Showing 78001 words to 81000 words out of 98004 words

Chapter 27 - SAUYIN KADDARA COMPLETE HAUSA NOVEL

06 Jan 2025

11621

wayar sa a kashe, hakuri ya bata ya dora

"Babu chargy ne Ummi, sai yanzu na samu sakawa, ayi min afuwa."

"Babu komai, Allah ya bada sa'a."

"Amin Ummi nah."

Dariya tayi ta ajiye wayar, sai ya danna Number Maryam, tana ta ringing baa d'auka ba har ta katse, d'an jim ya sake yi sannan ya kuma kira a karo na biyu, Walid ne yaji ringing d'in a d'aki suna wasa da Habubu ya shiga da sauri, daukowa yayi ya daga.

"Hello, Yaya Maryam ɗin bata nan sun je asibiti da Umma bata da lafiya."

A kwance yake sai ya mike da sauri

"Me ya sameta? Walid ne ko Abubakar?"

"Walid ne, bata da lafiya ne shine suka je asibiti."

Dafe goshin sa yayi, jiki a sanyaye yace

"Shikenan , idan sun dawo zan kira."

Kashewa yayi, duk sai yaji babu dadi, ya tuna tun a gida take dan shiga toilet, be kuma bada hankalin sa har ya kaita asibitin ba, gaba daya sai yaji yana jin haushin kansa, kasa zaman yayi ya mike ya fito yana dan zagaya wa hannun sa sakale ta bayan sa.

Tsaye take a kofar bangarenta, tana hango shi ta kafe shi da ido daga nesa, kallon ta yayi, sai ya sauke kansa da sauri yana chanja direction din sa, da sauri ta juya ta shige ciki tana buga kofa.

Yawo yayi sosai a cikin masarautar da tafi kama da gari guda, sosai abun ya bashi sha'awa yadda suke kiwo sosai, kiwo shine sana'ar da suke yi tun iyaye da kakanni, kowanne bangare ya nufa sai ya ga ana kiwo a wajen. Tafiya yayi sosai ba tare da ya sani, wani babban waje ya hanga cike da ya'yan itatuwa birjik babu kalar da babu iya ganin mutum, gefe wani dan karamin ruwa ne daya saka lambun a tsakiya, kai tsaye wajen ya nufa ya shiga yana tafiya a nutse, iska ce me matukar dadi ke kadawa, wani irin yanayi yake shaka yana ayyano wasu abubuwa a ransa, daga chan gefe ya hangi wasu kujeru masu matukar kyau da kyalli, sai ya nufi wajen ya zauna yana daga kansa sama. Sosai wajen yayi masa dadi, waje na da zai dace da yanayin ma'aurata wanda suke cikin shauki da begen juna, masoya masu son su tabbatar da soyayyar su ya kamata su kasance a irin wajen, sai ya shiga auno kansa da Maryam suna zaune suna hira, hira me cike da nishadi, so yake ya ji labarin ta, kuruciyarta, komai nata yake so ya sani, shiyasa yake son shirya musu wata yar tafiya da zasu kadaice ta juna, hakan zai kara kusanci a tsakanin su, a lokacin ne zai fallasa mata asirin zuciyar sa, lokacin da ya riga ya san babu wani nauyi ko tunani akansa.

Tsawon lokaci ya dauka a wajen ba tare da ya sani ba, sai da wayar sa ta dawo dashi daga tafkin daya afka na tunanin ta, a dan zabure ya ciro wayar yana tunanin ita ce, jikin sa ya bashi itace, aikuwa ita ɗin ce, babu wani bata lokaci ya daga cikin tausayawa yace

"Mero ta."

Sai taji wani yar, yadda ya narke murya sosai da yadda ya fadi ta ɗin yasa ta a wani yanayi na soyayyarshi, bata iya amsawa ba har sai daya sake cewa

"Baby kina jina? Ya jikin naki?"

Cikin hado kalmomi ta cije tace.

"Da sauki, drip ake samun."

Muryar ta kasa tayi maganar, da sauri yace.

"Subhanallah, abun har ya kai haka?"

"Uhum..."

kawai tace ganin umma ta shigo dakin, abu ta dauka ta fita, tana jin sa ya cigaba da jera mata sannu babu kakkautawa, uhum kawai take binshi dashi dan bata da wani kuzari gaba daya jikin ta babu kwari dalilin kenan da ya saka ake sa mata drip din amma a gida.

"Me suka ce yake damun ki?"

"Ciwon ciki nake, wai naci wani abu ne."

"Ayya, basu kuma ce ga wani abun ba bayan nan?"

"Me?" Tace da sauri

"No I'm asking ai, bayan ciwon cikin, basu ce wani abu ba?"

"Basu ce ba." Ta amsa a gajarce.

"Shikenan, Allah ya Baki lafiya kinji, get well soon."

"Amin."

"I miss u." Yace yana chanja topic din dan son ya ga ta dan ware dan yaji muryar ta wani iri, sai kawai tayi murmushi ba tare da ta mayar masa ba.

Hira ya cigaba da jan ta har yaji an fara kiran sallah a masallacin cikin Masarautar, sallama yayi mata da alkawarin zai kira anjima. Yana kashewa ya jefa wayar a aljihu yana barin wajen.

Bayan sun gama wayar Maryam bata bar mamakin shi ba, duk yayi laushi kamar bashi ba, sai kawai ta bar abin a matsayin dan ya ga bata da lafiya ne yake lallabata, duk da haka taji dadin yadda yayi mata, ita kadai take murmushi tana kallon takardar serum test din da akayi mata and it's positive, sai ta kunshe fuskar ta kunyar Umma na sake kamata tunowa da tayi da ta san komai.

***
Da k'yar hafiz ya bude idon sa guda daya, wani irin mugun sarawa kansa ke masa, juyi ya fara yi yana son tuno abun da ya faru, daya bayan daya komai ya dinga dawo masa a kwakwalwa, da sauri ya yunkura zai tashi, a daddaure yake ta ko ina, yar karamar kara yayi jin duk ko ina na jikin sa ya dauka saboda daurin daya sha, kalle kalle ya shiga yi a dakin, babu komai sai wasu tarkacen kaya a wani dan karamin buhu,jikin sa ya shiga jaa a hankali yaji an budo kofa. Da sauri ya daga kansa, tare suka shigo ita ce a gaba suna bin ta, ransa a matukar bace yake kallon ta, ji yake kamar yaje ta shako ta ya kashe ta kowa ya huta, ya rasa hatsabibancin ta, da rashin tsoro kamar namiji. Kama shi daya daga ciki yayi ya daure masa baki sannan ta nuna masa wani katako,

"Kuyi masa laga-laga har sai ya bar numfashi sannan kuje ku wurgar dashi chan bayan gari, wannan shine sakamakon sa ma cin amana ta, iya kacin adalcin da zan iya yi masa kenan, wawa, be san setup bane daga ganin mota ka fara bin ta."

Babu bata lokaci suka cika aikin su,tana tsaye suka kwashe su suka fita dashi a bayan mota sannan ta koma ciki tana jin tayi wani abu da ya saka ta farin ciki.

***
Gidan babu kowa duk sun fita makaranta, Maryam ta dan ji karfi ta fito ta dau tsintsiya zatayi shara Baba ya fito zai tafi kasuwa, yana ganin ta yayi saurin cewa ta ajiye, a kunyace ta ajiye tsintsiyar ta koma ciki tana tunanin ko Baba ya san labarin ne? Rufe fuskarta tayi tana jin kamar tayi tsuntsuwa ta gudu daga gidan saboda yadda take jin kunya.

Yana fita kai tsaye gidan Hajiya Mama ya shiga dan gaishe ta, kwana biyu kenan be shiga ba saboda abubuwan sun kara yawa, yana shiga Alhaji Faruku ya tsaya da yake kokarin shiga shashen Hajiyar, gaisawa sukayi a mutunce cikin girmamawa kafin su nufi bangaren zasu shiga a tare.

Tana zaune ta bude wasu kayan ta,duk ta barbaza su, kayan jaririya ne a ajiye a gefe ta kura masu ido, duk da girma da tsufa sun kamata gashi dama kwana biyu abun nata kara gaba yake, ita kadai sai tayi ta soko zance marasa kan gado, asibiti aka kaita suka ce sai hakuri tsufa ne ya taba ta, haka aka dawo da ita gida ana dai bata magani amma abin babu wani sauki.

Gaishe ta sukayi ta amsa acikin nutsuwa, dan jim baba yayi sai kuma ya mike zai fita,

"Garba..." Ta kira shi a karo na farko bayan wasu lokuta masu tsawo, sai ya ja ya tsaya yana jin kamar bada shi take ba.

"Zo ka zauna zamuyi magana."

Be Musa ba ya dawo ya zauna a in da ya tashi.

"Zaka iya tuna kanwarka A'isha? Da aka sace ta a ranar sunan ta? Duk da lokacin baka fi shekara goma ba."

"Na tuna Hajiya, dalilin kenan da Gwaggo ta kamu da hawan jini me tsanani har yayi sanadiyyar mutuwar ta."

Kallon sa ta ke tayi har yayi shiru yana sake sauke kansa kasa. Gaban Alhaji Faruku ne ya fadi yana tunanin abinda zata faɗa dan har ya gano in da ta dosa. Kar dai???


"Nice nasa aka sace ta, saboda sanadiyyar da mahaifiyar ku tayi min na bar gidan mijina, shiyasa ni kuma nayi mata abinda zai kashe ta a hankali, kai naso a lokacin na dauke sai dai matsalar duk san da aka zo sai a tarar da kai tare da Umar, dalilin kenan da ya saka na...."

Wata irin zabura Alhaji Faruku yayi, shi kansa baba zaman yan bori yayi,

"Hajiya... Ma..ma..." Alhaji Faruku yace yana mik'ewa, kamar zai zare saboda yadda zancen ya kada shi, kallon Baba yake yana so ya fuskanci yanayin da yake ciki, gani yayi ya mike tsaye, be ce komai ba ya juya yayi hanyar fita, sai daya je karshe sannan yace

"Shari'ah ce zata raba mu dake wannan karon, bazan iya kyalewa ba, kayi hakuri Umaru."

Zuciyar sa na tafasa ya juya ya koma gida Alhaji Faruku ya biyo shi yana kiran sa, banza yayi masa ya shige gidan har da rufo kofa kafin ya kai ga shiga.

Gefe Alhaji Faruku ya samu ya zauna yana jin zuciyar sa kamar zata bullo kirjin sa ta fito.

***
Assalamu alaikum dearies
Ina gaisuwa
Thanks for ur supports😍😍

Rano
[3/18, 22:27] Hafsat Rano: *SAUYIN KADDARA*

*46-47*

ONAR TASFAH

_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A HALIN YANZU😁._

*ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma
*SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano)
*KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo)
*BURI ƊAYA!* (Mamu gee)
*WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull)

👇🏻karku bari ayi babuku

*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi  daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*

*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*

Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank

Saika tura shaidar biya ga wannan number ta WhatsApp

08030811300

Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN  ta wannan number din

07067124863
Sai kayi wa Number magana ta WhatsApp








***
Yana shiga ya datse kofar, Maryam na tsaye a bakin rariya zuciyar ta na faman hautsinawa Baba ya shigo a matukar fusace, tun da take bata taɓa ganin bacin ran sa irin na ranar ba, da kallo ta bishi har ya shige dakin sa ya ja kofar ya rufe.

Tashi tayi jiki a sanyaye ta nufi dakin Umma tana ayyana abinda ya faru da Baban, Umma na zaune tana gyara dakin Maryam ta shigo, da kallon umman ta bita har ta zauna a yar kujerar dake gaban keken dinki daya kusa shekara babu wanda ya haushi.

"Lafiya dai?" Ummm ta tambaya tana ajiye zanin

"Baba ne ya shigo a wani yanayi, ya shiga dakin sa ma ya rufe."

"Toh!"  Umman tace tana ajiye kayan hannun ta,

"Bari naje naji."

Taso wa Maryam tayi ta dawo saman gadon ta kwanta zuciyar ta duk babu dadi ga wani zazzaɓi zazzaɓi dake son rufe ta.
Tana nan kwance ta fara jiyo muryar baban a sama, da alama fada yake sosai, sai tayi lakwas tana sake gyara kwanciya tana hasaso abinda ya saka baban yake wannan fadan ba karami bane. Bugun kofar da ake ta faman yi ne ya dawo da Maryam daga baccin daya sace ta, tashi zaune tayi tana sake kasa kunne sosai, fitowar umma taji, chan sai taji Muryar Alhaji Faruku tsakar gidan suna magana da Umma, tasowa tayi ta fito, yanayin fuskar sa kawai ta kalla ta san akwai matsala, sai ta rakube a jikin bangon, gaishe shi tayi ya amsa a takaice, shiru yayi bayan umman ta gama masa bayani, jikin sa a sanyaye ya juya ya fita. Hada ido sukayi da Umma, sai ta girgiza kai kawai ta koma dakin baban, gaba daya sai kanta ya kulle, so take taji me yake faruwa, duk da alamu sun nuna yar matsala ce tsakanin Baban da  Alhaji Faruku tun da har yaki fitowa da yazo. Addu'a kawai tayi Allah ya gyara komai ta juya daki.

***
Hayaniyar su Zainab da Rauda ne ya sake bata mishi rai, fada suke kamar zasu cinye kansu, Hajiya Mama na zaune a falon tana ta jera charbin data tsinka dazu, idan ta gama shiryawa sai ta sake tsinkasu, haka take tayi, kamar zai yi kuka ya shigo falon, ta zubo masa ido tana kallon sa, kamar zai yi magana sai ya fasa ya nufi dakin da suke ciki, suna ganin sa sukayi shiru, a fusace ya daka musu tsawa

"Wanne irin hauka ne haka? Tun daga waje nake juyo hayaniyar ku."

Kansu a kasa babu wacce tayi magana, kwafa yayi ya juya ya fita, harara Rauda ta sakar wa Zainab kafin ta tashi ta bar dakin gaba daya.

***
A gaba Umma ta saka shi, babu irin nacin da bata yi masa ba akan ya sanar da ita me yake faruwa amma fafur yaki, kayan sa da yake ta ajiya tsawon wasu shekaru ya tattaro ya fito dasu kaf, dayan bayan daya yake binsu yana dubawa, sai daya gama duba komai sannan ya tattara ya ajiye yana kokarin fita ta sake tsaidashi

"Haba, ya kamata ka sanar dani me yake faruwa, shirun nan naka be dace ba, na chanchanci nasan me yake faruwa karka manta ni matar ka ce."

Kallon ta yayi, wajen sakan biyar yana nazari kafin yace

"Zaluncin da aka dade ana yi mana ne yau Allah ya bayyana shi, labarin dana taba baki na batan A'isha, yau da kanta ta bayyana kanta, ashe Hajiya Mama ce ta shirya komai."

Da sauri umma ta dafe kirjin ta dan tasan babu abin da Baban yake jin ciwo kamar wannan,tsawon zaman ta dashi tasan babu abinda ke dauke walwalar  sa idan ya tuna kamar batan yar uwar sa da mutuwar mahaifiyar su.

"Wannan karon hukuma ce zata raba mu wallahi, ko zanyi yawo tsirara sai na bi hakkin wanda aka cuta."

Kafin tayi magana ya fice, Maryam dake jin komai ta fito

"Umma menene yake faruwa, wallahi na kasa sukuni.?"

"Sirrin boye ne ya fito fili, bansan yadda zata kaya ba, amma tabbas ko ni ban yarda da kyale wa ba, wannan zaluncin yayi yawa."

Ciki umman ta shige sai tabi bayan ta da sauri. Zama sukayi umman ta shiga bata labarin abinda ta sani har zuwa yanzu da abinda ya faru, sosai maganar ta kada maryam, shiyasa ashe baban nasu bashi da kowa da wasu dangi sai Abba (Alhaji Faruku da suke uba daya)jiimanin abin suka wuni sunayi yi, har sanda Baba ya dawo babu abinda ya sauya na daga fushin da yake, haka dole Alhaji Faruku ya hakura da jiran Baban ya kyale shi, dan ba karamin fushi yayi ba. Shi kanshi Baban baya so wata magana ta hadasu,,kar nauyi da kunyar da yake ji su hanashi aikata abinda yayi niyya tun farko, yasan yadda yake da Alhaji Faruku zai ji nauyin aikata wa mahaifiyar sa wani abu,amma idan ya fita harkar sa ya rufe idon sa shikenan, dan baya jin akwai abinda zai hanashi aiwatar da abinda yayi niyya.

***
Hajiya Mama surutan nata kara gaba yake, ras da ita idan ka ganta amma kan da sauki, Alhaji Faruku kuwa abin duniya ya hadu yayi masa yawa, ya rasa in da zai saka rayuwar sa,gashi dai duk tsiya uwa uwa ce, duk muni da rashin kirkin uwar mutum son ta yake kuma ba zai so abinda zai same ta ba. Ganin bashi da wata mafita yasa kawai ya fawwala wa Allah al'amarin da. Ya zuba ido ya ga abinda zai faru.

***
Kwanan sa biyu a gaban bular, gaba daya jikin sa jini ne, kasancewar hanyar babu masu wuce wa yasa har ya kai hakan, a kwana na biyun ne ya fara farfaɗo wa, da kyar ya bude idon sa daya yi masa mugun nauyi, a kumbure yake sosai ya ja jini, dishi- dishi ya soma gani kafin ya fara jin garin na juya masa, wani mutum ne yazo wucewa a mota ya ganshi, har ya wuce ya yi shahada ya dawo ya duba shi, ganin yana numfashi a galabaice yaayi saurin daukar sa ya sashi a mota da taymakon dan uwan sa da suke tare, asibiti suka wuce dashi, babban likita ne ashe saboda haka suna zuwa aka karbe shi babu wani bata lokaci aka shiga bashi taimakon gaggawa.

***
Kusan raba dare sukayi ranar suna waya da Arkel, duk rabi da kwatar hirar tashi ce, ita dai daga umm sai a'ah, sai kuma wani abun idan ya kure ta ta bada amsa, da kyar ya kyale ta kwanta bayan ta marairaice masa dan ba karamin bacci take ji ba, gobe take son komawa dan taji sauki sosai, gashi Ummi ta kirata jiya akan taji shiru, gidan babu dadi, da tace mishi ma zata koma sai yace tayi zaman ta idan ya dawo sai su tafi, amma kiran Ummin yasa ta ga kawai gwara ta koma din.

Da safe ta tashi da dan ciwon kai,  da kasala, tunanin labarin da Ummi ta basu akan rayuwar datayi da kuma labarin da Umma ta bata na Baba da kanwar sa da aka sace take ta hadawa waje daya tana tattaunawa da zuciyar ta, chan kasan zuciyar ta tana jin kamar akwai babbar alaka a tsakanin labaren biyu, sai dai ta rasa da wa zata tattauna,Anty Maryam ce abokiyar hirar ta gashi kuma sun yi tafiya sun ji garin su mijin ta biki, dole ta yanke shawarar sanar wa umma. Bayan tayi wanka ta saka riga da skirt na material ta daura dankwalin, sai ta fito tsakar gida wajen Umma, tana tsaye gaban kejin kajin da Habubu ya sake zubawa tana dubawa ko basu da ruwa, sai data tabbatar komai daidai sannan ta dawo ta zauna tana kallon ta

"Yaushe zaki tafi?"

"Zan jira broda din sa, Ummi tace zai zo ya dauke ni bayan magriba."

"Ok, kinci abincin?"

"Wallahi umma abincin ne yaki shiga, awara nake so."

"Daurewa ake ai, sai kin kula da cikin ki, ki godewa Allah ma bakya laulayi me wahala."

Kunya ce ta kamata.

"Kin ga dazu kuwa kawar nan taki zango ta kiraki kina wanka na daga, wai an saka muku lecture ranar asabar."

"Kash... Ni wallahi duk karatun nan ya ishen, ga project da zamu fara."

"Allah dai ya taimaka, aski dama idan yazo gaban goshi yafi zafi."

"Haka ne."

"Umma magana zamuyi."

"Ta me?"

"Wani abu nake ta tunani."

"Na me fa?"

Gyara zama tayi ta sanar wa umman komai, shiru umman tayi itama tana auna maganar kamar akwai alamar tambaya a cikin ta, duk da basu da tabbas amma zasuyi iya kar kokarin su suga sun

27, January 2025
Rukayya

Good

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login