Showing 39001 words to 42000 words out of 98004 words
kallon ne tazo kan hoton Hafiz, da sauri ta kalli kofar dakin, runtse idon ta tayi tana jin kamar zatayi kuka, hannu kawai tasa ta danna delete bayan ta rufe idon ta. Ji tayi kallon ya fita daga kanta, ajiye wayar tayi ta kwanta rigingine tana tunani.
Tunawa tayi da Ummi da halin da take ciki, abun ya tsaya mata sosai, juyi ta hau yi tana tunanin hanyar da ya kamata ta taimaka mata
Tana nan kwance har karfe goma babu motsin kowa, zaman ne ya kundure ta gashi datar ta ta kare balle ta hau whatspp ta duba. Tashi tayi ta kwashe kayan jiya da daddare ta fito falon, tsaf tsaf ko ina ga wani sanyayyen kamshi dake tashi, kallon ko'ina tayi tana tunanin kofar Kitchen, a saman Centre table ta ajiye kayan ta bude kofar dake kallon ta, tayi sa'a kuwa nan ne kitchen, kayan ta dauko ta kai Kitchen din, kallon tsaruwa da haduwar Kitchen din ta tsaya yi, kafin ta zuba kayan a cikin sink ta fara wankewa.
Sai data gama tas sannan ta zuba ragowar kayan a fridge ta jawo kitchen din ta fito. Kofa taji ana bugawa ta bude, Sadiya ce tsaye da kaya a hannun ta, da fara'ar ta tace.
"Ƙaraso mana."
Kin karasowa tayi ta ajiye kayan kawai tace
"Ina kwana Anty?"
"Lafiya lou ya gida.".
"Gashi nan inji Hajiya tace na kawo muku."
"Toh mun gode."
Jera su tayi a saman Centre table din ta bude dayan dakin, yana kwance daga shi sai gajeren wando babu ko yar singlet, da sauri ta ja kofar tana zaro ido.
Karar kofar ce ta tashe shi ya bude idon sa, wayar sa ya jawo ya duba time, dan yatsine fuska yayi ya sake mai da kansa, kasa komawa yayi kawai ya tashi, har zai fito a haka ya tuno, komawa yayi ya maida doguwar rigar ya fito.
Kallon kayan dake kan table ɗin yayi ya wuce dakin, yana bude kofa ta juyo da sauri, kallon ta yayi da shanyayyun idon sa da sukayi kalar bacci, dauke kanta tayi da sauri,
"In shigo?" Yace tana takowa ciki, a gaban ta ya tsaya ya harɗe hannun sa,
"Ina kwana?" Ta fada duk ta duburburce, sai daya ja fasali kafin yace
"Shine kika tashe ni ko? Are you dat desperate to see me da kika kasa hakuri na tashi?"
Marairaice wa tayi
"Ba haka bane? Na fa ganki kina leke na."
"Allah ba leken ka nake ba, zuwa nayi fa naga..."
"Ki ganni ko? Toh gani, what did u have in store for me ?" Ya fad'a yana matsowa. Da sauri taja baya, ya sake matsowa ta sake ja baya taku biyu yayi ya rikota, hannun ta ya mayar baya ya rike su yana mata shu'umin murmushi. In a low voice yace
"Lemme just..."
Hugging din ta kawai taji yayi from no where, mamaki ta hau yi, shi kuma wannan haka yake ko wani abun ne ya hau kansa?
Sai daya dade sannan yayi breaking hug din ya dan matsar da ita baya,
"Muje muyi breakfast."
Kamar mutum mutumi ya juya ya bar ta a wajen yana murmushi kasa kasa da shi kadai ya san manufar sa. He just don't know me yasa duk sanda yake tare da ita sai yaji wani nishadi na ratsa shi.
Haka sukayi breakfast din duk da ta kasa sakewa, shi din ma ba wani ci yayi sosai ba ya matsa kawai yana kallon ta, duk sai taji ta takura da yadda yake kallon nata, wayance wa tayi ta hau kwashe kayan ta shige kitchen ta hau wankewa.
Jin shiru bata fito ba yasa ya bita Kitchen din, da sauri ta waigo jin mutum a bayan ta, hannun sa zube a cikin aljihun rigar sa ya babbake kofar ba hanyar da zata bi ta fita gashi sai wani irin kallon kasa kasa yake mata.
Ganin ta gama abinda take gashi tana son fita yasa kawai tayi ta maza ta nufo shi yana dan yarfe hannun ta, kin matsawa yayi ta kalle shi ta kalli kofar, bata yi aune ba sai ji tayi kawai ya saka hannu ya jawo ta, babu wani dogon tunani ya hade bakin su waje daya🤭🤫🚴🚴
Ba ruwana ba hannu na bane oo🤣 hannun Teema Gabas ne.
Gaba daya Maryam ta rasa in da Arkel ya saka gaba, abubuwan da yake mata gaba daya sun girmi tunanin ta, bata taɓa zaton sa haka ba sai taga ashe ya wuce hakan.
Sai wajen sha biyu na rana sannan ya riko hannun ta suka sauko kasan, Hajiya Mero kamar ta shako su har suka ƙaraso falon be saki hannun nata ba.
***
Gaba daya abin duniya ya hadu yayi masa yawa, duk yadda yaso ya boye wa inna kasawa yayi, gashi manager ya ishe shi da waya akan lallai ya dawo kan aikin sa dan basa son daga farawa yazo musu da kailula.
Sosai ya fira hayyacin sa a yan awannin da basu gaza goma ba, sakonnin da yake karbar duk bayan wani lokaci daga wajen Asi shi ya sake saka shi cikin halin da yake ciki, baya so ya amsa musu tayin su sai dai ya lura ba zasu taba hakura ba idan ba ya amsa ɗin ba.
Shigar da yayi gida ya tarar da inna a kwance zazzaɓi ya rufe ta ko abinci ta gagara ci ne yasa ya juya kawai ya fita ba dan yasan in da ya nufa ba. Tafiya kawai yake yi ba tare da ya san in da zai nufa ba, a karshe ya yada zango a kofar wani shago bayan doguwar tafiyar da yasha a kafa ba tare da sanin adadin nisan da yayi ba. Zama kawai yayi daga gefe yana sauraron hirar da suke yi sama sama, hankalin sa ya sake tattara wa jin wani a cikin su yana bada labari me shige da kalar nasa, zumbur ya mike ya bar wajen bayan ya gama jin komai. Tafiyar da yayi ne sosai da zai koma gidan ne yasa ya gane ba karamar tafiya ya sha ba dazu dan dai baya hayyacin sa ne. Sai daya fara tsayawa a shagon layin su ya saka katin hamsin sannan ya kira lambar Asi, bugu daya kuwa ya dauka dan dama jiran kiran nasa yake yi.
"Ka gaya wa Hajiya na amince da tayin ta."
Wata irin mahaukaciyar dariya Asi yayi cikin jin dadi yace
"Ka ceci kanka dan samari, ka shirya anjima zan zo na dauke ka."
Be yi magana ba ya kashe kawai yana jin karfin guiwar aikata abinda ya yanke. Da farin ciki ya shiga gidan sabanin yadda ya fita, wanka yayi a gurguje ya shirya ya fito waje yana jiran shi, yana nan zaune ya hango shi yayi parking a dan gaba kadan, tashi yayi ya karasa babu wata magana ya bude mishi motar ya shiga ya ja suka bar unguwar.
Yau be shiga cikin gidan ba a waje ya tsaya ya kira wayar ta, ok kawai tace ta ajiye wayar tana murmushi me cike da ma'anoni.
Tun da ta fito ya ke kallon ta da yanayin ta, har ta shigo motar ta zauna kafin tace
"Muje gidan ko?."
"Owk Hajjaju."
Wata unguwa me yanayin gidajen masu rangwamen karfi suka nufa babu wanda ya kula shi shima kuma beyi magana ba har suka isa, bude masa kofa Asi yayi bayan ya bude mata ta fita, mukulli yasa ya bude gidan sannan suka shiga gaba daya, karamin gida ne sosai zaman mutum daya da karamin tsakar gida sai rijiya daga chan gefe, toilet da Kitchen sai dakuna guda biyu falle daya daya sai dan karamin falo daga gefe. Daga mukullin tayi ta mika masa,
"Gashi nan daga nan zuwa kowanne lokaci zaku iya tattaro kayan ku ku dawo, komai zai fara ne daga ranar da kuka dawo gidan, amma zan so ku dawo a gobe ma saboda yadda nake so komai ya tafi yadda na tsara."
Kamar ba zai karba ba sai kuma ya danne zuciyar shi ya karbi mukullayen ya zuba musu ido kamar me son gano wani abu, bubbud'e kofofin duka Asi yana shafa kansa
"Duba ka gani, gaskiya kana da sa'a sosai gida haka sukutum, Allah ya taimaki Hajiya."
"Wannan kadan daga cikin tanadin dana yi masa kenan idan har ya bani hadin kai, shi yasa zan ajiye takardun gidan a wajena har sai lokacin da ya cika sharuddana daga nan zan damka masa a hannun sa halak malak.
"Zan yi kokari na cika duk sharadin da kika saka, sai dai kema ki cika alkawari kuma karki yaudare ni."
Kafe shi tayi da kallo tana mamakin kalaman sa, ko dai ya san abinda take shirya wa ne? Amma ta yaya? Bata jin ya sani kawai dai yanayin nasa ne haka.
"Karka damu, zan yi maka yadda nace."
"Shinkenan, zan koma wajen aiki na gobe zan sanar musu na ajiye aikin, zan dawo washegari daga nan sai komai ya fara, duk abinda za'a yi ayi shi a cikin wata daya nayi gaba."
"Hakan yayi, sai su dawo goben tun da dama gobe aka ce ku tashi ko?"
Kallon ta yayi tayi saurin waskewa
"Dazu naji kamar kace gobe masu gidan da kuke sun ce ku tashi ko? Ko dai kunne na ne?" Ta kalli Asi, da sauri yace
"Haka ne Hajjaju."
"Shikenan kawai." Yace yana kokarin fita daga gidan, yana fita ta kalli Asi da sauri tana rufe baki
"Na kusa nayi banbarma fa."
Dariya ya saka
"Wallahi Hajiya, Allah dai ya kiyaye kamar be fuskanci komai ma"
"Toh Allah yasa dai."
Fita sukayi aka jawo gidan, yana tsaye daga gefe sai da suka shiga motar sannan ya shiga, a hanya ya ce su sauke shi ya wuce gida, dubu biyar Hajiya Mero ta mika masa, da zai ki karba sai kuma ya tuno ko kudin kwaso kayan nasu basu dashi shiyasa kawai ya karba beyi ko godiya ba ya wuce kawai.
A daren ranar suka gama tattare komai da sassafe kafin gari ya waye suka tattara suka bar gida tun kafin azo ayi musu tijara. Inna na son tambayar sa yadda akayi ya samu gida sai dai ganin yadda yake ta tsare gida yaki bari sam suyi doguwar magana yasa ta share kawai ta bari idan ya zauna sai suyi maganar.
Ana gama saka komai a gidan ya dau hanyar Gumel.
***
Kuyi hakuri da wannan pls
Ko editing banyi ba wlhi.
_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A HALIN YANZU😁._
*ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma
*SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano)
*KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo)
*BURI ƊAYA!* (Mamu gee)
*WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull)
👇🏻karku bari ayi babuku
*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*
*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*
Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank
Saika tura shaidar biya ga wannan number ta WhatsApp
08030811300
Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN ta wannan number din
07067124863
Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.
*Karki bari ayi babu ke, Abari ya huce shike kawo rabon
Rano🚴🚴🚴
[3/18, 22:25] Hafsat Rano: *23* S K
©*Hafsat Rano*
*_ZAFAFA BIYAR na kudi ne idan kana son kowanne daga ciki ka nemi Wannan numbers din_*
*08030811300*
*07067124863*
*_Daurin boye_*
_safiyya huguma_
*_Buri daya_*
_mamuhgee_
*_Wutsiyar rakumi_*
_billyn Abdul_
*_Kai min halacci_*
_Miss xoxo_
*_Sauyin kaddara_*
_Hafsat rano_
***
A hankali ta zame hannun ta tana karasawa gaban Hajiya Mero, duk kunyar yadda take kallon ta ya rufe ta. Da sauri ta taro ta tana kokarin zama a kasa
"Karki soma zama a kasa sanyin tiles." A kunya ce tace
"Ina kwana Hajiya?"
"Lafiya lou amarya, ya bakunta?"
Kallon Arkel tayi da ya dauke kai yana kallon dakin Ummi
"My son an fito kenan, an tashi lafiya?"
"Ina kwana?" Yace yana dan zama a kujerar falon,
"Lafiya lou ango, babu wata matsala dai ko?"
Dan kallon ta yayi kamar zai yi magana sai kuma ya fasa, murmushi tayi kawai tana kallon Maryam
"Ki sake fa nan gida ne, ko da yake kwana nawa ne ma?"
Ita dai Maryam bata ce komai ba, tasan dai tun asali ba wani alaka ce da ita dasu ɗin ba, kuma tasan harda ita a kara tunzura wutar kiyayyar su ga Hajiya Mama, shiyasa ita sam matar bata sabgar ta amma sai tayi mamakin yadda take ta nan nan da ita yanzu. Toh koma dai meye ita ta sani.
Tashi yayi kawai ya fita yana danna kira a wayar sa. Chan suna nan zaune babu me magana a cikin su sai gashi ya dawo.
"Taso." Kawai yace yana nufar dakin Ummi, da sauri ta mike dan dama zaman ya ishe ta, hankalin ta kuma na kan dakin tana so ta kara ganin matar, da kallo Hajiya Mero ta bisu baki sake dan bata kawo hakan ba, har suka shige dakin tana kallon su cikin wani yanayi.
Zama yayi a gefen gadon nurse din dake ciki tayi sauri gaishe su sannan ta fice.
Tana fita hajiya Mero ta Kira ta cikin daki
"Ya ake ciki? Akwai wani cigaba?"
Dan kallon gefe tayi kafin tace
"Hajiya babu komai, allurar nan dai ita nake mata ko yaushe, duk jikin ta fa yayi saba sai ma kinga bayanta."
"Yawwa haka nake so, kije kawai yau tun da uban iyayin yana gida gaba daya yau ga dukkan alama."
"Shikenan Hajiya, Nagode bari na tafi."
"Owk bari kiga."
Kudi ta ciro ta mika mata sannan ta tafi, kallon kanta tayi a cikin mudubi tana tuno wani abu da take shirya wa, dariya tayi kawai ta juya ta bar d'akin.
***
Wunin ranar Maryam a dakin tayi, taki motsawa ko nan da can tana lura da komai, mamakin abinda zai kwantar da mutum haka take sannan kuma ace duk anyi magani babu? Tana nan zaune duk farkawar da Ummi zatayi akan idon ta take yi, mamaki ne ya kamata ganin hannun ta daya yana motsi a hankali wanda idan har ba ka kula sosai ba ba zaka ga komai ba, da sauri ta mike tana sake kallo da son tabbatar wa, hakan kuwa ne da gaske motsi yayi, kokarin nuna abu take daka chan saman drawer sai dai bata san menene ba, wajen ta kalla sannan ta sake kallon Ummi, idon ta fes akanta ko kiftawa batayi, a hankali ta taka har gaban wajen tana sake kallon komai na kai,magunguna ne birjk akai da allurai kala kala, bata gane me take nufi ba ta cigaba da kallon magungunan daya bayan daya tana karanta jikin kwalin, rubutun da ta gani ne a jikin allurar data dauka a karshe ne ya ta sake tsorata ta ainun, sake karanta wa tayi a karo na biyu, kanta ne ya kulle baki daya, da sauri ta hau bubbud'e drawers din dakin tana binciko wa, katin asibiti ne ya fado ta dauko shi da sauri tana dubawa, duk magungunan da suke jikin katin ba sune a wajen ba, hasalima wadandan magungunan da ta gani basu chanchanci mutum ya sha ko yayi amfani dasu ba, wani irin jiri-jiri taji ya fara daukar ta, kwalla me zafi ta biyo gefen idon ta, a yanzu ta fuskanci komai, ana amfani da shi ana cutar mahaifiyar sa, toh amma ta yaya? Kamar be shiga makaranta ba ko me? Dama ita tun data ga halin da Ummi take ciki sannan ta tuno da Hajiya Mero a matsayin kishiiyar ta sai taji sam hankalin ta ya kasa kwanciya, daren jiya gaba daya da abin ta kwana ta tashi.
Tattare komai tayi ta cire dankwalin ta ta zuba su a ciki ta kulle tana goge fuskar ta, fara lekowa tayi taga babu kowa a tayi saurin hayewa saman ta bude dakin ta ta zuba su a cikin wardrobe d'in ta ta rufe sannan ta koma kasan da sauri, murmushi taga ummin tayi hakan ya sake karyar mata da zuciya ta gane lallai akwai wani babban al'amari, abinda ta fuskanta ma shi be masan da wani abu ba, yawancin maza basa fuskantar irin wannan sai ayi ta maganin asibiti a banza.
Tana nan zaune tana tunanin mafita kiran sa ya shigo wayar, bin wayar tayi da kallo ta kasa d'agawa har ta katse. Tsaki yaja a hankali ya ajiye wayar ya cigaba da trading(Forex) din da yake, chan ya gaji ya ajiye komai ya kashe computer ya fito, bata san ma yana gidan ba sai ganin shi tayi ya shigo dakin, kallon ta yayi ya kalli wayar dake hannun ta..
"Baki ga kira na ba."
Ya tambaya yana kallon ta
"Na gani, kafin na daga ne ta zama misscals."
"Uhum... Dont lie malama. Ki jirani a saman ina zuwa."
Bata ce komai ba ta tashi ta fita,ita wallahi kunya ma yake bata yadda ko kunyar magana da ita bayaji a gaban ummi, ko dan yaga bata da lafiya ne oho."
Tana tsaye ya shigo yana nannad'e hannun rigar sa zuwa sama, hannun ta ya kama suka shiga dakin da yake aikin Forex din sa, sauke computer yayi daga kan kujerar ya karasa tattare ragowar kayan ya ajiye su a gefe sannan ya nuna mata wajen zama. Babban album ya d'auko ya dora mata a saman cinyar ta, kallon shi tayi sannan ta kalli album din, Ummi ce rike da yara biyu maza akan kafarta suna dariya da babban cake a gabanta, twins? Ta fad'a a ranta, bude na gaba tayi, yara yan shekara biyar identical twins babu abinda ya raba su a tsaye, haka ta cigaba da kalla cikin tsananin mamaki, sai data kusa kai wa karshe sannan yace
"Ba zaki tambaya ba?"
Rufe wa tayi ta kalle shi
"Twins?"
Daga mata kai yayi yace
"Yes."
Baki bude take kallon shi, bata taɓa tunani ba, kenan irin sa guda biyu ne to ina dayan
"Kina mamaki ko? Am the youngest, shine babba."
"Yana ina?" Ta fada tana sake bude hoton tana kallo
Dage kafad'ar sa yayi kafin yace
"I don't know ko yana ina."
Shiru tayi da tunanin ko ya rasu ne? Amma kuma ai da sai yace mata ya rasu, bata ce komai ba ta cigaba da kallon hotunan tana admiring nasu. Ji tayi yace
"You can ask me kome kike so ki sani, i dnt know why kawai naji ina so nayi sharing abubuwa da ke, feel free to ask komai, banda maganar shi amma."
Ajiyar zuciya ta sauke tace
"Ummi?"
Idon sa ne ya dan kada kadan, be ce komai ba tsawon wani lokaci har ta fara dana sanin tambayar sai kuma taji yace
"Komai ya faru ne bayan na tafi anambra saro kaya. Kamar yadda kika gani a pictures din nan mu uku ne a wajen iyayen mu, ni da shi sai Yaya Nabila, it was a nice family saboda yadda muke komai a tare, bani da hayaniya kamar shi and he's more friendly,
27, January 2025
Rukayya
Good