata ita ma shine kuma za'a ce a karo mota, i cnt gaskia."
"Kayi hakuri dai, kasan sha'anin mata, ayi a gama lafiya shine."
Hararar sa yayi
"Ka taimaka dai kaga ta sake kira."
"Sai ku hada data Alhaji, biyu kawai sun isa ai, kai ka dau wannan sai shi ismo ya dau ta alhajin."
"Yauwa babban yaya, sai kayi Arkel Poultry farm."
Duka ya kai masa ya goce yana dariya.
"Zan kamaki ne."
***
Kuka sosai take kamar ranta zai FITA, tana ji tana gani aka fito da ita daga gidan iyayen ta, gidan data taso ta saba yau ta barshi, sabuwar rayuwa da bata saba ba bata san da ita ba zata fara ta da mutane da bata taba sanin su ba iya kar rayuwar ta.
Tausayi sosai ta bawa kowa masu raunin zuciyar ciki sai da suka tayata koka wa, a haka aka ɗauki hanyar Arkel Mansion da ita kowa yana kulafucin so zuwa su bawa idon su abinci.
Sadiya da Asma'u kowacce ta kame a gaban mota, abinda Zaid da Ismo ke so dama kenan shiyasa suka dage aka karo motar.
Lokacin da suka isa tangamemen gidan sai da yawun bakin kowa ya kusa daukewa dan babu wanda ya taba zaton abin ya kai haka tun da ko jere ba'a zo anyi ba dan yace musu ba'a bukatar komai, duk da haka sai da Alhaji Faruku ya bata kayan da yayi mata a take tace ta bar wa umma aka zuba mata ita ma dakin ta ya fito fes kamar na sabuwar amaya.
Hakan kuwa ba karamin bata wa Hajiya Mama rai yayi ba, Rauda kuwa ko a jikin ta sun sake hadewa da saurayin ta Aseem dan dama fada sukayi a lokacin da maganar Arkel ta fito.
Duk suna zazzaune a falon aka shigo da amarya, da kafar dama ta shigo bakin ta dauke da addu'a haka aka hau gaishe gaishe tsakanin ahlin biyu. Bayan doguwar gaisuwa da yan al'adu na malam bahaushe suka damka musu amarya, kukan ta ne ya karu har tana kokarin shidewa, damƙe hannun Anty Maryam tayi da suka mimmike, kallon su Hajiya Mero tayi cikin kasaita tace
"Ku rakata saman kawai naga kamar akwai masu son ganin dakin Amarya."
Shiru sukayi dukkan su dan sun gano magana ta gasa musu,babu wanda ya bi ta kanta suka haura saman suka dangana ta da hadadden shiryeyyen dakin ta daya sha lafiyayyen zanen gado fari kal da wasu jajayen fulawowi masu masifar kyau da kawa.
Tsayawa Bayyana haduwa ko tsaurwar da dakin yayi ma bata baki ne, a gefen gadon ta zauna tana jin su suna ta santi da yabawa, Asma'u dai ta rasa bakin magana dan gaba daya gidan ya tafi da zuciyar ta, sai da Sadiya zango ta dungure ta sannan tayi saurin rufe bakin ta dan har wani kuda yana neman fadawa. (Amma fa babu kuda a wannan hadadden gidan sai dai in ta abinta tazo
27, January 2025
Rukayya
Good