Showing 6001 words to 9000 words out of 98004 words
ba tayi ficewar ta tana ji Rauda na fadar wani abu akan ta sai dai bata ji ko menene ba.
©Rano
[3/18, 22:22] Hafsat Rano: *HAFSAT RANO*
3
***Gaba d'aya ya gama barbaza takardu a tsakiyar gadon, mouse ne rike a hannun sa yana duba wani Pdf na Forex a cikin computer, tun da ya dawo yau ya shiga ya duba Ummi be sake sakkowa kasan ba, so yake ya gama had'a komai kafin ya sauka gaba d'aya don yana son zuwa suyi magana da Alhajin su akan Ummin, bashi da wata bukata a yanzu a duniya sama da ya ga Ummin sa ta dawo daidai, shiyasa bashi da wani lokacin kansa sai na aiki saboda ba kananun kudi rashin lafiyar tata ke ja ba, tun daga kan tests da magunguna hada da nurse d'in da aka dauko me kula da ita duk kuwa da ya kori nurses a k'alla goma kafin ta yanzu wadda ita ma yana gab da korar ta.
Tun bayan abin da ya faru, sai ya zama baya iya yadda da kowa sai shi kansa, shiyasa da yaga suna yin wani abu da be gamsu dashi ba yake saurin korar su, dama Hajiya Mero ce ta d'age akan sai ta kawo din kuma ita ce ma take kawo sun shi nasa biya ne kawai.
Hannu yasa ya wargaza sumar kanshi ya saka biro yaana sosa wa a hankali, tunanin Poultry farm d'in sa ne ya fad'o masa a take ya jawo wayar sa ya shiga kiran number Salim, bugu daya ya daga ya sake gyara zaman Bluetooth din dake kunnen sa yace
"Kun tashi ne?"
"A ah muna shirin tashi dai."
"Owk good, Please ka duba wajen nan da nake so a zuba kajin nan , na riga nayi komai zasu iya zuwa gobe ko jibi ma, a tabbatar komai daidai "
"Owk sir, an gama in sha ALLAH."
"Thank you."
Rufe komai yayi ya tattara takardun da yayi jotting important abubuwa ya isa gaban mirror ya gyara kansa ya sake fesa turare sannan ya fito, shiru saman babu kowa dama shi kadai ne duk sauran a kasa suke.
Da fuskar Ya Nabila ya fara tozali yana sauko wa yarinyar ta Amna ta taho da gudu yayi saurin karasa sauka ya daga ta sama.
"Ashe kana ciki."
Yaya Nabila ta fad'a tana murmushi, murmushi yayi shima ya karasa gefen ta ya zauna fuskar sa dauke da farin cikin ganin ta yace
"Ina nan wallahi, aiki ne ya rik'e ne, yanzu kuka zo?"
"Sannu agogo, wajen minti talatin fa da zuwan namu."
"Wai... Sannun ku, ina wuni yasu Afnan?"
"Lafiya lou Arkel, ya aiki ya jikin Ummi."
"Alhamdulillah." Ya fada yana kallon dakin jiki a sanyaye,
"Allah ya kara sauki, na shiga naga tana bacci ai."
"Amin... Baccin ai ko da yaushe ne."
Zuciyar sa ce tayi rauni ya mike sa'be da Amna ya nufi dakin, daga jikin kofar ya tsaya yana kallon ciki, girgiza kai yayi ya fito bayan ya ja mata kofar.
"Abinci fa?"
Zee ta tambaya tana kallon sa dauke da murmushi, tun dazu take zaman jiran sa dama, yatsine fuska yayi ya girgiza mata kai alamar a'ah
"Abincin ma?"
Ya Nabila tayi magana tana rike ha'ba
"Allah bana son cin komai, bari zan sha wani abun kawai anjima."
"Da ka daure amma..."
"Owk tam, anjima."
"Kawo masa kawai kinji Zee."
Ta fad'a tana hararar sa, zama yayi ta kawo mishi a plate sai ruwa da cup ta ajiye ta dauki Amna ta wuce ciki, fara ci yayi a kasalance kamar dole haka yake turawa, kallon sa take cike da tausaya,
"Kanina... Ta
"Na'am."
"Wani tunani nayi, me zai hana ka auri..."
"Zainab?" Ya karasa yana kallon ta, daga masa kai tayi alamar eh, girgiza kai yayi ya ajiye spoon d'in ya fuskance ta sosai
"Please sis, I can't wallahi, kinsan dai komai."
"Amma baka ganin hakan shine daidai? Atleast tafi nurses din da ake kawo wa, in ka aureta zata cigaba da kula da Ummi kai ma kaga hankalin ka zai kwanta nawa ya kwanta nima."
"Amma why Zainab?".
"Saboda ita muka sani, a rashin yardar kan nan ita kadai zata iya da kai da wannan murdadden hali naka."
"Shikenan dai, zanyi tunani akai."
"Owk think hard, zaka gane me nake so ka gane."
"I hope so."
Amsa wa kawai yayi saboda baya so a ja maganar, babu yadda za'a yi ma ya aure ta.
***
Tsalle tayi ta dire a saman gado ta fara daga Amna tana dariya, idan har ya yarda da shawarar Ya Nabila shikenan ta samu cikar burin ta, chocolate ta dauko a jakar ta ta shiga bare musu ita da Amna suna ci tana yam wake waken ta cikin tsantsar farin ciki.
Duk maganganun da sukayi taji komai
***
A tare suka fito tana rike ta hular sa a hannu, a tsakiyar falon ya ja ya tsaya yana kallon dakin da take ci, kallon sa tayi taga in da yake kallo ta taɓe baki ta dawo gaban sa, rike kai tayi alamun tunani kafin tace
"Kash... Allah dai ya yaye min mantuwar nan tawa wallahi."
"Me ya faru?" Ya tambaya yana kallon ta
"Maganar Muhammadu fa zanyi maka tun jiya, kaga na manta wai me yasa in dai ina tare da kai nake manta komai ne?"
Yarfe hannu tayi, hakan ya sashi yin dariya cikin jin dadi yayi kasa da murya yace
"Hajiya tah kenan, me ya faru da Arkel din"
Dan marairaice murya tayi kafin tace
"Bana son naga yaron nan cikin rashin walwala kullum, hankali na baya taba nutsuwa idan na ganshi yana kunci, na zauna nayi tunani babu abinda zai saukaka zuciyar sa fiye da aure Alhaji."
Tagumi tayi da dukkan hannun ta cikin wani irin yanayi ta karashe maganar tana kallon yadda maganar tayi tasiri a zuciyar sa. Gauron numfashi ya sauke cikin gamsuwa da bayanin ta yace
"Kinyi tunani me kyau wallahi Hajiya, kinsan ban kawo hakan ba."
"Nima jiya ne na kasa bacci duk juyi sai ya fado min, sai kawai nayi tunani me zai sa ba zamu hada shi da Rauda ba, kaga tuwo na maina kenan kuma soyayyar mu zata sake karfi tun da zamu hada ya'yan mu aure."
"Gaskiya samun mace ta gari ma wani abu ne, kinsan tunani wa zai aura nake a zuciya ta sai kawai kika kawo Rauda, Nagode Nagode Nagode sosai da karamcin ki a gareni."
"Ba komai ai yiwa kaine."
"Masha Aallah, idan ya dawo kice ya sameni a head office dan ba zan iya jiran sai na dawo da yamma ba."
"A dawo lafiya, zan sanar dashi sakon ka."
Cikin kissa ta dora
"Baka shiga ka duba ta ba fa zaka fita kuma."
"Ba yanzu ba, sauri nake bari in na dawo."
"Amma... Shikenan toh, Allah ya kiyaye."
"Amin."
Komawa tayi ta zauna tana murmushi, number Hajiya Mama ta kira don tayi mata albishiri, sai dai bata daga ba. Lokacin Yaya Alhaji yana zaune a falon tana yi mishi maganar Rauda, ransa babu dadi yake sauraron ta yana ayyana abubuwa da yawa a ransa, ya riga ya san halin Hajiyar tasu shiyasa kawai yake biya mata a haka, yanzu ma data zo da maganar Rauda yasan komai amma babu yadda ya iya amsa mata da toh kawai yake don shima yafi so Rauda tayi aure ta bar gaban Hajiyar ko hankalin sa ya kwanta, abu daya ya sani shine abun da ya tsara ba zai taba yadda a samu matsala ba.
***
Zaune yake yana kallon komai na cikin dakin, maganar da Ya Nabila tayi masa ce take masa yawo akan sa, kallon Ummin ya sake yi, tabbas tana buk'atar makusanci, auren shi ne kadai mafita a halin yanzu, runtse ido yayi yana tuna wa zai aura da zai iya damka amanar kula masa da ita, babu kowa zuciyar sa ta amsa masa, idan kuma yace ya nema wa ya sani da har zai iya neman ta? Gaba daya kansa ya kulle ya rasa mafita, mafita daya yake hangowa ita ce Zainab, ba son ta yake ba sai dai kawai zai aure ta ne don mahaifiyar sa, babu bata lokaci ya amince da abinda zuciyar sa ta hasaso masan.
Tashi yayi tsam ya chanja shigar shi zuwa manyan kaya don da beyi niyyar fita ba saboda ranar Ummi ce, ya kan ware mata rana daya a cikin sati ya kula da ita yayi mata komai, sai dai dole yaje ya ga Alhajin su ya sanar dashi abinda ya tsara game da maganar Zee.
Durkusawa yayi a gabanta cikin sanyin murya yace
"Kiyi min addu'a Ummi, Allah yasa abinda nake shirin yi ya zame mana maslaha, kar naje na jawo mana matsala."
Murmushi ya gani a saman fuskar ta, hawaye ne ya biyo fuskar sa yasa hankici ya goge, runtse ido yayi yana hango abin da ya faru a baya, take jijiyoyin kansa suka fito sosai, wani irin bacin rai yake ji idan ya tuna dalilin sa ne komai ya faru. Tashi yayi ya soma bin bango dafe da kansa kamar wanda yasha ya bugu, tsabar bacin rai da k'yar ya daidai ta kansa ya fita yana ja mata kofar.
Direct head office din ya nufa in da yasan zai same shi, zaune suke da wani abokin sa suna maganar kasuwanci sakatariyar sa ta sanar dashi zuwan Arkel din, izinin shigowa.
Gefe ya samu bayan ya gaida mutumin ya tsaya yana jiran su gama, hada komai yayi ya fita ya barsu su biyu, kofa yaja musu hakan yasa Alhaji kallon Ahmad sannan ya nuna masa kujera yace
"Zauna magana zamuyi."
Zama yayi ya sauke kansa k'asa yana sauraron sa
Da sauri ya d'ago kansa jin abinda yace
"Rauda kuma?"
Ya tambaya ido waje,
"Ita fa, mun riga mun gama yanke magana da Hajiya, bana son kuma kace a'ah don hakan kamar cin fuska zai zama wajen ta."
"Nagode."
"Yawwa, Allah yayi ma albarka."
"Amin." Ya amsa a hankali
"Ya wajen naka? Ina fatan babu wata matsala."
"Babu komai."
"Madallah, shikenan zaka iya wucewa, akwai tarin aiki a gaba na."
Jiki a sanyaye ya tashi ya fita yana son tuno wacece ma Rauda? Har ga Allah ya kasa tuno me sunan, yana tuki wayar Alhaji ta shigo, d'agawa yayi kafin yayi magana yace
"Zaka iya zuwa ka fara ganin ta, ba bata lokaci za'ayi ba."
Jin zai katse yasa shi bud'e baki da k'yar yace
"Ina ne gidan?"
"Gidan su Hajiya mana, ko baka gane wa nake nufi bane?"
"Na gane." Ya amsa da sauri ya katse kiran, sai a lokacin ya tuno yarinyar ai, tana zuwa sosai gidan su ya gane ya sarai, duk rawar kan Zee da yake gani ta dame ta ta shanye.
Saurin taka burki yayi ransa ya gama baci, da ya san ita ce tun farko bazai taba yadda ya amsa ba duk da dama rashin son aja maganar ne yasa shi saurin amsawa kawai.
Da k'yar ya saita kansa kamar zaiyi kuka ya kira Yaya Nabila ya fad'a mata yadda akai.
***
Gaba d'aya satin cikin farin ciki tayi sa a wajen, tun ranar farkon data fara zuwa wajen bata sake ganin shi ba, shi din ma yayi busy sosai da harkar Forex shiyasa bashi da lokacin duba wajen sai Salim ne yake kula da komai, a hankali a hankali suka fara sabawa da Hafiz har sukayi exchanging number sukan yi waya da chatting ma, tuni zuciyar ta ta fara nutsuwa da Hafiz ya sanar da ita komai da sanar da yake saboda ya rufawa mahaifiyar sa da kanwar sa asiri.
Ranar juma'a yanayin garin ya sake rikicewa da sanyi sosai, da wuri ta shirya don sunyi waya da Hafiz yace zai rakata, atamfar ta me kyau ta sallah ta saka coffee and milk colour ta dora katuwar rigar sanyi ta yafa mayafi kalar milk a maimakon hijabin da ya zame mata dole, har ta fito ta koma ta dauko glasses d'in ta ta saka, Umma tayi wa sallama ko ta kan abinci bata bi ba tana sauri ta tafi.
Jin ta take sakayau saboda rashin hijabin, a daidai in da suka saba haduwa ta hango shi ya saka wata doguwar rigar sanyi da hula, dariya tayi ta k'arasa wajen, gaishe shi tayi ya amsa yana kallon ta daga sama har k'asa, shigar tayi mata kyau sosai, jerawa sukayi suna tafe suka hira har suka isa, ciki suka shiga ta dauko musu kujerar roba suka zauna suna cigaba da hirar.
Suna zaune wajen ya fara cika a hankali don ma kowa ya makara saboda sanyin da aka tashi dashi.
Duk wanda ya wuce sai yayi mamakin ganinsu a wajen, salim ma da ya zo ya gansu sai ya dauke kansa yaki bari ma ya kalli wajen balle har yayi mata magana, ganin haka yasa ta d'an sha jinin jikinta, kallon shi tayi ta karyar da kai
"Zaki gudu ko? Nima bari na wuce kinsan juma'a karamar rana ce yanzu zai kiji kira."
A tare suka mik'e, shigowar sa kenan wajen ya hango su tsaye, ransa ne ya ɓaci ganin yadda take ta dariya, babu abinda ya tsanan irin rashin jan aji mace ta wage baki a waje tana dariya.
Parking yayi ya fito bayan ya had'e girar sama data k'asa.
"Oga yazo."
Ta fada muryar ta a hargitse, tashin hankalin da ba'a sa mashi rana, kallon wanda ta kira da Oga Hafiz yayi sannan ya kalli Maryam yaga yadda ta rud'e, haushi ne ya kamashi yace
"Sai kije kar ya kashe ki."
"Kisa kuma?" Ta fad'a tana kallon shi
"Baki ga yadda kika rikice bane."
Ya amsa a dakile, zatayi magana ta hango salim ya nufo su, yana karasowa yace
"Oga na kira."
Be jira amsar ta ba ya juya cike da jin haushi.
"Muyi magana a waya kawai."
Da sauri ta bar wajen ta nufi office d'in.
Kamar munafuka haka ta tura kofar ta shiga tana sand'a
Ajiye Inhaler hannun sa yayi ya kalle ta tayi saurin sauke kanta kasa.
#Sauyin Kaddara
_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A HALIN YANZU😁._
*ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma
*SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano)
*KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo)
*BURI ƊAYA!* (Mamu gee)
*WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull)
👇🏻karku bari ayi babuku
*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*
*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*
Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank
Saika tura shaidar biya ga wannan number ta WhatsApp
08030811300
Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN ta wannan number din
07067124863
Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.
*Karki bari ayi babu ke, Abari ya huce shike kawo rabon wani*🤝🏽🤝🏽🤝🏽
[3/18, 22:22] Hafsat Rano: ©*HAFSAT RANO*
# *SK*
4
Ido ya zuba mata yana kallon ta, haushi ne ya sake turnik'e shi ganin ko gaishe shi bata yi ba, tsaki yaja da karfi ya bigi table d'in,
"Baki iya gaisuwa bane?" Ya tambaya rai a bace
Da sauri tace
"Ina kwana?"
"Ban ganshi ba, aikin da kika zo yi kenan?"
"Na'am..."
Rainin wayo, ya fad'a a ransa, a ƙufule yace
"Fita."
Raba ido ta fara yi kafin ta juya ta nufi hanya
"Baki iya bada hakuri ba?" Ya katse ta ganin da gaske fitar zatayi
Juyo wa tayi da sauri tace
"Kayi..."
"Jeki kawai."
Tsayawa tayi taki fita, komawa yayi ya zauna zuciyar sa ba dad'i, tari ne ya taso masa da karfi, tun daya tashi yake jin alamun Asthma, mantawa yayi be fito da inhaler ba sai da yazo ya tuna, duddubawa yayi babu duk sai emty container.
Matsawa tayi gaban table d'in tana kallon sa, sannu ta shiga jera masa ganin yadda yake tari sosai, a hankali tarin ya tsaya yaja baya da kujerar ya daga kansa sama, idon sa a rufe ya daga mata hannu jin sannun taki karewa, cikin tausayawa ta juya ta fita tana waiwaye.
Ranar gaba d'aya kasa yin komai tayi, tunani biyu ne ya haɗe mata , ta kira Hafiz wajen sau uku yana k'in d'agawa, ta san fushi yayi ita kuma sam bata ga abin fushi ba.
Sha d'aya nayi tayi musu sallama don bata so ta hadu da masallaci, in da suka saba haduwa da Hafiz tafi sai dai baya wajen, bata yi tunanin fushin nasa har ya kai hakan ba, duk sai taji ba dadi har ta k'arasa gida tana tunanin yadda zatayi.
A kofar gida ta tarar da Baba da Alhaji Faruku zasu tafi masallaci, k'asa ta tsuguna ta gaishe su ta shige ciki.
Tana shiga ta gane Umma bata nan, kamar zatayi kuka ta shiga ciki tana hararar Habubu dake wasan ruwa, da gudu Walid ya fito ya fito yana fad'a mata Anty Maryam ta haihu ta haifi twins, murna ta hau yi ta shiga kiran wayar Umman, a gurguje ta shirya su Habubun ta basu abinci suka tafi gidan Anty Maryam d'in, saboda zumud'i ko ta kan abinci bata bi ba, zuwan su gidan yasa ta manta da fushin da Hafiz yake da ita ta shiga cikin yan'uwa ana ta hira da farin ciki, wajajen magriba Umma ta sa suka tafi gida don ita achan zata kwana, a hanya ne kiran sa ya shigo mata, bata fuska tayi kadan kafin ta d'aga, shiru yayi be ce komai ba, sallama tayi ya amsa a cunkushe
"Fushin ne?"
Ta tambaya jin yadda ya amsa matan, katse kiran yayi kawai cikin tsananin mamaki tabi wayar da kallo, mene abun haushi kuma? Ta tambayi kanta, shiru tayi tana tunani, bin bayan kiran tayi har ta katse be d'aga ba, ajiyar zuciya ta sauke ta maida wayar jaka daidai lokacin da me napep ya ƙaraso kofar gidan su.
***
Tsaki yaja yayi cilli da wayar yana mik'ewa akan yar katifar sa, globe din dakin ya kurawa ido yana tuna yadda Maryam ta rud'e daga ganin wani kato, tun dazu zuciyar shi bata kwanta ba yana ta tunanin abubuwa da yawa game da ita, mik'ewa yayi kawai ya fita waje. Dakin Inna ya shiga ya tarar da ita zaune da suwaiba suna hira, rake suke sha suna hira gwanin sha'awa. Gefe ya samu ya zauna ya dauki nasa raken ya hau sha don kawai ya manta da haushin da yake ji.
***
Weekend d'in gaba daya a gida yayi shi saboda yadda tarin ya matsa masa, so yake ya fita yaji yadda abubuwan suke tafiya shi yasa ya shirya da yamma lik'is ya fito, Alhaji ne a falon tare da wani bako da be san waye ba, gaishe su yayi zai wuce ya dakatar dashi
"Ya tarin?"
"Ya tsaya ma, zan d'an fita ne."
"Allah ya kara sauki." Bakon ya fad'a
"Amin." Ya amsa a ciki ya juya zai fita,
"Am... Muhammadu, nace kaje kaga yarinyar nan fa, dama nayi shiru ne saboda tarin naka, tun da zaka fita yanzu sai ka biya ko?"
Da toh
27, January 2025
Rukayya
Good