Showing 24001 words to 27000 words out of 98004 words

Chapter 9 - SAUYIN KADDARA COMPLETE HAUSA NOVEL

06 Jan 2025

11631

min wannan alfarmar Abba,kuma dan Allah karka ce a'ah. Ina ganin hakan shine kadai zai sa na biya maka da karamcin daka nuna min."

"Kana ganin babu matsala?" Alhaji Faruku ya tambaya yana jin wani irin farin ciki na ratsa shi

Daga masa kai kawai Arkel yayi dan yadda yake jin zuciyar sa na bugawa da sauri da sauri be taba fuskantar irin hakan ba, tashi Alhaji Faruku yayi ya shiga cikin gidan, dakin sa ya wuce da sauri ya chanja kayan jikin sa, waya ya ciro ya kira wasu numbobi, cike da farin ciki ya fito ya dawo falon, lokacin Arkel na magana da Salim a waya, yana ganin Alhaji Faruku ya shigo ya kashe yana gyara zama.

"Dama nayi waya ne da yan uwana suna kan hanya yanzu zasu ƙaraso." Ya fada yana sauke kansa kasa

"Madallah, kira su toh kace su same mu a masallacin cikin buk nayi magana da limamin masallacin yana kusa, in Sha Allah muna zuwa zai daura auren."

"Owk tam."

Direct masallacin cikin buk suka nufa kowa a motar shi, suna zuwa dukka suma suna karasowa, da sauri ya isa wajen Kamal yana jin shi kamar ya fita da gudu saboda tsabar zulumi, dariya Kamal ya hau yi masa yana leka fuskar sa, kasa kulashi yayi ko ya maida mishi komai har salim ya iso da uban alawa da goro na daurin aure, dariyar sa kawai yake kunshe wa ganin yadda oga yayi kicin kicin da fuska kamar zai saki kuka. Sallah suka fara gabatarwa kafin ayi sanarwar daurin auren, mutanen masallacin suka zauna aka fara gabatar da daurin auren bisa sharad'i na addinin Islama.

Tun daga sama har kasa yaji wani abu ya tsirga masa lokacin da yaji limamin masallacin na cewa

"Alhamdulillah, an daura auren Malam MUHAMMADU ALMUSTAPHA DA AMARYAR SA MALAMA MARYAMA ABUBUKAR HAMZA akan sadaki naira dubu d'ari lak'adan ba ajalan ba... Allah......"

Iya nan ya iya ji gaba daya sai yaji jin sa ya dauke, wani irin yanayi me wuyar fassarawa ya samu kansa a ciki, yana jin lokacin da Kamal yake dora masa babbar riga a saman kayan jikin sa, bashi da kuzari ko ƙarfin jikin sa zai iya buɗe baki yayi magana.

Farin cikin da Alhaji Faruku ya shiga ba zai misaltu ba, ya rasa in da zai kansa, a daddafe ya amsa gaisuwar mutanen wajen yayi sauri ya yakice ya fita daga cikin masallacin, kamal da Salim na hango shi ya fito sukayi saurin isa wajen sa, hakan yasa Arkel ya bi su suka karasa gaba daya suka zube, gaishe su suka yi sannan suka yi godiya.

"Ka sameni a gida da daddare Muhammadu."

Kamal ne ya amsa suka tashi, sauran kayan alawa da goron suka zuba masa a booth ya ja ya bar masallacin.

"Wai kai baka da abokai ne?" Kamal ya faɗa yana hararar sa

"Kaga nan." Ya maida mishi yana kokarin cire babbar rigar, rike hannun sa kamal yayi yace

"Aiko karya kake ni wan ka ne wallahi, kar ka cire rigar kuma ka bari muje my wife ta ga kanin ta ango tasan ta girma ta daina abun yara."

"Uhum.."

"Wai ya akayi hakan ta faru ne duk dazu baka min wani bayani ba."

"Allah ne ya tsara, kana ganin zan iya gujewa faruwar hakan?"

"Gaskia dai a'ah.".

"Toh mu barshi kawai a matsayin wata babbar ƙaddara, Allah ne kaɗai yasan dalilin juyawar al'amarin."

"Allah ya sanya alkhairi kanina, ho ango ho ango."

"Allah bana so."

"Dole kaso angon Maryama, muje muyi wa Baba Karami godia muji ko ya samu Alhaji a waya ya sanar masa, ni fa ban masan Alhajin baya gari ba sai da kake fada min wlhi, Allah ma ya taimaka Baba Karami yana nan ya karbi auren da kuwa ni zan maka aure yaro."

'Dan cije bakin sa yayi ba tare da yace komai ba yayi gaba dan ya gano kamal so yake ya kaishi kasa da tsokana, sun sami Baba Karami a cikin masallacin suka gaisa da sauran wanda suka rage kafin su jashi gefe, godiya kamal yayi masa sannan ya tambaye shi ko ya sami Alhajin a waya,

"Na same shi, har ma munyi magana, sauran bayanin nace zakayi masa."

"Owk nagode Baba, Allah ya kara girma."

"Amin, Allah ya sanya alkhairi."

"Amin."  suka haɗa baki.'

Tun da suka fito kamal yake ta tsokanar sa yaki tankawa wa, kansa ne ma yake neman damun sa gashi yau ko Forex din be duba ba, haka suka jera har wajen mota Kamal be daina tsokane tsokanen nashi ba, dariya kawai salim yake bashi da bakin magana, kamal ɗin ne kawai zai iya yi masa ya zauna lafiya amma shi kuwa yanzu sai ya faɗa masa bakake.

Dan yatsine fuska yayi ya shiga motar kamal, jefa wa salim mukullin motar yayi yace.

"Ka barta a nan wajen naka, anjima da daddare zan dawo unguwar sai na dauka."

"Zaka dawo wajen amarya kenan, wai kanina an shigo layin manya."

"Amma dai kanaji yace na dawo na same shi da daddare ko? Ni ina ruwana da ita da zan dawo wajen ta?"

"Kai ka sani dai, ango ango, a daina kwana kwana kar a zo ana yar murya dan wallahi na saurarar ka zan ba."

Be sake cewa komai ba suka dauki hanyar gidan. Jingina yayi da saman kujerar motar ya lumshe idon sa yana tariyo komai kamar a lokacin yake faruwa, har suka isa be d'ago ba sai da kamal ya bude motar sannan ya cire kansa da k'yar yana kallon harabar gidan.

Yaya Nabila ce ta fito tana guda  yaja dan karamin tsaki kafin ya ɓalle murfin motar ya fito.

****
Alhaji Faruku na komawa gidan be ko shiga gidan sa ba ya kutsa kai gidan bakin sa dauke da sallama, Hijabi Walid ya miko wa umma ta saka Anty Maryam ta gyara ita ma sannan ya shigo, Baba na d'aki ya dan kishingid'a yana jiran sa ashe har bacci ya dan dauke shi, jin sallamar sa ce yasa ya mike da sauri yana gyarawa, gaisawa sukayi da Umma kafin yayi sallama a kofar dakin baban yana cire takalmin sa,

"Shigo mana Umaru, kaima kamar wani bako."

"Sannu da hutawa yaya, kana ta jirana ko?"

"Toh ya za'ai, nasan ai wani uzurin ne ya rike ka."

"Tabbas kuwa, uzuri ne babba ya rike ni, sai dai komai ya zama yadda nake so Alhamdulillah."

"Ah toh Masha Allah, kaji abinda yaron nan yake so yayi mana ko? Nace idan ma fasawa Yayi ai ya turo magabatan sa asan kan maganar ko? Amma hakan shiru ga abu yana matsowa ai babu dadi kuma dai kasan mata da saka damuwa."

"Haka ne, sai dai fa sun zo sun same ni, kayi hakuri yaya na rashin sanar maka da ban yi ba, yaro dai ya turo wakilan sa akan shi fa gaskiya aure ba yanzu ba, saboda haka idan yar mu ta samu miji muyi mata auren ta, idan kuma zata iya jiran sa har ya gama shiri a tsanake toh sai ta jira.".

"Ashhssha. Ashe haka akayi, shi yasa ya daina kira kenan." Baba ya fad'a yana kokarin danne zuciyar sa

"Tabbas haka akayi, rai na ya ɓaci sosai dan ba karamin cin mutunci bane sukayi mana, tun daga ranar nake neman mafitar yadda zai sanar maka da wannan labarin hade da wani na farin ciki da zai maye gurbin sa, toh alhamdulillah, yadda suka so tozartamu, Allah be basu dama."

"Basu kyauta ba gaskiya."

"Kansu sukayi wa yaya, yaro dai bashi kadai bane namiji a duniyar ba."

"Haka ne, kansu sukayi wa, babu komai Allah yasa haka ne mafi Alkhairi."

"Yama zama alkhairin yaya."

Karkace wa yayi kadan ya ciro kudin sadakin daga aljihun sa, ya ajiye a gaban sa

"Yau ma a karo na barkatai na sake yi masa shishigi a al'amuran ka yaya, sadakin Maryam kenan, na daura mata aure da wanda nake ganin shine daidai da ita, na yarda na aminta da tarbiyyar sa, haka ita ma Maryam na gamsu da ita nasan ba zata watsan k'asa a ido ba, dan haka nake baka hakuri a bisa wannan, ka yafe min dan Allah yaya."

"Me zan ce maka? Da wanne irin ido xan kalle ka na gode maka? Me zan ce maka a rayuwa ta? Yau a karo na biyu ka sake yi min abun da ba zan taba mantawa dashi ba a rayuwa ta, na rantse da Allah da ace akwai yan uwa irin ka masu zumunci da kaunar juna da kowa ya zauna lafiya a duniya, Allah Ubangiji ya faranta maka kamar yadda ka faranta min, Allah ya raba ka da sharrin duk wani abun ki ya raya maka gaban ka da bayan ka."

"Amin yaya, hakan shine zumunci, kai ne ya koya min yadda ake son dan uwa, kaine ka dora ni akan turbar daidai lokacin da ban samu ingantacciyar tarbiya daga wajen mahaifiya ta ba, kaine ka sadaukar min da komai naka har na kai matakin da na kai a yanzu, ni kuwa wanne irin butulu ne da har zan manta wannan? Allah karya nuna min ranar da zanyi maka butulci a rayuwata."

"Naji dadi sosai, hakan shine zumunci, Allah ya saka maka da Alkhairi ya raba ka da mahaifiyar ka lafiya, ya jikan iyayen mu da suka rasu."

"Amin ya Allah."

"Yaya... Ka sanar da su dan Allah, nasan nayi musu laifi na aikata abu ba tare da izini ba, abu me girma irin aure, suyi hakuri in Sha Allah alkhairi ne zai biyo baya."

"Kana nufin Maryama da mahaifiyar ta wai?"

"Su fa yaya... Kasan babu dadi abu daga sama haka."

"Babu matsala in Sha Allah, na san wacece me daki na, babu wani abu da zan zo mata dashi ta bijiremin, kar ka damu da wannan."

"Itama Maryam din..."

"Wai Umaru baka da iko akan ta ne? Baka isa ka yanke hukunci akanta tabi bane da har kake shakku?" Ya katse shi a hasale

"Allah ya huci zuciyar ka yaya,bari naje na sanar wa Hajiya."

"Yawwa, ita zaka bawa hakuri dan ita akayi wa laifi ma, tana matsayin uwa ya kamata a sanar da ita, karka sake irin haka ba tare da ka sanar mata ba."

"Tuba nake yaya, bari na saka Fahad ya shigo da kayan daurin auren."

"Toh uban Amarya, duk yadda kayi yayi." Ya fada yana dariya,

Fita yayi tsakar gidan umma na ganin ya fito tace

"Yau mutumin ka akayi dambu, bari na sa Walid ya biyo ka dashi."

"Amma naji dadi,dama na kwana biyu banci dambu ba, a ajiye min bayan sallar magriba Maryama ta kawo min."

"Toh shikenan."

"Ayi hakuri nayi laifi, yaya zai sanar dake komai." Ya fada yana ficewa, kofar da yabi umma ta kalla sannan ta kalli kofar dakin Baba, jin yana kiran ta yasa ta tashi tsam ta nufi dakin tana ji a kasan ranta akwai wani abu a kasa.

Tana shiga ya nuna mata wajen zama, sannan ya kira Maryam, a d'arare ta shigo ta samu gefe chan ta rakube tana sauraron shi.

Sai da ya fara da tuna musu karfin zumuncin da yake tsakanin sa da dan uwan sa Alhaji Faruku kafin ya sako maganar auren, daga Umman har Maryam ba karamin kada su maganar tayi ba, kuka Maryam ta saka tana tuno Hafiz, lokacin da taji Baba yana mika mata sadakin ta ne yasa ta k'ara tabbatar wa kanta ta rasa Hafiz har a bada, toh wa aka aura mata? Kila ma sadaka aka bashi saboda Hafiz din ya fasa auren ta, nasiha sosai Baba ya shiga yi mata, har ya gama bata samu kukan da take ya tsaya ba, a haka ta fito ta shige daki Anty Maryam na ganin haka ta bita da sauri, kuka take tayi ta kasa fada mata komai har umma ta shigo dakin ta same su.

Zama tayi a gefen gadon ta shiga bawa Anty Maryam labarin abinda ya faru, dukkan su shiru sukayi kowa da abinda yake sakawa a ransa.

***
Hafiz na zaune ya saka shinkafa da wake a gaba yana kallon, yau saura kwana biyu ya koma gida, tunanin Maryam yake da halin da ake ciki, gashi babu waya a hannun sa balle ya kira tun da wayar ya siyar ya bawa su Inna kudn da zasu d'an rike kansu kafin ya dawo, Allah Allah yake kwana biyun su cika ya zo gida yaji in da labarin su da Maryam ya kwana, Allah yasa iyayen nata sun yadda zasu jira shi din. Da haka ya saka chokalin ya fara ci yana yi yana duba lokaci saboda manajan gidan man ba mutunci ne dashi ba.

Allah sarki Hafizu 😭 laifin inna ne.

***
Yana kwance a falon gidan Yaya Nabila har akayi magriba, sai datayi mishi magana sannan ya mike da k'yar yayi alwala, a falon yayi Sallah saboda masallaci sun idar, shiru yayi yana kallon Tv yana tuno dan uwan sa, a haka ta fito tarar dashi, zama tayi a kusa dashi ya d'ago yana kallon ta

"Tunani ko?"

Ta fad'a tana kallon shi

"Mamaki nake ne,wai nine nayi aure, unexpected aure.".

"Haka Allah ya tsara."

"Haka ne kam, kana taka Allah ne  nashi, ban taba imagining rayuwar haka ba, na kasa iya figuring abinda nayi wa Arab."

"Mu cigaba da addu'a kawai, Allah zai kawo mana mafita."

"Haka ne." Ya koma yana jingina a jikin kujerar dakin.

Ba zaka je gidan su bane naga kana kwanciya?"

"Zanje, am just too weak, ga tunanin Ummi yau duk na barta ita kadai."

"Daurewa zakayi, ka sani ko a bamu amaryar mu a yau ma."

"Wa? Ba dani ba wallahi, su barta chn ma ni naje da abinda yake damuna."

"Tashi Ni dai toh." Ta fada tana dariya.

Da kyar ya tashi ya shiga karamin dakin da yake falon, watsa ruwa yayi yana yi yana tunanin Maryam, dan murmushi yayi lokacin da ya tuno wayar da yaji tana yi wa salim, zaki bayani dalla-dalla. Ya furta yana cije kasan lips din sa.

Sabon kaya ya tarar a saman kujerar dakin ya dauka yana dagawa, yasan aikin kamal ne dan haka babu bata lokaci ya saka ya fito fes dashi.

Yana fitowa falon Kamal ya shiga tafi, banza yayi masa yace

"Mukullin motar ka Please."

"Wai kai zaka kai kanka kake nufi? Toh baka isa ba sai naje naga kalar amaryar tamu."

"Dear kafa samun k'ani a gaba gaskiya, ka barshi yaci lokacin sa kai naka ya wuce.".

"Haka kika ce?" Ya daga mata gira

"Bari na dawo zakiyi bayani ne."

"A Dawo lafiya." Ta fad'a tana dariya.


Anty Maryam ce ta ciro mata kaya a cikin jerin sababbin kayn da Alhaji Faruku yayi musu na cin biki saboda ba lefe, sawa tayi duk idonta ya kumbura saboda kuka, hadaddun turarurruka ta shiga fesa mata ta shirya ta tsaf ta fito sosai kamar ka sace ta ka gudu.

Flask d'in dambun Walid ya daukar mata suka shiga gidan Hajiya Mama.

Suna shigewa su arkel na karasowa, gefe Kamal yayi parking yce

"Zan d'an samu waje na makale idan ka gama sa ka kiran ko ango?"

Bude motar yayi ya fito sannan yace

"Ka je kawai in na gama zan dau mota ta a wajen salim."

"Owk shikenan, a gaida amarya."

Dariya kawai yayi bece komai ba ya saka kanshi a cikin gate din, bangaren Hajiya Mama ya kalla yaga an saki labule da sauri, wucewa yayi ya tsaya a bakin kofar part din Alhaji Faruku yana tunanin yadda zai sanar masa da zuwan sa.

Walid ne ya bude kofar ya fito yayi saurin riko shi,

"Ina wuni?"

Be amsa ba yace

"Abba na ciki?"

"Eh shi da yaya Maryam ne."

"Owk shiga kace nazo."

Juyawa yayi ya sanar wa Alhaji Faruku, izinin shiga aka bashi ya shigo kansa a kasa, kamshin turaren sa ne ya daki hancin ta tana durkushe a kasa, da fara'a Alhaji Faruku ya karbe shi suka gaisa sannan ya mike

"Ina zuwa." Yace yana fita hadda jawo musu kofa.


Dan Dan.... Ga Arkel ga Maryam. Babu ruwana Yasin🚴🚴🚴🚴🚴🤣😌🤣🚴🤣🚴🤣🚴





_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A HALIN YANZU😁._

*ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma
*SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano)
*KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo)
*BURI ƊAYA!* (Mamu gee)
*WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull)

👇🏻karku bari ayi babuku

*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi  daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*

*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*

Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank

Saika tura shaidar biya ga wannan number ta WhatsApp

08030811300

Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN  ta wannan number din

07067124863

Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.

*Karki bari ayi babu ke, Abari ya huce shike kawo rabon

Rano🚴🚴🚴
[3/18, 22:24] Hafsat Rano: *SAUYIN K'ADDARA*

*15*
©*Hafsat Rano*

*_ZAFAFA BIYAR na kudi ne idan kana son kowanne daga ciki ka nemi Wannan numbers din_*

*08030811300*ii
*07067124863*

*_Daurin boye_*
_safiyya huguma_
*_Buri daya_*
_mamuhgee_
*_Wutsiyar rakumi_*
_billyn Abdul_
*_Kai min halacci_*
_Miss xoxo_
*_Sauyin kaddara_*
_hafsat rano_



*Bangaren Hajiya Mama ya shiga bakin sa dauke da sallama, tana kan abin sallah tana lazimi, kasa ya samu daga gefen ta ya zauna sannan yace

"Barka da gida Hajiya."

Bata amsa ba sai data gama addu'o in ta sannan ta amsa, shiru yayi kamar ba zai magana ba dan be san ta ina zai fara ba, kallon sa tayi tasan akwai abinda zai faɗa mata, tunowa tayi da alawa da goron da Sultan ya shigo mata dasu dazu tayi tace

"Kayan daurin auren da naga an shigo dashi daga ina ne?

Ajiyar zuciya ya sauke jin ya samu hanyar da zai yi maganar yace

"Kayan auren Maryama ne Hajiya."

"Maryam kuma? Ban gane ba."

"Eh Hajiya, dazu aka daura auren  nata da..."

Katse shi tayi

"Auw ka ji magana ta kenan ka fasa hada auren, ya yi kyau hakan ai."

"Ba haka bane Hajiya, yaron da zai aure ta ne..."

"Ya nemi alfarmar a daura da wuri ko? Baya so a haɗa dana masu arziki yaji kunya kenan, toh ai ya kyauta wa kansa."

Kallon ta kawai yake ya rasa ta ina zai fara sanar mata ma, dafe kansa yayi da dukkan hannun sa yana kallon saman dakin. Nannad'e sallayar tayi ta mike da k'yar tana barin dakin, jiki a sanyaye ya biyo bayanta, zama tayi tana kallon kayan kafin tace

"Ka turo Sultan idan ya dawo yazo ya tattare kayan nan ya mayar musu, gayyar tsiya."

"Haba Hajiya, wai yaushe zaki daina irin haka ne? Yaya fa kamar d'an ki ne duk wata biyayya ta d'a ta mahaifi yanayi miki kuma naga..."

"Kul ka fadan magana wallahi, kuma ni ba d'ana bane bana gayyar cin amana, wai duk ka manta abinda uwar sa tayi min, ta auren miji ta riga ni haihuwa dashi sannan a karshe ta shi ya sake ni, ni ko uban me zan yi da ahalinta?"

"Amma Hajiya..."

"Dan Allah barni na sarara,  zancen ya ishe ni haka,alawa

27, January 2025
Rukayya

Good

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login