Showing 93001 words to 96000 words out of 98004 words
min wallahi, ka tafi kafin Ummi ta dawo ba ruwana Allah."
"Kora ta kike? Ni, Ni Ko? Shikenan bari na tafi."
"Sai da safe."
"Haka ma zaki ce."
Daga kanta tayi ya tashi ya fita yana cewa
"Zaki neme ni ne yarinya, Ni da nasan ki."
***
Shirye shiryen taron suna aka ake tayi, komai an tsara shi, ba karamin kudi Arkel ya kashe ba wajen ganin yayi komai cikin wadata, raguna hudu manya manya aka yanka aka rada sunan sannan aka aika dasu gidan su Maryam ɗin, in da za'a yi aikin su a chan. Tun azahar Yan uwa da abokan arziki suka fara zuwa na kusa dana nesa, har jama'ar Mali ma sun zo tawagar su guda ana gobe suna.
Sallar la'asar akayi sannan aka fito harabar gidan in da aka saka kujeru akayi decorating wajen, ba a san ran Arkel ba amma Ummi da Ya Nabila suka ce sai anyi, abinda ba wani taro aka tabayi a gidan ba, haka ya hakura ya bar musu gidan ma gaba daya tun bayan da akayi yanka. Babban Photographer aka dauko yake ta aikin sa, gefe kuma mutane ana ta cin abinci baka jin komai sai tauna, Maryam na zaune a in da aka tanada ta hango kawayen ta na buk sun shigo, zuwa sukayi suka gaisa akayi hotuna sannan suka samu waje suka zauna aka kawo musu abinci. ( Yau dai kawar zango bata diba wa Ya Bello ba
kamar yadda ta saba😂😂).
Yana tsaye a waje yana kallon wayar sa, shigowar ta layiin ya hango motar , gyara tsaiwar sa yayi har suka ƙaraso. Hannun sa rataye a saman kirjin sa ya zuba mata ido yana kallon ta, Lace ne a jikin ta purple and Ash yayi masifar yi mata kyau, simple shiga tayi irin ta classy mata wanda suka jiku da wayewa, tare suke da Hidaya kawarta, bude mata kofar motar yayi yana murmushi
"Sannun ku da zuwa."
"Yawwa sannu ango."
Hidaya tace tana dariya, dariyar yayi ya kalli Lubna data bata rai taki kallon sa yace
"Ayi min afwa princess."
"Wai me akayi ne, tun da muka taho take bata fuska."
"Wai fa mantawa nayi ban fada mata haihuwar ba sai yau shine take fushi dani."
"Gaskia baka kyauta ba."
"Shiyasa ai nake ta bada hakuri, idan ma so ake na durkusa har kasa ne toh sai nayi."
"Shikenan, karka sake."
"Ba zan sake ba, i promise, ke da ma zaki shigo gidan kwanan nan."
Dariya sukayi suka jera har gate din gidan, a kofa ya tsaya ya matsa baya
"Sai kun fito."
"Ok."
Shiga sukayi kallo ya dawo kansu gaba daya, babu karya kaf wajen babu wanda ya kaisu haduwa da gayu, text yayi wa Ya Nabila saboda haka suna shigowa ta gane su, da fara'a ta karbe su ta samar musu waje suka zauna kafin ta je ta sanar wa Maryam ɗin.
Abinci ta fara kawo musu sannan tace su taso, wajen su Ummi ta kaisu da suke cikin gida duk kunya ta kama Lubna musamman yadda aka ɗin ga nuna ta ana ga wadda Arab zai aura, wajen suka dawo suka je wajen Maryam anan ya Nabila ta barsu ta koma wajen mutane, a mutunce suka gaisa ta karbi Huda ta rike a hannun ta tana jin kaunar yarinyar, tsabar kamar da take da iyayen ta twins kana kallon ta zaka ga kamar, har sai da aka tashi taron bayan magriba sannan suka tafi bayan ta bada uban kayan Barka akwati guda.
A kafa suka fito tawagar kawayen Maryam suna neman abun hawa, ran Teema Gabas a bace yake ko takeaway din da aka raba bata iya tsayawa ta karba ba, Sadiya zango ce ta dafa ta tace
"Kawata me akayi miki ne?"
Yatsine fuska tayi kafin tace
"Ki bari kawai, na sa rai da twin brother d'in Mijin Maryam wallahi gayen yayi min ya tafi dani sai gashi naga wadda ta yaga min a haduwa da komai, tun daga nan naji komai baya min dadi."
"Ayya... Gaskia babu dadi, amma fa ta hadu ba karya."
"Shine matsalar ai, naji ance Barrister ce ai."
"Auw haba, ah dole, mu muna nan muna fama da biology gwara ma ni nayi na gama ke kuwa har yanzu kin kasa wucewa."
"Kawata ya da cin fuska ne, haba daga fada miki matsalata.?"
Goyon Afaf Nabila Rano ta gyara tace
"Kuyi sauri mu samu ko ma samu abun hawa ga magriba tayi baban Afaf nake tsoro kar naje ya koma."
Sauri suka kara babu wadda ta sake magana da yar uwar ta.
🤣🤣🤲😂🤣🚴
***
Sauke kayan barkar Anty maryam tayi aka bude su, kaya ne hadaddu atamfofi da kayan jarirai masu masifar kyau,daga uwar har yar sun samu kaya masha Allah, waje daya aka saka su bayan an nuna wa Ummi.
Tana zaune tana bawa Hudah mama ya shigo, bata yi tunanin ganin sa ba, tun safe take ta kiran wayar sa bata shiga, da kallo ta bishi ganin ya tafi gaban warmers din dake ajiye a gefe ya hau bubbuda wa,
"Karka ce min baka ci abinci ba yau gaba daya."
"Toh kin bani ne?"
"Ai ban ganka ba, nayi ta kiran ka kuma bataa shiga."
"Ina chan na shiga busy."
"Busy busy kullum dai Baban Hudah."
Da sauri ya kalle ta, sai kuma ya kwashe da dariya har da rike ciki, sai da yayi me isar sa sannan ya dawo ya zauna yana miko mata hannu
"Kawo ta ki samo min plate naci abinci please, Wai Baban Hudah ko dadi babu."
Dariyar tayi ita ma ta mika masa ita tana gyara zip din rigar, wajen yake kallo bako dauke ido tayi saurin rufewa tana dariya
"A gama boye boyen da za'a yi, ina nan ina jira bawan Allah."
Ta sani sarai jan magana ne sai kawai tayi waje tana dariya a hankali.
Bayan ya gama cin abincin ne ya ciro keys guda biyu ya mika mata, hannu tasa ta karba tana masa kallon tuhuma
"Alk'awari na dauka da zuciya ta tun sanda kika shigo rayuwar mu, sai yau Allah ya cika min buri na, motocine guda biyu, taki daya dayar kuma ki bawa Baba."
Wani irin yanayi ta shiga, bata taba kawowa ko a mafarki ba, bata san sanda ta rungume shi kam ta saki kukan farin ciki, abun ka dame jiran kiris da sauri ya maida hannun sa saman nata ya rike ta kam kam yana shaƙar kamshin jikin ta, gaba daya sun saki jiki tuni ya fara mantawa da duniyar da suke, kukan Hudah ne ya dawo da su tayi saurin janyewa yana sunne kanta, yaushe ta haihu da har zata saki jiki haka, taso tayi wauta Allah ya taimaka mata Hudah ta ceceta, juya bayan sa yayi jiki a sanyaye ya gyara kwalar rigar sa yana cije leben sa, babu niyyar komai a ransa be san ya akayi yaso zarmewa ba, yayi browsing yaga illolin dake tattare da hakan ba zai so ta samu matsala ba, zai bi komai a sannu har zuwa lokacin da zasu dawo daidai.
Tashi yayi zai fita tayi saurin dakatar dashi ta hanyar cewa
"Ummi fa? Har da ita ma ka bata?"
Murmushin jin dadi yayi ganin Allah ya cika masa burin sa na samun wadda zata kula da Mahaifiyar sa kamar yadda zai yi, ya san ba kowacce mace bace dan mijin ta yayi mata kyauta zata tuna mahaifiyar sa fa, dawowa baya yayi ya mika mata hannu cikin son sake tabbatar wa yace
"Kawo taki sai na kai mata, idan yaso sai nan gaba sai a sai miki wata idan Allah ya hore."
Babu musu ta mika masa tana bata fuska
"Dama ita ai ya kamata ka fara saiwa bani ba, baka kyauta ba."
Murmushi yayi ya rankwfo daidai saitin fuskar ta yace a hankali
"This is what makes me love u more and more everyday, u are so special with pure heart, Allah yasa Hudah tayi halin ki, I love U endlessly my wife."
Lumshe Ido tayi a hankali tace
"I love You more."
***
*SAUYIN KADDARA*
55
© Hafsat Rano
***
Yana fita ta kira Umma ta sanar mata, godia sosai ta din ga yi tace ba zata fadawa baban ba sai ta kawo masa da kanta ta fada masa, tana ji daga wayar su Habubu nata ihun murna, dariya kawai tayi ta kashe tana tunanin rayuwa. Babu yadda Allah baya maida bawa, idan yaso a rana daya zai sauya maka rayuwa daga mara shi ka koma me shi, ko daga me shi ka dawo mara shi, gashi dai irin sauyin da ya samu tasu rayuwar, sau da dama abu na faruwa da mutum yaji kamar shi kadai duniya ta juya wa baya, sai dai ashe alkhairi ne yake bibiyar mutum ba tare da ya sani ba, kowacce rayuwa tana da kalar jarabawar ta, walau ta dadi ko akasin haka, kowanne bawa da yadda kaddarar sa take zuwa, ƙaddara na sauya wa ne da yadda aka tsara wa mutum, bashi da zabin guje mata face ya karbe ta hannu bibbiyu, ya mutunta ta watakila shine alkhairin.
***Shirye shiryen Biki ya kankama, sati daya ya rage, dukkan su ukun sun shiga busy Ya Nabila nata korarin hada lefe gashi har lokaci ya kusa kurewa ba'a kai ba, ginin gidajen da sukeyi guda biyu a kusa da juna shi ya saka duk suka kara shiga busy sosai, Arkel ma so yake ya tashi daga cikin gidan su tun da yanzu ko da yaushe Alhaji yana gida sai dai da la'asar ya fita gate ya zauna abokan sa suzo ayi hira, ga Baba Ladi ma ta dawo gidan saboda haka Ummi tana da masu ɗebe mata kewa ga Sadiya me aikin ta, so yake shima ya haɗa family sa waje daya shiyasa yayi hakan amma ba wai dan baya son zaman gidan bane sai dan kowa zai zama comportable da iyalin sa.
Baby Hudah ta yi yawo sosai a dan lokacin nan masha Allah, suna ta kokarin yin arba'in ga shirin biki, haka dai take daurewa tana yin gyare gyaren ta wanda yawanci Ummi ce tsaye akanta sai wasu abubuwan da Anty Maryam ke aiko mata.
Sati ya zagayo aka shiga biki gadan gadan, events hudu amarya tayi amma daya ango yaje dinner sauran ita da kawayen ta ne sai kamu hade da mother's Eve da Maman ta tayi, ranar Lahadi aka kai amarya gidan ta in da sati daya bayan nan Arkel zai koma shima.
Washegarin ranar ne Maryam tayi arba'in, murna a wajen Arkel baa magana, gida ya fara kaisu in da zatayi kwana biyu ta je duk in da ya kamata, yana ajiye su ya juya wajen aikin sa, a yadda yake sa rai sati me zuwa za'a bude shagunan, babu abinda ba'a zuba ba sai dan abinda ba za'a rasa ba.
Gaba daya yadda rayuwar gidan su ta chanja kadai take kallo tana jin wani irin dadi, kauna da kimar Arkel ƙara nin kuwa take a zuciyar ta, da yamma ta leka gidan Maman Walid suka sha hira, wasu kayan ta sake bata sannan ta dawo gida. Washegari tayi gidan Anty Maryam, bata barta ta dawo ba tace sai ta kwana, kiran umma tayi ta fada mata kar ta ji shiru, daren ranar kusan raba shi sukayi suna hira da Anty Maryam, anan ta sake fahimtar wasu abubuwan yadda zata sake kai mi wajen kula da mijin ta da yan uwan sa baki daya.
Daga nan kuma sukayi gidan sauran kannen Umman da yan uwanta na kusa, sai gidan Hajiya Mama bisa tursasawar Umma, anan ne taji labarin bikin Raudah sati biyu bayan na Arab, ta dan tausayawa Hajiya Mama ganin yadda take jin jiki komai sai dai ayi mata hatta da kashi wani lokacin a kwance take yin abinta, gashi yar ta ta data gatata bata nan balle ta tausaya mata, Maman su Raudan ce ke kula da ita da wata yar uwar su da Alhaji Faruku ya dauko daga kauye take kula da ita, kullum cikin zagin ta take da hantarar ta, sai tayi ta kuka idan Alhaji Faruku ya shigo duba ta tana so ta fada masa amma ba dama. Sai yamma likis ta koma gida da daddare sai gashi yazo, kamar kar ta tafi haka taji, haka ta tafi a ba yadda zatayi gashi Baba baya nan ko sallama batayi masa ba.
Washegari ta tafi gidan Ya Nabila daga nan suka tafi gidajen yan uwan Alhaji, daga nan sukayi gidan ango Arab.
Yana manne a gidan be je ko ina ba, gaba daya ya rasa yadda zai misalta aure, sai alokacin yake dana sanin shekarun daya dauka be yi aure ba, gashi ya hadu da Lubna wayayyiya, sai yake ganin kamar yafi kowa sa'a a duniya.
A falo suka tarar dashi ya wani bararraje yana kallo a cikin tafkekiyar Tv dake girke a tsakiyar falon, da sauri ya mik'e yana dariya
"Mun yi fushi."
Dariya suka sa Ya Nabila ta kalli Jallabiyar jikin sa tace
"Wai kowanne ango burin sa yasa jallabiya ya zauna a falo ne?"
Share ta yayi yayi dariya kawai ya mika mata hannu
"Bani princess dita, naga alama so kika ki kai ni kasa."
"Ina wuni ango?"
Maryam tace tana kunshe dariyar ta
"Auw kema wai? Toh ai shikenan tun da yar haka ce."
Zama sukayi aka gaisa Ya Nabila ta cigaba da tsokanar sa kafin tace
"Ina amaryar ne?"
Bude murya yayi yace
"Baby!" Shiru bata amsa ba ya mik'e yana cewa
"Ina ga tana toilet, bari na dubo."
Hada ido Maryam sukayi da Ya Nabila suka yi dariya, wucewa yayi dauke da Hudah a kafad'ar sa Amna ta bishi ya shiga corridor da zai sadaka da master bedroom d'in, turawa yayi ya shiga, tana tsaye ta sake wanka tana fesa body spray a jikin ta, murmushi ya sakar mata ta mayar mishi, mika masa hannu tayi bayan ta yafa dan karamin mayafi ta karbi Hudah sannan suka jero a tare suka fito yana rik'e da hannun Amna
" Sannun ku da zuwa."
Gefen Maryam ta zauna tana murmushi suka gaisa, wasa take wa Hudah kafin ta mike tayi Kitchen bayan ta mik'a wa Arab ita, kayan snacks ta doro akan tray ta hado da lemo ta kawo musu, hira suka cigaba kamar dama sun saba bata wani jin nauyi ko kunyar su, duk abinda take yi Maryam na ta lura da ita, dole ne ta sake saban zama yadda ta ga ana kallame miji kowa na adana nata dole ita ma ta zage damtse ta kula da nata.
***
Gaba daya satin sun yi shi ne cikin zaga dangi, na kusa da na nesa duk ta kai wa kowa ziyara, a na gobe zasu koma sabon gidan su ne jikin Hajiya Mama ya sake tsanani, bata san ma waye a kanta ba, kiranta Umma tayi tace lallai tazo ta duba ta idan zai yiwu a yau ma, kiran Arkel tayi bayan sun gama wayar ta fada masa, cewa yayi ta jirashi, chanjawa Hudah kaya tayi ita ma ta sake kaya ta sakko kasa ta sanar wa Ummi, suna zaune da Ummin ya shigo, tashi tayi ta bar Hudan a wajen ta bishi, sai daya fara watsa ruwa ta taimaka masa sannan yaci abinci, tun da dadewa ta gane Arkel baya wasa da harkar abinci, musamman na gargajiya, ta rasa a ina ma ya koyi cin ire iren abubuwan gargajiya duba da yanayin gidan nasu, haka take daurewa tana yi masa da taimakon Ummi da Baba Ladi.
Sun fito Ummi tace su je idan ba dadewa zasuyi ba su bar Hudah tun da tayi bacci har ma ta goya ta, irin murmushin gefen bakin nan Arkel yayi da Maryam ce kadai ta san manufar sa, kamar tace a kawo ta haka dai ta bishi suka tafi, suna shiga mota ya kalle ta yana dariya
"Ya akayi?" tace tana gimtse fuska
"Da sai kice wa Ummi ta baki yarki ai ba zaki barta ba."
"Ni nace maka haka?"
"Gashi nan a fuskar ki."
"Ni bance ba, kawai nasan halin Baban Hudah ne, nasan me kake shiryawa."
Dariya ya saka har da buga sitiyari yace
"Da yake ni kuma kullum sai aka ce miki abinda nake kenan."
"Toh ai kai ne."
"Zakiyi bayani dalla-dalla yarinya, wanne asibiti take?"
"Bari na kira Umma, na manta ban tambaya ba wallahi."
"Owk." Yace yana rage speed din motar, kiran Umma tayi tace mata suna AKTH, chan suka wuce suna tafe suna hira gwanin sha'awa.
Suna shiga asibitin suka tarar da Alhaji Faruku zai fita hankalin sa a tashe, be gansu ba har sai da Arkel ya yi masa horn, tsayawa yayi suka samu waje sukayi parking suka fito, suka karasa wajen motar tasa.
Gaishe shi sukayi ya fada musu dakin ya tafi su kuma suka shiga cikin asibitin. Su Umma zaune a waje suka karasa, saurin sauke kanta Umma tayi data hango su sun nufo wajen, har suka ƙaraso bata daga kanta ba saboda nauyi da kunya irin ta surukunta, ciki suka shiga suka duba Hajiyar suka dawo wajen abin tausayi dan ba karamin jiki take ji ba.
Komawa mota yayi ya barta ta zauna a wajen su Umman kadan sannan ta tashi ta tafi.
A hankali yake tukin yana so ya ga iya gudun ruwan ta, chanja hanya yayi a dawowar ma duk sai ya ga ta kagu aje gida, ya san tunanin Hudah take sai, murmushin yayi ya kai hannu saman rigar ta yana dariya
"An ce idan yaro yana kuka uwa tana iya ganewa ko?"
Kallon sa tayi ta kalli in da hannun nasa yake kai, tasan me yake nufi sai kawai ta dauke hannun nasa tayi dariya kawai batace komai ba, cikin son sai ya kure ta yace
"Ko za'a taimaka min da kaso na ne? Kar baby Hudah ta ci da rabona fa."
"La'hailah wai baka jin kunya ta anymore?"
Tace tana dauke kanta gefe, dariya yayi kawai be sake magana ba har suka zo gida, sai data zo fita ya rage murya yace
"Just get ready hakuri na ya kare, I need u back."
Sauka tayi tayi cikin gida tana mamakin shi.
***
Washegari aka tare a sabon gida, sosai gidan ya hadu babu karya, komai na ginin gidan irin na Arab ne sai dai kayan ciki su banbanta, a ranar Maryam ta jisu sukayau, bayan yan rakiya sun watse ta rufe gidan ta ta saka dan karamin bom short da half vest ta dinga yawo tsakanin falo zuwa kitchen da dinning area, yau kam ji take kamar ta samu wani freedom da da bata dashi duk da kuwa a sama suke a chan din Amma ba kamar kai kadai ba, sai dai zatayi kewar Ummi tasan ko dan yadda take rainon Hudah, sai ta dade bata yi kuka ba ta goye ta.
La'asar
27, January 2025
Rukayya
Good