Showing 57001 words to 60000 words out of 98004 words
na rasa me xance ga dare ya soma yi ina zamu fara?"
Mota suka shiga suka bi hanya ba wai dan suna tunanin zasu gaan su ba, gaba daya Arkel ya rikice masa har wasu maganganu yake da be san yana yi ba saboda tsabar yadda abin ya taba shi. Duk iya tafiyar da sukayi babu ko alamun su, maimakon su koma sai kawai Arkel yace su tafi gidan su maryam ɗin,
"Baka ganin tada musu hankali zamuyi a daren nan? Me zamu ce musu? Yar su an sace ta? No be kamata ba ai, mu jira gobe dai mu gani idan Allah ya kaimu."
"Yanzu ita kadai zata kwana a wajen su? Ita kadai? innalillah."
"Addu'a zamuyi kawai, in Sha Allah babu abinda zai faru."
Hannu kawai ya dora aka yana juya shi cikin tsananin tashin hankali.
Juyawa sukayi suka koma gidan Kamal ɗin, yaya Nabila bata san me ake ciki ba sai da kamal ya taso ta bayan sun shiga gidan, aikuwa sai da yayi danasanin tashin ta dan kuka ta saka musu wiwi abun ka da mace.
Arkel kuwa juya kansa kawai yake shi kadai ya san me yake ji, duk sanda ya tuno tana waje tare da wasu maza sai yaji hankalin sa ya kara tashi fiye da yadda yake a da. Ganin bashi da mafita yasa ya shiga toilet ya dauro alwala ya tada sallah.
***
Bayan an gama taskar labarai Baba ya kashe radio, bacci ne yake daukar sa daga zaune yana neman kwantar dashi, Umma kuwa da yake yau ta fita kasuwa da wuri tayi bacci saboda gajiya saboda haka gidan yayi tsit babu motsin kowa in ka cire radion Baba data zama kamar wajibi a gareshi duk daren duniya sai yaji shirin siyasa da labarai har zuwa lokacin da za'a gama taskar labarai sannan fa yake kashe wa ya kwanta. Kwanciyar sa kenan Umma ta farka a dan firgice, kallon ta yake har ta nutsu tana ta faman sharce gumi, muhucin dake gefe ya jawo ya mika mata kafin yace
"Da alama dai yau bakiyi addu'a ba ko?"
"Nayi wallahi, wani mafarki nayi mara dadi wallahi akan Maryam."
"Mtsw." Ya ja dan gajeren tsaki yace
"Shedan ne, Maryam da tana gidan ta, me zai same ta? Ki sake addu'a ki juya ki chanja bangaren da kike kwance, babu abinda zai faru mafarki ai ba gaske bane."
"Haka ne, abin ne da ban al'ajabi."
"Allah ya rufa asiri." Kawai yace ya juya ya kwanta yana addu'a. Shiru umma tayi tana tunanin mafarkin, sosai abin ya tsaya mata a rai, ganin ko ta kwanta ba baccin zatayi ba yasa ta tashi ta fito tayi alwala kawai gwara tayi nafila ko ta samu saukin abin da ya tsaya mata a rai.
***
A zaune ya tarar dasu kowanne ya dora ƙafarsa akan kujera, Inna da suwaiba na durkushe a kasa sun hana su kwakkkwaran motsi, suna ganin shi suka kwashe da mahaukaciyar dariya
"Aka ce baka ji?" Sambo ya fada yana dariyar shakiyanci.
"Ina take?" Asi ya fada bayan ya mike yana tarar shi
Runtse idon sa yayi kawai yace
"Tana mota."
"Ka tabbata?"
"Kuje ku duba mana."
"Owk muje."
Da sauri inna tace
"Ina zaki kaishi?"
"Old woman, danki fa yanzu ya zama nama, ya shiga fadan da ba nashi ba, kiyi ta addu'a kawai ya fi karfin mu."
Kuka inna ta saka, da sauri ta rufe bakin ta ganin ya nuno mata bindiga.
"Karki tara mana jama'a mana tsohuwa."
Kan Suwaiba Sambo yayi ya riko hannun ta yana murmushi
"Allah oga babe din nan ta min fa , a lamunce min."
Kaga Hafiz yasa ya bige hannun sa
"Karka kuskura ka sake taba ta wallahi, muje kuyi abinda zakuyi ku wuce kawai."
Kallon Asi Sambo yayi, daga masa kai yayi alamun ya share kawai,
"Shikenan." Kawai yace yana gid'a kai kamar kadangare.
Fita sukayi Hafiz ya jawo kofar gidan ya rufe ta waje, dariya suka kwashe da ita Sambo ya nuna masa key din hannun sa
"Muna da spare ai."
Motar suka nufa kirjin Hafiz na bugawa sosai, wayam babu kowa a motar, da sauri Asi ya kalle shi, boyayyiyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya sake leka motar don san tabbatar wa, babu ita babu alamar ta, kenan ta gudu? Amma ina ta tafi a wannan daren? Beyi niyyar barin ta dasu ba, tare yayi niyyar su tafi duk in da zasu da ita, amma kuma dama ba kowa ne zai zauna ba, ka zauna zaman me kenan? Dole ka nemi hanyar da zaka kubutar da kanka.
"Ina take.? Kai karamin kwaro har ni zaka raina wa wayo."
"Me yasa zan yi maka karya bayan ba tsoron ka nake ji ba? Na kawo ta har nan, bansan kuma me ya faru ba bayan shiga ta."
Hade rai yayi dan kar su ga alamun wasa ma, shiru sukayi suna tunanin gaskiyar maganar tasa,
"Mu bi hanya kawai."
gani yayi kawai sun shiga mota sun bar layin.
Kalle-kalle ya farayi yana tunanin in da zatayi a wannan daren.
😭😭Maryam.
***
Tsawan daren babu wanda ya runtsa, Hajiya Mero tayi ta kira Asi amma ya kashe wayar sa gashi babu Arkel babu Maryam ɗin da alama dai sun cika aikin su, Allah Allah take gari ya waye taji ba'asi, in Sha Allah ta gama da Maryam kenan,sai daji da abinda yanzu yake gabanta na hada auren Arkel ɗin da Zainab dan cimma babbar manufarta.
Arkel kuwa tun asubah bata karasa ba yayi alwala yana zaman jiran a kira, anan kira kuwa ya gabatar da sallar sa ya fito, be jira fitowar Kamal ba ya kama hanyar gida, yana zuwa ya shige daki ya hautsuno komai, takardar da mutumin nan ya kawo mishi ya fito da ita ya sake dubawa sosai, ko zai gano wani abu, be gani ba haka ya fito ya koma wajen su Buzu, basu ko tashi ba ya buga musu, buzu ne ya fito da sauri dan be san sanda bacci ya dauke shi haka ba,yana ganin Arkel a tsaye gaban sa ya fadi yasan babu lafiya, cikin in da in da yace
"Ranka... ya.. dade."
"Ina habu driver?"
"Yana ciki yallabai."
"Mutumin ranar nan, ya akayi ma ya gudu ne?"
"Am amm ni dai lokacin na shiga wajen Hajiya ne zan duba abu toh kafin na dawo sai na tarar ya gudu."
"Aikin ka a bakin kofa ne ko a cikin gida."
Zaro idon sa yayi
"Ai Hajiya ce tace na zo na duba mata."
"Habu fa?"
"Am am shi kuma kamar shima ɗin Hajiya ce ta aike shi ranar, na dai manta."
"Ka manta kace!??"
"Eh...eh, a ah na tuna ma, tabbas ita ta aike shi ya siyo mata masa,saboda bayan ya dawo ma mu ta barwa masar tace muci."
Be yi magana ba kawai ya juya ya koma ciki, computer din sa ya dauko ya jona da wata yar karamar na'ura, kasan kayan takardun sa ya daga ya dauko takardar da yake ta ajiyar ta tsawon wannan lokacin, zama yayi a gaban ta yana bada dukkan hankalin sa akanta.
Komai ya fara ne daga ranar, ranar da ta zama ainihin ranar da ke cike da babban kalubele, babban al'amarin da yayi sanadiyyar ruguza komai na wannan family, sanadiyyar shigowar ta rayuwar su, da dalilin ta na ganin bayan wani me numfashi a cikin ahalin nasu.
Are You guys ready for this? Hmmm rugumtsumi ya fara.
Me arkel yake shirin aikawata? Kar dai?????? Ba ruwana🚴🚴🚴
***
Mustapha na zaune ya zuba mishi ido ganin yadda duk birkice dakin, babbar jakar sa data fi kowacce girma yake kwashe kayan sa yana zubawa a ciki, har ya gama be ce komai ba ya tattara komai ya ajiye a gefe yana rike kugunsa, dubawa yake ko akwai abinda be dauka ba. Ganin ba shi da niyyar magana yasa mustapha cewa
"Man me kake shiryawa ne wai?"
Hannun sa ya saki ya juya falon, chan sai gashi ya dawo dauke da wani k'aton kwali, dire shi yayi kansa na sake daukar zafi, lek'awa Mustapha yayi yaga menene a ciki, duk wasu tarkacen kayan shaye-shayen sa ne a ciki. Da ido ya nuna masa su kafin yace
"Wannan fa? Duk na menene.?"
"Ko kana so ne? Wannan uwar tambaya haka?"
Dariya Mustapha yayi kafin yace
"Ah sun fi karfi na, kune manya ai."
"Dah kenan, Please anjima kadan zaka yi dropping dina a airport."
"What did you mean, Ina zaka haka unexpectedly?"
"Kano!." Ya amsa masa boldly yana shigewa toilet. Mustapha be san sanda yayi tsalle ya dire ba saboda murna.
Ghen ghen. Hajiya mero we are coming for u🚴🚴🚴🚴🚴💃💃💃💃💃💃 Three against 1 Masha Allah
Ku fito wasan zai fara. This is just a halfway
#Arkel
#Arab
#Hafiz
Masu tambaya Novels dina zaku iya shiga link din nan na wattpad zaku samu in sha Allah.
ttps://my.w.tt/ALaIc4HB43
Dont forget to follow please. Thanks
[3/18, 22:26] Hafsat Rano: *SAUYIN KADDARA*
*32-33*
©*Hafsat Rano*
*_ZAFAFA BIYAR na kudi ne idan kana son kowanne daga ciki ka nemi Wannan numbers din_*
*08030811300*
*07067124863*
*_Daurin boye_*
_safiyya huguma_
*_Buri daya_*
_mamuhgee_
*_Wutsiyar rakumi_*
_billyn Abdul_
*_Kai min halacci_*
_Miss xoxo_
*_Sauyin kaddara_*
_Hafsat rano_
***
Sai data tabbatar da shigar sa ciki sannan ta fito da sauri, gudu ta saka iya kar karfin ta, sai data yi gudu sosai sannan ta fita bakin titi, wani me adaidaita sahu daya dauko passenger daga airport ya juyo zai gida yana ta sauri, tana hango haske ta shiga daga masa
hannu, kamar ba zai tsaya ba sai kuma ya ga mace ce, gashi daf yake da shiga gida, tausayin ta yaji ya tsaya, sai dai unguwar da tace ne yayi masa nisa, ganin ya tsaya yana tantama yasa tace ya kaita gidan anty Maryam bayan ta tambayi sunan unguwar da suke dan ba ma gane ina take tayi ba. Da sauki yafi kusa akan gidan su data ce masa da farko shiyasa ya amince ya dauke ta.
Har suka isa tana ta addu'a ga mugun tsoro daya cika ta, tunanin ta daya halin da yake ciki, kadan kadan take share kukan da yake sauko mata har suka isa, knocking tayi bayan ta rok'i ya tsaya a bude mata saboda tsoro, daidai lokacin Mijin Anty Maryam na shirin kwanciya yaji ana bugu, kallon lokacin yayi cike da mamakin me bugawa, har ya share yaji bugun yayi yawa kawai yayi shahada ya tafi budewa
"Waye?" Ya fada yana dan tsaya wa kafin ya k'arasa kofar, jin Muryar Maryam yasa yayi saurin budewa yana kallon ta ta dan hasken daya leko,
"Subhanahi, Maryama? Kece? Shigo ciki."
Shiga tayi ya kalli me dan sahun
"Sannu malam, an gode sosai, bata sallame ka ba ko? Bari nazo."
Ciki ya koma ya dauko kudin ya bashi ya sake masa godia sannan ya rufe gidan ya koma ciki da sauri, tana rakube a gefe Anty Maryam ya shiga ya taso yau tun wuri ta kwanta saboda rigimar da twins sukayi ta mata, daga zuwa ta lallaba su ta bige da bacci, a gigice ta taso ta fito tana salati.
A gaba suka sakata da tambaya duk sun dauka ma ko matsala suka samu, labarin abinda ya faru ta basu cikin tashin hankali Anty Maryam take salati, bata san abin ya kai har haka ba, sun jima suna maida zancen kafin su kwanta a zuwan a bar wa gobe komai.
Kasa barci tayi tana tunanin halin da yake ciki, ita tsoron ta daya kar suyi masa wani abu, ga Hafiz ma da take tuno ko ya zasu kwashe da su, har asubah tayi tana abu daya, tashi tayi ta yi sallah sannan ta zauna tana jira su tashi.
***
A hankali yake kallon ko ina yana sake shaƙar iskar dake busawa kadan kadan, iska ce me cike da ni'ima irin yanayin zafi-zafi hade da iska, kwallar da ta taru a idon sa yasa hanky ya goge yana tuna lokacin da ya bar gari, lallai gaskiyar bahaushe da yace kowa ya bar gida, gida ya barshi. Wayar sa ya jawo yana kokorin duba Bolt, sai dai sam ntwrk din yaki bashi hadin kai, tsaki yaja ya kalli uban kayan dake gaban sa, hannu ya yarfe ya shiga waige-waige kamar me neman wani abu.
Daga nesa ta hango shi tayi saurin taka birki, kallon ta Hidaya tayi da sauri.
"Ya dai Lubna?"
"Babe kin ga wani handsome? Ohh my G... He's so handsome."
"Handsome kuma? Aina?"
"Bari kiga kawai."
Balle murfin motar tayi ta fito tana gyara nadin veil din ta, har ta karaso gaban sa be ma lura ba, duba wayar sa kawai yake yana jan tsaki saboda sam babu ko alamar network ɗin ma zai dawo.
"Hi handsome!"
Dan kallon ta yayi ya kauda kai
"May i help?" Tace tana kallon kayan dake gabansa
"Be my guest." Ya amsa mata yana sake duba wayar sa
Kayan ta hau ja ganin tana kici-kici yasa ya rik'e da sauri, idon su ne ya hadu da juna yayi saurin basarwa
"Karki damu zan samu taxi."
Marairaice fuska tayi tace
"Please allow me to help handsome."
Dakata tawa yayi yana sake kallon ta
"Please." Ta hade hannayen ta
Dauke kai yayi ya ja kayan ya nufi motar ta, a booth suka zuba kayan ta bude wa Hidaya kofar.
"Please koma baya kinji."
Kamar zatayi magana sai kuma ta fasa ta bude ta fito, shiga yayi ya zauna sannan ta ja motar suka fita daga airport din.
"Ina mukayi?" Ta tambaya tana saita mirror sosai
"Are You Serious? Dama wai baki Sanni ba amma kika dauko ni a motar ki?"
Dariya tayi kawai bata ce komai ba
"Owk ki aje ni anan sai na samu cab."
"No Dan Allah bari na ajiye ka, ka dawo daga tafiya ka kaya Please Please."
"Owk janbulo." Runtse ido yayi daya ambaci sunan unguwar.
Be sake magana ba ya hau tunanin yadda zata kasance
***
Tun da ya fara kalla har ya gama yana share gumi saboda tsabar yadda ya rikice, da kyar ya daure ya karasa kalla, tsawon wannan lokacin yana ajiyar shi be taba ko da tunanin duba wa ba sai yau, be taba tunani ko kawo hakan a ransa ba, ya san dai tun daga dawowar sa daga crossriver ya saka ido akan komai, duk wani abu da yake faruwa ya sani tun daga kan magungunan da komai ma, hatta ranar da suka tarar da Hajiya mero a dakin Ummi ya ga komai yadda ya wakana, tun daga lokacin ya sake bata wani babban matsayi a ransa, akwai babban dalilin sa na boye komai bayan komai ya bayyana, gashi yanzu ya gama hada komai, yayi mata kofar rago ya kamata da hujja, a yau ba gobe ba zai damka su a hannun da ya dace, ya daura damarar yakar duk wani me hannu a ciki.
Yana gama duba komai ya rufe yana mik'ewa, toilet ya shiga ya dauraye fuskar sa kawai ya yi fito,kayan jikin sa ya sauya ya rufo kofar, kallon dakin ta yayi, duk babu dadi, girgiza kai yayi ya wuce kasan, dakin Ummi ya buda Baba na zaune tana goga goro a mogogin karfe irin na iyaye da kakanni, Ummin kuma na kwance kamar ko yaushe sai dai yau tayi wani iri da ya kasa gane dalilin hakan, gaishe ta yayi ya duba ummin sannan ya juya ya fito duk da yana tunanin abinda yake shirin yi shine daidai sai dai yana jin tausayin Ummin matuka , tsawon wannan lokacin tana a wannan halin da yake dashi da marabar sa da mutuwa banbancin babu yawa.
Hajiya Mero na jin sa tayi saurin fitowa daga in da take labe, dan ta sake tabbatar da komai, shirin yi masa magana take kawai ya fice be ko kalle ta ba, murmushi tayi ta sake danna wa Asi kira, a kashe dai har yanzu gashi babu wani bayani gamshasshe da taji daga gare su, hakan yasa hankalin ta yaki kwanciya sam tana tunanin ko an dace ko akasin haka. Hakan ya saka ta a tunani.
Yana fita ya kira wayar, yana kashewa ya maida ita aljihu, a kafa ya taka har titi ya tari abin hawa. Daidai Arkel Poultry farm ya ajiye shi ya sallame shi ya taka ciki yana jin kansa na dan masa dum, Salim na tsaye daga waje yana jiran sa.
"Ka same shi?" Abinda yace masa kenan yana kallon ciki alamun ba shiga zai ba
"Eh yana jiran mu ma."
"Owk."
Gaba kawai yayi salim ya bi bayan shi, sai da suka dade a titi sannan suka samu abin hawa, suna tafe shiru kamar kurame babu me cewa wani kala har suka isa. Yana tsaye a kofar gida yana jiran su dama, da fara'a ya sauke su, suka gaisa sannan ya shigar dasu gidan, tabarma ce a shinfide a tsakar gidan da alama su ake jira ga rana nan ta fara fitowo sai dai bata tadda in da suke ba, sai daya fara cire takalmin ƙafarsa sau ciki sannan ya ajiye a gefe yana zama hade da tankwashe ƙafafuwan sa.
Daki ya shige chan ya fito da komai ya zube gabansa, salim ne ya mike yana dan rissinawa
"Oga bari na jira ka a waje."
Daga kansa yayi bece komai ba har ya fita sannan ya mai da kallon sa wajen mutumin yana sake gyara zama.
"Malam Nagode kwarai da duk taymakon ka, komai ya tafi yadda muka tsara, sai dai matsalar data faru jiya bata cikin shirin mu, shiyasa na kasa hakuri ina ganin lokaci yayi da komai zai bayyana."
"Gaskia ne, an dade ana ruwa ƙasa na shanye wa, kuma tabbas kayi hakuri ka bi komai a sannu har Allah ya nuna maka komai, tabbas kai jajirtacce ne me nagarta, a yau ni kaina ina goyon bayan komai da zaka aikata, sai dai ina baka shawarar kabi komai a sannu, har mu kai in da muke san xuwa, kaga idan ta warware daga nan zamu ji ainihin yadda komai yake.."
"Haka ne."
"Amma sai dai wani hanzari ba gudu ba...
Kira ne ya shigo wayar sa, kurawa number ido yayi yana tuna in da ya san number, ganin ya kasa ganewa yasa shi daga wa.
Da sauri ya mik'e annurin fuskar sa ya sauya zuwa tsantsar farin ciki, yana ajiye wayar ya kalli malam yana kunshe murmushin sa.
"Zan je na dawo anjima in Sha Allah, duk yadda mukayi da shi zan sanar maka."
"Hakan yayi, Allah ya taymaka ya bada sa'a."
"Amin."
Da sauri-sauri ya fita, salim na ganin sa ya taso.
"Mu wuce ko? Na kira yace yana jiran mu tun dazu ya zo."
"Kira shi kace yayi hakuri zan kira shi, an samu change of plan abinda zamuyi magana akai zan je naji, pleasd ka bashi hakuri it's urgent ne "
"Owk ba damuwa, bari na sameshi kawai achan din, in ka gama sai muyi waya."
"Owk... Ga kamal na kira na ma, sai mun yi magana." Kara wayar yayi a kunnen sa
"Wai kana ina ne? Mun tashi babu kai gashi ya kamata muyi reporting case din as soon as possible."
"Haba, sai nayi ta
27, January 2025
Rukayya
Good