Showing 75001 words to 78000 words out of 98004 words
nan da lokaci kadan zaki ji ya bude murya."
"Toh shikenan, Nagode sosai, sai na jiki." Ta karanto mata Number sannan tayi mata sallama ta tafi.
Umma ta dawo ta bude kayan data siyo tana dubawa maryam ta shigo, gefe Habubu ne akan sabon keken sa su Walid sai binshi suke yi, da kallo Umma tabi Maryam har ta zauna.
"Ke kuma daga ina?"
"Wallahi zaman ne ya ishen, sai na shiga gidan Maman Walid, Sannu da Dawowa."
"Yawwa."
Kallon su Habubu tayi tace
"Habubu an siyo keken kenan, yaro me zuciyar nema,wai da gaske umma kajin nasa ya siyar ya sai keke?"
"Gashi kuwa kin gani, amma fa ni nayi kiwon, shi dai ya tara yan kuɗaɗen sa da wanda mijin naki ya bashi ranar ya siya kajin, amma kam ai ni nasha wahalar kiwo."
"Ai gaskia wallahi ya burge ni, haka fa ake son mutum me zuciyar nema, ji fa tun yana karami kenan."
"Aikuwa dai."
"Allah ya sanya alkhairi, Walid zo ka siyo min awara dan Allah."
Da sauri Habubu yace,,
"Ni zan siyo miki, sai naje a keke."
Walid ne yace
"Eh sai muje tare."
Dariya Maryam tayi
"Ai fa yanzu Habubu zai zama Sarki a unguwa, yara da keke yanzu za'a yi ta masa biyayya."
Dariya kawai umma tayi ta tashi ta shige ciki ta barsu suna ta faman yi.
Bayan sun gama hira ta sake gwada numbr sa shiru, sai kawai ta kwanta jikin ta a mace tana tunanin dalilin da ya hanashi kiran ta. Kasa baccin tayi lokaci zuwa lokaci sai taji kamar wayar ta na ringing, da sauri take dubawa sai ta ga babu komai, tashi tayi, ta dauro alwala tayi sallah tana fatan komai lafiya, ba tare da sanin ta ba bacci barawo ya sace ta a wajen sallar sai kiran farko ne ya farkar da ita.
Da kyar tayi breakfast waina bandashe da kunu duk san da take musu amma sai taji ba dadi saboda tunanin halin da yake ciki, bata so ta sawa zuciyar ta wani tunani amma kuma ba zata iya sakin jikin ta ba ba tare da taji daga gare shi ba. Umma na lura da ita duk tayi sukuku da ita, wajen azahar zawon da take kwana biyu ya sake dawo mata, haka ta wuni sur tana abu daya, ga wani irin murdawa da cikin ta yake, dole umma ta kira Baba ta sanar masa, shiryawa tayi suka tafi asibiti duk jikin ta ya mutu bata da kuzari.
***
Yana ajiye shi a airport ɗin daya tabbatar ya fita sai ya da dau wayar sa ya kira Salim, jim kadan sai gashi ya zo, daukar sa yayi suka je suka dauki mutumin nan sannan suka dau hanya.
Tafiya ce me nisan gaske, sunyi ta ne cikin wahala da tashin hankali, babu wani titi me kyau sai rubud'i cike da tarin kasa babu ko bishiya a hanyar, hakan ne ya tabbatar masa daf yake ta in da yake shirin zuwa, sai ya sake zama yana kallon hanyar sosai.
Dare ne ya riskesu har lokacin basu kai in da suke so ba, saboda yanayi na wajen yasa suka tsaya domin kwana a wajen saboda tsaro. Zaune suke a cikin motar baka jin karar komai sai tsuntsaye garin yayi shiru, tunanin Maryam ne ya fado masa ya kalli wayar sa, samun kansa yayi da shiga gallery ya bud'e hoton ta da yayi mata ba tare da ta sani ba lokacin tana kula da Ummi, tsaya wa yayi chak yana kura mata ido, komai nata simple and unique yadda yake son mace ta zama, babu baragada ko hayaniya a duk abinda take yi tana yin sa ne cikin sanyi. Murmushi yayi yana dan shafa wayar, sai ya kashe ya rufe idon sa yana jin komai ya taho karshe idan har abinda yake fata ya tabbata, kaddarori ne da yawa suke bibiyar rayuwar su, ya riga yayi imani da kaddara me kyau ko mara kyau kuma yana fata da sa ran tasu ta zame musu wani tsani da zai kaishi ga rahamar Allah.
Lokaci zuwa lokaci yana duba wayar sa,babu wanda zai iya wani ishashen bacci a cikin su, duk da salim na ta gyangyadawa a zaune amma shi da malam babu ko alama ko digon baccin har zuwa lokacin da asubah ta riske su. Alwala sukayi suka yi salla a cikin motar, kayan Dan snacks din da Salim ya taho musu dashi duka dan ci suka sha ruwa sannan suka cigaba da daukar hanya suna fatan isa kafin lokacin sallar azahar.
Sai da suka sake ninka wata doguwar tafiyar sannan suka hangi Gari. Gari ne da yake kasar ta Mali, ajiyar zuciya Malam yayi ya kalli Arkel
"Mun kusa nan da awa biyu zamu shiga kauyen Mandar, duk da ni kaina rabona da garin shekaru ne masu yawa, sai dai ina fatan mu samu abinda muke je nema."
"Allah yasa." Arkel da Salim suka haɗa baki.
"Mu biyu ne muka fara fita daga kauyen namu, tun daga lokacin bamu sake waiwayar gida ba, shi me sunan naka da yake tare suka tafi da me dakin sa, Ni kuwa achan nayi aure."
"Kun dade gaskiya." Salim yace yana jinjina kai
"Dadewa ma bata wasa ba, karka manta bayan nan suka haifi Arabu wanda suna ne na dan uwan shi Arkel ɗin ya maida wa dansa ,shi kuma Arabun shine ya haifi ita kakar taku, ita kuma ta haifi mahaifiyar taku da wan ta namiji, idan ka fahimce ni, Arkel shine asalin ku, bayan ya zo Nijeriya sai ya haifi Arabu, daga nan shi kuma arabu sai ya haifi kakar ku wadda ita ce ya haifi mahaifiyar ku, kafin kuma azo kanku."
"Wai, ni wallahi kaina ya kulle gaba daya." Salim yce Yana sosa kansa dan be fuskanci komai a alakar ba."
Murmushi Arkel yayi
"Na gane ni kuwa, abu daya nake son tababtar wa shine rayuwar shi wan Ummin, shin yana raye? Idan yana raye zan fi kowa farin ciki, ina da yakinin zai san wani babban dalili da ya sa aka raba Ummi da iyayensu"
"In Sha Allahu da ransa."
Kallon sa Salim yayi, daga masa kai Arkel yayi yace
"Kana da tambaya ko? Feel free kayi tambayar ka, trust ne yasa na saka ka akan komai nawa, Allah ne ya hada mu amma ina jin ka kamar wani nawa makusanci."
"Ni ɗin ma hakan take oga, ni kawai wasu abubuwan ne idan kayi suke ban mamaki, ya akayi ka gano Malam ne wai?"
Murmushi Arkel yayi irin na gefen bakin nan ya kalli malam
"Allah ne ya duba zuciyata ya kawo min komai cikin sauki, watarana ina zaune abubuwa sun min yawa, na rasa yadda zanyi sai kawai na fita dan na wasa kafata saboda zaman waje daya, ina tafiya ne ba tare da sanin in da zani ba sai naji ana kiran sallah, tsayawa nayi nayi alwala a dan karamin masallacin dake kusa da wajen, bayan an idar ne na fito zan wuce sai nji ana kira na a waya, gefe na matsa na daga kiran, kaya ne da nayi order online ne suka zo saboda haka sai da suka fara tambayar suna na saboda su sake tabbatar wa ni ne me kayan, kai tsaye nace musu Muhammad Arkel , a lokacin Malam na gefe, jin sunan da na fada ne ya saka shi sai dani bayan na gama wayar. Kaji yadda muka hadu, sauran bayanin kuma sai nan gaba, ka daina mun kallon wani daban, ni ne dai Muhammad Mustapha daka sani."
"Angon Maryama kuma ba."
Salim ya fada yana dan matsawa, dadi ne ya kama Arkel ya sake sakin fuskar sa, a tunanin Salim zai ce ya bari amma sai ya ga akasin haka, sai ma wani lumshe ido yake yi yana murmushi kasa-kasa.
***
Iska ake sosai a garin, da sauri Arkel ya lalubi hanky a aljihun sa ya rufe hancin sa saboda asthmar sa, gidaje ne tsilla-tsilla suke wucewa har suka zo tsakiyar garin, da kallo suke bin babbar masarautar dake girke a tsakiyar garin, gine ne irin na zamani wanda aka kawata shi da ado irin na sarautar Fulani, mutane ne kyawawa suna ta hada-hada a wajen kowa da abinda yake yi, kallon motar suke har suka samu gefe sukayi parking, Babu Wanda ya motsa a cikin su, shi kanshi Malam ji yayi bashi da kuzarin fuskantar mutanen gari da yake ganin tsantsar chanji tattare dasu, lallai duk wanda ya bar gida gida ya barshi, gefe Arkel ya kai idon shi inda ya ga wajen cike da dabbobi tun daga kan shanu har zuwa kan zabbi da kaji sun fi duba wane dari, basu da adadi, lallai shi yasa kenan yake masifar kaunar kiwo a rayuwar sa, gado ba karya ba, sai yaji wani sanyi na ratsa dukkanin kofofin jikin sa, take yaji shi kamar ya zo gida cikin dangin sa. Wani magidanci ne ya nufo su ya tsaya daga dan nesa dasu sannan yace
"Barkan ku da zuwa, me kuke so? Shanu ko kaji, zabbi, agwagi, ko akuyoyi?" Cikin harshen sa na Fulani da baya fita da Hausar sosai, kenan ana shigowa sarar dabbobi wajen su kenan shiyasa sukayi tunanin ko su ne.
Malam ne ya fito yana kallon sa.
"Sarki muka zo nema."
Da sauri ya kalle su,
"Sarki ?"
"Eh sarki." Juya harshe Malam yayi zuwa Fulatanci, da sauri mutumin ya washe fuska,
"Bari ayi muku iso, sannun ku da zuwa."
Da sauri ya juya, fitowa sukayi suka tsaya, Arkel dai sai kalle kalle yake ya rasa inda zai sa kansa, da sauri ya koma motar ya dauko hoton nan da sauran abubuwan da yake ganin zasu taymaka wa, mutumin ne ya dawo ya basu umarni su shigo ciki, bin sa sukayi suka kutsa kai cikin gidan da yafi kama da gari guda saboda girman sa.
Manya manyan gine gine suke din ga wucewa, duk in da suka wuce sai an kalle su an gaishe su, yara ne kanana daga gefe gwanin sha'awa suna ta wasa, har suka dangana da babbar fadar basu ci karo da mace ko daya ba, salim da yake ta zare ido ko zai ga wata saboda yadda yaga tsananin kyau da mutane suke da su shiyasa ya kwallafa rai yana so ya ga ya matan su suke.
Yana zaune akan karagar sarki irin tasu, gefe da gefe manyan yan fada ne ana ta fadanci cikin harshen Fulatanci, kansu a kasa suka shiga, da kallon Sarkin ya bisu yana kurawa Malam ido, tsantsar kamar da ya gani ne yasa ka shi kasa dauke idon sa, sai ya cigaba da rarraba idanun sa tsakanin kan Arkel da Malam.
***
Ganin yana bin su ne ya saka suka kara gudu sosai, gudun shima ya kara don san tabbatar da zargin sa, idan har da gaske itan ya gani ya zama lallai Arkel ya sani, a yi gaggawar daukar mataki akanta, cigaba da binsu yayi ba tare da ya bari sun kubuce masa ba har suka sauka daga kan titin suka gangara wata hanya mara kyau, cigaba yayi da binsu, ganin yadda suke shiga layuka ya dan tsorata shi, amma kuma ba zai taba yarda su kubuce masa ba, gwara yayi risking life din sa ya tabbatar da ita akan ya koma saboda mutane ne da yawa zasu shiga a matsala a dalilin hakan.
Gani yayi sun taka birki sun tsaya, daga gefe chan ya tsaya shima yana hangen su, yana kallo ta fito, mika tayi irin ta gajiya tayi magana da direban motar sannan tayi gaba, a kafa take tafiya shi kuma direban ya juya ya shiga wani layi, ganin haka ya saka Hafiz bin ta da sauri, layin da ya ga ta shiga ya shiga shima, ashe layin baya fita, juyowa tayi tana murmushi. Da sauri yace
"HAJIYA MERO!!!"
Wani abu yaji an buga masa a kansa, daga nan be sake sanin komai ba ya fadi a wajen sumamme.
Hafsat Rano
Sauyin ƙaddara 43-44
#Not edited,
[3/18, 22:27] Hafsat Rano: *SK* 45
©Hafsat Rano
***
Jan sa sukayi suka shigar dashi gidan dake gefe hannun hagu, bin bayan su Hajiya Mero tayi ta shiga falon,dan karamin dakin dake gefen wajen suka chillashi suka datse kofar, daga waje suka tsaya suna gadin kofar.
Zama tayi tana jan dan karamin tsaki, ba karamin haushi Hafiz ya bata ba, dan karamin kwaro dashi amma yace zai kara da ita, shi ma uban daya tsaya matsan Arkel sane take dashi, ba banza ta maida kanta mahaukaciyar karfi da yaji ba ai, ba zata kyale kowa a cikin su ba, cin amanar da Ummi tayi mata ba zata tafi a banza ba, sai ta cire dankwalin kanta ta mike kafarta tana lalubar number sa.
***
Duk wajen kowa yayi shiru yana sauraron Malam, Arkel kansa a kasa be yadda ya sake dagowa ba saboda yadda ido yayi masa yawa, gaba daya manyan wajen wani irin kallo suke bin sa dashi kamar zasu cinye su, Sarkin kansa ya gaza dauke idon sa daga kansa har wani dan zamowa yayi daga kujerar sa yana sake fuskantar sa,tsufa da tarin haifa da suke tattare da Sarkin kadai zaka kalla kaji ya maka kwarjini, komai nasa yana nan be yi wani mummunan tsufa ba duk da akalla ba a kasaru ba ya bawa dari baya.
Cikin rada rada Salim ya ce masa
"Oga kaga yadda suke kallon ka kuwa? Ni fa abin ya fara bani tsoro, kar muje malam ya kawo mu ni a sayar damu fa."
"Kayi shiru dan Allah."
Yace cikin kuluwa, daidai lokacin Malam ya karasa bayanin sa, gani sukayi Sarkin da kansa ya sauko daga karagar sa ya nufo su, kafin suyi wani yunkuri sai gani sukayi ya saka dukkan hannun sa biyu ya rungumo Arkel, cikin Yaren da Salim da uban gayyar suka zama kamar wasu dolaye yayi wa sauran dake fadar magana, ai sai suka hau murna suna sambarka, shi dai Arkel sai yak'e yake yana kallon fuskar malam don neman garin bayani, daga masa kai kawai yayi alamn kar ya damu, sai kawai ya saki jikin sa ya biye musu suka cigaba da kawo gaisuwa kamar yadda suka fara bayan Sarkin ya koma wajen zaman sa.
Wasu maza ne su biyu suka rike hannun malam suka fita dashi daga fadar, dan zabura Arkel yayi zai tashi Sarkin yayi saurin dakatar dashi cikin kwararriyar Hausa yace
"Karka damu dashi, ya riga yazo gida, su yanzu wannan sune iyayen garin nan, kai kuwa dan mune, jikan mu ne, tattabakunnen mu ne."
Duk sai aka sa dariya, Arkel ma sai ya samu kansa da murmushi kad'an, ɗorawa Sarkin yayi
"Tun shigowar ka nan duk muka tabbatar da kai din ahalinmu ne, jini ba karya ba, ya riga ya nuna akanka."
Kallon juna sukayi a tare shi da Salim suka sakar wa juna murmushi.
"Allah ya kara maka lafiya, kenan an yarda da abinda muka zo dashi?"
"Tabbas mun yarda, saboda babu in da ka bar mu, komai naka namu ne, sannan zuwan ku da shi ardo ya sake tabbatar mana , ka sani babu ta yadda wani namu zai taba guje mana mu kasa shaida zuriyar sa, Arkel be taba barin ranmu daidai da rana daya ba, duk kuwa da nisan dayayi mana, muna tuna wa dashi a kullum kuma muna yi masa addu'ar amince, Allah yayi maka albarka yaro, lallai ka cika mutum nagartacce da har kayi kokarin sada zumuncin da ya dade da yankewa."
"Alhamdulillah." Arkel yace yana kai goshin sa kasa, ji yake kamar ya zuba ruwa a kasa ya sha, haka aka cigaba da tattaunawa da dawo da tarihi da kuma wasu tambayoyi da Sarkin yake tayi masa, sai ya ciro hotunan nan ya mika wa sarki, hawaye ne ya biyo fuskar Sarkin, mika wa sauran yan fadar hoton yayi suka kalla, daya bayan daya duk suka gama gani sannan Sarkin ya karba yana sake dubawa
"Allah sarki dan uwana, ashe ka tafi chan ka tara zuri'a, Allah yayi maka Rahma."
Hada baki sukayi wajen cewa Amin, haka aka cigaba da tattaunawa har aka dawo da malam cikin shiga irin tasu sai gashi ya fito sosai, gefen sarki aka sashi, sannan sarki ya cigaba da bayanin rayuwar su ta baya, a cikin bayanin ne Arkel ya fuskanci shine Arabun kenan dake jikin hoton, hakan ba karamin dadi yayi masa ba, sai ya shiga ayyano kalar farin cikin da Ummi zata shiga, a rayuwa bashi da wani buri kamar na farin cikin Ummin, tun ranar daya karanta labarin ta, ya shiga kunci, babban abinda ya katse mishi hanzari tun da ma rashin lafiyar ta ce, a yau ya san ko babu ransa Ummi zata samu farin ciki, zata san dadin yan uwa, zata san dadin dangin ta.
Cikin gidan Sarki Arabu ya sa aka rakasu, tun daga hanyr shiga suka fara cin karo da mutane masu yawan gaske, kalle kalle kawai suke cike da burgewa. Dakin wata tsohuwa aka kaisu, aka gabatar dasu, sai gashi har da yan koke koken ta na farin ciki, a nan suka zauna aka shiga jere musu kayan abinci kala-kala, wasu abubuwan ma basu taba sanin akwai su a duniyar nan tamu ba sai yau, da ido suke bin kowa kawai basa wani jin abinda suke cewa tun da masu jin Hausar cikin su kadan ne. Abinda zasu iya ci suka chacchakala sannan aka tafi kaisu masauki.
Suna tafiya suka ji ana maganar ga Gimbiya Bongel nan ta dawo, duk sai sukayi jere suna jiran ta, tsayawa bawan da zai raka su yayi alamun shima jira yake tazo ta wuce, baki hanci Salim ya bud'e yana kallon halitta, cikin tsananin ado fuskar nan ta ta sam babu walwala, sanda tazo gaban su ne taja ta tsaya tana kare musu kallo, kallon ta Arkel yayi cikin ido, hakan ya saka ta saurin janye idon ta daga kansu ba tare da tayi magana ba ta wuce kawai masu bin ta suka take mata baya.
Dan karamin tsaki Arkel yaja sannan sukayi gaba, haushi duk ya kamasa tsaida sun da tayi, dan dai be san wajen bane da babu abinda zai tsaidashi. Allah Allah yake ashe dama su isa masauki, da sauri ya hau rage kayan jikin sa saboda zafin da yake ji, dariya kawai salim yake masa har ya shiga toilet dan watso ruwa.
Bayan ya fito ya ciro wayar sa dake a kashe tun jiya ya kunna, yayi tunanin zai ga ko da sakon Maryama ne, amma sai ya ga wayam, duk sai yaji ya damu, har ya ajiye wayar yaji ba zai iya ba kuma, Ummi ya fara kira suka gaisa, tayi masa korafin
27, January 2025
Rukayya
Good