Showing 60001 words to 63000 words out of 98004 words

Chapter 21 - SAUYIN KADDARA COMPLETE HAUSA NOVEL

06 Jan 2025

11615

zama sai kun tashi, my wife gone missing ai banga ta bacci ba."

"Haushi kaji? Please kayi hakuri wlhi makara mukayi kasan bamuyi bacci ba sai wajen asubah ya sace mu dukka, ka gan mu ko breakfast mun kasa yi wallahi, ina ta kiran ka Kuma not reachable."

"Ba damuwa, zan kira ka anjima, kace mata ta kwantar da hankalin ta, yanzu ina sauri ne akwai in da zani."

"Arkel!?"

"Just pray for me, sannan dan Allah kar kowa yaji maganar, she's fine and healthy tana gidan aunt din ta ma, zanje chan ne, sannan maganar Barr. Nasir Kayi mishi magana Please."

"Ahh Alhamdulillah, shi yasa naji kanin nawa strong, jiya kuwa baki ya mutu murus."

Dariya yayi

"Sai anjima."

Be wani bata lokaci ba ya isa kofar gidan, yana zuwa ya kira Number Mijin Anty Maryam, yana ciki sai gashi ya fito, da sauri ya rissina ya gaishe shi, hannun sa ya kamo ya riko cikin nasa suka shiga gidan, duk da safiya ce amma komai an gama gyara shi neat har turaren wuta an saka sai kanshi gidan yake, a gefen kujerar ya dan saka jikin sa hankalin sa gaba daya ya koma kan kofar dake cikin falon wanda ta nuna alamun nan ne ainihin cikin gidan, kayan breakfast aka hau jere masa sai dai shi sam hankalin sa baya kansu, so yake ya ga ta in da meron sa zata bullo, ganin ta ne kawai zai tabbatar masa da tana gidan da kuma kwanciyar hankalin sa, da hira ya ja shi ya dai daure yana amsawa duk da tarin abubuwan da suke kansa a yau gashi babu ishashen lokaci hakan ya hakura da yana sake duba hanya, be ko kalli abincin ba, ganin haka yasa ya kira Anty Maryam, tana fitowa yace

"Kuzo tare da Maryamu."

Boyayyiyar ajiyar zuciya ya sauke ya kuwa kafe hanya da ido, Anty Maryam ce a gaba tana bin ta a baya fuskar nan ta kode saboda kukan data sha jiya tayi fayau da ita babu komai a kan fuskar ko arzikin powder balle lipgloss, babu yadda Anty Maryam batayi da ita ba akan ta dan shafa ko kadan ne kemaimai taki haka ta fito duk idanun kuwa sun kumbura. Akan shi ta fara dora idon ta, shi din ma hakan take, tsadadden murmushi ya sakar mata me narkar da zuciya, da sauri tayi kasa da kanta dan yadda taji sakon nasa har tsakar kanta, ya gane sarai yadda hakan yayi tasiri a tattare da ita sai kawai ya basar ya cigaba da jujjuya hannun sa har suka zauna.

Alhaji Muhammad Rabi'u ne (Mijin Anty Maryam) ya fara bayanin abinda ya faru daren jiya, zuwa lokacin da Maryam ta sanar musu abin da ya faru, daga karshe ya dora

"Gata nan sai ta sake sanar damu dukka abin da ya faru bayan barin ku."

Tsuru tayi kunya duk ta kamata, tana lura da dukkan motsin sa yana kanta, ga wani irin kallo me wuyar fassarawa da yake aike mata dashi, sai da Alhaji Rabi'u ya sake magana sannan ta shiga bayani bayan guduwar Hafiz da ita.

Har ta gama idon sa na kanta ko kiftawa bayayi, wani abu me kama da mayan karfe yaji yana fusgar sa zuwa gare ta. Anty Maryam ce ta yi magana sannan ta bada shawarar lallai a tsaurara bincike sannan Maryam ta zauna anan har zuwa lokacin da komai zai daidai ta, in yaso ita kuma sai ta je ta sanar wa gida abinda yake faruwa. Duk abinda akace be musu ba saboda hakan ma duk wani tsari ne nasa, hakan kuma shine zai kara wa komai sauki.

Tashi Alhaji Rabi'u da Anty Maryam sukayi suka basu guri, shi gaba daya ma Alhajin ficewa yayi daga gidan dan dama ya riga ya shirya daga nan zai wuce kasuwa ya samu Baban su Maryam ɗin ya sanar dashi komai.

Thanks da uzurin ku, jiki alhamdulillah naji sauki Nagode kwarai.


_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A HALIN YANZU😁._

*ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma
*SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano)
*KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo)
*BURI ƊAYA!* (Mamu gee)
*WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull)

👇🏻karku bari ayi babuku

*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi  daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*

*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*

Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank

Saika tura shaidar biya ga wannan number ta WhatsApp

08030811300

Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN  ta wannan number din

07067124863

Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.

*Karki bari ayi babu ke, Abari ya huce shike kawo rabon

Rano🚴🚴🚴




***
[3/18, 22:26] Hafsat Rano: *SAUYIN KADDARA*

*34*
©*Hafsat Rano*

*_ZAFAFA BIYAR na kudi ne idan kana son kowanne daga ciki ka nemi Wannan numbers din_*

*08030811300*
*07067124863*

*_Daurin boye_*
_safiyya huguma_
*_Buri daya_*
_mamuhgee_
*_Wutsiyar rakumi_*
_billyn Abdul_
*_Kai min halacci_*
_Miss xoxo_
*_Sauyin kaddara_*
_Hafsat rano_

***
Suna fita yayi saurin dawowa kasa in da take zaune, sosai ya matsa daf da ita, ƙafarsa na gogar ta ta. Murmushi tayi ya sa hannu ya riko fuskar ta

"Sannu." Yace yana murmushi

"Uhum." Ta amsa ta a sake kasa da kanta

"Babu wani abu da yayi miki? Babu in da ke miki ciwo?"

"Umm babu."

"Are you sure? No bari na duba na gani."

Hannu yasa zai daga dan mayafin da ta yafa a saman kanta tayi saurin rike masa hannu tana marairaice murya

"Allah ba komai fa."

"Toh bari na duba da kaina mana, me kike tsoro.?"

"Ni ba komai, kawai dai."

Dungure mata kai yayi yasa dariya

"Bafa abinda kike tunani bane, so nake naji wani flavour be da turaren da kika sa."

Ido waje ta kalle shi, wai flavour, har wani flavour ne da turare kenan?

"Baki sani ba kenan? Yar kauye."
Dariya suka saka a tare

"Me kika sani game da matsalar ummi?" Daga sama taji tambayar, gaba daya sai ta duburburce dan bata zata ba, ganin yadda tayi ne ya sake fahimtar lallai ta san wani abu akai, be zai matsa mata ba amma zai nemi taimakon ta nan gaba, tunanin yadda zata sanar masa take a zuciyar ta, tsoron abinda zai je yazo takeyi ga shi bata san yadda al'amarin zai juye mata ba, wasa take yi da hannun ta tana kisisima yadda zatayi sai kawai taji yace

"Ki adana duk abin da kika sani zuwa wani lokaci kadan, i ll need ur help kinji?"

Kallon sa tayi ya daga mata kai

"In Sha Allah." Tace a hankali

"Thanks dear."

"Bari na tafi, zan dawo da daddare, ayi min tuwo kinji?"

"In kuma ba tuwo za'a yi ba?"

"Dama ai ba ina nufin ayi dukka ba, ke zaki yi min nasan dai Anty Maryam ba zata hana ba, zan shiga busy ne ba lallai na samu naci ba, and kinsan ni da abinci dai musamman tuwo."

"Allah ni ba wani son shi nake ba."

"Whatever, ni dai ina so."

"Owk tam."

"Good girl, yi wa Anty magana zan wuce."

Tashi tayi ta shiga ciki ta sanar wa Anty Maryam zai tafi, fitowa tayi sukayi sallama sannan ta koma ciki, kudi ya dauko ya mika mata ya juya hannayen sa zube a cikin aljihun sa, har ya kai kofa ya juyo ganin ta a zaune bata taso ba, bata fuska yayi tayi saurin tashi dan ta san nufin sa, a harabar gidan suka tsaya jim sannan ya mika mata hannu alamun ta bashi nata, a kunyace ta mika masa ya rike cikin nasa yana dan murzawa a hankali a hankali.

"Ki kula da kanki, just three days zakiyi anan, i ll come and take you home."

"Owk Tam."

Murmushi yayi mata ya saki hannun ta ya juya ya fice gaba daya, sai da taji gaba daya komai ya tsaya mata, wani irin abu me kama da iska na kada ta, gaba daya sai taji dama kar ya tafi suyi ta zama a haka, he's so cool and nice, dama an ce ba zaka taba sanin ainihin halin mutum ba sai kun zauna, ita da ganin mutum me tsauri take masa, sai yanzu ta gane baya son wasa da aikin sa kuma da gaskiyar sa shi kadai yasan wahalar da ya sha kafin ya tara, ajiyar zuciya ta sauke ta koma ciki jiki a sanyaye duk sai taji ta nemi walwalar ta rasa, sai da Anty Maryam tayi ta jan ta da hira sannan ta saki jikin ta. Da yamma likis sai ga umma ta zo gidan bayan sunyi waya an sanar mata da abinda ke faruwa.

***
Ya kasa zama sai zagaye yake yana tunanin mafita, ya san tun da hakan ta faru Asi ba kyale shi zasuyi ba, damuwar sa daya su Inna gashi duk sun tsorata sosai, tunanin yadda zai yi dasu yake idan yaso shi sai ya nemi Arkel ya sanar dashi komai idan ma abu ya baci dai zai taimaka. Shawarar ya yanke kawai ya shiga gidan, Inna na jin sa ta taso da sauri dama zaman jiran sa take shiyasa yaki shigowa gidan ya tsaya a waje,

"Hafizu, me yake faruwa? Me ka aikata musu kuma menene hadin ka dasu?"

"Inna?"

"Ka fada min kawai, wanne irin bala'i ka jajibo mana? Na shiga uku ni."

"Ba wani abu bane babba, ku shirya kuje Gumel zan zo."

"Ai ko baka ce mu tafi ba dole tafiya zamuyi, sai dai kafata ƙafarka ba zan barka su kashe min kai ba, wacce yarinyar suke nema ka hana su? Wannan wacce irin rayuwa ce haka?"

Dafe kansa yayi kamar zai rabe biyu saboda zulumi, iyakar kokarin sa na son ya fahimtar da inna ya kasa, haka dai ya bita da to suka tattara kayan su suka nufi Gumel, har suka isa inna bata daina mita ba, shi dai nasa ido ya gama tsara yadda zai baro Gumel din da zarar sunje.

***
Tsoron sa ne ya dadu ganin sun shigo layin, duk sai yaji kamar ya koma bashi da idon da zai iya duban su, abubuwan da suka faru ne suka shiga dawo masa daya bayan daya, haka dai ya daure ya hau addu'a har ya samu ya ɗan ji daidai, nuna mata hanya ya cigaba da yi har suka karasa kofar gidan, kallon gidan yake ganin yadda ya sauya sosai, tun daga kan gini da tsarin gidan  da komai ya zama sabo, ajiyar zuciya ya sauke ya kalle ta, itama shi take kallo.

"Thanks alot, can I have ur number pls? Saboda watarana."

"Yeah of course."

Da farin ciki ta karanto masa ya saka yana murmushi, bude kofar yayi ya fito tayi saurin fitowa ta tayashi kwashe kayan, hannu ta sa ta rike kofar tana kallon shi,

"Suna da?"

Dafa kansa yayi alamun mantuwa yace

"Kinga na manta ma, I'm Muhammad , U?

"Barr. Lubna Abbas."

"Ok Masha Allah, nagode sosai sosai, Allah kawo ranar da zan saka miki, sai anjima."

Juyawa yayi ya fara takawa har gaban sa na dukan uku uku, sai da ya tura gate din ya shige sannan tayi ajiyar zuciya ta shiga , ita dai Hidaya ta kasa magana saboda tsabar mamaki dan bata taɓa ganin kawar ta a irin wannan yanayin ba.

****
Buzu na zaune yaga ya shigo, da sauri ya mike yana kokarin karbar kayan hannun sa a tunanin sa Arkel ne, kallon harabar gidan yake baki bude ganin irin girman da aka kara wa gidan ba kamar yadda ya tafi ya barshi ba, shekara biyar ba kwana biyar bace komai ya sauya, da sallama ya bude falon ya shiga, babu kowa a ciki sai karar na'urar sanyaya daki dake dan kara kadan, a cikin sakan da be wuce biyar ba ya gama kallon ko ina na cikin falon da duk wasu kofofi dake manne da falon, idon sa ne ya tsaya a kan dakin da ba zai taba mantawa dashi ba, duk da gyare gyaren da akayi wa gidan dakin na nan a yadda yake, Sadiya ce ta fito daga kitchen, tana ganin shi ta rissina har kasa ta gaishe shi, amsawa yayi ba tare da ya maida hankali a kanta ba, ganin zata wuce ne yasa ya dakatar da ita.

"Ina Ummi?"

Dakin da take ta nuna masa, da sauri ya nufi dakin sai mamaki ya kamata, ya zai yi yace ina Ummi bayan yasan babu in da take zuwa balle har ta iya fita?ita kadai take ta tunanin hade da mamakin sa bayan shine mutum mafi muhimmanci da zai san komai. Duk a tunanin ta oga kwata-kwata ne tun da duk cikin su babu wanda yasan shi balle yayi tunanin ko shi ne yazo.

Cikin dakiya ya murd'a kofar, tana kwance kamar ko wanne lokaci idonta a rufe, sakin kofar yayi jin ƙafarsa na neman gagarar sa tsaiwa da abinda ya gani, tuni hawaye ya cika fuskar sa, har a lokacin wani sashi na zuciyar shi na kalubalantar zuwan da yayi sai dai Shashi mafi karfi ya fi bashi kwarin guiwa. Hakan ya daure ya karasa gaban gadon yana sauke guiwowin sa dukka a kasa, a daidai lokacin Ummi ta bude idon ta, a kansa ta sauke su tayi wata irin zabura tare da kwalla masifaffiyar karar data saka gaba daya gidan amsa kuwwa, Hajiya Mero na zaune a daki tana shirya wa fita wajen su Asi taji karar, wata irin faduwar gaba taji take wani abu me kama da ruwa ya biyo kafarta, cikin tsananin tsoro tayo waje, ƙarar na fitowa daga dakin Ummi hakan ya sake hautsinata ta nufi dakin da mugun gudu.

Kokarin tashi take Muryar ta na fita chan kasan makoshin ta, rike ta yake ganin da gaske yunkurin tashi take bayan babu yadda zatayi ta iya tashi bayan dogon zangon data dauka tana jinya a kwance, kuka suke dukka su biyun sai dai nasa yayi karfi sosai na Ummi kuwa kadan kadan yake fita, kusan shidewa Hajiya mero tayi ganin wanda ke durkushe a dakin.

"Muhammad!" Ta kwala masa kira tana ja da baya da baya, tashi yayi ransa na suya ya fuskance ta yana daure fuskar sa, babu alamun sassauci ko afuwa a tattare dashi hakan ya sakata kokarin juyawa, ji tayi ta bige da abu, da sauri ta d'ago, Arkel ne ya harɗe hannun sa a kirjin sa ya zuba mata ido yana kallon ta,

"Me ye HakA wai, me kuke nufi dani?"

Babu wanda yayi magana a cikin su, cigaba da takowa yayi yana saka idon sa cikin idon dan uwansa rabin jikin sa. Lallai ba karamin cutar dasu akayi ba, iya kar rudewa Hajiya mero ta rude dan bata taɓa kawo ranar ba, bata taɓa hasashen ta ba.



_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A HALIN YANZU😁._

*ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma
*SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano)
*KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo)
*BURI ƊAYA!* (Mamu gee)
*WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull)

👇🏻karku bari ayi babuku

*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi  daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*

*za'a tura kudin ta wannan accnt number din*

Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank

Saika tura shaidar biya ga wannan number ta WhatsApp

08030811300

Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN  ta wannan number din

07067124863

Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.

*Karki bari ayi babu ke, Abari ya huce shike kawo rabon

Rano🚴🚴🚴
*SAUYIN KADDARA*

*35-36*

©*Hafsat Rano*

*_ZAFAFA BIYAR na kudi ne idan kana son kowanne daga ciki ka nemi Wannan numbers din_*

*08030811300*
*07067124863*

*_Daurin boye_*
_safiyya huguma_
*_Buri daya_*
_mamuhgee_
*_Wutsiyar rakumi_*
_billyn Abdul_
*_Kai min halacci_*
_Miss xoxo_
*_Sauyin kaddara_*
_Hafsat rano_

***
"Kinyi mamakin gani na ko, kinyi tunanin ba zan dawo ba ko, kin tuna maganar da muka yi ta karshe?"

"Idan kin manta bari na tuna miki, na raba ka da kowa naka, dangi yan'uwa da duk wani jin dadi na rayuwa, kaje chan kayi rayuwa irin ta mutum mara inganci, rayuwar kunci da wahala.."

"Wacce amsa na baki a lokacin?"

Ya dora

"Na fada miki zan dawo,ko mai
daren dadewa zaki girbi abinda kika shuka, a yau gani a gabanki, bayan tsawon lokaci na dawo, ba zan taba barin ki ba, ko zanyi spending last kobo dina akanki, wannan Alk'awari na ne."

A yadda taga yana magana ta san tabbas karshen ta yazo, amma ya akayi haka? Bayan madugu ya bata tabbacin babu abinda zai iya karya shi, abinda yayi a tsakani babu wanda ya isa ya karya shi, Arkel na tsaye ya rungume hannun sa yana kallon ta, juye juye take tana neman in da zatayi, daidai lokacin Ummi tayi wani irin nishi, nishi me matukar firgitarwa, da gudu sukayi kanta hakan ya bawa Hajiya Mero damar guduwa, kofa tayi ta jita a rufe kam alamar an shirya kenan, da gudu tayi d'akin ta zata shiga, nan ma a rufe, wuri wuri ta tsaya yi yana neman hanyar guduwa, babu wata hanya sai kawai ta tsaya a falon ta ɗora hannu a ka.

Magana take tayi amma basa jin me take cewa saboda rashin murya, duk sun rikice musamman Arab da ya ke ganin kamar ganin shi ne ya haddasa hakan, har lokacin kallon juna suke babu wanda ya yi wa wani magana har suka samu numfashin ta ya daidai ta, ajiyar zuciya suka sauke a tare, hakan yasa suka kalli juna, Arkel ne ya yayi saurin basarwa ya dauke kai kamar be gani ba, gefe ya samu ya zauna yana kura mata ido. Arab kuwa sai ya tsaya a tsaye yana karewa ko ina kallo tare da share kwallar dake faman bin fuskar sa babu kakkautawa, ya rasa ta ina zai fara magana gashi ko fuska Arkel yaki bashi yana harɗe yana juya kai. Chan sai wayar sa tayi kara yayi saurin dauka.

"Ina gida, ku shigo kawai."

Abinda yace kenan ya datse kiran  yana lankwasa hannayen sa, jin ana knocking yaasa shi mik'ewa a nutse kamar babu abinda ke faruwa, yayi hanyar fita, da sauri Arab ya bi bayan shi, Hajiya mero na ganin sun nufota su biyu ta sake rikicewa, Arab da ko ganin ta baya san yi, da gudu yayi kanta, hannu yasa ya shako mata wuya, take idon ta ya firfito waje ta shiga kakari, hannu kawai take yarfewa cikin tsananin zafi, daidai lokacin Zainab ta fito, ihu tayi ganin abinda yake faruwa, da gudu tayi kansa, hannun sa take kokarin rikewa tana ihu, be ko ji ta ba, Arkel daya fasa bude kofar ya tsaya yana kallo ganin zai mata illa yasashi karasawa ya rike shi, da sauri Zainab ta riko ta tana kallon ta, gaba daya bata hayyacin ta, dakin ta ta ja ta tana kuka, sakin sa yayi ya juya ya bude kofar, police ne su uku suka shigo, biyu cikin kakhi daya babu dayar mace

27, January 2025
Rukayya

Good

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login