Showing 36001 words to 39000 words out of 98004 words
a mayafi)😂😂
Sorry kawar zango😝
Assalamu alaikum dearies
Yan uwa masu kamshin apple
Nasan dai kuna ta jira kunce wannan ina ta makale
Kamar yadda wasu suka sani dai wlhi ido ne ya saka ni gaba, babu yadda na iya dan a halin yanzu ma gobe asubanci zanyi naje naga likitan ido, kar kuyi tunanin ko wai da chan Ina da matsalar idon, haka nan wlhi dalilin ZAFAFA biyar ido ya samu matsala.
Nasan zakuyi mun uzuri saboda dai ido babbar kadara ce kuma ba abin wasa bane
Nagode muke da kauna in Sha Aallah zaku samu Sauyin Kaddara fiye da yadda kuka yi zato
_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A HALIN YANZU😁._
*ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma
*SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano)
*KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo)
*BURI ƊAYA!* (Mamu gee)
*WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull)
👇🏻karku bari ayi babuku
*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*
*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*
Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank
Saika tura shaidar biya ga wannan number ta WhatsApp
08030811300
Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN ta wannan number din
07067124863
Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.
*Karki bari ayi babu ke, Abari ya huce shike kawo rabon
Rano🚴🚴🚴
[3/18, 22:25] Hafsat Rano: *SAUYIN K'ADDARA*
*21*
©*Hafsat Rano*
*_ZAFAFA BIYAR na kudi ne idan kana son kowanne daga ciki ka nemi Wannan numbers din_*
*08030811300*
*07067124863*
*_Daurin boye_*
_safiyya huguma_
*_Buri daya_*
_mamuhgee_
*_Wutsiyar rakumi_*
_billyn Abdul_
*_Kai min halacci_*
_Miss xoxo_
*_Sauyin kaddara_*
_Hafsat rano_
***
A hankali ta dinga rage kukan da take bayan tafiyar kowa, shiru saman kamar babu wata halitta a ciki, dan bude fuskar ta tayi ta kalli dakin, da ido take bin komai kafin ta dire kallon ta akan jerin sabbin akwatunan dake zube a chan wani d'an karamin corridor, ba kad'an ba suka yi mata kyau, shiru tayi tana nazarin yadda abubuwan suka sauya baki daya.
Kwance yake a kan resting chair a dan karamin dakin da ya mayar study room din sa, yana jin hayaniyar jama'ar kadan kadan har ya daina ji baki daya, tashi yayi ya fito idon sa akan dakin nata ya sauka kasa.
Hajiya Mero da jama'ar ta wanda sukayi saura na zaune a falon, dauke kai yayi ya wuce bangaren Alhajin yana tunanin samun sa ko akasin haka.
Da kallo dukka suka bishi kafin Aziza ta kalli Hajiya Mero tace
"Yaron nan fa akwai girman kai, ji yadda ya ɗebe mu yi watsar ko yar gaisuwa babu."
"Haka yake ai,barni dashi."
"Gwara dai kiyi maganin sa tun wuri, in ba haka ba duk ranar da komai ya fito a yadda yake jin kansan nan ba zai miki da dadi ba."
Dan shiru tayi kadan sannan tace
"Ba ma za'a kai nan ba."
***
Da kallo Alhaji ya bishi har ya karaso cikin dakin, a kasa ya zauna ya tankwashe ƙafafuwan sa kamar me shirin daukar karatu, yau ce rana ta farko shekara biyar baya da har hakan ta shiga tsakanin su da mahaifin sa, tun bayan abinda ya faru ya dauke shi ya ajiye shi a gefe a tunanin sa baya son ummi ne kuma tun da ta hadu da lalunar nan, tun daga lokacin ya cire idon shi akan duk wani abu na Alhajin ya dage ya gina kansa domin mahaifiyar sa .
Tsawon wannan lokacin be san halin da take ciki ba, babu ruwan sa da maganin ta, hakan ne ya sake tunzura Arkel ya fita daga sabgar shi.
"Ango ne da kansa." Alhajin ya fada cikin son tabbatar da hakan, dariyar yak'e kawai yayi ya dubi mahaifin nasa yace
"Alfarma nazo nema a wajen ka, ba dan na isa ba, sai dan matsayin ka na mahaifi a wajena, zuciya ta kasa nutsuwa da komai da yake faruwa, ba ina neman alfarmar ka dawo da ita kamar da ba, sai dai ina neman alfarmar ka taso muji ka ganta."
"Arkel..." Ya kira sunan sa cikin faduwar gaba
"Ka daure dan girman Allah, yau ne rana ta farko dana nemi hakan, ka sani ba zan iya aiwatar da komai da nake so nayi ba face sai da sa albarkar ku ku biyu, xan so ace kune gaba da zaku sani a kan hanya daidai duba da irin rayuwar da zan shiga a yanzu."
"Hakan shine kawai bukatar ka?"
Daga masa kai yayi kawai,
"Je ka ka kira matar taka, mu hadu a dakin."
Da sauri ya kalle shi dan beyi tunanin hakan ba, fita yayi kamar zai tashi sama saboda sauri ya haura saman, sa'a daya yaci duk yan falon sun tashi babu kowa.
Murd'a kofar yayi tayi saurin d'age mayafin ta sama zuciyar ta ta hau dukan uku uku, tsaye yayi a bakin kofar ya kasa shiga, kallon ta yake yana jin wani abu me kama da tsoro yana kokarin dakusar dashi, cikin takun sa na kasaita ya taka har gaban gadon, batayi aune ba sai ji tayi ya riko hannun ta, da sauri ta zame hannun jin wani irin abu me kama da mayan karfe ya bigi hannun nata. Hannu yasa ya kama kafad'ar ta ya miƙar da ita tsaye, mayafin ya gyara mata sosai yadda fuskar ta zata rufe ruf sannan ya matsa daf da kunnen cikin wata irin murya yace
"Calm down, ba abinda zan miki, matsoraciya."
Kasa tayi da kanta, hannun nata ya saka cikin nasa suka shiga takawa a hankali har suka bar dakin, ita dai tana cikin mayafi tana kallon ikon Allah. Sai da suka zo step ɗin karshe sannan ya dan sa hannu ya janye mata mayafin ya saki hannun ta yana matsawa dan nesa da ita
A tsakiyar falon suka tarar da shi ya makale hannun sa ta bayan sa yana Safa da marwa, yana jin motsi ya juyo da sauri, tun dazu ya fito sai dai ya kasa karasawa dakin, da yayi yunkuri sai yaji ya kasa, hakan yasa ya tsaya a falon yana ta zagaye chan kasan zuciyar sa na son ganin ta sai dai wani abu ya danne hakan har ya kan ji kamar zai bar numfashi daga lokacin da ya shiga cikin dakin.
"Ga Alhaji ki gaishe shi." Ya rada mata a kunne
Da sauri tayi kasa cike da wata masifaffiyar kunya tace
"Ina wuni Abba?"
"An wuni lafiya? Ya bakunta?"
Bata iya amsawa ba, bude kofar Arkel yayi ya nuna mata ciki da hannu. Shiga tayi ya mai da kallon sa wajen Alhaji, da kyar ya d'ago ƙafafuwan sa ya isa kofar, a bude kofar take babu wani makari hakan ya bashi damar hango ta a kwance sambal kamar gawa, da sauri ya kalli Arkel da shima shi yake kallo, kafar sa daya ya saka a cikin dakin yayi saurin ja baya
"Ba zan iya ba Muhammad."
Ya fada yana juyawa da sauri.
"Ba zan iya ba?!" Ya maimaita a ransa, da kallo ya bishi har ya shige dakin sa ya rufo har da saka key.
Duk abinda ke faruwa tana kallon su, da sauri ta juya ganin ya kalle ta, a take idanun sa suka kada sukayi ja sosai, shiga dakin yayi ya maida kofar ya rufe.
A gaban gadon ya tsaya yana, idon ta a bude tana kallon sa, fuskar ta a sake alamar tana cikin farin ciki. Samun kansa yayi da sakin fuskar sa
"Matso nan." Ya kalli Maryam, taso wa tayi ta dawo gaban gadon, da hannu ya nuna mata wajen zama.
"Umma?" Ta tambaya tana kallon shi, daga kansa yayi sama alamar eh, da saurin ta sake kallon ta, tausayi ne ya kamata ta kalle shi idon ta na cicciko wa.
"Please don't."
Ya fada yana zama a daf da ita, duk abin nan ummin na kallon su, so take tayi magana babu halin yi, kamo hannun ta yayi ya saka cikin nasa sannan ya kamo na ummin ya rike a dayan
"Wannan ita ce mahaifiya ta."
"Shekara biyar kenan tana a wannan yanayin, babu in da bamu buga ba dan neman mata magani, amma Allah be sa mun dace ba, ni namiji ne sannan akwai abubuwa da yawa a kaina, dole tana bukata ta a ko da yaushe, ina neman alfarmar da ki tayani kula da ita dan girman Allah, wannan shine babban dalili na na yin auren nan..."
Dan dakatawa yayi sannan yace
"Ina da son kai ko? Daga zuwan ki na dora miki babban nauyi akan ki ko?"
Girgiza kai tayi da sauri cikin raunin murya tace
"Nima mahaifiya tace ai."
"Nagode sosai, in Sha Allah zaki same ni me sauke dukkan nauyin da Allah ya dora min."
Shiru tayi tana tunanin matsalar, shima sai yayi shiru kawai be sake cewa komai ba tunani yake kamar yayi wuri da ya sanar da ita, kar ta ga kuma kamar dama amfanin ta kenan, amma ya xai yi? Bashi da zabi da ya fi hakan, tun da dama ai ko su Ya Nabila da suke maganar yayi aure yayi aure ai dama dan ummin ne.
***
Babu wanda yayi wa dan uwan sa magana har suka dangana da dakin su, shine a gaba tana bin sa a baya, saman gadon ya haye da dukkan jikin sa ya saka fillo a kasan kansa ya kwanta rigingine yana kallon sama, ja tayi ta tsaya tana tunanin in da zata zauna, dan cire kansa yayi ya kalle ta,hannu yasa yayi mata alamar tazo, ba musu ta karasa tana dan hada hanya saboda yadda idanun sa ke yawo a kanta yasa taji tafiyar na harhade mata, tana zama ya mike da sauri yana dafe kai yace
"Ina zuwa!"
Fita yayi tabi bayan sa da kallo,jim kadan sai gashi ya dawo dauke da ledeji manya guda uku, zube su yayi a kasan gadon ya kalleta
"Ga kayan ki nan in ji kamal."
A kunyace ta jawo ta bubbuda, roasted chicken da wani haddin veggies a gefe leda daya,dayar ledar kuwa soft drinks ne da fresh milk sai dangin su fruits a dayar ledar, rufe wa tayi ta kurawa kasa ido dan bata san ya zatayi da shi ba.
Yana nan kwance yaji shiru bata fara ci ba, tashi taga yayi ya fita, plate da cups ya shigo dashi ya buɗe ledojin ya zuba mata ya tura gaban ta,
"Sako malama."
Marairaice fuska yayi tace
"Na koshi."
"Kika isa ma, sauko nace."
Kallon sa tayi
"Stop looking at me, sauko nace "
Saukowa tayi ta zauna ya nuna mata hannun ta, kadan kadan ta shiga ci yana kallon ta, gashi ya tsare wajen gaba daya duk sai taji ta kasa sakewa musamman idan ta daga kanta taga yana kallon ta, da sauri take saukewa saboda yadda idon sa ke mata. Tun tana ci har taji ta fara koshi amma duk da haka ya ki barin ta ta tashi da tayi yunkurin zare hannun ta zai sake hade rai ya kuma kafe ta da ido, sai data ji kamar zai dawo mata ne yasa ta hade hannun ta waje daya tace
"Please ka barni haka wallahi na koshi."
"Sai kin kara."
Zaro ido tayi
"Zan dawo dashi Allah idan na kara ci."
"Idan kika dawo dashi sai ki kara samun space ɗin xuba wani."
"Na shiga uku." Ta fad'a ba tare da ta sani ba ma.
Murmushi yayi kawai ya tashi,
"Jeki wanke hannun kiyi alwala daga nan."
"Eh....?" Tayi kamar bata ji karshen ba
"Yes, yadda kika ji. Ina zuwa." Ya juya ya fita
Tattare komai tayi tasa a gefe ta bude handbag din ta dake gefen gadon ta ciro pad da sabon pant ta shiga toilet, sai data fara gyara jikin ta sauƙin ta ma ta samu ruwa a heater hakan yayi mata dadi ta shirya tsaf ta fito, be dawo ba har lokacin, hakan yasa tayi saurin buɗe wardrobe d'in ta zura handbag din tata a ciki ta rufe. Da sauri sauri ta haye gadon bayan ta kashe wutar dakin ta kwanta ta rufe idon ta, bata san ya dawo ya sake yi mata maganar alwala bata san yadda zata ce masa tana period ba.
Ta na nan kwance taji ya shigo, tsaye yayi a kanta yana nazarin ta, hawa gadon yayi ta sake runtse idon ta, wayar sa ya ciro ya haske ta, idon ta ya gani yana ta rawa alamar barcin karya take,
"Kinyi alwalar?" Ya tambaya yana kashe hasken wayar. Kin magana tayi wai ita bata yadda ba irin me baccin nan, be sake magana ba ya sauka, toilet ya shiga ya jima a ciki dan da alama wanka yayi dan taji karar ruwa, fitowa yayi ya kunna hasken dakin, da sauri ta sake runtse idon ta, yana ganin ta murmushi kawai yayi ya hau shirya wa.
Light kaya ya saka marasa nauyi saboda garin akwai dan zafi, sallaya ya shimfida yayi shafa'i da wutri yayi yan addu oinsa sannan ya kashe wutar dakin ya kwanta.
Babu wanda yayi bacci a cikin su, kowa da abinda yake tunani. Tunanin maganar dazu ne ke mata yawo akai, idan har da gaske abinda ya fada saboda mahaifiyar sa yayi aure, kenan yana nufin baya son ta kenan, ya aure ta ne saboda mahaifiyar sa, tausayin kanta ta fara ji hakan ya saka wa zuciyar ta rauni, ta rasa dalilin da yasa maganar tasa ta yi mata zafi duk kuwa da iya kar gaskiyar sa tasan ya fada amma ta kasa jin hakan a zuciyar ta.
Matsowa taji yayi sosai ya dora kansa a saman pillon da take kai, hannu yasa ya matso da ita jikin sa yayi mata rumfa da dukkan hannayen sa. Cikin maganar rada rada yace
"Kwana nawa kike yi?"
"Na'am??" Ta zaro ido waje, sake matse ta yayi yace
"Eh... Naga pack din a dustin din toilet so don't pretend."
"Na shiga uku."
"Just tell me." Ya fad'a yana saka hannun sa a cikin gashin kanta
"Please ka bari."
"Naki, fada min or else?"
"Dan Allah...."
"Kawai ki faɗa min ina jin ki."
Gaba daya ta rasa yadda zatayi gashi ya bi ya kanainaye ta da dukkan jikin sa, hannun ta ya kamo ya matsa da d'an karfi tayi kara kadan
"Fada min toh."
Da sauri tace
"10."
Dariya yayi sosai bayan ya dan matsa, shiru tayi tana kallon sa a cikin duhun dakin, sai da yayi dariya sosai sannan ya matsowa ya sake nanike mata, mutsu mutsu ta hau yi ya sake rike ta gam, a kunne ya rada mata
"Please..."
Bata sake motsawa ba tayi lamo tana mamakin shi.
🚴🚴🚴🚴🚴😂 Ba ruwana Yasin
Gudnight Malama Maryama.🤭🤫
***
Haji Hafiz abun duniya yayi masa yawa, tun da ta shige daki yake tunanin maganganun da Matar tayi masa, ya rasa yadda zai yi gashi ga dukkan alamu babu abinda ba zata iya aikata wa ba.
Bugun kofar gidan ne yasa shi tashi ya fito, malam rabe ne a tsaye ya dafe saman kofar yana kada kafar sa, gaban Hafiz ne ya fad'i.
"Malam Rabe..."
"Ba wannan ne ya kawo ni ba, kasan dai alƙawarin da kayi akan zaka biya kudin nan, na kara maka wajen wata uku gashi har an doshi wata shida babu labari."
"Kayi hakuri dan Allah, wallahi abubuwan ne.."
"Ai hakuri ya zama dole, dan zancen da nazo yi maka ma akan cewa ku bar duk kudin da ake bin ku na zaman da kukayi."
"Alhamdulillah... Amma."
"Dana katse min hanzari mana malam Hafizu, gida dai na riga na sai dashi tuni, a takaice dai wanda suka siya sun ce na sanar daku kwana uku suka baku ku tattara naku ya naku ku bar musu gidan zasu yi gyara."
"Innalillah wa inna ilaihi raji'un,haba malam rabe, ya zakayi mana haka? Yanzu dan bamu biya ba shine zaka saida gidan? Naga fa nayi maka alkawarin zan biya, zan biya wallahi."
"Ai kuwa bakin alkalami ya riga ya bushe, ni yanzu gida ya bar hannu na, kunci Sa'a ma sun biya ni har kudin da nake bin ku na wata biyar da kwanaki, yanzu sai ku fara shiri."
Yana kai wa nan ya juya ya bar kofar gidan.
Kamar zai yi ihu haka yaji, zafi goma da ashirin. Gefe ya samu ya zauna kawai hankalin sa a matukar tashe.
Asi dake gefe yana kallon komai yayi murmushi, text messages ya tura masa ya juya ya bar unguwar.
******
Wayyo Hafiz kana tsaka me wuya😭😭😭
Nagode da adduoin ku. Ido Alhamdulillah toh😔😔
_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A HALIN YANZU😁._
*ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma
*SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano)
*KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo)
*BURI ƊAYA!* (Mamu gee)
*WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull)
👇🏻karku bari ayi babuku
*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*
*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*
Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank
Saika tura shaidar biya ga wannan number ta WhatsApp
08030811300
Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN ta wannan number din
07067124863
Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.
*Karki bari ayi babu ke, Abari ya huce shike kawo rabon
Rano🚴🚴🚴
[3/18, 22:25] Hafsat Rano: 22*_ZAFAFA BIYAR na kudi ne idan kana son kowanne daga ciki ka nemi Wannan numbers din_*
*08030811300*
*07067124863*
*_Daurin boye_*
_safiyya huguma_
*_Buri daya_*
_mamuhgee_
*_Wutsiyar rakumi_*
_billyn Abdul_
*_Kai min halacci_*
_Miss xoxo_
*_Sauyin kaddara_*
_hafsat rano_
***
Farkawa yayi jin ana ta kiraye kirayen farko a wasu masallatan, zare jikin sa yayi bayan ya gyara mata kwanciya ya fada toilet, wanka ya fara yi sannan yayi alwala ya fito, ko motsi batayi ba daga in da ya barta, murmushi yayi ya janye mata mayafin da ke jikin ta ya dan kara gudun Ac dakin doguwar rigar sa ya saka ya tada raka'atanul fajr. Bayan ya idar ya dauko Alkur'ani me girma ya shiga karantawa a hankali har aka kira sallah sannan ya tashi ya fita masallaci. Bayan an idar ya hango Alhaji yana fita daga masallacin, ya ganshi amma sai ya ki bari su hadu, girgiza kansa kansa kawai yayi yayi zaman sa a cikin masallacin. Sai da gari ya dan fara haske sannan ya fito ya koma gida, yana shiga gidan aka dauke wuta gashi wani bacci ya ji yana dan fusgarshi, ko dan basu yi bacci da wuri jiya bane oho. Har yayi hanyar sama yaji ba zai iya ba ya koma ya saka aka tada gen.
Mamaki ne ya kamashi ganin har lokacin baccin ta take hankali kwance, fita yayi ya rufe mata kofar ya koma dayan dakin ya kwanta. Be dade da fita ba ta farka, ganin baya dakin ne yasa ta tashi da sauri tana duba jikin ta, da sauri ta dauko pad ta shiga toilet.
Har ta gama shiryawa bata ji ya dawo dakin ba, zama tayi kawai ta ciro wayar ta kunna, karfe bakwai lokacin da yan mintuna, rasa me zatayi ma tayi kawai sai ta shiga gallery ta hau kallon hotunan bikin, tana cikin
27, January 2025
Rukayya
Good