Showing 69001 words to 72000 words out of 98004 words
na me girma ne.".
"Ka yarda abinda kake tunani ba haka bane in Sha ALLAH."
"Hmmm."
"Karka damu, kazo gobe da safe nasan me zanyi."
"Shikenan, Allah yasa muji alkhairi."
"In Sha Allah."
"Amin."
***
Wani irin kallo yake bin ta dashi kamar yaga wata sabuwar halitta, duk ta gama tsorata da yanayin sa, kasa k'arasa wa kusa dashi tayi ya tashi yana kallon ko ina
"Alhaji nah." Ta fada a dan tsorace da son tabbatarwa kanta abinda take tunani
"Ina A'isha?"
"Na'am." Ta zaro ido
"Nace ina A'isha? Me kike anan? Waya baki izinin shigowa daki na? Ban miki katanga da ahlina ba?
"Alhaji..."
Daka mata tsawa yayi, ja da baya da baya ta hau yi yayi kanta da sauri ya rik'e ta
"Muguwa bakar azzaluma, yau sai naga bayanki wallahi."
Rikon da yayi mata ba karami bane, gaba daya idon ta ya firfito waje ta kasa magana, babu wanda yasan me yake faruwa, gaba daya ya haukace mata, babu yadda zai ya kyale ta ta tafi, wani irin naushi ya kai mata a fuska tuni bakin ta ya fara jini, gefe ya wurgar da ita cikin jina ya fito daga dakin yana kwala kiran Ummi, Baba ce ta fito da sauri yayi wajen ta
"Ina A'isha? Me ya same ta? Tana ina?"
"Alhamdulillahi, Allah shine abin godia, Maddapha ka dawo hayyacin kenan."
"Baba Ina take.? Ina sauran yaran? Naji gidan shiru me yake faruwa.?"
Budo kofar da akayi ne ya saka su dukka kallon kofar, Arab ne a gaba sai Arkel na binsa Maryam a kusa dashi, da sauri Alhaji yayi kansu yana tambayar inda Ummi take, kallon juna sukayi a tare cikin tsananin mamaki aka rasa wanda zai yi magana,
"Baku ji bane wai?" Ina take? Me ya ke faruwa ne da ba zaku sanar min ba?"
"Tana gidan Ya Nabila."
Arkel ya bashi amsa, da sauri yayi hanyar waje, bin sa sukayi maryam dai sai ta sulale ta haye saman ta tana mamakin al'amarin, yana fita yayi wa driver magana ya fito da mota, ko ta kan su be bi ba da suke ta magana yace da driver su tafi kuma yayi sauri.
Basu yi yunkurin binshi ba, dan dukkan su wannan shine abinda suka dade suna neman, ranar da suka dade suna jira kenan, ciki suka koma Arkel yayi sama ya bar malam Arabu yana cizar yatsa.😅
***
Gaba daya fuskarta ta haye tayi suntum da ita kamar wadda akayi mata shegen duka, da k'yar take fitar da numfashin wahala, a hankali ta rarrafa bayan gidan yayi tsit ta koma dakin ta ta murza masa mukulli, ba karamin wuya tasha ba ita kadai ta dinga juyi saboda azabar da take ji a bakinta, iya kar tunanin ta bata taɓa kawo wa rayuwa zata juya mata baya a dan taki kadan haka ba.
Nace Kadan kika gani ma.
***
Jirgin sassafe suka hau, saboda haka da wuri suka fice dan Maryam ko tashi bata yi ba sanda suka fitan, ko data tashi babu alamar su, gyare gyaren tayi da taimakon Sadiya me aiki suka hada breakfast sannan ta koma sama dan yin wanka.
Direct suna dauko su gidan ya Nabila suka koma, Alhaji na nan, tun asubah ya sake komawa dan a daren Nabila ta sanar dashi komai da yake faruwa, kamar yayi kuka haka ya dinga la'antar mero saboda ba karamin zaluntar shi tayi ba dashi da iyalansa, shiyasa ya kudira a ransa tilas ne yaga shima ya saka ta a kwatankwacin rayuwar data jefa su.
Addu'io da magungunan hade sai turaren hayaki haka duk yazo da su, a ranar aka fara yi mata komai aikuwa ta ga sauyi sosai dan maganar ta ma ta sake fitowa kuma ba laifi taji dadin jikin ta sosai har tana kokarin tashi da taymakon masu daga ta sai dai tafiyar ce sai a hankali.
Zuwan malam ya sake warware abubuwa da yawa, ana i sauran kwana biyu za'a koma kotu asirin da Hajiya mero tayi ya gama warwarwa tsaf, babu wani abu daya yi saura, suna ta murna da farin ciki duk sun taru ana maida magana Arkel yafi kowa murna ya rasa in da zai saka kansa dan tsantsar farin cikin da yake ciki, gida ya koma ya dauko Maryama dan ita ma ayi da ita, yana shiga gidan yaji kamar ihu a dakin Hajiya mero, babu wanda ya san takunkumin daya sa mata har na fitowa ne illa kawai a tura mata abincin ta, Hajiya Mama ma da tazo hanata shiga gidan akayi haka ta k'araci zage zagen ta da tsine tsinen ta ta hakura ta tafi, shiyasa babu wanda ya damu da halin da take ciki, Maryam kam dama ba wani saukowa take ba idan ba kowa sai tayi zaman ta a saman hakan ya saka ba'a san halin data ke ciki ba.
Yana bude kofar yayi saurin ja da baya ganin ta jefo babban glass Allah ya taymaka Bata same shi ba, dakin yake bi da kallo ganin komai ya hargitse duk wani abun fashewa ta fasa shi tas kayayyakin ta duk ta yayyagasu, gefe kwanunan da ake kawo mata abinci ne birjik wasu taci wasu kuma ba'a taba ba, maganganun da yaji tanayi ne ya sake tsorata shi, babu abinda take sai maganganun hauka tana yi tana jan gashin kanta kamar zata tsinke shi, kofar ya maida ya rufe tana jingina a jiki wani irin tashin hankali na ratsa shi, da sauri ya haura saman Maryam na kwance rigingine tana duba wayar ta ya shigo, hannun ta ya kama ba tare da yace komai ba, kayan jikin ta ta kalla doguwar riga ce sai dai babu dankwali a kanta hakan ya saka gashin kanta bayyana,
"Bari na rufe kai na."
Tace ganin da gaske be ma lura ba, sakin ta yayi ta saka hula sannan suka fito, dakin ya bude yana nuna mata ciki
"Kalli kiga...."
Da sauri ta ja baya taana zare idon ta,
"Is she ok?"
Girgiza kanta tayi kwalla na kokarin zubo mata, hannun sa taji a saman fuskar ta ya sa ya goge mata
"Karki kuskura ki zubar mata da hawaye, bata chanchanci tausayin mu ba, Allah ne ya nuna ikon sa Maryam, wannan matar ta dade tana cutar damu, sau daya bata taba tunanin wannan ranar ba, nagode Allah daya kawo komai cikin sauki, duk abinda ya shuka dama shi zaka girba."
"Amma..."
"Shissh..., Dont say a word, muje kawai I'm hungry ma me Kika shirya min?"
"Uhumm..."
"Comman... Dont tell me kinji tausayin ta?"
"Allah naji."
"Wasa kike."
Hannun ta ya kama suka haura saman, sai daya fara rage kayan jikin sa sannan ya dauki waya ya jira Zainab, ce mata yayi kawai tazo ya kashe ya kira su Ya Nabila ya sanar musu.
Abincin da take jera masa ya kalla, shifa yau yadda yake jin sa so happy abinci ma ba zai shiga ba, kallon kasa-kasa yake mata, tana gama jera wa ya damko hannun ta
"Bismillah." Tace tana nuna masa kayan
"Yunwa ta tafi wallahi."
Shagwabe fuska tayi
"Kai fa kace yunwa kake ji?"
"Na koshi toh ai, kinga... Zo kiji."
Make kafada tayi tana dariya dan sarai ta gano wayon sa, hannu biyu ya hade alamar roko
"Um um.."
Wata kujerar ta koma ta zauna tana hard"e hannun ta, tsam ya taso ya dawo, zata tashi yayi saurin rikota yana dariya, kamar zatayi ihu haka ya maida ita ta zauna ya dora kansa a saman cinyarta.
"Muyi hira toh, na fasa abinda nayi niyya."
"Innalillah..."
"Me? Ko kar na fasa ne?"
Da Sauri ta rufe bakin ta
"Ni wallahi bance ba."
"Toh ni nace."
Tashi yayi zaune yana duba wayar sa, kiran Zainab ne, be daga ba kawai ya kama hannun ta suka wuce other room.🙈🤭🤾🚴
***
Sai daya gyara jikinsa ya chanja kaya sannan ya fito, Zainab na zaune tana ta kuka bayan ta leka taga halin da Hajiya Mero take ciki, bata iya zama ba ta dawo falon dan saura kadan tayi mata illa sai jefe-jefe take tana maganganu mara sa dadin ji, yana kallon ta yaji tausayin ta ya kamashii, Bata da wata illa sai ta rashin samun uwa ta gari, da wucewa zai yi amma sai ya fasa ya samu waje ya zauna
"Kin duba ta?"
Daga kanta tayi
"Me kike ganin za"a yi? Ko zaki kira chan gidan ne?" Ya fada kamar be damu ba.
"Wai Hajiya Mama?" Ta fada cikin Muryar kuka
"Su."
"Na fada musu a waya, suna waje an hana su shigowa ne."
"Oh okh."
Tashi yayi hannun sa zube a cikin aljihu, kamshin turaren sa daya bar mata ta cigaba da shaka tana kallon saman tana ayyana irin sa'ar da Maryam tayi da irin rashin sa'ar da tayi ita kuma. Yana fita hajiya Mama tayi saurin saukowa daga mota, kuka take sosai Alhaji Faruku na gefen ta ya harɗe hannu, nauyi da kunyar yaron yake ji dan yasan ba karamin dauriya yake ba, ba dan da alaka ba ma babu yadda za'ai yi haka, toh ya san alakar Maryam suke ci, bude musu akayi suka shiga shi kuma suka tsaya waje tare da Alhaji Faruku da yace ba zai shigo ba, shi kanshi Arkel ɗin kunyar Alhaji Faruku ke hana shi aikata wasu abubuwan tun da duk tsiya dai shine ya shige masa gaba a lokacin auren sa.
Da k'yar suka fito da ita aka saka ta a mota bayan an daure mata hannu da kafa da k'yar, suna kuka suka tafi da ita, ajiyar zuciya Arkel ya sauke yana juyawa sukayi ido biyu da Arab, be san yana wajen ba sai daya ganshi, yanayin fuskar sa kadai zaka kalla kasan akwai wani abu daya ke ji, shi din ma hakan ce, danne wa kawai yake yana nuna babu komai, ciki suka koma daga nan kuma suka sake fita dan zuwa wajen Barr. Nasir. Sai da suka gama dashi sannan ya samu ya bi kiran Hafiz, bayan sun gama magana ne ya kashe sannan suka koma gidan ya Nabila.
Washegari Hafiz ya tattaro ya dawo amma sam inna tace ita da Kano sai ko gawarta, yana zuwa suka hadu da salim ya nuna masa aikin da zai yi a Arkel Poultry farm, cike da farin ciki ya fara aikin cikin kwanciyar hankali.
***
Gaba daya sun hallara a babban falon gidan, Ummi ta warware sosai, har tana takawa abinta, babban taro aka shirya saboda kowa ya fadi ainihin abinda ya faru, Maryam da Ya Nabila ankon lace sukayi dan ubansu, shi kuwa Arkel da Arab Getzner suka sa me masifar kyau, suna zaune ana hira kafin fitowar Ummi da Alhaji,, lokaci zuwa lokaci Arab duba sakon Lubna yana murmushi, haka Ummi ta fito cikin shiga ta alfarma kayan su kala da ya da Alhaji, Babban me hoton da aka ɗauko Ahid Sufi ne ya fara aikinsa cikin kwarewa da iyawa, sai da aka fara bude taro da addu'a sannan aka fara komai cikin ilimi da wayewa.
Yadda CIkin ta ke hautsinawa ne ya hanata sukuni, wani irin tashin zuciya irin me tukukin nan ne ke taso mata, Arkel dake gefe yana lura da ita, ganin ta tashi da sauri ta bar wajen yasa ya bita da sauri. Da ido suka bishi dukkan su, Ya Nabila da dama tun tuni take hasashen wani abu game da yadda taga sauye-sauye a tattare da Maryam ɗin yasa ta sake sakawa ranta abinda take tunani.
***
THE BEGINNING OF SOMETHING NEW, SAUYIN ƘADDARA DAI SHINE TITLE DIN LITTAFIN, SO DONT EXPECT A HAPPY ENDING😂🧚
***
Pressure din mutane yasa nayi rushing din page din Nan walalhi, please allow me nayi shi a nutse saboda ido na kar nazo na yanke labarin kuma azo ana abu ba dadi.
In Kuma kun fiso nayi rushing din toh ba damuwa na iya rushing Yasin 😂😂😂😂😅🤣
*41-42*
©*Hafsat Rano*
*_ZAFAFA BIYAR na kudi ne idan kana son kowanne daga ciki ka nemi Wannan numbers din_*
*08030811300*
*07067124863*
***
Da gudu ta shige toilet, cikin tane ya baci shiyasa ta tashi da sauri, kafin ya k'arasa ta rufe, buga kofar yayi, a tunanin sa ko wanne abu ne, kamar zata yi ihu take matse jikin ta bata so yayi kara, gashi a matse take gashi ya tsaya a kofar yana tambayar ko lafiya? Da sauri tace
"Dan ALLAH ka tafi, ciki na ne ya ɓaci wallahi."
Wata irin dariya ce tazo masa sai ya sake rike kofar yana kyakyatawa, ashe gayu ma ana fafatawa, ganin yaki tafiya gashi iya kar yadda zata iya matsewa ta matse saboda bata so yaji karar, magiya ta cigaba da yi masa, gaba daya ta rude zufa kawai take fitarwa ta ko ina, sai daya gama tsonarta sannan ya juya ya tafi, sai data tabbatar ya tafi sannan ta saki jikin ta, ta zuba harkar ta a nutse, kunya take ji sosai bayan ta gama kawai ta watsa ruwa ta fito, riga kawai ta zura ta fesa turare ta sauko, duk suka zuba mata ido, ji tayi kamar zata harɗe, ido ɗaya Arkel ya kanne mata da suka hada ido tayi saurin dauke kanta, sannu duk suka hau jera mata, kanta a kasa take amshewa kunya kamar ta nutse dan bata san sannu me ake mata ba, Ummi dake ta faman fara'a tace ta dawo kusa da ita ta zauna, a kunyace ta koma ta zauna har lokacin taki yarda su hada ido dashi, dan ta lura ma har wani farin ciki ya kara akan dazu, shiyasa sam taki bari ma suyi magana balle ya fallasa ta.
Dukkan su sun bawa Ummi hankalin su waje daya, Alhaji daya dan tashi amsa waya ne kawai baya wajen, a hankali ta soma da asalin labarin.
"Abu daya na sani a rayuwata shine na taso a gidan mu muna da matukar yawa, gida ne babba irin gidajen hayar nan masu dakuna a ƙalla 20, Ni kadai ce a wajen Baba yelwa, da ita ba taso na buda ido duk da tace min ba ita ce ainihin mahaifiyata ba, a haka nayi rayuwa ta me cike da kalubale da gwagwarmaya, duk wanda yasan gidan haya irin wannan yasan ba zai rasa kalubale da tashin hankali ba, hakan kuwa akayi wata rana Baba Yelwa sukayi wata rigima da wata mata dake kusa da dakin mu, rigimar har ta kaisu da police station, aka bawa Baba Yelwa rashin gaskiya dan dama itace me fitina kaf gidan, dalilin haka yasa aka tattara mu aka kore mu daga gidan, ni dai ba zan ce Baba bata yi min komai na rayuwa ba, sai dai dani da almajira banbancin mu kadan ne, kullum ina cikin mummunar shiga, abinci kuwa sai taci ta koshi take bani, haka dai muka harhada muka koma Kaduna da zama, daga Niger Minna, komawar mu Kaduna ne muka hadu da mutane kala-kala, wanda suka fi Baba Yelwa wayewa da komai, a lokacin ne kuma suka zuga Baba Yelwa akan ta kaini aikatau kawai ta huta da wahala dani,a take ta amince ta bukatar su, a daren naga ta koma gefe tayi waya, ta dade tana wayar kafin ta ajiye tana me matukar farin ciki dana kasa gane dalilin sa, washegari muna tashi da sassafe muka shiryo mukayi Kano, gidan da ake kai yan aiki aka kaini, ina kallo Baba Yelwa ta tafi ta barni, nayi kuka sosai haka na hakura, sati na daya wata mata babba tazo ta dauke ni.
”Tun daga lokacin rayuwa ta ta saka sauya wa, aiki ne babu dare babu rana, haka na jure wa duk wata wahala, ana nan kuma sai Allah ya taimake ni maigidan ya saka ni a islamiyya asabar da lahadi, tun daga lokacin rayuwa ta samu haske, na san addini, wanda da duk bansan komai akai ba. Sosai na sake a gidan, ayyukan da nake sun riga sun zama jiki na, bana jin komai, gashi na fara jin dadin karatun nawa shiyasa na sake jajircewa dan bana son abinda zai jawo min na rasa karatun.
"Akwai wata rana na shigo daga islamiyya kenan sai ga Hajiyar da ta badani aiki, gaba na ne ya yanke ya fadi ganin ta danayi nasan ba alkhairi bane, bayan na gaishe ta naje na cire kayan jiki na sai kawai na zauna a dakin na kasa fitowa ina jiran tsammani. Ina nan zaune Hajiya ta leko, gaba na ne ya yanke ya fadi, sai data gama kallon dakin sannan tace
"Shirya Indo, tafiya zakuyi marikiyarki ce ba lafiya, kiyi sauri kar kuyi dare."
"Jiki na na rawa na tashi, ba hada yan kayana na fito, muka kama hanya, sai dare muka isa dan mun tsaya a gidan matar, halin dana ga Baba Yelwa ne ya firgita ni sosai, ciwon kafa take kafar ta rube gaba daya ga wani mugunyar wari da kafar ke fiddawa, haka na cigaba da jinyar ta dan kudin da muke dashi har yazo ya kare, daga nan ne kuma na shiga gararin rayuwa, na rasa yadda zan yi da ita gashi ko abincin da zamu ci da kyar muke samu.
"Ranar da ciwo ya ishe ta ne ta saka na kira mata wannan matar, a handfree na saka mata wayar sai da tayi ta ringing sannan ta d'aga. Gaishe ta Mama Yelwa tayi cikin tsananin ciwo, dakile take amsa gaisuwar kamar zata kashe kiran,
"Lafiya Yalwa? Akwai matsala ne?"
"Akwai Hajiya, jiki na yaki dadi, komai na iya faruwa dani, shiyasa na kira ki kizo ki dauke ta, bana so Allah ya kamani da laifi."
"Toh... Kin kusa tafiya kenan? Toh a gaskiya Ni dai ba zan iya zuwa daukar ta ba, kina gani da kyar na samu na koma daki na, ki san yadda zakiyi dai da ita ta riga ta bar hannu na yanzu ba zan iya wani abu akai ba."
"Dan Allah ki taymaka Hajiya, yarinyar nan abar a tausaya mata ce, ni dai nayi nadamar abinda na aikata wallahi Allah, ki taymaka kizo ki dauke ta ki mayar da ita wajen iyayen ta."
"Zancen kike so, na gama magana ta sai anjima."
"Shikenan, tun da haka kika zaba, zan kawo ta har in da kike, sauran bayanin sai ki nemi yadda zakiyi ai."
Tana kaiwa nan tayi min alamar na kashe, kashe kiran nayi na kura mata ido ina neman karin bayani. Bata ce komai ba ta nuna min wata babbar akwati
"Miko ta kinji?"
Tashi nayi na dauko ta, kallon akwatin tayi nima n kalla,.
"Wannan ita ce komai naki, ita ta ƙunshi duk wani abu daya shafe ki, na cutar dake sosai,na taymaka wajen kashe miki rayuwa, amma zan Allah ki yafe min."
A yadda take maganar da kyar ne yasa nace tayi shiru kawai, fita waje nayi na samu wani waje na zauna nayi kuka na, kukan rashin
27, January 2025
Rukayya
Good